Showing 57001 words to 60000 words out of 347556 words

Chapter 20 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8764

alheri Allahuma amin Allah.
Kallon juna mukayi nida gwaggo data daina bani takaitattacen labarin daya daga min hankalina lokaci guda akan mahaifiyata da take fadi alokacin cewa da hannunsu a cikin barina haka a wullakance cikin wani hali na maraicin uwa agareni.
Gashi su din da zansan wani abu a game da ita suma ayanzu amsa daya suke ban kamar babana ina zasu ganta su roketa gafara abinda ya faru a baya.
Shigon wani matashi da buhun shimkafane ya sani daina tunanen nabishi da kallo yazo har tsakan gidan gwaggo din ya girke shi ya juya baicewa kowan mu kalaba.
Yana fita wani ya shigo da kwalin indomei guda ukku jere a hannunshi sai ga wannan na farkon daya kawo shimkafa ya shigo da jerin kwalin taliya guda uku jere a hannunshi shima.
Gwaggo ta mike tsaye tana fadin wanan abin haka daga ina ya fito wanine yazo dasu a mota yace wai a kawowa Fadimatu daya sauke dazun ta kallo inda nake .
Uncle kaine nace cikin wani murya mai rauni uncle wanan ya zama wahala Why uncle zakayi wanan hidiman haka bayan irin taimako na dakayi yau zuwa dani da kayi yasa nazo na taimaki gwaggona dana samu a wani halin rashin lafiya.
Yanzun kuma kazo muna da wanan dawainiyar haka hidimar yayi yawa sosai wallahi ina magana kamar zanyi kuka dagowa yayi da zumar magana ya kallo inda nake tsaye din cikin wani yanayi na damuwa.
Sai naga kawai ya kura min ido na dan lokaci kafin can ya dan furta yanzu ina ita gwaggon taki nace tana ciki na sayo mata aji garau na bata ruwa masu zafi taji sauki harta fito waje yanzu.
Wani shuumin murmushi yayi iya labanshi yace shike nan wanan treatment din da kikai mata kina ganin ta samu lafiya ke nan ke kije ki shiryata ku fito na saukeku asibiti.
Zanyi magana ya dago hannu har lokacin yana cikin mota a zaune binshi nayi da kallo naga ina mamaki ganin ba fuskan gardama dashi yasa na juya zuwa ciki na samu gwaggo ta saka kayan a gaba tana kallo a cikin mamaki saidai tana dunkule a cikin hijjab wai sanyi takeji kuma dan fitowan da tayi din waje don zafi.
Gwaggo wai ki shirya ya saukeki asibiti na fada a sanyaye ke yar nan wani asibiti kuma aini naji sauki bayan wanan dawainiyar dayayi yanzu wani asibiti zai kaini kuma ?
Haka yace dai shi din kanin mamace ta kaduna wanan matar da muke mutunci da ita shiya kawoni dazun dana dawo mama din tasa ya rage min hanya shine yaga gidan nan ya dawo yanzu.
Ba zan iya masa gardama bane gwaggo don yana kanin mama din ko yaranta manyane amma naga suna bashi girma sosai suma.
Ikon Allah yanzu dai na tashi ke nan muje asibitin kike nufi nima kada nayi mai gardama ko na dukar da kai ina nufin eh ta shiga daki ta shirya ta fito ta samu na shigo da kayan ta cikin barandan dakinta sai shinkafan ne kawai na barshi a inda yake don ban inmasa ni kadai.
A mota muka sameshi ya rufe ko ina na motan gwaggo ta rufe gida ta miko min dan makulin gidan na karba na bude jakkar hannuna na saka a gefe daya.
Kwankwasa jikin din motan nayi hakan yasa ya bude da sauri ganin tare da gwaggo muke yasa ya fito yana fadin sannu mama ya jikin naki yanzu take fadin ta samu baki da lafiya ai.
Nace gara aje asibiti zaifi don kada ciwon ya dawo daga baya dan nan dawainiyarce tayi yawa ai daka barni ai ta siyo min magani chemist nasha na samu lafiya sosai dan sanyi kawai nake ji yanzu dai.
Like the mother like daughter inba shirme ba wanan maganin ne zai maku amfani a jiki banda shirmensu ya fada a zuciyarshi amma a fili cewa yayi.
Alaman da sauran zazzabin ke nan har yanzu a jikin ki dama lafawa yayi kawai baije ko ina ba zakace shi din balarabene yadda yake magana a cikin wata hausa na daban yadda nake jin lafazinsa.
Mota ya bude mata baya ta shiga ya dan kalleni kamar harara nayi saurin bude gaban motan na fada ciki da sauri ya shigo yana fadin sannu mama gwaggo ta amsa daga bayan motan.
Muka isa asibitin na dauka ajemu zaiyi ya kama gaban shi sai gashi naga ya fito shi yayi komai akai allura aka bata magani ya biya ya dawo damu gida.
Adduan kan yashashi a wurin gwaggo shida mahaifansa ranan ya saukemu ya kawo kudi ya bata yai muna sallama ya tafi.
Ajiyan zuciya na sauke muka nufi ciki da gwoggo dake tafiya da kyat a lokacin tsaye muka samu mijinta a waje wanda yayi saurin dawowa gida a ranan saboda yanayin daya barta a ciki na rashin lafiya da zaifita.
Nasa hannu na dauko makulin gidan a jakkata da sauri naje nake gaidashi nasa key na bude gidan yar gwaggo ashe kin dawo daga kadunan ?
Gashi kuma kin samu gwaggon naki ba lafiya nace wallahi baba Allah ya turoni na dawo da wuri da sai yamma ai zan dawo sai na samu lift aka saukeni.
Haka abin Allah yake dama ya juya yanawa gwaggo ya jikin muna shiga gidan yake fadin ina kuma kuka tafi haka naga wani ya saukeku yanzu din.
Asibiti muka fito malam wanan dan albarkan ne ta fadama banda lafiya shine ya kaini asibiti suka dubani sun min allura sun ban magani muka dawo.
Ikon Allah wasu nada kokari kan abinda suke so ya gada kafin idonshi yai arba da buhun shinkafa da muka bari yashe a tsakar gidan.
Wanan kuma fa ya fada a cikin mamaki yana kallon buhun shinkafan dake yashe a tsakar gida cikin dauriya gwaggo tace na yar nan ne don Allah malam barni hakana don idonane ke rufe min kwanciya nake sonyi a yanzu kawai.

KADUNA
Hjy hajjara tana zaune a falo waya takeyi a cikin harshen larabci ko wanda baiji yaji yadda take maganan yasan fada takeyi da maishi a lokacin.
Don yadda take dan daga murya Al,amim ya shigo ya zauna a kusa dasu yana kallon uwar kafin ta aje waya tana jan tsuki tare da fadin wanan matar ni take son ta rainawa wayau don kawai bani kasan take ganin zatayi min abinda taga dama ko me ?
Mami wai har yanzu uncle bai dawo bane dan ya tambaye ta juyo gareshi tana fadim idan ya dawo boyeshi zan yi Al,amin nima shi nake jira inga isowanshi don ya kamata ace by now ya iso tun dazun ai.
Tunda munyi waya da fulani tace min ya gama da mai martaba tun dazun har ya saka mai hannu kaga incan daura zasu rainawa mutane ga fannin uwa sun karbemu da hannu bibiyu.
Nima mami nayi mamaki da har yanzu bai karaso ba beside nasan dai uncle bawai abokai bane dashi haka barkatai ?
Koma meye Allah dai ya dawo dashi lafiya akwai dai inda ya tsaya ta juya ta dauki wayanta data aje a gefe ta kira layinshi din yana gani yaki dagawa.
Karfe shidda da rabi ya shigo get din gidan Aliyune zaune da matarshi ya hango a garden suna hira yayi parking ya fito yana kwaso takardun daya kaishi zaria din cikawa bai kara kallon inda suke zaune din ba.
Sallama yayi ya shigo suka juyo suna kallonshi tare da mai sannu da zuwa a gajiye ya karaso ya zauna yana amsawa .
Al,amin din ya mike ya karbi dan jakkar dake hannunshi din ya haura sama dashi hjy ta kwallawa mai mata aiki kira sai gata ta fito tana amsawa .
Ki kawo masa ruwa da abinci nasan baici komai ba tunda ya fita gidan nan indai Mohammed ne no ta barshi wanka nake son inyi sai nafito don lokacin sallah ya kawo jiki.
Karfe tara kowa na zaune yana cin abinci hjy hajjara ta kalli kanin nata tace a cikin gida ka samu kawu din ko a fadarsa shiru yayi yana kai cibin daya dibi tuwo a bakinsa ya hade ya aje cibin ya dauko ruwa a kofi ya korawa cikinsa ya aje cup din ya dago tare da kallonta yana fadin.
A part dinsa na karban baki na sameshi don ina ganin ya tashi fadane a lokacin ina shiga ya karba baya mum gaisa ya saka min hannu.
Kafin yai min nasiha kan kula da zumuci mu dinga zuwa duban yan uwa ba sai bukata ya taso ba muzo yayi min fada sosai akan kula da zumuci dana baya damu.
Ai kawu saidai idan bakaje wurinsa ba wanan nasihan sai yayima shi komai kankantaka gareshi kuwa haka yacw nayi mamaki yadda ya saka min hannu ko tsayawa baiyi ya duba ba.
Kawune fa shi yasan muhinmamcin zumuci sosai yasan komai ai tunda nayiwa Fulani bayanin komai game da takardan nasan kuma zata fada mai.
Amma a can gida sunki sakama hannu sai yawo sukewa mutane da hankalin don bakinciki kada wani yazo ya fisu daga baya shine kawai abinda sukewa.
Uncle amma baka dawo da wuri ba na dauka zaka iso in time har na shirya ina jiran isowanka mu fita sai gashi baka dawo ba ?
Nima ai na dauka zai iso da wuri tunda munyi waya fulani tace min har ka gama ka wuce da wuri kabar gidan ai hjy ta fada.
Eh Ukuthi na tsaya nakai wata mata asibitine taga likita sai na kamo hanya gaba dayansu suka kalloshi lokaci guda don jin abinda ya fada din alokacin kowa na mamakin wata matace wanan kuma da har uncle di da kansa ya tsaya yakai asibitin.
Hjyce ta iya furta mata wace mata ke nan kuma tana kallonshi abinci ya debo yana fadin gwaggon wana yarinyar da kika hadani da ita in sauketa.
Dariya Aliyu din ya kume a bakinsa har yana tara hannu ya dan juyo ya kalleshi tare da aje spoon din dake hannunsa din yace.
To be Frank yau na wahala ukuthi akan yarinyar nan duk kuma saboda ke wani kazamin unguwa nasu na sauketa babu komai sai kwata a unguwar.
Bayan na fito daga wurin mai martaba kuma na tuna da alkawarin da nayi maki na idan munkai zan saya mata provision a can kada mu makara.
Wallahi haka na koma nayo mata shopping nakoma wanan kazamin wurin nasu dakyat nagane gidan ana saukewa sai gata ta fito wai min godiya.
Irin godiyan nan dogo na hausawa anan take fadin wai tayi arziki dana kawota gashi tazo ta samu gwaggonta cikin wani hali wai ta gode tayi treating dinta ta sawo mata magani a chemist ko aji gau ta bata ta mike.
Naso in wuce sai na tuna da zancen mai martaba daya gama min nasiha mu taimakawa mabukaci dariyane sosai Aliyu ya kwashe dashi lokacin filon kusa dashi ya dauka ya jefa masa cikin haushi.
Aliyu yace so Uncle watau kaso ka gwada zancen mai martaba ke nan ka fara taimako Aliyu you know me well kada ka kara bata min rai yanzu don Allah.
Dariya gaba dayan su suka dauka lokaci guda a falon dole shima ya dan dara a gefen fuskanshi hjy tace aika kyauta kasan ko taimakon akanka kayisa.
Bangane ba yace tace kwarai kaga na farko wayasan abinda Allah zaiyi gobe akan hakan duk suka kara kwashewa da dariya yace ban fahince ki ba Ukuthi ?
Eh to kasani ko taimakon naka sanadin hakan yazama alheri a gareku ko yarinyar nan rabon kace ita innalillahi ya fada ya runtse idonnunsa lokaci guda tace wallahi kana wasa da ikon Allah ne kome ?
Don Allah Ukuthi ki daina wanan maganan yabar fitowa a bakinki please tace ita din ba mace bace mace ce har mace wallahi kawai dai gyara take bukata saboda porvati dake damun su amma yar nan wallahi mace da takai mace kaga ta,,,,,,,
Karan wayantane ya dakatar da ita ga fadin abinda tayi niya ta dauka ta duba nice na kirata a lokacin ta daga tare da sallama a bakinta.
Mama ina wuni ya gida da sauran yan uwa tace duk muna lafiya dama na kira in fada maki irin alherin da uncle yayi muna yau.
Nan dai na zayano mata komai tana fadin masha Allah ai yana da kirki sosai kawai dai barshi da miskilancin nan nasa kawai amma shi mutum ne gaskiya.
Mama ai muna godiya don Allah gwaggona tace a gode masa tace ba komai mamana adai kula da karatu don Allah nace insha Allahu mama.
Amma zan turo maki da layinsa don ki kirasa ki masa godiya da kanki zaifi a,a mama basai na kirasa ba don Allah ina tsoronsa sosai adai muna godiya agunsa.
Bakomai ai ki kirasa kiyi mai godiya hakan ba wani abu bane kinji ki kula da rayuwanki sosai kinji mamana ta kashe wayan.
Tsuki yaja yana gyara zama tare da fadin ban ma son in tuna wanan unguwar wallahi Ukuthi please kada a kara hadani da wani har nabar kasan nan kan taimako.
Kai Mohammad baka sani bane idan?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? kaji tarihin yarinyar nan ita din abin tausayine kasani nima ban yarda da mutane irin haka bakuyi mamakin ganin yadda na yarda da ita bane wai ?
Nan ta fara basu labarin da mai aikinta harira tabata akaina sukai shiru suna saurare ta kare tana fadin ka fada min idan wanan yar ba abin a taimakawa bane don Allah ?
ZARIA
Bayan na ba gwaggo magani zan fitane tace dani dauki kayan nan daga nan waje kikai dakinku ki ajesu banson malam ya dameni da tambaya a kansu.
Hakan yasa na kwashe komai zuwa dakin da muke ciki saida na zubawa baba abincine na koma daki lokacin na bude ledojin naga irin hidiman da ya hado min na ban mamaki.
Hakana na tasa kayan a gaba ina kallon kayan tare da tunane kafin na mayar a cikin leda din dana cirosu na aje a gefe daya don nasan Samira zata dawo a ranan .
Mikewa nayi na gyara dakin na share ko ina na gyaro na gama na fito na gyara gidan tas lokacin magariba ya gabato sosai na shige dakina.
Nurane ya dawo gida yana shigowa hasken dakin mu daya gani yasashi fadin big girl kin dawo ke nan ?
Nura yane ka dawo ke nan na fada ina dagowa daga kwancen da nake nafito na sameshi tsaye a kofan dakin nace Nura ya kasuwa yace kai kasuwa Alhamdullahi.
Ashe yau zaki dawo nace eh yana leka dakin yace Samira fa ta dawo ke nan ko nace ba tare muka dawo ba don tunda safe na taso amma tace da yamman nan zata shigo.
Kai anya gashi har dare yayi naga baku yarda kuyi tafiyan dare hakana nace eh nadawo dazun na samu ashe gwaggo bata da lafiyane haka kwana biyu ?
Yace wallahi amma dazun da zan fita na sayo mata yan hadiya tasha gaskiya yaji jiki yanzun dai ta samu barci tundazun ka kama min shinkafan can mu shigo dashi dakin nan.
Ok bari ma ai zan iya dauka nan dakin za a shigo dashi nace eh ina kaucewa a kofan dakin ya cicibo ya shigo min dashi zuwa ciki ya aje ya fito tare muka jera dashi zuwa wurin gwaggo.
A dakin gwaggo din baba na zaune yana cin abinci mukayi sallama muka shiga tare da gaidasu gwaggo ta amsa muna daga kwancen da take baba yace gata nan taki tashi taci abinci wai bakinta baida dadi.
Bari na hado mata shayi mai zafi tasha sai tasha magani kafin ta kwanta akwai kayan shayin ne Nura ya fada nace eh ga sauran nan dana sayo dazun ai.
Washegari ganin jikin gwaggo din da dan sauki yasa na fita zuwa school nayi tsamanin samira zata dawo kafim yamman sai gashi har lokacin nan bata dawo ba.
Girki na dora muna nayi tuwon masara miyar kuka na saka daddawa da kayan yaji na daka citta mai dan yawa gyadan miya itace na saka kwara biyu sai kanufar baifi kwara biyar ba hade na dakasu wuri daya saida ya lus na kwashe na debo attah kwara uku da abasa na daka.
Nayi hakan ne don ya dan gyarawa mama bakinta dan ruwan toka na dan dinga kadan rabin ludayin miya na debo kwaran wake da baifi sha biyar ba na watsa aciki banyi amfani da nama ba kifi na bare na zuba ruwan zafi na wanke na zuba a cikin miyan na barshi yana tafasa saida ya game sosai na gama wanke yan kayan da aka bata na dawo nakada miyan na barshi ya dan dahu sosai.
Kafin na juyo a wani dogon kulla da gwaggo ke juyewa gudun kada yayi sanyi kafin iyalinta su dawo kasuwa ina gamawa na wanko tunkuyar na kife.
Na dauki tsintsiya ya share ko ina nagidan tas kana na shiga wanka nafito na saka yar bubu ajikina na yadin silk da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login