Showing 165001 words to 168000 words out of 347556 words

Chapter 56 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8769

ba bakin ciki irin nasa ba.
Ke dai kawai kada ki yardama ya gano cewa ranki ya baci dama abinda kawai yake son yagani a tare dake ke nan don haka ki fito a karasa wanan sha,anin dake.
Nagode na fada tare da fadin yanzun zan fito yaron nan da yayi barcine nake duba har na kwanta mikewa tayi zata fita tana fadin ki dai fito na fada maki kada ki yarda ya fahinci kin sare dashi.
Ajiyan zuciya na sauke bayan fitan ta ummu ne ta aiko ummah hani wai nazo ayi sallama da baki wasu zasu tafi haka al,adan yake mata zasu tsaya da yan uwansu mata ayi sallama maza kuma tare da nasu yan uwan amma duk iyali zasu zo suyi sallama da kowa da yazo .
Don haka ban fito din ba don ummah hani dama ta samu na fito wanka don in rige gajiyan dake jikina lokacin ina sauya kayana zuwa wani riga atamfa din nan dan Dubai danazo dashi.
Na gyara tsab na dauko yaron nan danayiwa wanka na fito uwar ta taso tana murna takai hannu ta karbi yaron ya kara makewa yana son sa rikici ganin hakan yasa ta barshi don mijinta na ciki tare dasu Abbu suna meeting lokacin.
Hakana nake dashi suna barin wurin ana bankwana ga kyaututuka nan an tara birjit a gefe daya kowa zaizo da abinda yake dunkulewa ya kawo kyauta.
Amma fa wai kungiyace bawai kowa ne mazaunin can ke wanan al,adaba sai idan kayi register na dan Africa a cijin wanan kungiyar zaka halarci taron nasu ke nan tarone dai na manya mazauna can saudiya din a yadda na fassara abin a raina.
Daga nan inda nake tsaye naga wa????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
nan matar mai da ta nufoni tare da wasu tun daga nisa na hango tsayin mutumin da suke zuwa tare suna karasowa nagane mutumin wanan mutumin na Jirgine tare da ita.
Sunan nasa nayi kokarin tunawa na gaza har suka karaso inda nake tsaye da yaron shima mamaki yaji sosai don ya ganeni duk da nasa gyale na rufe fuskana sosai nayi rolling.
Amma hakan bai hana ya ganeni ba shima don ya nuna mamaki karara a fuskanshi don ganina gaidasu nayi da turanci yake min magana cewa wanan din sister shice .
Ya nuna min matar shi suna min hausa a nan na gane cewa iyalinshi mazauna saudiyane najeriya kila harkan business yake zama a najeriya ko kuma dai yana da wasu iyalan a can.
Wani dan kulli matar ta miko min na kalli hannun nata ba tare dana karba ba sai na girgiza kaina alaman a,a gareta ta kara miko min tana yare dasu naji wanan mutumin yace.
Ki karba ai baki tayi ba rokonta kikayi ba ashe gida Ambassador zakizo ranan nace eh yace ai baki fada min hakan ba dana rago maki hanya daga jidda nace anzo an daukenine lokacin.
Ummu ce ta karaso wurin yadda ta samu muna magana da mutumin take tambayanshi a harshen larabci da yasan nine dama yace ehh a jirgi muka hadu kujeran mu daya dashi.
Engineer naji ta kira mutumin hakan ya ban mamaki a raina suka karbi dansu suna godiya bansan me sukacewa ummu ba na dai ga ta dan juyo ta kalleni tare da fadin insha Allahu bansan me take fadaba a lokacin suka tafi cikin wata babban mota mai kyau.
Ummu ta juyo tana fadin ke dince mamana da shiga zuciya kike ji wanan karamin yaron yadda ya dafe maki kamar ya saba dake kowa yana zancen ki a wajen nan suna yaba hankalin ki sosai wlh.
Dan ledan da matar ta bani na nuna mata tace kin gode ki shiga dashi kya duba idan kinje dakinki ai ba a nan ba ido yayi yawa a wajen nan jeki falo Alh na jiran mu nan na samu salima muka shiga indasu Al,amin suke nan muka tsaya muma.
Kaina a kasa sai da naji an gama dogon sharfi na dan dago kai caraf a idon Oga bashir dake zaune cikin shiga irin ta suit da sauri na mayar da idona kasa kafin na kara dagowa ina kallonshi.
Tabbas shine shi dinne dai zaune nake gani yana dan tura sako a computer shi ya dago muka sake hada ido karo na biyu naji gabana ya fadi lokaci guda da ganinsa.
Don ban taba zaton hakan ingashi a wanan taron nasu Abbu ba haka kuma yadda naganshi nasan akwai sanaya a tsakaninsu ke yasa na tambayi kaina da kaina a kasan zuciyana..
Dama Oga nada wani halaka dasune ko kuma shima yazone kawai kamar yadda nima nazo hakan yasa na kara dago kai karo na barkatai.
Sai akai daidai a lokacin shima yana dagowa daga abinda yakeyi wanan karon kan idon mu ya sarke a cikin na juna nayi mamakin ganin dan murmushin daya makale a gefen fuskanshi kadan.
Ummuce ta shigo a daidai lokacin take fadin na barku zaune ko Bashir ina dai ba tafiya kaima zakayi ba ko zan tafi Ummu ina son zuwa makka inyi dawafi kafin in wuce Japan.
Kai ke nan baka zama kamar fulani kulun yawo Bashir hjy na min korafin suna son ganinka amma kullun amsa da kake basu shine aiko yayima yawa baka da lokacin hakan.
Ya mike bayan ya hada kayanshi cikin yar jakkarshi ya juyo yana fadin zan samu lokaci inje mu gaisa dasu insha Allahu.
Kallon Abbu yayi yana fadin Abbu zan tafi ya kalli lokaci a jikin agogon dake hannunshi yace saidai idan munyi waya kan zancen duk bayanin da ke nan zan fadama daga baya.
Na kula da kyar Abbu din yake bashi amsa kamar akwai wani takon saka atsakanin su amma suna basarwa a gaban jamma,a
Fatima kizo ki rakani bakin mota ya fada kai tsaye sai da kowa dake wurin ya kalloni don jin abinda ya fada kai tsaye a kaina.
Badon komai ba sai sanin ko wayeshi da sukayi a baya sunsan bai wani mu,amula da ko wace mace a rayuwanshi asalima har ana mashi zargi akan mata.
Wani iri naji a wajen ba yadda na iya dole na mike nabi bayanshi muka fita tare saidai ba wanda ya rakoshi don sunana daya ambta a wajen kuma muna tare dashi.
Cikin mamaki kowa ke kallona a lokacin har na fice daga babban falon wanda ke a makeken gidan nasu mai babban haraba don kowa yasan cewa baya mu,amula da mata ko kadan hakan har ya jawo suna masa zargi kamar yadda Oga Abbas ya fara labarta min a baya.
Yana gaba ina binsa a baya har muka danyi tafiya na secondni zuwa wajen motar da yazo dashi wanda wani matashin balarabe ke jasa yana zaune a ciki yana jiran fitowanshi alokacin.
Yana ganinsa da sauri ya bude masa motan kamar zai shiga ya manta da ina binshi a baya lokacin sai kuma naga yaja ya tsaya tare da juyowa ya fuskance ni lokaci guda.
Ok ki koma nagode ya fada hakan na samu bakina da fadin safe joining yace ya gode na juya da zumar in koma naji ya dakatar dani a cikin muryan shi ta maza mai tsorata mace tashi daya yace I hope baki da matsala a nan ?
Jin hakan yasa na juyo ina dan kallonshi tare da karkada kaina alaman a,a yace OK amma be careful don kusan you are not safe anan bautar dake kawai zasuyi a nan don koda yake ki barshi zaki gane nan gaba ai.
Alaman tambayane a cikin idona lokacin haka kuma yasa kai ya shige motarshi kai tsaye ya rufo duk ina tsaye a wajen can ya sauke glass ya leko ya yafutoni da hannu na tako zuwa gaban shi ya miko min kudi kalan kudin saudiya yana fadin gashi kisai abinda kike so dashi kada ko takurawa kanki please saboda nasan halinsu.
Sukaja mota suka tafi na juya tare da tunanen wani haline yake magana nasu da yake fadi don in ban manta ba ya fadi hakan lokacin dana fada mai zanzo saudiya ya tambaya na fada mai sunan mai gidan.
Gashi kuma ni banga wani hali a garesu ba daga iyayyen har yayan gidan zuwa masu aikinsu tun zuwa na dakina na nufa ban koma falon ba na adana kudin a jakata na koma na kwanta ina tunane.
Ni dai ban fito ba sai wajajen goman safe saboda gajiya a nan ma din abinda ya fito dani shine yunwa don rashin cin abincin da banyi ba ga jiya muna tsaye muna fama da jama,an taron su.
Na samu masu aikin su sunata faman wanke kayan da akai amfani dashi a wajen gaidasu nayi da kwana na shiga store din nayi sa,a akwai abubuwan da suka rage na debo na dumama na dawo falo nazauna don inci.
Shigowa naji anyi a lokacin na dago uncle nagani yana ganina ya kara daure fuskanshi ya kawar da kansa gefe nayi mamakin hakan amma a fili nima shareshi nayi tankar ban ganshi ba lokacin .
Wani abu ya dauka a gaban Tv ya fita daga falon na sauke a jiyan zuciya naci gaba da cin abincina nagama na tashi ina tunanen ya akayi yau bai min maganan banzansa ba.
Sai na dauka ya shiga hankalinsane a lokacin don amsan dana bashi daya dace da abinda ya fada min din ashe ba haka bane.
A lokacin ma gun hjy ya fito don Aliyu ya fada mata komai daya faru amma iya abinda yasani yake cewa.
Ummu ki shiga tsakanin uncle da yarinyar nan don na sameshi a daki yana cicika na tambayeshi yace sai ya karkarya ta kafin ta bar kasan nan.
Hjy din ke tambaya meya faru ya dan fada mata iya yadda sukayi da uncle din a kaina ya kara da fadin na dai bashi hakkuri ban san me ya hadasu ba don bai fada min ba.
Ran hjy din ya baci shine da safen daya zo gaida ita da kwana nan hjy din ta tunkari shi uncle din da zancen tana tambayanshi meye hadashi dani har yake ikirarin zai karyani ?
Kallonta yayi cikin mamaki kafin yace ba komai ukteeh ya dukar da kai kasa take fadin ya zakace min ba komai bayan kaida bakinka ka fadi hakan a kanta.
Ya dago kanshi shi ummu din ta kurawa ido tana saurarenshi girgoza kai ya sake yi yana fadin ba komai kawai dai banson ta kawo min rainine gaskiya.
Dubanshi tayi irin na tuhuma duk sai ya dan tsargu da kallon da take masa din yana dukar da kai kasa.
Mohammad ka fada min idan akwai wani abune tsakaninka da yarinyar nan insani da sauri ya dago kai yayi mata wani kallo na mamaki yace.
A cikin bacin rai yace ni ba komai dake tsakanina da ita kawai dai banson rainine shiyasa don na gane bata da mutinci niko maganin ta zanyi idan ta shigo tsabgata.
Mohammad ka natsu kasan abinda kake yarinyar nan nasan bazatayi maka komai ba sanin halin kowan ku danayi in ma har tayi din nasan dole akwai dalili hakan din haka ka fita harka yarinyar nan.
Ya kamata ace yanzu kasan ka girma duk wasu abubuwa kaima ya kamata ka daina yawan saurin fushi din nan da girman kai don Allah duk ka ragesu ka aje hakana.
Ka duba yadda Bashir yakai yanzu don Allah da sauri ya dago kansa yana dubanta bai san lokacin da yace nima a yanzu nasan nayi kuskure mai girma a baya.
Kuma duk kallon da yake muna nagane nasan har gobe yana rike damu a cikin zuciyarsa bama abin da yaban mamaki sai sanin yarinyar nan Fatima da yayi abin ya daure min kai sosai .
Ummu ya kirarata cikin yanayin mai nuni akwai tsantsar bacin rai ko wani zance mai girma a bakinsa yace yarinya nan Fatima nagane yar damfarace.
Hjy taji maganan nasa a bazata don haka tace danfaran kuma ita fatiman kai ban yarda da zancenta ba kaidai har in sonta kakeyi gara tun wuri ka fada mi zaifi
Cikin fushi yace wanan yar talakawan ko don tazo nan ta dau zauna dakune zan hada kaina da ita ina dai aiki take maki ana biyanta shike nan kuma ai.
Kafin ya gama fadan abindake bakinsa tuni hjy ta dakatar dashi da fadin kai min shiru don Allah bana son shirmen banza yanzu yakamata kasan ka girma yanzu please .
Ka daina irin wanan don Allah kuma kada ka sake yarinyar nan tasan kana mata kallon kaskantata a wajen mu don ko idan haka ya faru zanci mutuncin ka gaskiya.
Kai har yanzu baka san halarci ba haka kayiwa bashir wanan butulcin mu kuma idon mu ya rufe da sonka muka mara maka baya a lokacin.
To kasani da tallaka da maishi duk Allah yayi kowa a cikinsu baka san me goben yarinyar nan zai zama ba don ni zuciyana yana ban yarinyar nan wata abuce nan gaba shiyasa yanzu nake son in taimaka mata ta yadda nake iyawa.
Kai kokan Bashir bai isheka ayyah ba a rayuwa ka diba yadda Allah ya mayar da yaron nan yanzu duk da nasan har yanzu ba zai gwada ma komai ba to amma ya kamata kayiwa kanka fada ka rage wanan halin naka zata koma fadan wani abin.
Da sauri ya tareta da fadin don Allah umma ki daina kawo min zancen wanan ai shima ya fini jin kan yanzu kome yake daukan kanshi ohh ?
Yana fadan hakan ya mike dama a zaune yake saman kujeran dakin nata ummu din tace ka daiji abinda na fadama kan yarinyar nan don haka ka kiyaye.
Ya dan juyo kamar zaiyi magana sai kuma yasa kai kawai ya fice daga dakin rai bace don ta gama bata mashi rai ambato bashir da tayi a cikin zancen bayan yana fama da kunan ran nawa daya kwaba dashi yana soya mai zuciya.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
5?? 2??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Salamu Alaikum yan uwana musulmai yan Nageria dama makwabtan Nageria ina mai alhinin wanan ranan ta murnan cikan Nageria sittin da uku cikin jimame da bakin cikin kan yan uwanmu dake daji a cikin kunci da halin hau,illa,i tare da yan uwansu dake gida a cikin jimame da tashin hankali.
Ya Allah ka kubuto muna da bayin Allah nan acikin sallama ya Allah duk wani mai halin a kasan yaki magana ubangiji ka tillata mashi yin magana badon yaso ba ya Allah mun tuba ka yafemu ya Allah muntuba ka yafe muna badon halinmu ba.
Allah ka kubuto muna dasu a cikin sallama Allah ka dawo dasu ga iyayyensu da yan uwa lafiya Allahuma amin.


Shine yana fitowa daga dakinta kuma yayi tozali dani zaune ina karyawa ni kadai a falon ko daga kai nayi na kallesa bai sa bai samu ba lokacin.
Don haka yana hangoni yaji gabanshi yayi mumunan faduwa saboda tunawa da yayi ummu tace wai Bashir duk yadda akayi bashir ya sanni ashe.
To ta yaya har nasa Bashi don shidai a sanin sa bashir bai damu da mata ba ai asalima har suna zargin ko shi gay ne maza yan uwasa yake bi don hakane bai shiri da kowa.
Tuna hakan ya firgitashi lokaci guda ya baisan lokacin da yakai hannu a fuskanshi ba ya cire farin glass din dake manne a fuskanshi yana shafo fuskan nasa sayaji yayi masa nauyi lokaci guda.
A hankali ya lumshe idanunshi cikin kankanin lokaci kuma ya budesu zuwa lokacin idanunnasa sungama rikidewa zuwa ja kamar garwashin wuta.
Muryan Ummu ya tsinkayo tana fadin ina mamaki don duk yadda akayi sun san juna dashi a wani wajen to inane ya tambayi kansa lokaci guda.
Dan tunane yayi na tuhuma sai yaji kamar an tsinka masa jijiyoyin jikinsa lokaci guda gefen titi ya gangara ya packer motar ya fito ya rugume hannayensa yana tunane shi kadai shiga motar kuma ya komayi bayan ya dauki dan lokaci a wajen.
Nikan bayan fitanshi falon na ci gaba da cin abincina nagama na mayar da plate din kitchen na shiga daki ban kwanta ba saida na gyara nayi wanka na saka tufafi a jikina na koma kwantawa din jikina gajiya nake ji sosai a ranan.
Barcine ya daukeni a hakan har da mafarkina barci sosai na samu nayi sai wajajen sallah azahar namike da sauri don ina ganib na makara da sallah lokacin.
Saida na dauro alwalane nagane cewa ashe ban makara ba sallah na idar na zauna na jawo wayata dake gaban gadon


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login