Showing 147001 words to 150000 words out of 347556 words

Chapter 50 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8783

wanan wani abu zan kaiki can hanyan fita driver zaizo ya daukeki ya kaiki gida yana fadin hakan kuma yana kokarin tura hannu cikin Aljihunshi ya zaro kudi saidai ba kalan Nigeria bane don haka bansan kudin ina bane lokacin .
Ga wanan yace na baki zasu maki amfani idan kinje can naso ace ya baki dollars ki canza tun a nan ko akwai wani abinda zakiyi dasu ashe yana da kudin saudiya din a gida dama.
Karba nayi ganin ya kara miko min din ina fadin nagode amma daka barshi ka mayar mashi dasu don ganin karshe kila yai min a yanzu.
Kamar zaici burki yadda motan ta danyi kara yace kamar ya ganin karshe kuma kibarwa kanki fatan hakan don in tabbatar maki haduwanki dashi ko yaushe alherine insha Allahu.
Shi mutum ne mai kaifin ra,ayi idan yace yanayinka yana yinka har kasan zuciyarshi don haka ina fada maki ni nasan haduwan ku alherine saboda ban taba ganin hakan gareshi ba sai a kanki.
Don haka kiyi hakkuri yadda mukeyi kada ki gujeshi don Allah ki daure mu kwatoshi a tare dake yadda nake son in shirya komai.
Kusan tare muka iso inda yace drivern ya sameshi muna isowa shima yana zuwa kayana ya fitar a motan shi ya mayar motan da zai kaini azatona tasha din zamu tsaya a gaban idona yaba drivern kudi mukai sallama yace sai munyi waya muka dauki hanya dagani sai driver irin na ranan kamar wancan lokacin.
Wanan ma saida nayiwa su baba sayayya sosai muka isa kaduna misalin biyun rana har kofan gidan mu yakaini ya sauke nayi mai godiya ya tafi.
Sai gani kwatsan gida sukayi ana shigo min da kaya a gida kafin in shigo din cikini nadan jima da isah mai shago a waje bayan wucewan driver kafin na shiga gidan.
Da mama na fara cin karo kallon da raimin nasaba dashi don haka bai dameni bani gaida ita nayi na nufi ciki sai mama lanto dake wanki a bakin famfo.
Tana jin sallamana ta dan dago kai ta kalleni haka bai hana in gaida ita ba na nufi dakin mama uwa ashe tana kitchen lokacin tana girki daga bayana naji muryanta tana fadin bakin zaria ne tafe ?
Mama ashe baki ciki na fada ina juyowa ta karaso tana fadin ashe kina tafe yau kafin in bata amsa muryan anty Altinen mama ke fadin zaria kuwa ai wanda ya fito zaria ba a bace yake ba kema daga gani daga wani wurin take tunda bata shigowa saida alama don gagara.
To ai bahaushe yace kyakyawan jumma,a tun daren alhamis ake ganeshi ga mutum, ta karasa fitowa daga dakinsu din tana fadin wanan din ake saka rai kai haba Anty kullun abu daya kamar cin kwan mahaukaciya Usaina ta fada.
Indai karatune yanzu gidan kowa akwaishi ai fata na gari lamari mama uwa ta fada tana dan wuceni tare da fadin shigo mana daga ciki ki huta kin tsaya nan.
Tun shekaran jiya take gidan nan bataji da abinda ya dameta ba kinji yanzu kuma ta fito ta tsula tsiya niko ba kyale mace zanyi ba a yanzu idan tayi.
Don naji Usaina ta bata amsa yasa ban tsaya wani dogon magana ba a yanzu amma ai taci bashin hakan tunda tana gidan haba wanan bala,in da me yayi kamane wai haka ?
Ban iya cewa komai ba dakin muka shiga na zauna nayi shiru ina tunane me nakeyi na assha da mutane suke ganin ba daidai ba gareni.
Shigowan Usaina tare da hassana dakin yasa na katse suna fadin ashe yau zaki shigo da fita zamuyi fa da baki samemu ba ai nace tun jiya naso inzo sai ban samu gamawa da wuri ba jiya sai yau din nan Abuja nafito yanzu.
Au daga Abuja kike ke nan haba naga tsaraba ka kamar na hanyan don su kayansu masu kyaune ba irin na nan ba dama.
Ruwan pure water ta aje min tare da fadin ga ruwa nace nagode ban ko karya ba tun safe don a lockacin na fara jin yunwa a cikina .
Haka kika biyo hanya da yunwa keko ta fada tana kallona cikin mamaki nace ga kuma abincin da aka sayo banci ba tun na jiya duk suna nan na kulle nazo da abina.
Suna zaune sai bina da kallo sukeyi kamar suna mamakina kikai kayan abinci tundaga Abuja har nan nace mama ba mai lalacewa bane ai yasa na dauko abina.
Haba dai in waye haka ina kamarkin nan, zan tsaya ina dauko takeway zuwa gida yanzu dana barshi can karshe zubarwa zasuyi ai kila yasa na juye abina nazo dashi gashi yanzu zanci har wanima yaci.
Kayan nawa mama ta kwaso zuwa dakinta nan na fara bude ledojin ina firarwa suna mamaki har wana breakfast din da akai min takeway naci a hanya shina karba na fara dan ci don dahuwan yayi dadi sosai kunya ya hanani ci a can din lokaci.
Zance kowa an kwantalawa wanan abin ya lasa a gidan can mukaji anty Altine na fadin lalai dole kuja baki in an dawo ta zubar din ashe dadi kukeci a gidan nan haka ?
Ka daiyiwa dan uwakan shedan kwarai sheri karene idan baka da mace kana da maza lalacewa yanzu kuma ba mace kawai ake lalatawa ba.
Don har mazan nawa akayi munaji muna gani wasu ma sunsan lalacecene mijin nasu amma kuma hakan suke zaune dashi suna hakkuri.
Ke maman Nura naji tun dazun in nayi magana ki sharbe koda yake ba mamaki tunda ana baku kamun baki haka shiyasa gidan kowa ya toshe bakinshi yanzu.
Mama gobe zan koma na fada akan me zaki koma gobe don zancen da wanan ke haukan fadi kome gida gidan ubankine ba mai hurumin koranki daga gidan nan don kema yace kamar kowa.
Ba zama nazo yi ba nazo na sai kuma nayi shiru don Hassana da take ce min halan Samira bata san zakizo bane Bantu bata baki gyalena kin kanwo min ba ?
Samira kuma na tambaya cikin mamaki tace ita man tazo wancan zuwan ta daukar min gyale datazo satin can nake tambaya tace yana gunki da zata fito kina amfani dashi.
Samira kuma yaushe rabona da samira tunda yanzu ba wuri daya muke ba da zan karbi gyaleki a hannunta.
Ba wuri daya kuke ba zaune a gidan gwaggo nace ai tafi wata shida bamu tare da ita yanzu ina ta koma kuma nace wallahi ban sani ba don ko mun hadu batayi min magani nima kuma banayi mata.
Samira fa bata gidan gwaggon ku kikace mama ta amshe zancen daga inda take zaune kafin in magana mama Lanto ta fito tana fadin ai ba wani wuri take ba balle a saka mata baki dakin dalibai ta koma da zama.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
4?? 5??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Ina kwance dakin mam uwa danayi masauki barci na samu sosai na gajiya ban tashi ba itama bata tayar dani ba sai yamma da baba ya dawo na fito don sallah magariba.
Banje mun gaisa ba sai bayan sallan isha,i daya dawo yana zaune yana cin abinci mama uwa dake girki tana tsaye gefenshi rike da wani tsohon roba da suke zuba mashi manshanu a ciki.
Jin sallamana yasashi fadin a, a fadimatu yanzu uwarki ke fada min zuwanki ai sai gaki ya wajen ita gwaggon naku da iyalinta kuma ?
Nace suna lafiya baba tace agaisheku to ya ita yar uwartaki kuma baku dai tafiya tare baba ai yanzu, , , ,
Wai malam kaima baka san basu tare ba yanzu Samira ta bar gidan sa,adatu ashe wani irin dagowa cikin mamaki baba dake shirin kai loma a bakinshi yayi lokaci guda yace bata gidan kika ce.
Nan dai mama ta fada mai komai dana dan fada sai baba ya kalloni kaina sada kasa ya danyi shiru na dan lokaci kafin yace haka akayi fadimatu kuma baki fada min ba ita gwaggon naku kuma bata kira ta fada min ba abisa wani dalili kukai min hakan ?
Baba na dauka da yardan ka ta kwashe kaya kuma an sani a gida don naga nan gida na barta a lokacin ban dauka bada izinin ka ta aikata hakan ba.
Loma ya yanko yaci gaba da cin abinci kafinbya hade ya sake dago kai ya dubeni yana fadin yanzu ina ta koma ke nan nace wallahi ban sani ba baba amma naji mama na fadin danzun cewa wurim kwanan dalibai ta koma da zama.
Allah ya kyauta muka amsa da Amin kun samu hutun ke nan nace eh baba yanzuma nazone akan wanan zancen ina fara fadin hakan mama uwa ta fita daga dakin jin muryan Nura ya shigo zai fita sai ta fita da sauri ta bishi.
Hakan ya ban dama yiwa baba bayanin komai akan tafiyan da zanyi daya karato ya dan kara min nasiha tare da ja min kunne kafinta dawo dakin na samu n fice daga wurin baba din dakinta na koma na kwanta.
Don na samu Nura zaune a dakin yana cin binci muka fara dan hira dashi yake tambaya ya bude min dakine nace ya barni in kwana a nan don gobe zan koma zaria.
Nan yake min hiran Samira din yace ai yanzu tare suke da ya habibi sosai bayan ance baba ya gargadi kowa da ya fita harkansa a gidan kema daya nuna yana so kin fita zancen shi aini kin burgeni da kika nuna masu hakan .
Lokacin bakiga yadda mama ta rude ba a gidan nan kamar zatayi hauka kan wanan zancen sai gashi kin nuna ke bai isheki tsara ba don dole jiki yayi laushi yanzu tsakanin sune dasu ai sun fi kusa dama.
Kinga mama Lanto din nan makirane sosai ko yanzu da zan shigo naji suna gulman ki a vakin famfo ita da Anty Altine ita kuma mahaukaciya da bata san inda ke mata ciwo ba yanzu.
Wai wanan mijin nata ne har take hauka a kansa don yace zai kara aure ko me yake tsinana mata dama oho da har ta tsaya take wani kishi akansa.
Nace kai Nura mijintane fa mijintane da take da yaya dashi zakace haka yace yayan banza yayan ma da ba ruwanshi dasu haka yake tafiya ya barsu yayi wata da watanni a can kudu in zai dawo haka zai dawo a wahalce babu komai.
Kallonsa nakeyi ina fadi a raina shima ya iya irin tsegumin gidan mu kamar mace koda yake haka gidan yake da kananan maganganu har da yara sai uwa ta zauna tana gulma a daki don haka ba laifinsa bane don shine babba a dakin mama uwa don haka dashi take zama suyi gulma.
Nura ya dan girme min a shekaru amma yanzu kasancewanshi na miji ni ina mace idan ka ganmu zakace nice yayanshi shima kuma din ya bar min girman samira daice bata yarda ba tunda ita mace ce saidai kuma bata kaini gaban jiki ba.
Duk da dai mudin yan gidan mu dan tsayin da muke dashi bai bari muyi jiki sosai gashi mu din muna biyu mahaifinmu da hasken fata don gaskiya babu bakake sosai a gidan mu.
Ainihin bamu san dangim mahaifan mu ba sosai munfi wayewa dasu gwaggo sa,a da gwaggo dije don sune suke kusa damu nidai na bude ido naga ko wani sha,ani akeyi su kadai muke gani a matsayin yan uwan ga baba sunzo.
Wanan yasa muke daukansu da muhinmanci sosai gadon mama uwa data gyara min shi na haye na kwanta banjima ba sai barci don haka ban san meke faruwa ba kuma a gidan.
Washegari dana tashi nayi sallah na koma na kwanta don indan hantse kafin in kama hanya zuwa zaria barci nakeyi sosai a can cikin barcin nake jin hayaniya a kunnena.
Wanda hakan yasa na falka daga barcin da nakeyi mai nauyi na fara danjin magana sama sama muryan Anty Altinece dake fadin saudiya fa ni abin ma ke ban mamaki don haka nake jin zancen kamar a mafalki.
Wa akafi sa,a ko farin jini da kullun za ace mutum dayane me sa,a a gidan nan kaf don an mayar da mutane basu san komai ba za a fadi hakan ko ?
Amma ai abinda kunya mutum dai yasan hanyar da yake shige da fitansa yana mayar da mutane wawaye da basu san komai ba shi gashi wawa.
Amma zuwa saudiya banzane da wata mace macefa wai zata biya maka kudi ka taka kasa mai tsarki dole aji kunyar fadin namijine za a tare dashi aka labe da fadin wai mace ta biya mata kudi don kawai tazo wajenta.
Ni baba yafi ban mamaki yadda ya yarda ana shata masa karya haka yake yarda kamar ba baban da muka sani mai fada da tsanani a daba.
Keko kin manta yar kunamace tafi uwa zafin harbi abar mata gadon mugun abu ta iya komai fiye da uwar banza zata barshi haka dole kema da ganin wanan abin kisan aikin malamai da bokayene ai.
Yaya taka fada min karan dafi aka bar muna a gidan nan ban yarda ba sai yanzu da abubuwa ke faruwa kamar a mafalki nake gane hakan magananta gaskiyane ashe.
Humm, kai mutum hoo idan dai abu ba a kanka yake ba yanzu shike nan sai kyashi da hassada kuma yazo ya shiga har yaushe alheri irin hakan ya faru da dan uwanka zaka kasa boye hassadaka a fili mama uwa ta fada tana tsaye a tsakar gida yadda duk wanda ke gidan lokacin zai iya jinta.
Meye na hassada a cikin zancen nan daga fadin gaskiya balaifin ki bane tunda ana lasa maki kina ci boye don haka dole ki tare kada ayi zancen ki juyashi zuwa wani manufa
Ban juya ba kudin dai ke son ku juya zancen da nufin cewa namijine zai kaita ko ai gara ku fito fili ku fada yafi wanan kame kame da yanzu kukeyi.
Fada sosai ya kaure inda mama uwa take kareni take fadin kowa yasan tsakaninta da matan nan ladabi da biyaya yaja mata alheri amma kun juya zancen yanzu kuncebin maza yayi rana ko bin mazan ai iyawane wasu sun gwada ba sa,a.
Abu kamar zai kaisu da bugawa a tsakaninsu har yakai makwabta sun shigo suna rabo nan suke jin abinda ya kawo fadan lokacin.
Mikewa nayi na shiga hada kayana ina hawaye a gaban kowa na fito da kayana na bargidan bayan na ajewa mama uwa abinda zan bata na bar gida duk kiran da wasu ke min a cikin makwabtan haka naisa na dawo ba.
Ina zuwa tasha na samu mota saura mutum daya don haka ba bata lokaci mota ya daga sai zaria na isa da wuri yadda gwaggo ta ganni take fadin .
Lafiya kuwa na ganki haka yar nan ba komai gwaggo na fada ina shiga dakin kuka yazo min na zauna inayi a dakin ba komai yasani kukan ba sai tunawa da cewa gidan ubanane fa.
Ta ya matan ubana zasu kakara min sherin da gari zai dauka gaskiyane ace wai harda yar uwar haihuna kuma baban yanmu ta gidan mu da bakinta sake take fadin kalamin banza haka a kaina.
Nasan baki karya ba yar nan ga abin kari ki karya sai kuma taja tayi turus ganin yadda nake zaune ina hawaye ni kadai a dakin to nasan sunyi tsiyan ke nan kuma ko ?
Jin hakan yasa na kara sakin sautin kukana lokaci guda tayi tsaye tana kallona kafin ta juya ta fice daga dakin can sai gata da ruwa a kofi tana fadin karbi maza ki dan kurba kiji sanyi azuciyarki .
Karban ruwan nayi na kora komai na babba yafi na yaro don ina shan ruwan naji hawayena ya lafa zuciyana yana sanyi sannu a hankali.
Gwaggo bazan kara, zuwa gidan mu ba komai ya faru don basu kaunata duniya da lahiri akul akul na karajin kin fadi hakan.
Ai abinda suke nema kenan dama yadda suka kori uwarki kema yanzu haka suke son su koreki da karfi da yaji kinga ko sun samu galaba ke nan yanzu a kanki.
Dolene gwaggo don kiyayya kawai zasu jefeni da kalman bin maza har suna dora min kazafin cewa tafiya nan da zanyi namiji zanbi zuwa saudiya.
Allah sarki to sai me idan sun fadi hakan koda hakane aiba kanki aka fara ba hakan kuma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login