Showing 231001 words to 234000 words out of 347556 words

Chapter 78 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8731

nace ban ganki ba nan take fadamin abinda ke nan a tsakanin ku ai itama iyar kusan matsalan da aka samu ke nan suka zarga mata sheri don kawai ta bar gidan wai anshiga an masu barna ni a lokacin ina gida ina jinyar matana data kare nisaida na dawo nakeji.
Ban dade da dawowa ba iyan ta kwashe ta bargida tunda sun nuna jikokin iyar subar masu gidan ina zata barsu inbada da ita ba don haka itama ta tattara kinsan Alh da hjy sunzo kasan nan suma bukin nadin sarautan kaninshi da akayi nan cikin zaria.
Sun dan kwana biyu suka koma kasar saudiya din itama ta tambayeni ko ina ganin ki kina zuwa nan gidan nace gaskiya na dade ban sakaki a ido ba.
Munyi sallama dashi daga nan kwatance gidan iya yayi min nakama hanyazuwa can din don inson ganin iya kafin na tafi din.


ZAINAB IDDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
7?? 3??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Zaune nake cikin mota ba a,abida nakeyi sai tunane agun da nake zaune ba komai nake tunane ba kuma sai makomar rayuwata gani dai na fito gida da niyar zuwa yobe duk da nasan akwai aiki ja a gabana.
Amma hakan bai sare min gwiwa ba wurin aniyar dana dauka din don neman mahaifiya don a yanzu zuciyana ya gama bushewa kan hakan tundai da hjy balaraba ta fada min cewa aikin asirine karfa akai mata nata bar gidan har abada ta manta dake dashi ga baki daya a rayuwa.
Sai na hau nayarda da hakan kan cewa shiyasa baba baison in kawo zancen uwata a gaban shi kirkiri zai share zancen ya kawo wani magana ta daban a bar wanan zancen alokacin.
A hankali na kara kwantar da kaina saman tagan motar dayake a gefe na zauna ina sauke ajiyan zuciya a hankali har wace ke kusa dani ta dan kalloni tana fadin mun matse gashi tafiyan yanzu muka farashi.
Dan murmushi na sake a fuskana ba tare danayi magana ba na lumshe idanuna a hankali zancen iyane ya fado min a rai lokaci guda da da take fadin .
Bari yar nan ashe kallon mai a saman ruwa mukewa hjy halinta nanan ta boye sai daga bayan nan nagane hakan yasa nayiwa kaina kiyamallaini da ita a yanzu don irin mutanen nan ne ita masu daukan tallaka a matsayin bawa koda yaushe saidai ka tabbata a karkashinsu suna mulkanka yadda sukaga dama.
Tace na sallami yan marayun jikokin nan nawa don ni kadai taba gida bada iyalina ba ina take son suta ni ina zaune don kwadayi kome ko duniya take ban a yanzu na yafe.
Macen da mijin in zaima alheri take hanawa ko a gaban ta kiri kiri zatace kada yai mata haka ba haka takeyi ba ita kada yasa mata baki a cikin harkanta koke nasan akwai babban dalilin dayasa ta daukeki ha??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????r zuwa saudiya dole tana da wata manufa akanki gayin hakan.
Murmushi nasake a inda nake zaune cikin motan don nabawa kaina amsa ba komai bane sai dalilin taronsu da sukasan zasu samu kudi nazo kawai suyi amfani da baiwana su karu dani alokacin.
Suna ganin sun min wayau a wajena kuma ni ina fadan Allah yana sona da arziki tunda yakaini saudiya ta hanyarsu na ziyarci ma,aikin Allah duk abinda zasuyi ragagene a wajena don nafisu cin riban abin harga Allah.
To shikuma Uncle neman meyazo yake min gani yarga aiki in tafi in ta masa girki yana kwasa kome yake nufi da neman da yake min dayazo din garama da Allah yasa ban garin hakan ya faru.
Tafiyace kan mai nisa gaskiya kafin mu kama yobe sai wajajen yamma sosai muka isa garin yobe state ban yarda na nuna bansan hanyar garin da nazo nema sai motar zuwa garin dana fara cigiya a nan tashan.
Wanan matar da muke tare tace dani mota daya ke nan don ni har gaba da nan zan tafi ai ta fada min sunan wani kauye dama ban taba jinsa ba.
Hausan mutanen jahar ya bambanta da namu na kaduna amma duk hausane saidai nasu din ya dan surka da kamar yare nake jinsa munyi arziki don motan garin saura mutum uku suke jira ta tashi.
Haka muka matsa muka shiga motar ga mutanen wasu kala amma hakan bai dameni ba ni dai burina shine na ganni a garin Gashuwa din shi kawai nake fata a lokacin.
Gani tun safe dana fito komai ban saka a cikina ba har wanan lokaci dana dan fara jin yunwa muna tsaye muna jiran motan naji wayana dake cikin jakkata ta dauki kara na lalubota da kyar na duba mai kirana a lokacin hassanace a layin .
Muka gaisa take tambayana ko nakai nace da saura yanzu na shiga motar garin tace huu,umm ashe ba karamin nasane da garin ba da nan kaduna nace akwai nisa gaskiya gamu dai a hanya ta dan min barkwanci muka kashe wayan ina kokarin mayarwa a cikin jakata wani kiran yana shigo min na duba.
Oga Abbas nagani a rubuce haka kawai naji gabana ya fadi yake na daure na daga kiran a cikin sallama sai baji yana fadin amma dai kanwata kin ban mamaki ranan daga nace zan kira da kikaji ban kiraba kema baki nemeni ba.
Hakkuri na basa a daidai lokacin da dan Union din tashan ke fadin sunan garuruwan su saitin inda nake zaune yace wait wai kina ina haka nace yobe.
What ya fada yobe fa ya tambaya cikin mamaki nace wallahi yanzu haka na shiga mota gaba zan tafi ina zaki hakane nace gashuwa kai tsaye what ke kadai a wanan hanyar me zaki tafi yi har wuri mai nisa haka ?
Dan murmushi na sauke kafin nace zanje neman wata yar uwar mahaifiyatace a garin you're too crazy Fatima a ina kika san zaki sameta yanzu ya fada cikin mamaki.
A wanan garin akace take shine zanje ingani ko zan dace bayani naji yanayiwa wanda suke tare a lokacin fisgan wayan yayi daga hannunsa yana fadin don't be stupid baki san darajan kanki bane da zaki kama wanan hanyan zuwa Yobe ke kadai mace ?
Ya akayi gida suka barki kika tafi wanan wajen da baida security ko kadan kai amma yarinyar nan baki da hankaki inda yake shiga ba nan yake fita ba.
Ni mamaki abin ya bani don haka nayi sororo ina sauraran shi kafin nace dakata malam kada kaga laifina a cikin zancen nan don bai shafi kowan ku ba yasa zakaga laifina don ku kuna tare da mahaifiyan ku ko yaushe na kashe wayan ga baki daya.
Ko sunyi nemana nasan ba zasu sameni ba da gaiya kuma na fada masu magana a cikin zafi don kada su kira gida jin ba,asin dalilin da baba ya barni zuwa yobe din ni kadai su tayar min da balli.
Acan bangaresu kuwa cewa yayi you see duk haka suke basu da wayau kaji abinda yarinyar nan take fada kuwa Abbas ni zata dakawa tsawa tace don ina tare da mahaifiyata zan hanata zuwa neman nata ?
Ni tawa uwarma bata duniya don haka bansan dadin uwa ba saida na hadu da mami acayuwana nasan me akeji gun mahaifiya lokacin nasan me uwa ke nufi a rayuwan mutum.
Gaskiya banyi tsamanin zakaji zafin wanan maganan ba koni ba zance naji zafi ba tunda nasan pain din da take ciki gashi yanzu kaima ka fadi da bakinka yanzu kasan me ake nufi da uwa ga mutum.
Koda wurin yafi hakan risk haka zata rufe ido taje don uwa ba wasa bane don haka be cool please kada hakan ya batama rai son Allah saboda Allah kadai yasan dalilin fitan ta zuwa jin inda zata sameta.
Wani kallo ya watsawa Oga Abbas din dake gefen shi yana magana don ba zai iya magana ba a lokacin don haka ya dauke kanshi yana jin zuciyarshi tana masa tafasa sosai ya kiyasta abubuwa da dama dan lokaci guda kafin ya kuta a fili wanda yasa Abbas din ya dan kalloshi.
Hanya ya mayar da hankali ga tuki kafin yace nasan rantane a bace ta fadi hakan kaiwa ya fadama amawa ma mata fada haka kai tsaye .
Please idan baka iya jana ka saukeni a nan in fita ya fada a cikin hasala No kadaice in tsaya ka sauka zaifi sauki da ban iya jankanw aida ban daukoka ba ayanzu.
Daga hakan kowansu yayi shiru har suka shiga haraban gidan Bashir din yana tsayawa ya bude motar zai fita Abbas din yace zuwa nine saika kirata kaji kota sauka lafiya nima zanyi trying dinta inji.
Wani irin juyowa yayi kamar zaiyi magana a lokacin sai kuma yasa kai kawai ya karasa fita daga motan ya bugo kofan motan da karfi yasa kai ya shige ciki ba tare da kara juyowa gareshi ba.
Dariya sosai Abbas din ya kwashe dashi shi kadai a mota kafin yayi ribas da mota yaja ya fice zuwa nasa gidan wurin iyalinsa da tun safe bai koma gidaba yana gun aiki.
Zasuyi daidai ya fada a zuciyarshi don na fahinci in ba irin wanan ya samu ba akwai aiki don duk wace zai nema a nan ko cikin dangi wace zata soshine don abin hannunsa.
Sai daji muke bugu hawo tundu haw gangare a cikin duhu idan motan ta daga kaina saiya bugu da saman motar abokan tafiyana sai hiran su sukeyi hankali kwance da gani sun saba da bin hanyansu.
Niko ihu ne kawai ban masu ba gashi sai karni nake jin yana tashi a motar kamar mun dauki kifi ko wani abu mai kazzini a cikin motan amma duk wanan bai damu yan cikin motan ba donsu hankalinsu a kwance yake.
Dan tunane nayi nace ni Bantu idan wani abu ya sameni a dajin nan mezance ya kawoni nan wata zuciya tace mahaifiyar ki mana amsa daya sai wanda baisan zafin mahaifiya bane zaiga laifin ki.
Karfe tara na dare muna cikin garin duhune don haka ban ganin kowa daga can baya ina jin mutane suna fadan inda driver zai saukwsu nima nace don Allah driver unguwar zan sauka .
Jin hakan yasa yan motan suka kalloni wani dake ta gaban mu yace unguwar hausawa kan sai kin sauka hanya kin samu mashin ya karasa dake can don akwai dan jayawa da titi.
Can nayi sai a sauke mu a waje daya mu samu mashin wata mace mai yawan surutu dake zaune da wani a gaban mota ta fada driver yace yauwa ga hjy sai ku jera ku shiga ciki yafi sauki.
Halan ke bakuwace wani ya fada yi nayi kamar ban jisa ba na kyale sai wanine ya bashi amsa yace bakuwace aida gani tunda tace ga inda zata tun nan gamboli.
Yauwa ajemu daidai nan anfi samun mashin matar ta fada jin hakan yasa na fara dan dago hand bag dina ina gyarawa don fita motar ta tsaya muka fito a cikin motar.
Ta kuma tsaya rakadi da mutanen motar saiga masu mashin nan wani yazo yana wanu magana kamar yare ashe hausa takeyi wai ina zan tafi ?
Lokacin matar ta juyo tana fadin gangaren hausawa dari biyar aisai ku tafi don nan ba baki bane mu ta fada a cikin yanayin fada wani yace dari biyu idan yayi maku kai dari da hamsin zamu baka koshi don dare yayine ta fada .
Na dauka zai tafi sai naga ya tsaya yace mu tafi wai ashe nufinta mu hau mashin daya da ita a raina nace lalai wanan matar hatsabibiyar mace ce don da ganintama yar duniyace .
Tace ki zo mu hau don dare ya soma yi kada wani yazo ya hau kuma na dan kalleta don ni ban masan yadda zan hau mashin ba balle har mu hau mu biyu tace bari to ta fara hawa sai in hau bayani.
Haka muka matsa da ita saman mashin din dana samu na hau da kyar cikin dabara mai mashin ya fisgemu diiiii iska kamar ince wayo Allah a lokacin.
Can yanayin unguwar da muka dosa saina fara danjin iskan sanyi yana bugo muna yanayin ya dan canza da wanda muka baro a baya kamar ba gari daya bane.
A wani kwana zaki sauka ta dan juyo tana tambayana nace gidan Liman Hamza tsoho zan sauka tace oho kice gidan malamai kikazo ashe naji dadi a raina lokacin da naji tanawama mai mashin din bayani inda zai ajeni.
Sai hira sukeyi da mai mashin din muryanta rara tana kwasan dariya saman mashin a cikin dare nace ni fatima Allah ya kawoni yau hasken fitilun unguwar ya fara haskamu ga yara nan gungu gungu zaune a baranda suna karatun allo irin na zaure.
Mata masu fita unguwar dare kuma muna ta haduwa dasu masu motoci a unguwar sun parker a gefen gidajensu a kofan wani gida mai babban masalaci muka tsaya na sauka tace ga gidan mun iso amma dai ke sai ta kalleni da kyau kafin tace ki tambayi wancan zasu kaiki ciki ta hau mashin din nayi mata godiya sukayi gaba.
Na zata ai garin kauyene mai bukkoki yadda na zata ashe garine mai dan girma da yawan jama,a acikinsa hasken kwan fitilan daya haskoni yasa mutanen dake zaune suka zubo min idanu suna kallona.
Na dan kakabe jikina don kura dana kwaso na duka nadauki dan travelling bag dina zuwa inda suke nayi masu sallama da alama magidantane don ga kwanonin abinci nagani a wajen wasunsu ma basu dako riga a jikinsu.
Nace sallamu Alaikum ina wuni kun hausan dai ga shinan nake jinsa suka amsa nace gidan Liman Hamza tsohol nake tambaya gashi can wancan hanyar zaki shiga.
Nagode na fada na soma tafiya nan naji muryan wani a cikinsu ya dago yana tambaya gun wa kikazo nace hajja Maria na bashi amsa daga inda nake tsaye .
Hajja Maria ba,a nan take ba yanzu suna can gaba inda kikaga hasken can ya fada sai wani ya mike yana fadin bari nazo muje na kaiki wurinta ya taso shiya karbi jakkar hannuna yace mu tafi.
Ba laifi don gidan yana da dan kyaushi da makari don yafi namu a baya makari sosai da nuna jin dadi shiya fara shiga da sallamanshi kafin na biyoshi a baya.
Yana shiga wani part a gidan ya kara sallama aka amsa yace hajja bakuwa kikayi fa daga ciki naji matar ta amsa da bakuwa daga ina gata dai ya fada yana aje min kayana daya dauko min..
Tashigo man ta fada itama daga cikin hakan yasa nasa kai zuwa shiga cikin dakin a nan nayi arba da wata farar mace mara jiki sosai azaune saman kujera tana fuskantar kofan dakin nata ma,ana tana ganin me shige da fice a cikin part din nata.
Duk yan matan dake falon nata su biyu suka bini da kallo na karaso har gabanta na zube a kasa ina gaida ita ta amsa cikin kura min idanu kamar tana son gano imda tasan fuskana.
A,a don Allah tashi ki zauna bakuwa daga ina hakan banko wayeki ba ta fada tana dan murmushi a fuskanta cikin wayencewa dason tunowa.
Nace daga kaduna nake Ammi ina dan murmushi tace fuskan nakine kamar na dan santa amma kuma na manta a inda na santa sai na danyi dariya na dukar da kai kasa ga ruwa wata daga cikin yan matan ta fada tana aje jug din dake cike da ruwa mai sanyi Fadilama ta fimu hankali yau tunda ko ruwa bamu tsaya bata ba mun hauta da tambaya hajja din ta fada tana kallon wace ta aje min ruwan a gabana da cup.
Saura abinci a kawo mata abinci don Allah ta fada tace to Ummi ta juya ta tafi lokacin wanan guy din daya kawoni yake mata magana har yarinyar ta kawo min abincin a cikin plate rufe ta aje a gabana nace nagode banki ciba tunda yunwa nakeji a lokacin sosai a cikina don haka banki ba ana aje min na gyara don inci miyar kifi ne danye amma an soyashi manya a saman abincin.
Sai shimkafa da ganyen salat dayaji hadi cikin zumudi na fara ci don yunwan da nake ji alokacin sannu a hankali na fara rage saurin kai spoon din abincin don karnin kifin daya fara hawa min kai sai na koma dan cakulan abincin kadan kadan na sha ruwa na ture plate din gefe daya.
Har ta farga da hakan don tana can tana magana a kan wani mutum da wanda ya kawoni gidan ta dan juyo tana fadin a,a ya kuma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login