Showing 201001 words to 204000 words out of 347556 words

Chapter 68 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8741

Bantu ce har da sanadin dauko malam zuwa nan karin gashi kuna wai har malam fa malam dai yana rokawa Bantu arzikin zama wani abu nan gaba.
Ke nan yaji dadin auren yarsa Samira da mijin yar uwarta wanan kuma yana mata kokarin wani mijin suko yan biyu ko oho ke nan ?
Mama ki dauka zafin ciwo yasa baba fadin haka tun jiya nace ki share zancen nan son Allah kada ya tsaya maki a rai kina bata ranki a banza da wofi kan haka.
Dama ai saurayin Bantu ne ai mutumin nan ko ko baba ya fadi haka ko bai fada ba mudai ta dalilin ta muka sanshi a yanzu ai Allah kuma bai manta dasu Usaina ba idan anyi hakkuri suma nasu mazajen ai suna tafene ko ?
Ni bana son kina yawan maganan nan haka har yarinyar nan taji zancen nan yazo ya zama wani abu nan gaba kuma gashi ko banza sunan ki yayi kauri a kanta don ma tana da saurin yafiyane ko mantuwa yasa take daukan komai ba komai don Allah dai ki bar zancen nan hakana zaifi.
Ni gashi har ina zancen ta roka min su ko goge goge na samu a wajensu yafi min tafiya Lagos din nan da mukeyi kullun mutum yana wahala a can ai.
Ka bari Amadu abin ne da ciwo wai mutum yana kallo yar nan kullun sai cigaba take samu mu muna zaune a gida kamar wasu sakarkaru damu can.
Wake ja da ikon Allah haka mama ina son ki gane Allah ne maiyi ba mutum ba kowa da nasa sa,an a duniya don da wanike bada ai kinsan ba za a ko kalli bantu ba amma kuma ita Allah kebawa Sa,a kullun kowa yasan da hakan.
Maganan banza ke nan kake min ko ayanzu din wa kake tunanen Bantu tafi cikin yayana saidai kai da kake neman mayar da kanka baya danaji kana zancen banzan ka wai ko share,shere da goge goge ta nema maka wajen farkunan nata.
Ni bari kaji duk wanan bai tsone min ido don kawar da kara ba aiki bane a wajena yadda na kawar da uwarta har abada ga malam ko ita yarta ba wani jan aiki bane in kawar da ita bat kowa ya huta.
Ba karan dafi ba kuwa ko karan mallaka take ni wanan ba aiki bane a wajena namayi kuskuren barinta nan da nace a hada da uwar da yar ga baki daya a batar min dasu kowa ya huta da tsiya.
Gabana yayi mumunan faduwa lokaci guda da ace mama tasan idona biyu nasan da batayi gigin furta wanan kallamin ba a lokacin saidai ina a lokacin idon mama ya rufe sosai da kishin yar mijinta.
Wace furcin baba ya razanata a lokacin kaina don ganin Bashir da tayi a matsayin wanda baba ya dankawa amanan mu dani dasu ga baki daya kota Allah ta kasance a gareshi yanzu din.
Ina gaban da shiga naji ya Ahmed na fadin ammako in har hakane wallahi mama kiyi gagawan tubawa Allah don akwai hisabi gobe kiyama ta ya zaki hana mata da yarta ki rabasu har abada kuma baki bar yarta ba kina binta da sheri haka.
Ina jin hakan na juya na dawo dakin kowa yasan yadda wasu ginan abuja suke don haka ba dole bane kasan da mutum a wajen naji mama ta hausa da fada sosai ni dai ban tsaya karasa ji ba na shige dakin da muke kwana da ita a cikin tsoro.
Kuka nake sosai gudun kada ta jini yasa na shige bandaki na kule kaina na sake ruwa yana zuba ashe kuwa sun lekoni bani saman gado amma ga karan ruwa da alaman wanka ko wani abu nakeyi a bayi.
Kodana fito banfita ba don yunwan da nake jima A yanzun na daina jinsa a lokacin don yadda zuciyana yake faman bugaw a lokacin cikin tashin hankali.
Nan hiran da geaggo ta taba bani ya fado min a rai lokaci guda ina tunanen yadda take fadin mama din ta tafi tana sharan hawaye ko waigosu batayi ba tafiyan da har yau bata dawo garemu ba ke nan kuma.
Ina share kwallan dake shirin gangarowa ga idona naji wayata ta dauki kara lokaci guda hakan yasa na dago ina duba mai kiran nawa a lokacin.
Oga Abbas ne ya kira gab da zai tsuki na samu na dauki wayan abinda na fara jin yana fadi a lokacin shine amaryan Boss bakya laifi ke haka akeyi kanwata ko kamshin amarcin ne aka fara ko wayan bakya iya dagawa .
At list dai a kya kira kiji ko ya lafiyan baba yake amma kin share mu kawai haka ba kira naso ace ina da wayan brother dashi zan kira in fita batun ki a yanzu tunda kina jin kamshim amarci tun yanzu.
Haba dai Oga kaida kanka kake fadin haka gareni kuma yanzu kaima kasan zafin ciwo yasa mahaifina fadin haka da lafiyan baba kalau ba abinda zaisa ya furta hakan a gareni ai.
Amma kin san Allah ya sauwaka in hakn ya tabbata kin zama amarya ke nan sai mu gama makoki mu koma kuma shan buki tunda an babu mun kuma sheda ga baba yace zamuyi alfahari dake kuma.
Mun tafi asibiti dazun da safe amma basu yarda munga baba din ba saidai wata nurse ta tabbatar muna da ya samu sauki sosai fiye da yadda muka kawoshi jiyan.
Kwarai yanzu hakama mun fito wajen shine munso muzo mu dauki brother muje dashi saidai maigidan ki ya hana hakan don bamu san halinda zamu sameshi a ciki ba lokacin yasa muka tafi bada shi ba.
Alhamdullahi gaskiya yanzu ana son ya samu karfin jikinsa sai suyi masa aiki nan da sati daya mai zuwa don haka sai kun kara hakkuri ki fadawa mama zamu shigo mu gaida ita kinsan angon naki shi baisan duk wanan abin ba.
Sai an koya masa amma zan rarasheshi muzo muyi sarakuta mu kara kwantar mata da hankali don nasan tana cikin damuwa a yanzu sosai halin dataga baba din ciki.
Amma kuma naji muryanki kamar baki cikin dadin rai a yanzu me yake damun ki ina dai ba wanan zancen bane ya saki hakan kuma ?
Magana nake sonyi a lokacin na kasa na rasa wazan fadawa damuwana naji sanyi maman saudiyace sai gwaggona sune abokan shawarana a baya yanzu kuma maman saudiya din ta dauki zafi dani naba gaira ba dalili don ni bansan abinda nayi mata ba take fushi dani haka.
Mun dai gama magana ban iya bashi amsa komai ba sai cewa danayi ba komai a lokacin shi kuma ya kyaleni hakana bai kara tambayana ba kuma.
Da yamma din kuwa misalin karfe takwas da wani abu na dare suna gidan namu saidai dashi da oga Yusuf ne wanan karon sukazo suka gaisa da mama da ya Ahmed tare da muna bayanin cigaban da jikin baba din ya samu yanzu.
Ina daki don a ciki na wuni kwance ban fito ba duk zuwan da yaya keyi yana tambayana ko wani abune ke damuna karshe inavjin mama na fadin.
Kayi ka gaji indai Bantu ne yanzu haka ta koma zaman daki baya taba damunta ko gobe za akai ga hakan yace nasani mama amma dole in binciki lafiyan kanwata ai.
Gidan ma haka take kamar mai gudun yan uwa ko yaushe a dakin nan zata wuni a cikinsa bata fita ko ina inba fitan ya kamata ba shi kuma yana zargin duk yadda akayi naji hiransu da mamane wanda baiso hakan ba gaskiya.
Shigowan su oga Abbas yasa na fito ina saye da rigar shan iska ta gida na cotton na matan kasan Indonesia mai dan mayafi kamar gyalen fashiminer na danyi rolling kadan don kinsan rigan baida hannu armless ce rigan dinkinshi.
A madina muka sayoshi nidasu Salima wani fita da mikayi na sayo ja da fari guda biyu don naga kowansu ya saya da yawa nima na dauki biyu a lokacin.
Gashi yanzu yai min rana sosai ina jin dadin sakashi sosai abinda zan tuna nake zargi yanzu a raina shine yadda Abbu yakan bamu kudi idan yazo don gaskiya a gun Abbu da yayansa ba karamin alheri na samu zamana dasu ba.
A lokacin hjy takan nunawa Abbu bata son hakan da farko yake bamu kudi masu yawa yace mu sayi abinda ran mu yake so amma daga bayan nan tunda akai wanan taron nasu danaje don shi sai naga abubuwa sun caza don tun wanan lokacin zaman mu da maman saudiya ya fara samun rauni.
Na rasa meya kawo muna hakan don niba iya sanina gaskiya ina gujewa bacin ran mutum idab ina tare dashi don na koyi hakan tun a gidan Anty Safiya mariganyiya.
Sai gashi kuma kare rikice abin shine fadana da Mohammad sai kuma sayen sarkan da nayi tun wanan lokacin gaba daya hjy ta sauya min har yakai yanzu bata daukan wayana idan nakira.
Nima a karshe na hakkura na daina kiranta tun bayan bayanin da iya tayi min kuma na gwada kiranta taki dauka nawa kaina salama da ita ga baki daya kuma nasha alwashi na barta ke nan har abada insha Allahu.
Don dama suke moriyana fiye dani don da kudi za,a dinga biyana dole zaifi alherin da take min din duk da cewa kuwa a sanadinta na sauke falari abinda ban taba kawowa a rayuwana nan kusa ba.
Yanzun kan nagama yarda da zancen boss din mu cewa su din mutane masu son kansu da yawa halinsu zai baiyana kanshi a gareni shi nake yawan tunawa idan zancen hjy ya fado min a raina.
Na dauka dashi sukazo gidan namu saidai dana fitone sai na samu su biyune ashe sukazo din muka gaisa yaci gaba da muna bayanin aikin da za aiwa baba din wanda yace shine yake haifar mashi da matsala a yanzu.
Ya Ahmed ne ya fara magana don yanzu tsoron furta wani abu nakeyi kuma kada sanadin hakan mama ta janyo min barnan suna ga yan uwa da yan gari yasa nake bin komai a sannu yanzu.
Bayan sun kare zasu tafine muka rakasu nida ya Ahmed a wajene yakw min bayanin cewa Boss yayi tafiya zuwa kasan Hong Kong da yamman nan mukai masa Allah ya tsare.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
6?? 4??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Kwana hudu tsakani muka hade dasu asibiti wajen duba baba gaskiya mutanen nan sun man kokari sosai don gaskiya bazance ga dalilinsu ba nayin hakan garemu.
Tunda bani kadai bace mai bukata a duniya ai saidai nafi aje abin da Allahne ya jefosu a rayuwan mu don su tallafa muna da alherinsu saidai daga baya kuma na kula bamu kadai yakewa hakan ba ashe don ranan na gaskanta hakan .
Saboda bai bar asibiti ba saida ya shiga kamar daki uku yana gaida mutane ya dan dade kamar namu daga baya nake ji wurin wanan nurse cewa duk shine ya dauki nauyin aikinsu ashe a nan saina gane hakan wani hikima nasane ashe na tallafawa mai bukata ashe na kasa dashi.
Zasu tafine muna zaune ya kallo inda nake karona farko da tun zuwan mu yabada lokacinsa gareni yana fadi cikin saurin maganan nan nasa da ke ya kamata ki koma school hakana fa.
Tunda ga mama ga brother sun isa su duba baba ki koma makaranta ki facing din studies dinki hakana ko a turo wani kuma ki koma ya fada in a serious voice irin na tsawatawa gana kasa dakai.
Kai kawai na gyada masa ba tare danayi magana ba ya kuya gun baba ya duka yana dan magana dashi mu dai munga baba din yayi murmushin karfin hali a fuskanshi haka yasa.
Dole na koma makaranta saidai ban bar Abuja ba saida Nura yazo naje na tarosa muka dawo masaukin mu tare dashi tun a hanya nayi mai duk bayanin da nakeso dashi.
Yazo washe gari ni kuma na taso zaria na nufa kai tsaye don karatuna washegari na fada school naci gaba da daukan lectures kamar yadda aka saba din.
Ban dawowa gidan sai yamma lis idan na dawo kuma ina dakina ba irin yadda na saba fitowa mu dan taba hira da gwaggo ba yanzu gaba daya nakoma wata shiru shiru haka dani ko yaushe.
Har akai sati haka yau ba zan fita ba sai shadaya amma ina daki ban fito ba hakan yasa gwaggo zuwa kofana ta dan tsaya daga kofa tana fadin niko yar nan ko lafiya kuwa ?
Tunda kika dawo gaba daya kin canza kina daure min jin hakan yasa na taso da sauri ina fadin lah gwaggo ba hakana bane kinsan yanzu muna matakin karshe ga karatu banda lokaci sosai a yanzu.
Shikan ko dan nan Aliyu yayi wanan zancen jiyan nan na sake fadin ba hakana bane gwaggo ni dai kawai na rasa meke min dadi a zuciyana kawai ga kuma karatu.
Nazata dai wani abune kike boye min ai nace a,a gwaggo babu komai wallahi ta juya tana fadin yanzun ne tsegumi baida kadan a wajen yan adam.
Ina komawa daki tana fadin ki fito ki samu abinda zakici a cikinki na amsa da to kafin na fito na dauki bucket don in debo ruwa in watsawa jikina ga kaina yana son gyara a lokacin don yana damuna da kaikayi tsufa sosai nakeji.
Don haka nake son zuwa saloon daga school ban dade a bayin ba don tsufansa a gurguje nakan watsa ruwa in fito ina shafa mai wayata tayi kara da sauri na duba.
Sunan salima nagani hakan yasani dan sake murmushi kadan don tunda muka dawo saudiya bamu hadu ba har wanan lokacin na dauki wayan ina receiving tare da fadin hajjaju ta katseni da fadin.
Na gane dai nice na kula dake Fatima ke ba ruwanki da kiran mutane dan dariya nayi ina fadin wallahi ba hakana bane kinsan bana cikin hankalina na fada maki matsalan mahaifin mu ai.
Ta tuna tayi min ya mai jikin nace da sauki yana Abuja asibiti yanzu haka aiki za ayi masa wai nan dai nake dan bata labari a kansa din.
Ya tausaya tana muna fatan samun lafiyansa kafin yace wai kinsan abinda yasa na kiraki a yanzu ma kuwa ina dariya nace sai kin fada hajjaju.
Tace bari kedai wani zance nakeji kinsan kishiyar mamana taje saudiya ita tadawo tana min wani tambaya a kanki wanda ya ban mamaki don nasan da gaskene dakin fada min gaskiya.
A rude nake fadin aka mefa Salima tace ni zancen ma na jisa wani iri don hankali baya daukansa gaskiya wai kinje kina son ki kwace mata Abbuh duk zance ya taso tunda kikaje saudiya dake Abbuh yake mata kwatance.
Zuwan ki bataji dadinsa ba sam ga uncle shima ya nuna yana sonki zai watsa mata kasa a ido yabar zancen yar kawarta da akai masu baiko da ita aure ya rage a yanzu .
Ke in gajerce maki dai hjy bata fadi wani alherim ki ba koni ga wanan matar gaba daya bata mu tayi a wajen ta tas har sata ta dafa muna kan muna diban mata kudi mu sai abu dashi.
Innalillahi na ambata lokaci guda nace ta dauki alhakina da mijinta kuwa don ni banda gaisuwa wani abu bai taba hadani da mijinta a bayan idanunta ba sai wanan don kamar uba nake kallonsa a idanuna.
Kawai ki kyale wanan mace kinji Fatima ita kawai burinta shine ta ganka kullun a kasan ta kacin arzikinta basu kaunar suga wani ya taso zai fisu a rayuwan su shine matsalan kinsan yayan gidan saurata da jin kai da basu son suga dan tallaka nason zartasu kawai.
Duk yadda akayi a wajen taron nan nasune ta hadu da shakiyan matan da suka zugata suka hura mata kunne akanki har ta yarda da hakan.
Don na samesu falo a ranan cikin wani yanayi tabbas a lokacin aka kitsa hakan a kanki don in ba karya zuciyana ta ban ba naji lokacin da hjy laila datazo daga Riyadh take fadin wanan ai sakacine babba a zamanin nan baka hada komai da mace ba ka daukota haka ka tsoma a cikin iyalinka tana abinda taga dama, don batan basira kome har zaki yarda da hakan.
Kalman kai na ambata ina dora hannu daya akaina na shafo har zuwa fuskana ina jin wani zafi a zuciyana lokaci guda kafin nace Salima ki bari kawai zan kiraki an jima nagode na kashe wayan ga baki daya lokaci guda da fadin hakan.
Kai jama,a meyasa duniya ta koma hakane wai yanzu shi tallaka ba mutuncine dashi ba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login