Showing 207001 words to 210000 words out of 347556 words

Chapter 70 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8785

kai ladidi asibiti a duba hannunta muji kome ke nan.
Sai lokacin uwar tace aiko angode ga hannun yarinya nason sa barkwanci gashi ba kudi a hannun mu wacan ma da taimakon Allah aka samu aka dorata sai gashi ashe dorin baiyi ba kuma.
Zamuje muji me zasu fada insunyi bayani duk a binda ke nan zamu dawo ayi shawara a kai daga hakan muka fita zuwa asibitin nayi arziki isah mai shago yana masalaci bai ganmu ba.
Munje anyi photon hannu dorin ya gwauce don haka sain an canza wani abinda za,a bayar dubu ashirin da biyar sai magani da zamu saya haka nayi kundunbalam biya sukace gobe tunda safe za,azo ayi aikin.
Da zamu dawo gida na dan sayo mata abubuwan karin jini dasu kayan tea gida na kawota na koma da dan keken kasuwa na sayo masu kayan abinci don nasan dama abincin su ya kare a lokacin.
Mun dawo gidane nasamu su yan biyu sun dawo gidan suma ban tsaya ba na koma ya kaini muka sayo masu icce har gawayin girki komai nasaya sai yamma lis nashigo gida.
Wanan aiko malam ke gari a tsaya nan yaushe rabon daya sayo muna cefanema haka saidai idan itace tayo muna hakan tun tasowanta din nan.
Nidai ina jin su saiga hassana take fadi sis ashe kinzo muna zaune fa nace muzo gida asheko gara da muka dawo din nace wallahi Abuja zan tafi in dubosu shine nace barin dan biyo ta gida inga lafiyan ku sai gashi kuma na samu ladidi ta karye ashe.
Maman ta fito nan nake masu bayanin komai tama rasa me zatace sai mama uwace me fadin Samira kan taji kunya idan ta sanshi ki aiko kudi akai kanwarki asibiti kice wai baki dasu.
Ina jin hakan na mike na daga wajen don nasan yanzune tana iya sakin layi nagama ganovhalin mama uwa wajen tsokana tana sake magana wanda banson hakan harga Allah.
Sis yaushe zaki dawo idan kin tafi na juyo ina fadin bai wuce two days ba don muna karatu ba hutu aka samu ba wallahi da ina da kudin mota zamu biki muje muga baba .
Nace gaskiya yadace kan aje a dubashi su mama ma naso hakan da akai masa aikin nan suje su dubashi koda wunine ayi a dawo yanzu kuma ga zancen hannun nan na ladidi.
Ai wallahi kamar kin shiga zuciyana kinga hakan Bintu mama uwa ta fada daga can inda suke indon Amirace ai sai nakaita barnawa gun yaya ta zauna dasu acan.
Tausayi mama uwa din tabani don nasan alakan boye dake tsakaninsu da baba a yanzu ko dan kudinsa a asirce yake bata ta ajemasa akwai wani abu na daban da namiji ke samu a cikin iyalinsa ko iyayye su samu a tsakanin yayan su don za a samu wanda yafi kwanta masu a zuciya su yarda dashi dari bisa dari bisa ga sauran yan uwa.
Wanan kalar halakance tsakanin baba da mama uwa a yadda na fahinta a yanzu don ko magana nazo mai dashi baya shakar fada a gabanta kamar sauran.
Wanan yasa na danyi guntun nazari kafin nace to mama idan mun tafi dake ita kuma mama Lanto fa sai naji tace to Bantu ya na iya wanan yar rawan kan taja min tagumin dare a daki yanzu.
Gobe din idan muje a duba hannun idan baida matsala ai sai atafi har ita din zaifi don barin ta a nan ko gun wani zai zama matsala inyaso sai su yaran su Adamu su kula da gida.
Na dade banji godiya akaina daga bakin mama Lanto irin wanan ba don ko lokacin bukin Samira da tasan munyi tsaye nida ya Ahmed anyi bukin wani kallon gani gani take min.
Amma sai gashi a yau kan zancen zuwa abuja ne ko zancen ladidi tana min godiyan a gaban kowa na nuna jin dadin hakan da nayi mata a kaina dakin na karasa shiga kwanciya nayi don nagaji dayawa kan sintirin da nasha ranan.
Washe gari ko kafin na fito har mama taga shiri ni take jira tare da hassana da yanzu tafi Usaina shige min don Usaina bata zama gida sosai wai tana koyon dinki ne tace min.
Munje anyi dorin na asibiti an bata magani bamu dade ba aka sallamomu tare da maguguna da zatayi amfani dashi hakan yasa muka dawo gida mama tana ta nuna jin dadin ta ga hakan.
Bamu taso a ranan ba sai washegari don hannun ladido din wanan driver nayiwa waya yazo ya daukemu zuwa Abuja asibiti muka dira munyi sa,a suna cikin asibitin tare da baba sai ganin mu sukayi kwatsam munyo tafiyan tafi da gidan ka gaba daya mu biyar sai ladidi da kanwarta diya mazan mun barsu gida.
Alhamdullahi don muna shigowa dakin baba muka fara hangowa zaune saman kujera saidai ya rame sai farin geme da suka watso mashi a fuska.
Da fara,a afuskanshi yake muna alaman sannun mu da zuwa ta hanyan hada hannayesa wuri daya yana hadasu fuskanshi dauke da murmushin jin dadin ganin mu a hakan.
Mamako sai dagowa tayi tace a,a dama wai kuna hanyane tafe bamu da labari aida bakuzo ba haka tunda yaji sauki a bari a sallamomu mudawo gida zaifi.
Zuwan mu ai ba wani mukazo gani ba sai mijin mu ba abinda zamu kara masa danan da can sai sannu da Allah ya karo lafiya gara dai da mukazo din muka gani hankalin mu yafi kwanciya.
Aiya kwanta dada tunda kunzo din ganin abinda akeyi a nan din kada a kwaraiku zuwan mu duba jikin malam kuma laifine yanzu daga zuwan mu ashe indon ta kece ba zamuzo ba.
Mama Lanto ta fada tana karasawa gaban baba tana fadin malam ya jikin naka kuma Allah ya mayar dashi zakkan jiki ansha jinya Allah yayi afuwa ya bada lafiya mai amfani.
Muna tsaye mudai muna kallonsu kafin na nisa Nura ya juyo yana kus kus yace naji dadin zuwan nan dasu da kikayi wlh na dade ina tunanen hakan saidai ba yadda zanyine yanzu bari kigani zata fashe haushin hakan a kanki .
Bari dai musamu lokaci akwai magana aiba yau zaki koma ba ko nace sai zuwa jibi zan komani su mama daine an bar gida ba kowa sai yara da yau zasu koma amma yanzun kuma sai gobe kila.
Hakan yayi kyau wallahi ya fada kodana juyo mam idon ta na akan mu wani kallon banza ta watsa muna na kawar da kai muryan ta naji tana fadin.
Ke Bantu kinsan zakuzo kikaki kira a waya mu sani laifin aiduk nakine dakin kira aida an tanadar maku abinda zakuci ban samu bata amsa ba naji Hassana tace mama kamar dai baki farin ciki da zuwan nan namu fa haba dai don Allah .
Mu aiba abinci ya kawomu ba munzo ganin jikin babane mu juya Usaina ta karbe da fadin nidai shina gani da shigowan mu an taremu da fada kuma.
Baba ya mikawa ladidi hannu ta tako zuwa inda yake yana tambaya meya sameta kuma nan mama uwa suke mayar mashi da yadda akayi.
Ido ya lumshe kafin ya kawar da kai gefe daya Allah kadai yasan abinda yake ji a lokacin shigowan ya Ahmed daya sayo masu take away ya gamu abin ya bashi mamaki sosai yace.
Ikon Allah ashe kuna hanya sannuku da zuwa muka amsa mai muna gaidashi yace Allah ya baku ikon tasowa amma kan kunyo sammako ?
Karfe bakwai duk mun bar gida muna hanya don mu iso akan lokaci mama uwa ke fada mai yace sai kuka samu baba a zaune baba kan ai Alhamdullahi gaskiya in jikin ya dore haka kilama a sallame mu nan bada dadewa ba.
Ya Ahmed ya Abuja ya kuma jinya don duk sunyi kyau sun murje baka cewa jinya sukeyi a lokacin yadda suka koma fresh dasu din nan yace.
Kai Abuja sai mutanen cikin ta ai koma ka taba garin nan kudine gaskiya ana harka a garin nan ni in badon an mun dariya ba ai tuni dana kafa teburin kayan fruits a gaban asibitin nan.
Dariya aka kwashe dashi lokacin mama tace kai miko min nan in karya ni kada kaja min ciwo abincine jeloup mai kyau dashi sai soyayyan nama manyan yanka gudu biyu sama.
Haka mama ta bude abinta zata soma ci lokacin nace ya Ahmed Nura in ganku mana ina fita daga dakin tambayansu nayi abincin nawa zai ishemu sukace sai kamar na dubu biyar jakka na bude na mikawa nura kudi nace ka hado muna da ruwa.
Nuran ya tafi na juya wurin ya Ahmed daidai lokacin su Usaina suka fito suma nan yake bamu labarin yadda akai aikin na baba yana fadin bari Bantu mutanen nan sun kashe kudi ba kadan ba wallahi akan mu.
Yanzu haka ko a gida muna da kayan girki mai yawa yauma don bamu tsaya mun karya bane don ranan da suke bari a dan zauna da mara lafiyane yau da gobe yasa mukayo sammakonzu nan.
Idan su mama sun karya zamu gida mu kai yarinyar nan ta dan kwanta don kada jikin nata yai mata tsami da yawa yace Allah sarki ainayi mamakin ganin ku harda ita.
Tau kasan halin Bantu ai nasan tana gudun ta bar uwar a can kuma ya zama laifi a gareta kasan halin gidan namu ai ga mama ma yanzu da zuwan mu saida sukaso kwasa dasu.
Ya kwalo ido waje tare da fadin saboda Allah dai usaina tace wallahi yaya kasan halin mama ai wai cewa tayi me kuma sukazo yi tunda yaji sauki don Allah ka duba min.
Yanzuma fa fitowan nan abinci tasa a gaba tanaci batayiwa kowa tayibba shine muka fito muyi gulma don Allah ka duba min fa.
Da sauri yace kai haba dai don Allah aidako yaran anbawa namu tunda ga wani can an aika a sayo masu ni sai yanzu nagane hikimar bantu din na saurin aikawa.
A,toh tasan abinda za a iya ai ita yasa ta aika muna wajen Nura ya dawo da ledoji har drink's ya hado dashi da ruwa muka shiga gaba dayan mu nace a bawa kowa yaci don mun fito gida ba wanda ya karya acikin mu .
Sai lokacin nasamu daman karasawa wajen baba na duka ina gaidashi y amsa ya dan lumshe ido yana kada kai saiga hawaye suna zubo mashi baba hawaye kuma na fada cikin rikicewa.
Lokacin hankalin kowa ya dawo garemu suma hankalin sune ya tashi nan sukayo kanshi ana fadin malam lafiya kuwa wani abinne kuma yake damunka ?
Kai ya dan girgiza yana nuna alaman ba komai da hannuwanshi ya mayar da kai saman kujeran da yake zaune akai malam wai lafiya?
Bamu taba ganinsa haka ba ai sai yau na fada maku dama kun zauna gida zaifi haba mama wanan wai wani irin magana kike fada haka sumafa suna da hakki a kansa na zuwa su dubashi.
Kukan baba ba akan zuwansu yake kuka ba akan Bantuce da take kokari haka da kowa ai baiyi kuka ba saida taje gabansa a yanzu ni nasan tausayinta yasashi wanan kukan a yanzu.
Kai baba ya kada alaman ehh haka dinne ohh to batu yafi karfin mu ashe maganan zuci yakewa hawaye sai kowa ya kama kansa yanzu kan.
Tsugunne nakai nace baba koma meye kabar kuka don Allah kabarwa Allah komai shi zai muna maganin damuwan mu insha Allah.
Bayan gama cin abincin muka bi driver ya kaimu gidan masaukin su ba laifi ana dan gyaran gidan saidai ba yadda ya kamata ba don haka kafin masu dawo mun gyara ko ina har zanin gado mun wanke don yayi dauda .
Na sallami driver akan inya shigo zaizo ya kwashesu su koma sam ran mama baiyi dadi ba na kira Oga Abbas ina sheda mai zuwan mu tare da yan gidan mu yace zasu shigo su gaisa dasu.


ZAINAB IDRIS MAKAWA


KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
6?? 6??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Labarin da Nura ke fada min ya girgizani a lokacin yadda akayi har mama ta samu ganin Boss ta fidda mashi damuwan dake tare a zuciyan ta a kaina.
Duk da dai shima Nura din bai tabbatar ba zargi yakeyi akaina ta kebe dashi sukai magana don yace bayan ya shigo ya gaida babane da zai fita ta bisu a baya ta dakatar dasu sai sukai magana.
Ni dai nasha jinin jikina cewa zancenkine tayi masu ko wani abu dai don tun ranan idan zasuzo a asibiti suke samun mu basu sake zuwa gidan nan ba kuma tun wanan ranan.
Aikin tane hakan bata wani a wajen wani don ni tasha yimun haka din a waje da yawa tun ina karama kaga don ance tayi hakan ai ba zanji mamaki ba a yanzu.
Ni lamarin mama mamaki yake bani murmushi nayi nan dai yaci gaba da bani hiran abubuwan da suka faru a bayana wanda bada abinda zan iya yi a yanzu fatana kawai Allah yabawa baba lafiya shine kawai a gabana yanzu.
Ashema shi Nura bai sani ba don asali shi boss din baya cikinsu yayi tafiya tun lokacin bai kasan Oga Abbasne sukewa daukan cewa shine Boss din namu.
Bamu koma asibitin ba dasu don haka muka dan shiga gari yawo dasu Usaina suka jani zuwa Sahad store muka danyo sayayya zamu dawo muka biya asibitin muka dawo tare dasu mama gidan lokacin.
Sunyi mamakin ganin gida haka dankarere waisu kadai ke zama a cikinsa don jinyan baba mai baki ba,a tsokanan shi akace aiko mama uwa nan tahau saman bakinta tace a lalai kuwa.
Dole yaya kice hakan ashe jinya mai kama da sakata akeyi a nan ke nan mutum kan na wanan gidan haka lafiya lau babu takura ina zaiso wasu suzo kuma.
To uwa nidai na fadi maganan nan bada wata manufa ba don naga kina kokari ki mayar da abin wano zance na daban kuma .
In mada wani manufa kika fada ai yaya damu dake bori daya mukewa tsafi dukkan mu don mujin mu mukazo nan din wace kuma kowan mu kecin arzikin ta naga dai itace ta kwaso mu zuwa nan.
A falon muke zaune gaba dayan mu don haka nace don Allah mama kubar wanan zancen kada yayi nisa maganan ai ya wuce tunda bada wata manufa ta fadi hakan ba.
Ashina gani itama mamane da zancen ta dai don me zata fada masu haka naga ai itama don baba take wajen nan su ance kada su zo don Allah hakan gaskiya bai dace ba.
In ma hakane aike mama uwa har mu ke nan yayansa ta fadawa hakan baki kadai ba son Allah ku bar wanan zance haka ya wuce.
Ance duniya me yayi shiru mama tayi ta kasa magana duk da nasan zata iya fada amma ina ganin bayan fitan mu ya Ahmed yayi mata magana kan haka.
Daki daya su mama zasu zauna dayan kuma da da muke kwana da mama mu da mama din zamu sauka a cikinsa don dakin yafi sauran dakunan gidan girma.
Basu shigo ba don suna falo zaune ana hira lokacin ni kadaice a dakin ina shirin kwanciya naji wayata dake ajiye gefe tayi kara yasa na duba Oga Abbas ne a layin na sake wani murmushi koba komai sun daga min darajata da kima a idon yan gkdanmu da wanan alherun da sukai min kawai don martabata a yanzu ba karamin karuwa yayi ba garesu daga yara har manya kuwa.
Na dauki waya naji yana cewa amaryan Boss dolene mukawo gaisuwan ban girma a gareki tunda Boss baya kasan kece babba yanzu ai.
Haba yayana kanwarka kake zolaya haka kuma kada kasa hutsun boss din namu ya kara tsanata mana gashi ance baison a dangantashi da mace saidai ku maza.
La la la lah a ina kikaji wanan zance kuma kanwa nace zancen duniya ai baya boyuwa yanzu saidai ba ayisa ba akwai magana ke nan a bakinki nace a,a wlh babu komai iya abinda dai naji ke nan na fada.
Yanzu dai ki bari mayi wanan zancen dake gamu a kofan gida nida Yusuf munzo mu gaida mata fiya kada miyi laifin rashin zuwa a wajen oga mu kara laifi.
Aiku na hannun damansane baku taba laifi a wajen sa saidai mu kananan kwari da munyi za,ace an dakatar damu daga aiki sai naji ya kwashe da dariya yana fadin baki da dama wallahi kanwa.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login