Showing 228001 words to 231000 words out of 347556 words

Chapter 77 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8723

duk akan kunnena sai daga baya nake godewa Allah da banfita ba.
Don ko sun kwasa dasu Hassana a dakinsu, sun nuna mata ta daina hakan gareni don su kan basuga abinda nayiwa mama da kullun take magana akanshi ba saboda haka ta daina zuga mama don Allah tana abinda ba daidai kullun.
Tayi kansu da zagi da cin mutunci inda take shiga ba nan take fita ba hassana ta fara fita dakin Usaina ta biyota a daki suka sameni kowacensu ranta a bace.
Na yarda dan Adam shike kona kansa wallahi ka dauki sherin duniya ka lakawa dan uwanka musulmi don kawai hassada da bakin ciki kawai da kasa a zuciyarka.
Don kawai Allah yayi mutum da kashin arziki saika dauki sherin duniya kabishi dashi abinda wasu keyi aiko kare baya ja ba gara bin maza din bama da bin bokaye.
Sai lokacin nayi magana nake fadin duk ba gara a cikinsa Allah ya rabamu da ko wanensa tunda ubangiji ya hanemu da aikatasu duka Allah kuma ya shirya duk mai irin wanan rayuwan tunda karshensa bai kyau gameshi.
Ba haka samira ba haka kawai ta dauki sheri ta dora a zuciyar ta tana dauka kowa a matsayin makiyi a gareta ko ta dauka tafi wanine yanzu aigata can ana gasa mata kwakwa a hannu.
Ba dadi har da saki tun ba,aje ko ina ba wai akan bata da tarbiya dan gidan nan za,akirawa rashin tarbiya dame yaran gidan nasu suka fimu ?.
A,a wanan tsakanin miji da matane kuma nasan halin ya habibi saiya zageta fiya da hakan kuma suna zaune kalau wani irin zagine baiwa Anty safiya waji waya san anyi ?
Ita dai inba zata zauna ta tsare aurenta ba ta zauna taita tsegumi in akwai wanda zai mata maganin hakan ita tace taji zata iya don haka ta zauna tayi hakkuri kawai ba yawan tsegumi ba.
Ni na auna arziki da mama ta tashi hadani dashi duk zugin maman tudun wadane da Anty Altine lokacin da naki bakiga irin bangan da sukai min ba lokacin ban ma son mu hadu dake amma ke ko a jikin ki.
Kinsan Allah ban taba jinson ya habibi a rayuwata ba don da baba ya biye masa dana gudu naje neman mahaifiyata a wanan lokacin abinda na yanke ke nan zanyi a lokacin.
Ashe Allah ya gyara nace babba kuwa ke bari kawai yanzu nake tuna wani abu wanan mutumin a barshi kawai ta dauka wani jan duniyace a gidansa baida dadi ko kadan wallahi.
Kai nayi zaton hakan wallahi amma nayi shiru don kawar da zancen nace banga su Jamal ba tunda na dawo wani jamal gidan nan ai sun bar zuwa tun lokacin da akai wani fitina kakarsu ta hanasu shigowa gidan nan.
Jamal da yanzu ko a hanya muka hadu sai yai wani dauke kai kamar bai ganmu ba nasan yasha dukan tsiya a wajen hjy yasa yake hakan nace haba dai ?
Zanje gidan in gani ai saidai keba, keda baki gudun zuciya nikan banga abinda zai kaini gidan nan ba kuma yanzu bandai rantse ba amma kan gaskiya ban san lokaci ba .
Muryan mama tudun wadace suke sallama dasu mama ni har na manta da cewa tana gidan lokacin lokacin da Usaina kewa hassananta rada ga mama can ta gama zata wuce.
Naji mama uwa na fadin aiko tayi mulki daidaine tunda babu shedan arziki akanta gareki yaya ballema suna ciki dasu hassana tundazun suna hirane.
Koda ta fita sun dade da mama a kofan gida don har na shafa ta raka mama a lokacin nasha tana dakinta tana wani abin don har yanzu duk da gyaran arzikin da gidan namu ya samu bai hanasu zaman tsakar gida ba ana saka ido.
Can sai ga mama din ta shigo lokacin ina kofan dakina zaune ina kallonsu suna harkokinsu da yaransu hassana tana daga cikin dakin itama kanta ta kofa ta kwanta muna hira jefi jefi daga inda nake zaune.
Wai sai yanzu kika shigo dama nina zata ai kina dakinki kwancene tundazun lalai kam hira yayi dadi rakiya har gidanta ke nan.
Kai mama uwa akwai daukan magana wana yasa bata iya zaman daki tana waje koda yaushe wanan dalilin yasa na dan jaye mata kadan duk da kirkin dake tsakanin mu kuwa amma nakan boye mata wani abin nawa dole duk da nasan ba zatayi zancena da kowa ba.
Ana sallah karfe hudu na shirya zuwa gaidasu hjy binta gidansu ya habibi a kofan gida na samu Alh zaune muka gaisa yake fada min ai baba ya fada masa nadawo daga bautan kasa.
Yayi min fatan alheri na shiga cikin gidan don ingaidasu hjyn ina sallama muka hade da hjyn data fito bakin famfonsu take fadin a,a,a Bintuce yau gidan namu dan murmushi nayi har kasa nakai ina gaisheta kafin hjy balaraba ta fito tana fadin Bintuce yau gidan namu ?
Jiyan nan Alh ke fada muna dawowan ki dama nace aikina tafe gidan nan don ba zaki biyewa zancen shirmem mutanen gidan ku ba ke kan .
Muka gaisa suke tambayana ya na baro wajen su Mahmoud nace wai rabona dasu tun zuwana garin dana sauka gidansu amma gaskiya ban koma ba tun wanan lokacin.
Jam keko dai ana gari guda haka baki lekasu kuma nace akwai nisa sosai da inda nakene kuma ga aiki bamu da hutu ko yaushe cikin aiki muke daga safe har yamma.
Aina fada bata zuwa gidan nan indai Bintace ko zuwan farkon ai yazama kamar dolene agareta da koshi ba zataje ba ai Jamilace ta rugumeni ta baya hakan yasa na juyo naga itace nan hankalina ya koma akan yarinyar da yanzu kamaninta ke juyewa yana zama na mahaifiyarta.
Mun kwasa munyi dakin hjy da yaran nan na zauna har magariba muna hira da ita kafin naci abinci nayi batun zuwa gida.
Koda na fito ban fita ba na shiga dakin hjy Balaraba nan ma na dan zauna muna hira da ita can tace dani Binta ina tausayin ki wallahi yadda Allah yayi maki baiwan nan amma ba mahaifiyar ki a kusa yanzu.
Nuriya ta tafi ta tabarwa makiyanta ya suna cin arzikinta a yanzu jin hakan yasa na mayar da hankalina gun hjy din tace inna tuna wanan nakanji bakin ciki a raina nan da Somalia in har can ta koma yaci ace ta dan waiwayeki a yanzu.
Duk da bansa zata tafi can ba don a yadda ta nuna min an kashe kowa nara a lokacin yakin da yunwa daya biyo baya a kasan lokacin yakinsu na basasa da akayi a kasan lokacin ne dayawansu suka ketaro zuwa wanan kasan.
Kina da kamani yanzu sosai da mahafiyar ki Binta saidai kin dan darata ma kyawo sosaima amma duk komai naki na Nuratu kika kwaso baki kama da yaran gidan ku kaf.
Uwa uba halin nan naki duk natane haka Nuratu take da son mutane ga halin kirki abinta bai rufe mata ido ba kamar dai ke din nan a yanzu a haka duk ta shiga ran mutane unguwar nan duk da bamu da yawa a lokacin amma tana hurdan arziki dasu.
Haka yasa matan gidanku a lokacin hade mata kai koda yake na dolene don suna tsoron maman biyu dolene mace ta bita kobatawa Allah idan ta shigo gidanku da sunan aure.
Rashin samun hakan ga Nuratu din ya kawo fitana a tsakaninsu don sam bata yarda da sai wanda ita maman biyun take hurda dashi dole kuma shi zakubi ke bari maman biyu tayi mulki sosai a gidan nan naku abaya.
Yanzu gashi kamar ba,ayi ba yazama labari haka ta hade kan yan uwan miji dana matan gidanku akaiwa boyan Allah nan koran kare abin dai ba kyau don kowa yasan aikin asirine haka barin Nuratu gidan nan.
Yadda mahaifin ku ya rufe ido yace saita bar masa gida kan dan abu kadan daya hadata da maman biyu kawai ya rufe ido yai mata tonon asiri alhalin yasan da babu inda zata tafi tawagansu sun koma kasansu an samu zaman lafiya a lokacin.
Nidai wuri biyu na saka a raina data bar kaduna can ta tafi shine Geshuwa don akwai yar uwarsu da itama tayi aure a nan sai ko Saudiya da tace akwai dan uwansu a can daya rage ubansu daya dama shi yana can yana karatuneshi.
A can nake sa rai da cewa zata tafi amma nayi mamakin yadda bata waigoki ba har yau din nan tasan da kinkai munzalin aure a yanzu abin yana ban mamaki.
Bata kula da hawayen dake zuba min ba a lokacin sai labari take ban saida nace cikin muryan kuka hjy ko kinsan gidan da zan nema idan naje geshuwa din ?
Ai kuka kuma kikeyi Nuratu wai bintu harkin sa na kiraki da sunan uwarki nan da kike ganina ni aminiyar uwarkice sosai saboda maman biyu na jayewa lamarin ki yanzu kuma dole in fada maki don na fahinci babu mai niyar fada maki hakan.
Ban taso ba saida nayi kuka sosai hjy tana faman bani hakkuri sai tara saura naje gida da mama na fara cin karo wai a lokacin take rabon abincin dare na gidan namu.
Kanta babu dankwali tana daure da gaba babu riga a jikinta hasken wutan Nepa ya hasaka kanta da kitso ya dankare mata yafi wata bakwai kila a kanta baka ko ganin tsagan kitson a lokacin wai a haka girki takeyi kuma.
Sai muryanta ke tashi tana kiran yaran gidan mu akan suzo su dauki abinci zuwa dakunan su tana ganina tace yawa Bantu ga naki nan ta dangwaro min shi zuwa gababa nima a wullakance nace akarawa wasu a koshe nake ina tafiya ban tsaya ba zuwa dakina.
A lokacin wani kallon tsana da kinjini mm akewa mama din gaba daya ganintama banso a idanuna muryata ina jinsa kamar zuban ruwan zafi a kunnuwana saboda tsanar da nake ji nata a lokacin.
Bandai tsaya inji me take fada ba na shige daki raina bace kuka yanzu ba nawa bane don haka dole in shirya zuwa geshuwa bakina alaikum ko Allah zaisa mu dace ko dai wani haskene in samo acan din gashi banma san ko a wani jaha garin yake ba ina dai jin sunan garin jefi jefi a wajen mutane.
Yau wanan zuwa gidansu hjy din yai min dadi sosai a raina don na samu wani haske da zai ban kwarin gwiwan zuwa neman inda mahaifiyata take ko wasu yan uwa nata.
Da wanan abin na kwana a raina zancen mu da hjy balaraba don har na,aje wani sati zan shiga geshuwa neman mahaifiyata duk da bansan inda zan dosa ba a lokacin amma zan matsa in sani inshiga garin ko Allah zaisa in dace.
Duk da haushin mama da nake ji ban nunawa kowa hakanba don ashe da gaskiyan hausawa da suke karin magana suce ko lahira wani nacin albarkacin wani.
Don ko mama taci albarkacin yayan ta dake manne dani a yanzu zakice basune manya a gareni ba don ko yaushe muna dakin muna hira ko muna kallo a wayan wata daga cikin mu.
A cikin hakan na samu lamban hjy balaraba son gudun zargi a kanta don nasan tsoron da takeji ke nan ace itace ta fada min har na tafi.
Allah ya taimakeni kuwa ta kwatantamin gidan da kuma sunan dan uwan mahaifiyata Nuratu dake saudiya din duk na karba a wajen ta bancewa baba komai kan tafiyana saidai ina shirina a cikin siri lokacin.
Ana kwana biyu in tafi wanda na yanke zan fadawa baba cewa bukin wata classmate zan tafi a geshuwa don ba zan boye masa garin da zani ba don gudun ta baci.
Muna kwance ne a dakina barci ke son daukan mu wayata tayi kara dagani sai Hassana son ita ba ma,abuciyar fita bace irinace tana gida ko yaushe sai in fitan ya kamata dole.
Ina dauka naga oga Abbas a layin cikin kulawa na dauka muka gaisa yake fadin wai har yanzu kina fatakwal din ne sister naji ki shiru ?
A,a yayana ina kaduna tun last week ai gashi har ina sonyin tafiya zuwa jibin nan insha Allah haba dai da izimin wa zakiyi tafiya brother ke nan sai kace wata macen aure can ?
Wama zan tambaya din kai yayana ko yace me kike nufi da alkawarin baba a kanki wani baba ke nan na tambaya sai naji yace subbahanallahi kada dai kice min zuwan kin nan Fatakwal kin koyo butulcine ?
Kamar ya butulci kuma yace gashi kina son yanzu ki nuna baki sanda zancen da nake nufi ba kefa kinsan yanzu a matsayin matar wani kike don an bamuke mun kuma karba da hannu bibiyu dan haka kibi a hankali don kadan ya rage mu sayaki a gida yanzu.
Bansan wanan zancen ba don haka kada ka tsoratani a yanzu ya wajen aiki na dawo na samu abin alherin da akaiwa baba ubangiji ya saka da Alherinsa bai bani amsa ba sai cewa yayi.
Bar wanan zancen mu koma kan maganan mu ta farko dake wai wani zancene baki sani ba kada ki bata min rai kisa muyi fada dake yanzun nan ajimu.
A,a brother aikai yayanane ba zaka so kayi fada da yar kanwarki ba mun kusa idan kina irin zancen nan gaskiya wani gari zaki kuma ya tambaya ?
Geshuwa zani na basa amsa sai naji yana fadin don Allah bani two minus ina zuwa zanyi magana da wani zankiraki hakan yasa na kashe wayan da sauri ina sauke ajiyan zuciya.
Muryan hassana dake bayana ke fadin Geshuwa ina jin sunan garin nan kuwa amma bansan a wani jaha yake ba idan ba dadewa zakiyi ba zanso na biki ta fada da sauri nace.
Wani takarda zanje nema a can in garin ba nisa wata kilama a ranan zan dawo insha Allahu a,a to gaskiya ba zan biki ba kada inje inta tsayuwa a can .
Naji dadin hakan dana fada mata tunda ta yarda da sauri don banson zuwa da kowa balle asan abinda ya kaini garin kuma ba zanso hakan ba don wanan sirinane ni kadai tunda niya shafa.
Nida basan ko siffan uwata ba balle na karasa da wani abu nata iya kwatance ne nawa kawai a yanzu don haka ba zanso naje da kowa ba wurin neman labarin nata.
Haka kawai tun safiya na shirya dan leka iya inji ko tana gidan hjy har lokacin saidai idan tana gidan zansa mai gadin gidan yayi min sallama da itane tafito mu gaisa ba zan shiga cikin gidan ba don tsohuwar batayi min komai ba.
Fita nayi kamar ba wani waje zani ba don banson kowa ya biyoni dole yanzu in dinga rufe sirina ga kowa don gaba ba kuma zanso asan akwai rikici na sabanin hankali ba tsakani da hjy a cikin gidan mu ba don haka na fita ni kadai kamar iyakata wajen isa a lokacin.
Nayi sa,a kuwa ba kowa na taka a kafa zuwa sama inda gidan yake a nan farkon layin mu akwaidai dan tafiya duk da yanzu unguwar ya cika sosai wasu gidajema bansan da anyisu ba tunda ban faye zama garin ba yanzu.
Gidan na rufe yadda yake kullun a zatona babu kowa don haka na dan tsaya ina shawara ko in komane kada in jawowa kaina matsala tunda banga abinda ya kawoni ba.
Bayan da nasan kashedin da hjy tayiwa Iya din a kaina yanzu banda gulma da rashin wayau meya kawoni gidan hjy din na tambayi kaina.
Najuya zan komane naji kamar an bude kofan gidan hakan yasa na juyo don inga ko waye zai fito ko zai shiga maigadin gidan ne ya fito yana dan dube dube a kofan ganin shi yasa na dawo baya ina gaidashi ya amsa saidai kamar bai shedani ba lokacin.
Nace baba ko iya mai aikin gidan nan tana ciki ya kara kallona da kyau kafin yace dani wai halan ke bakuwace dai ai iya ta bar gidan nan da dadewa nima na dawo ke nan abin ya faru.
Cikin mamaki bace tabar gidan nan kuma ina ta koma yanzu yace tana can kasan layin nan kadan can suka kama gidan haya ita da jikokinta da suka dawo wajenta sanadiyar mutuwar yar iya din babba data kare.
Inna lillahi na fada na danyi shiru kafin muryanshi ya dawo dani yace wai ko hjy Fati ce na dan sake murmushi nace ai naga baka ganeni ba tun dazun yace tunane nake ina nasan fuskarki a baya?
Kai kinga ko kwanakin baya wanan Alh karami na gidan nan yazo kasan nan yasa inyo mashi cigiyar ki ko kina gari nace Allah sarki wanne daga cikinsu ?
Yace wanan da suke kira da Uncle yazo garin nan ya kwana biyu naje har wurin iya din tambayan ki tace dani ai baki kasan nan wai kina kasan ibo wajen bautan kasa.
Gaskiya yaso ya ganki sosai amma iya tace dani kadama in nemoki in barki kawai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login