Showing 273001 words to 276000 words out of 347556 words

Chapter 92 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8750

mai kudi mu kuma talalka ko ?
Yadda baba ya haramta min shigowa sha,anin ki haka nima diyana ba zakiga kowa wurin sha,aninki ba insha Allahu don,,,,,,
Altine wanan shirmen banza kikeyi wallahi abinda ya kamata ki fuskanta yakamata kiyi a matsayinki na babba a gidan nan kinzo kina wanan shirmen a yanzu har rayuka na batun baci da farar safiyan nan.
Da kikaji ai sai ki tambaya a fada maki dalilin hakan don kema kinsan Bintu ba zata taba yin haka ga kowa ba kai tsaye amma kinzo kina aibanta ta kina wa mutane habaici kai tsaye kin nuna ke ,,,,,
Daga kofa baba ya sharbe zancen mama uwa din da fadin kinsan ta haifi mutane ai dole tazo ta nunawa mutane ita mai zuciyacevga issasa da wuyanta yai kauri a yanzu .
Mama Lanto ta karba malam don Allah abar zancen nan Bintu dai ta fadi abinda take nufi sai a fahinci juna ai Mardiya bata fita cikin sha,anin gidan nan tunda yar gida take itama
Nikan jin zance yanata tsawo yasa na juya na koma dakina don nasan dama hakan zai faru dolene tayi fada akan mardiya din donsu ba abin kunya bane fadan diya a wajensu.
Don haka na kafe akan duk wanda zai mun magana ba zan saka mardiya din cikin lamarina ba don ko banza ita din mun dan fita a shekaru .
Gadan gadan aka fara shirin buki kamar yadda fanin amarya ke gudanar da tsarinsu fiyema dana iyayye haka nake kallon su hassana da kullun cikin tsara yadda abubuwa zai gudana wajen buki suke.
Yan mata su gomane cur zuwa lokaci suna da number junansu ana communicate a tsakanin su kan komai har anko sun fitar suyi komai da sukeso nan nabada shawara a sayowa yan matasan yan matan nasu anko tunda kudin ya saura suma sunci arzikin da jinini da komai hassana taje kasuwa ta zabo masu wani zani mai kyau Green da dan adon brown din zanem ganye zanin ya hadu gaskiya ba laifi.
Dawowanta ke nan daga unguwa takaiwa wata kawarta ziyara tana kokari cire kayan jikinta wayanta ya dauki ringing ta dauka tana dubawa.
Ummu kina da labarin auren mamanki kuwa tambayan daya fara mata ke nan a lokacin ita kuma ta tambayeshi da wace mamata ke nan ?
Yace Fatima dai ta kaduna mana Bantu don ta gane tace fatima OK fatima dai aure zatayine yace kwarai kuwa don ta turo min da kati dazun nan zatayi aure.
Ayyah nayi mata murna ni yanzu na raba kaina da ire iren wa yan nam yaran a yanzu yaro karami ya shigema jiki yana maka wayau akan abinda baka zataba a kansa.
Fatima din mama ni nakan rasa wani irin abu tayi maki haka kike kiramata cin amana Ummu Al,amin nina haifeka kokai ka haifenine ?
Yarinyar nan ta dalilin waka santane ina ta dalilina haka kawai kai baka mamakin yadda tashige muna a jiki lokaci guda haka idan ba don hjy Laila data fadakar dani ba .
Don,ni na shagala da hakan don ban taba kawo cewa zata iya muna sheri ba ko wani abu sai gashi dana kwantar da hankali ina nazarinta zancen Laila yana fitowa fili.
Yanzu Ummu zancen wanan matar zakibi matar da duniya bata bar kowa ba inba kanta ba Ummu Abbu fa ya rabaki da sherin wanan matar ashe har yanzu kuna tare da ita .
Wanan fa ba komai bane a cikin halinta illa sheri kin sani Ummu ni wallahi na dauka wani abin na daban mara dadi Fatima tayi maki kika tsaneta haka.
Ummu matar nan kinsan halinta don me magananta zaiyi tasiri a zuciyarki kan yarinyat nan yanzu dai baki tambayeni ba don ni wallahi kwana bibiyu muna gaisawa da ita cikin mutunci har gobe kuma ko shawara take dashi tana nemana in bata shawara.
Kwanakima da zata wurin mahaifiyarta saida ta fada min na bata shawaran yadda zatayi da ace yarinyar nan da yaudara ko wani ha,inci take bin mu da ko sau daya ta nuna hakan.
Katse dan nata tayi tana fadin barin ma kashedi idan har baka rabu da yarinyar nan ba duk abinda tayima na ha,inci kada kace ta dalilina kasanta.
Yarinyar nan dai na fahinci gaskiya a yanzu dama hjy Laila ta fada min cikin biyun daya dai takeso dani ta asirceni ta shige min jiki haka ta karata can ni aurenta bai shafeni ba.
Kuma kaji kashedin da nayi maka kan yarinyar nan watau gani mai kudin banza zatayi aure ta fadama don ka tursasani gaba in samu abinda nayi mata to kwandala bazan bayar ba aje abi wani sarkin kuma yanzu.
Ummu kina ta fadan nan baki ko tambayi wa zata aura ba kowa zata aura ba sai fada kikeyi haka katseshi tayi da fadin ni meya shafeni da lamarinta a yanzu tunda ba hadin iya dana baba tsakanin mu.
Idan bakaji ba kaika sani bancewa ka rabu da ita idan ta kwaso talaicinta ta dora ma wanan kai ya shafa wanan yar me shegen wayau siya ta lafe kamar wata saliha da ita yar iska.
Ta kashe wayan ya tsaya yana mamakin irin shu,umancin hjy laila da har tayi galaba haka tsakanin hjy da Fadima yarinyar da take matukar so da tausayawa yau kuma ya kare tana kiranta da munanan kalamai haka.
Yaso ya fada mata komai amma yanzu din nan yadda ta hau din nan ba zata saurareshi ba kan zancen don haka yaja bakin shi yayi shuru don ta kula kiyayyar yayi yawa a yanzu.
Itako hjy din tsuki taja tana fadin haka kawai ka kirani akan zancen banza Laila tayi gaskiya akan yarinyar nan taje can ta karata cikin talaucin su na tsiya masu taja tsuki tana lumshe idanuwanta.
A gaskiya ita kanta banda zancen hjy Laila da take gani gaskiyane hakan na iya faruwa bazatace yarinyar ga abinda tai mata ba iya mutuntawa da daraja tana bata duk ko da sakin fuskan dake tsakanin su baisa ta taba yi mata ba daidai ba a rayuwa.
A yanzun kan gaskiya bata jin cewa zata iya taimakawa Fatima don tasan tana bukatan taimako kuma ga matsayin da take dashi wurin iyayyen yarinyar amma bata jin zata iya mata wani abu yanzu.
Batama son wani halaka kuma ya kara hadasu ko nan gaba don haka dole koshi Al,amin din ta kara ja masa kunne a kanta ya rabu da yar tallakawan nan gashi tasan kafin taje Nageria bukin Bashir da Abbu ya matsa masu zuwa lokacin an riga da anyi nata ko kuma ba,ayi ba tukun balle azo a dameta da maula na yan Nageria da zasu haifi diya akarshe kuma su kasa daukan dawainiyarsu sai a kama yawon maula ana neman mafita da yayan.
Kayan da aka aiko daga iyayyen ango acewarsu waina amare ya fara tsonewa kowa ido a unguwar nan aka dauki zance fa .
Kullun Ammi saka min ranan zuwa take amma tace ta fasa sai wani lokaci hakan yasa na karkare figewa nakoma yar karama sai hancina daya kara fitowa zaran tun daga nesa manyan idanuwana suka kara ba fuskan fasali don idan na kalleka zaki gansu farere sol dasu.
Damu yana saka jikin dan adam wani yanayi wani lokacin damuwa ya kara kiba wani kuma ya kara kyau wani ko yafige baida dadin gani haka dai abin yake ga dan adam dama.
Idan nace raina bai baci ba nayi karya don har gashi ana batun sakani lalai Ammi ko wani nata baizo ba wanan yasa nake kuka tun ina boyewa har na fitar a fili gashi idan na kira su maryama basu daukan wayana suma yanzu.
Ba irin mamaki da tunanen da banyi ba kan haka me Ammi take nufi danine wai dama shigo shigo ba zurfi tayi min ta dawo dani gida don kawai ta rabu dani.
Har ta tsayar min da mijin aure ta kuma tabbatar dana yarda da tsarinta a kaina don ban musa mataba kan abinda ta bukaceni dashi din.
Don me kuma yanzu zata nuna min hakanweb ta bar min abin fade ga mutane ko yar wayan nan sai ta bugo min muji dalilinta asan me za,a fada ga mama tun safe nake jin tana yadda magana a tsakar gida wai tanayi da Amira dake fadin zataje unguwar Dosa ai mata kumshi.
Sai mama Uwan ke fadin kya bari dai ai har a saka lalai ki tafi ace duk babu inda zaki tsaya kiyi kumshi sai kin tafi unguwar Dosa ni banda kudin da zan baki har zuwa can.
Sai naji mama tace ina ruwan gandoki muje buje buki yar kalan dangin karya gamu gani dai in karya na karko duk nan bai maki ba sai kin muna kale kalen wasu can wai yan uwa yanzu kan aji kunya idan an santa .
Don mungaji da gafara sa bamuga kaho ba gidan nan rana bata karya saidai uwar diyan tayi kunya ke nan mudai a gamu gani daki bata kudin mashin din muga iya karyan da za,a zano mata a kafan nata mana mu dai yan kallon karyane ai dama raminta kurarene.
Duk Amira keda wanan dogon sharhin haka mama uwa ta tambaya tace a wanda yace a bashi gari aisai a mikar mai a gani sai naji mama uwa tace Allah ya kyauta nikan nayi nan badani ba wanan zance mukan muga alherin nan da muke gani kullun.
Daga dakinta naji muryan hassana na kiranta tana fadin mama fa naji ta amsa rai a bace da meye ke kuma tace ki zo mana zaki kuma tsaya a can kuma naji ta yunkura ta tashi zuwa dakin.
Ba,afi minti kamar uku ba mama Lanto ta shigo min da kosaina da kunu na karin safe tana fadin Bintu ga abin karyawa ki bandai zuba maki da yawa ba naga bakya sha ko an cika kofin.
Na dago ina fadin nagode mama ina kwana ta amsa da lafiya antashi lafiya ko murya yasa ta fahinci nayi kuka a lokacin har ta juya zata fita sai kuma ta tsaya tana fadin.
Bintu a binda nake so dake shine hakkuri don Allah hakkurin nan da kika saba kiyishi ko yanzu kada ki nuna damuwa ga komai ki barwa Allah komai shi zai maki jagoran komai insha Allahu kamar yadda ko yaushe kike ganin haske a lamarin ki.
Kada ki saka zancen wanan dattijuwar banzan cikin lissafinki don ita ko yaushe burinta taga kowa a cikin matsala daga ita har babban banzan ku Altine halinsu daya da uwar nata.
Masu daman ke nan su yan biyu saiko marigayiya Safiya da Allah yaiwa rasuwa baya dasu kan gaskiya Allah ya kyauta ko kadan kada zancen ta ya bata maki shiri in Allah ya yarda sai taga har abinda zuciyar ta bai bata ba a kanki gidan nan.
Ballema ta gani rashin godiyan Allah ne kawai irin nata ni tsakanina da yaya sai Allah ya isa kawai bancewa komai yarone ka haifeshi baka haifi halinsa ba Bintu.
Amma yaya duk ita tayi ta hade hade lokacin a tsakanin mu saita koma daga baya kamar bata san komai ba don haka kinga jama,a za a tara gidan nan donke kuma ki gyagije ki fito ayi komai yadda ya dace ance ba,a maraya sai raggo.
Idan taga kin gyagije kina sha,anin ki zakiga kuma ta koma zaman daka saboda balin ciki a karshe sai ta takalo jidalin daya bata maki rai kuma.
Nasan yaya sarai kin sani don haka kada kibi ta nata don Allah kiyi wanka ki fito ku fara sha,anin ku zakice na fada maki dama kin taimaka min Bintu lokacin da ake son ganin kunyata don haka insha Allahu alkwari nayiwa Allah duk abinda za ace ko ayi min ba zan kara yarda shedan ya shiga tsakanina dake ba a rayuwan mu balle wani mutum can .
Don Allah ki yafe muna duk abinda ya faru a baya tsakanin mu wallahi zugine na gane gaskiyan akan komai kiwa Allah ki yafe muna wanan abin kada ki tafi dani a zuciyanki saiga hawaye a idanuwanta bar da sauri nace subbahanallahi mama a kaina kike kuka kuma mama.
Don Allah ki bari kada wani yaji ya dauka wani abune har gobe ni banda uwayen da suka wuce min ku a duniya kece ta farkon fiddani a cikin maraici gidan nan don haka ni ban manta halarcin mutum a kaina mama wallahi na yafe ni ban rike kowa a zuciyana ba dama don hakan baida kyau.
Ta amsa da nasani Bintu kuma na sheda hakan baki kuma daukan zuga duk ni shedan hakan ne gareki wallahi don Allah kiyi hakkuri.


ZAINAB IDRIS MAKAWA





KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
8?? 7??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI AUDIO.


Wanan abin daya faru tsakanina da mama Lanto ya zamo sanadiyar walwalana don na dan fahinci abubuwa a cikin zancenta wanda yake gaskiyane ta fada ba karya.
Hakan ya kara min kwarin gwiwa harna mike na watsa ruwa na fito a cikin shirina kujera naja na zauna a tsakar gida ina kiran hassana ta amsa ta fito .
Tun daga nisa tana hangoni take fadin dan kari wanan amaryan ko kina son sauki wanan shigar kamar wata amarya ranan daurin aureta fa ?
Ina Usaina ku fito muje hjy Zalihat Fashion express mu kai dinki don naga kamar har an taushe hannu bamu kai ba Usaina tace zancen dana gama ke nan jiya kema ashe kin kwana da zancen ke nan a ranki.
Dama yana raina abubuwane sukai min yawa amma bamu da matsalan hakan ai indai Fashion express ne ko yaushe akakai za,a samu insha Allahu.
Bari muje mu watsa ruwa saimu fito suka fada suna shigewa dakinsu hassana ta fara shiga don Usaina ta tsaya muna maganan shagon da ita a wajen da nake zaune din saiga mama uwa data fita ta dawo muka tsaya tana muna bayanin kayan cincin da taje ayi muna gidan yar sokoto mai dibila.
Hassana din na shiga daki mama take tambayanta ina zakune wai tace wani waje mama ta shige daki abinta bata tsaya ba saida muka gama maganan cincin din kafin ita Usaina ta shiga daki nasu.
Wai ina zakune ta tambayeta tace dinki zamu kai mama dinki wasu kaya zata dinka ta fito da kayan da suka boyene dama kayan yana garin nan ne ?
Haba haba mama wanan wani irin tambayane wai aisai kisa a zargi mutane maganan mu ba dole bane sai kin sani tunda abinda ya shafi yarane wanan .
Don Allah kada ki kara zancen kayan nan a gidan ga har wani yaji a zargeki akanshi tunda kinsan cikin bincike ake har yanzu bawai sun kyale abin bane
To uwata ki fara zargina a yanzu ma kinga sai ki fita ki fadawa mutane an kama barauniyan a gida yara haka baku san zafin kanku ba sai aukin cin mutunci ga manya bayan shi baku iya koma ba a rayuwa.
Ku sani Bantu ta gama daku ta wuce sanin ku duk abinda naso ku zama saidai tabi bayan ku yau Bantu ta zama shi har wanda ko mafalki ban taba yinsa ba balle tunanen hakan.
Allah ne ya bata mama muma ki muna fatan Allah ya bamu kwatankwacin nata din komai baikai nata ba Usaina dake debe rigan jikinta ta fada ta shige cikin dakin don tayi wanka.
Amma nasan maganin ku sai nayi karfan dana raba tsakanin ku da yarintar nan yanzu ma abinda zaku fada ke nan makin ku gano me nake nufi ina nufin saidai ku gani a wajanta ke nan fa amma kun kasa gane hakan.
Daku wasune mu taru mu hada kai a fasa auren nan ma ga baki daya bakin ciki ya kashe yar iska a rasa gane mata ga baki daya mu nuna mata cewa mun fita sanin hanyan databi ta samu mijin.
Nikan badani ba wana shawaran balleni hassana ta fada tana shafa mai a hankali naja baya na koma don muddin na shiga dakin nasan duk zasu tsargu danaji zancen su duk da ba laifinsu bane.
Allah ne ya turoni zuwa dakin nunawa Hassana din sakon da nagani a wayata har naji wanan zancen don ni ba gwanan shiga dakinsu bane har kilama gara sauran dakunan gidan nakan dan leka wani lokaci.
Amma na mama run ina karama data taba dora min sata nayi zuciya bani shiga duk da anga kudin a karshe amma dakin nata ya fita raina ga baki daya don duk yawan mu a lokacin ni kadai ta dafawa dauke mata kudinta.
Sai gashi yau ila ya kwasheni naje naji abinda ya tayar min da hankalina don zacenta gareni dai a fili ko a boye bana alheri bane don mama ji


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login