Showing 51001 words to 54000 words out of 347556 words

Chapter 18 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8819

ta kawo wuri muka zuzuba hakama kankara har an sayo an farfasawa kullun ayyah ko.
Karfe daya da wani abu mun gama komai Nura danta ya dauka muka tafi zuwa gidan hjy din tare da karaman yarta Basira get din gidan yana rufe kamar kullum don haka muka tsaya kwankwasa maigadi yazo ya bude muna.
Suna falo a zaune kamar yadda sukeyi kullun muka shigo da sallama Nura yana dauke da katon kullan kayan sanyi ni kuma na dauko na wara a hannuna.
Sallama mukayi muka shigo suka amsa min lokaci guda na gaidasu hjy din ke fadin mamata badai har aiki ya kammalu ba na danyi murmushi ina dire kayan a gabanta.
Kai wanan kan ai kila batayi barci ba fun jiya kinsan haka hjyn Daura ke kwana tana aiki kamar injin tsohuwar nan bata gajiya da aiki ko kadan ko yaushe ka falko zaka jita a tsakar gida tana sallah ko wani abin.
Mamata kin har kin karasa wanan aikin yanzu fa muke zancenki Aisha ke fadin saikin kawo zataci abincin rana shine suke mata sherin ashe zata zauna zaman jiranki kuwa don kila sai yamma ko dare.
Nan dai na fara budewa ina murmushi wanda aka kira da Aliyu cikinsu yace Uncle yana sama mami shiya kamata ya fara dandana test dinshi don dashi mukayi gardaman dadinsa.
Shi wanan din dukkansu basu wuce wasu yan awowi basu lalace ba inji dayan mai mata a cikinsu ya fada sai lokacin nayi magana nace.
Amma shi kunnun zai iya kai wasu kwanaki indai yana samun sanyi wandai ne zaiyi saurin lalace iyarkashi gobe yayi tsami baida matsala yar mami iyakanshi ai yau din nan su dai dandana suji.
Mama wancan shikafan ai yayi yawa kamar na buki don baku da yawa baifi a auna kwano biyu ba zuwa uku sai ta murmusa tana fadin to ai kyaba mutanen gida suci sauran idan yayi yawa.
Mama dawainiyar yayi yawa ai angode Allah ya umfana na fada ki daina min godiya don na baku alheri ina sane nai hakan .
Wanan uncle din ne ya sauko ya na tako a hankali duk suka juya gareshi suna fadin yauwa dama yanzu muke fadin a tasheka muci abin nan gashi nan an kawo.
Cikin wani daurewa yace wani kuma kusan halina ai ya kai zaune Aliyun ya taso ya bude masa sai kamshin suya dana yaji dasu albasa ya hade falon.
Nasma tashi ki dauko plates a kitchen ki zuzuba muna mamana ki bita a hado kofuna don shan kunnun uncle ya kamata ka gwada ci kaji .
No ya barshi mu kara don in yai min dadi kulan zan dauka na tafi sama dashi kai naso ace yau hjy babba na wurin nan da munji yabo tunkan muci zata fara yaba aikin me sunan kamar su sukafi kowa iya girki a duniyan nan.
Azuba min kodon kuji haushi tunda uwata kuke zagi a gabana haka kuma mai sunanta tayi wanko ya juyo yana kallon Aliyun da yai magana.
Muka fito da plate din da kofuna muka jera ganin yadda take zubawa din yasa na karba na dinga zuba abincin ina mika masu suna karba.
Shida mama na fara zubawa sai na dinga basu yadda mama tayi min bayanin girmansu duk suka zubo min ido suna kallon yadda nayi din.
Ina gamawa na mike ina fadin mama mu zamu tafi mun gode tana kai abu a baki tayi saurin fadin haba dai yanzun nan da shigowansu ko don kin gansune yau kika kasa zama ai dole tunda sun isheki da sherinsu.
Zan tafi na fara aikin wara kai mamana me zakuyi da kudin nan ne bakya hutu a rayuwanki an dawo weekend din ma ba zaki huta ba.
Ni dai murmushi nayi na fara tafiya ta kira kannena ta basu kudi alokacin bansan ko nawa bane ta basu tayi muna godiya muka fito.
Har mun fara hanya na tuna na aje dan post dina saman abu a kitchen hakan yasa na juya zuwa ciki ina fadin su jirani na dauko jakata na manta dashi a ciki.
Ina shiga na samu suna dariya wai wanan uncle din ya shanye gora ayyah yace su karo masa mamana lafiya ta tambaya na manta da jakata a kitchen na fada ayyah yi maza ki dauko abinki.
Nashiga na dauko nayi masu sallama ban tsaya ba na samu kannena suna murna wai ta basu dubu biyar nace kun gode.
Ban karbi ko kwabo ba har zamu shiga gida na tuna da zancen mama haka yasa nace dasu su shige zan tafi gidan su hjy in gaidasu .
Suka shiga gida da murna suna ihun sun samu kudi nakuma na kama hanya zuwa gidan hjy din ina shiga da jamal na fara haduwa ya sheko da gudu ya dane min jiki yana murna.
Nima rikeshi yaran suna ban tausayi sosai idan naga yadda suka koma yanzu hakan yasa idan nazo nakan dan basu kudi ko inyi masu sayaya wani lokacin.
Wanan yasa idan sun gani sai suji dadi suna murnan shigowa gashi yanzu tunda suka girma din nan sundaina shigowa gidan mu yadda suke shigowa a baya.
Su hjy din suna waje muka gaisa sukai min ya karatu zainab ta fito tana fadin an fada maki mun kawo maku anko gidanku ?
Kai wanan yar da garajen tsiya kike baki bari har ta zauna kafin ki fara mata wanan zancen nina rasa irin rayuwan wanan yar don yayuyunki basuyi muna wanan rashin kunyar ba gskiya.
Dakin hjy laraba din muka shiga tare ta nuna min anko din har kala uku tana min bayani na fara tambayan kudinsu ta fada nace sai idan na dawo zan biya ko kafin na wuce.
Muka dan taba hira na fito zuwa dakin hjy mun dan dade muna hira wanda duk hiran yaran na anty safiyace jamal yazo ya manne min a jiki yace.
Anty Bantu takalma nakeso na school nan hjy ta fara dura mai zagin da har naji raina ya baci da zan tafi na dauko kudin da mama ta ban jiya na bas hjy din dubu uku hjy laraba dubu biyu na fice da yaran su uku na fita dasu don haka basu dawo gidaba sai wani lokaci don kasuwa naje dasu na kaso masu dan kudin dake guna.
Kodana koma gida yamma yayi sosai a lokacin ban iya fita wurin aikinaba a ranan don haka dan kwanta don in huta duk da yamma yi ko mama ta dauka cewa na fitane.
Sai naji tana fadin wanan gantallan ta fita ke nan ga abin magana mutum yana kallo ba dama kai magana ubanta yace ka azawa yarshi baki a cikin gida.
Ke mama ina ruwanki ki barta mana inta lalace ai ba yarki ta lalace ba banga abin magana ba a nan gaskiya hassana ta fada don tafi bakin rai dama ita.
Kai kunjiku da wani zance kuma duk kyau bintu fa har yau bata da saurayi saidai inka ganta haka ka dauka kamar wagilace amma bata yarda tayi nisa da mutum hussai ta fada.
Wazai sotama ai in bakuyi aure ba itama ko saurinyin bata taba yi saidai ku ganta a hakan kai ko kunyi aurenma ai ban tsamani zata taba aure koda tayima sai wullankantace irin ta badai abin kwarai ba.
Murmushi nayi daga inda nake dama mama uwa ta taba fada min wai na tashi tsaye mamafa tana jifana da asiri tun ina karama ta goga min bakin jini ga kowa nace Allah ya fita mama amsan danabawa mama uwa ke nan a lokacin.
Wayanane ya dauki kara Nura dan gwaggo ya kirani a waya na dauka muna magana akan karatun da zai fara shima nan suka gane cewa ina gidan ashe lokacin.
Shiru naji sunyi har lokacin dana gama wayan ba wanda yayi magana mikewa nayi na shiga bayina na dauko bucket na fito don in dibi ruwa.
Mamace kadai zaune a dan filin gidan namu tana tsintar shinkafa na dibiruwa nacicika roban ruwana na fito kuma na fice kofan gida nan muka hade da mama uwa wace dawowanta gidan ke nan daga wurin buki take fadin .
Binta dazun nayi jira ki dawo har na fita baki shigo ba eh mama daga nan da muka dawo naje ganin su jamal shine yaron ke mun korafin baida takalmin makaranta da littafai kullun ana dukanshi.
Shine na kwashesu zuwa kasuwa na saya masu duk abinda basu dashi sai yamma din nan na dawo gida nagaji sai yanzu nake son fita.
Bakin uban nasu daya kawosu nan ya watsar dasu kamar almajirai da bai iya kula dasu don yayi auren bariki ya manta da kowa yanzu.
Ai maganin munafukan uwar nasa ke nan data rike yaran ta hanawa kowa nan ta dauka don yaran zai dinga turo abin duniya a gidane dama tana rikewa gashi yanzu ya koma mata ciki.
Yara sun zama abin tausayi a cikin al,umma idan ka gansu sai kayi kamar ka zubar da hawaye a kansu ni tun ina tausayin su suma yan banza yanzu na daina akidarsu daya data ubansu da daka jawosu jiki sai su gudu.
Allah ya gani ni tun farko banso auren wanan bawan Allah da safiya ba abu daine in anfi karfinka sai idanu kawai amma tun farko nikan basu kwanta min ba gaskiya mamace daga inda take zaune take fadin wanan maganan.
Banda abinki yaya mutum ya isa ya hana abinda Allah ya kaddara akan bawansane dama rabon diyan nan biyu shine ya hadasu yanzu kuma wanda yafimu sonta ya dauki abinshi.
Mama barin duba su Auwalu a waje na fada ina fita daga gidan na barsu nan suna magana saidai zancen mama da yaran???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ta akaina ya tsaya min a zuciyana sosai don bansan me hakan data fada yake nufi ba akaina.
Na isa gidan hjy na samu a lokacin suke karin safe sukai min tayi nace na koshi duk yadda hjyn tayi dani inzo mu karya naki cin komai a gidan nace na koshi alhalin ban karya ba a lokacin babu komai a cikina.
Haka na nufi kitchen din na fara yanka ganyen da zanyi amfani dashi kafin can yan matan su shigo kitchen din suna fadin boyar Allah mun barki ke daya kina aikin ko ba komai nace dasu.
Dayan wace ba matan aure ba ta karbi yankan carbejin tanayi kamar yadda taga na yankasu da dan girma don kada ya narke min a cikin dahuwan.
Da farko na fara hada wuta kafin na koma hada kayan mijiya irin attarudu da dan tatasai kadan sai hanta dana yanka ritsi ritsi don yayi dadin tauna a bakin mutum .
A lokacin ruwan ya tausa na dauko farin shikafa na nuna masu tare da fada masu cewa na tankadeshi tun a gida don mai taushin dake ciki ya fita na bar gurguzun daya barzu din dashi zamuyi amfani.
Na dauko na zuba a cikin kyalen da nazo dashi na hada komai yadda akeyi na fara sulalashi muka rufe a lokacin ne mai auren take tambayana ko yaya na hada kunun zakin da na kawo masu jiya nan dai nayi masu bayani suka gamsu.
Duk bayanin nan da nake masu hankalina yana gun dahuwan shinkafan saida na bashi kamar minti ashirin na sauke na ganin yadda yake tururi yasa suka wani jada baya wai suna gudun zafi.
Dariya abin ya bani wai diya mace ce take tsoron zafin wutan girki ganyen da albasa da muka yanka na dauko na zuba tare da wanan dan hadin attarudun na zuba kamshi tare da magi yadda zai wadata sai dan gishiri kadan na fara motsawa suna kallo kafin na mayar saman wutan na rufe yadda tururin zai hashi da kyau na dan rage gudun gas din kada yayi mai yawa.
A lokacin na dauko mangyadan dana soya tare da dan yaji na aje akusa waike a ina kika iya girki hakane dan murmushi na sake kafin nace gaskiya wurin antyna dana zauna kafinta rasu na iya girki dana gama kuma na jona wani women center na kara koyon na zamani duk da na iya dama amma saboda sauyin zamani na kara koya a nan.
Muka gama na dauko kwanon dana tanada nazo na juye a jiki na zuba mai bayan na tambaya ko akwai wanda baison mai sosai a cikinsu sukace kowa naci.
Na hada nace angama nan suka dauki cibi suna dandanawa sai yabawa sukeyi muka juye a wani babban wormer abinci ni plate na dauka muka nufi falon muka samesu zaune kowa na harkan gabanshi.
To gashi na hada yar matashiyan budurwan tace dasu, lokaci daya duk suka kallomu inda muke tafe sai mama din tace kin hada mefa ?
Tadai hada Allah yasa ba kunje kun tsaya kuna hiranku a can ba makin kun tsaya ku mayar da hankali ku koya hankali kwance amma saiku tsaya kuna hira ita kuka bari da aikin ita kadai yanzu kuce kungama.
Jera plates din na shigayi don na kula sunfi sonci a kasa ba saman dinning ba don hakane na aje plate din a gabansu na wanan dan kwalisan ne na dora saman dan karamin table dake gefenshi.
Aka fara zubawa kamshi ya dauka ko ina a falon saida na kawo kansane ya dago ya dan kalleni ya fadin tnx kamar dole akasashi fadan hakan.
Na mike ina fadin mama ni zan tafi akwai aiki na bari a gida da zan karasa don gobe nakeson komawa insha Allahu.
Haba dai yar nan da ace mu turawa sai mu zargeki akan zaki halakamu ki dafa abinci ki zuba muna sai ki mike kice zaki tafi.
Mama na dan diba a cikin leda zan tafi dashi gida ai jam a leda kuma mamana haba dai ai kardai wanan kankaren da kika zuba kina nufin shine rabon ki mama na dauka zubarwa zatayi fa.
Kinga Aisha dauko plate kizo dashi ki diba mata kinji a, a mama wallahi ko naje dashi baci zanyi ba zan dai ba kanne wanan din ya isa.
Kuma idan na dauki kula mama zai mun wahala gobe in shigo dashi gidan nan don gobe nake son komawa zaria din insha Allahu.
Au tafiyan naki da safene sosai don wa yan nan zasu tafi zaria gobe sai su rage maki hanya zaki kai goma zuwa sha daya.
Nace eh mama to zasuzo su daukeki idan sun gama shiriritansu zan dai zo mama kada aga an daukeni a zarga min wata manufa ta daban a gida.
Tace hakanefa kuma mutane yanzu sheri baida wuya garesu sai ki zo nan din su daukeki ina ke dayace nace inaga nida sister nane saidai ban sani ba sai naje gidan .
Ok koma ku biyu din ne ai zaiyi maku don wanan dam shiriritan naji yana tsumulmulan zuwa tare dasu don shi ba gwanin yawo bane dama.
Na dai masu sallama na fito na barsu suna santin abincin kowa na fadin albarkacin bakinsa a wajen kan dambun su kuma matan suna fadin yadda nayi aikin a tsanake.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
[8/9, 10:27 PM] KYAUTA: KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
1?? 6??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,

YA ALLAH KA GAFARTAWA AISHA COROFEE YASA JINYAN DA TAYI NA SHEKARA SHIDDA DA OXYGEN A RAYUWANTA YA ZAMA KAFFARA A GARETA ALLAH KAJI KAN DUKKAN MUSULMAN DA SUKA KWANTA DAMA TUN ZAMANIN ANNABI ADAM HAR IZUWA YAU DIN YASA ANNABI YA ZAMO MAI CETO A GARESU MUDA MUKA RAGE UBANGIJI ALLAH KA BAMU IKON CIKAWA DA IMANI AMIN YA ALLAHU.


Karfe goma naga duk wani shirin da zanyi munyi sallama da baba tunda dare da safe kuma na koma muka kara sallama duk da baba yasan ina da yan canjin a wurina hakan bai hana ya dan ban abindake hannusa ba lokacin.
Tare da nasiha a gareni na Jan hankali bayan na barshi nayi godiya na koma dakina naji muryanshi yana kiran samira ta Dan jima a tare dashi kafin ta fito.
Nasan dai nasiha yayi mata a lokacin na kamun kai saida take dakinsu ta Dan jima kafin naji ta leko dakina tana fadin zaki kai yammane baki koma ba abinda ta fada ke nan tana nude labulen dakin nawa Wanda ya tsufa sosai don't dadewa koshi hjy mairo kakan su Jamal ta banshi lokacin da baba ya gyara min daki shine nake amfani dashi har wanan lokacin.
Jin abinda ta fadane yasa na dago na dan kalleta nace zuwa eleven zan wuce don na samu lift a gidan su hjy hajjara na fada masu mu biyine zamuyi tafiyan wata kila sunce ba matsala muzo.
Gaskiya zuwa lokacin ban gama shiri bani don akwai abinda zan tsaya karba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login