Showing 117001 words to 120000 words out of 347556 words

Chapter 40 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8737

Abuja ?
Fata na gari lamirine kijawa yar uwarki kunne ta daina hassada da fatan banza kan wani don karshe hassada hasarane.
Ni kinga irin wanan yasa kona ji abu ban fadawa kowa wanan ma don yadda najine hankalina ya tashi har na fito na fadi waje.
Bai kara tankata ba don ranshi da ya baci a lokacin hakan yasa ya kyalesu a nan suka dinga fita daya bayan daya lokacin mama uwa na kauye wajen buki ita.
Lokacin muna hanya zamu koma masauki gidan wanan da suka saukeni don ko hotel ba a saukeni sai gidan wanan ma,aikaciyan cikin iyalinta.
Ina kallon yadda suke son junansu daga mijin har matan da yayansu biyu suna gwadawa junan su kauna da kulawa wanan halin ya ban sha,awa sosai garesu.
Washegari na dauka danaje zasu sallamenine don haka na zauna nayi kwalliya na hade cikin dinkin atamfan super wax wanda akaiwa buje dariga dan ban faye amfani dashi ba saboda tsadanshi da kuma haduwan dinkin daga cikin kayan khariya da maman saudiya ta bani.
Kayan sun matukar karban jikina sosai na yafa gyalesu sai takalmana half shoes mai dan tsini kadan ba sosai ba turaren nan da soja ya sayo min na dan fesa a gyale da dan kasan rigan wurin yadin da akaiwa rigan kwaliya don ban yarda na fesa a jiki ba tunda turare na illa wa mata a jikin su.
Tun a gidan mai masaukina take yaba kwaliyana na ranan har muka zo ma,aikatan nasu na dauka da nazo zasu sallameni in samu in isa gida da wuri ashe ba hakana bane.
Don haka nayi ta yawon office office ina saka hannu kafin zuwa yamma a kirani office din Mr Abbas dake sama sai dana dan jira sakatariya ta shiga ta fada mai zuwa na ta dawo tace min in shiga.
Kodana shiga su uku na sama a office din zaune saidai kamar hira sukeyi ko wani magana biyun sun bada baya shi kuma yana facing din kofa yana ganin mai shigowa office din nasa.
Saidai dayan mutanen naga ya duka ya dora kanshi saman desk din Abbas din kamar yana barci ko yana cikin wani yanayi a lokacin.
Sallama na danyi cikin siririn murya ina fadin malam Abbas ina kwana ance na kawo ma wanan takardan na fada da hausa ina kokarin mika mashi takardan.
Jin zancen hausa yana tashi yasa naga mutumin nan dake duke ya dago kai ya dan dubeni da sauri irin ke koma daga ina haka wai ?
Sai kuma ya mayar da kan nasa yadda na sameshi da farko sai lokacin na kula ashe wayace a hannunshi yake duba sai dai wanan karon bai duba wayan ba kanshi ya dora saman hannayenshi ya duka akai.
Abbas dinne yace dashi Mr C*E*O wanan ce ambassador din mu da muka dauko daga A B U
zaria itace na nunama vedio ta dazun a cikin harshen hausa da kuma yaren fulatanci da tayi muna kokari ba tare da mun dauko wata ba ta daban kuma.
Still baiyi magana ba hakan yasa Abbas din fadin miko takardan na saka maki hannu a ciki kin gama wanan matakin farko zamu nemeki insha Allahu nan bada jimawa ba idan lokaci yayi.
Gobe akwai motar company da zata shiga kaduna ina ganin zaki bisu su saukeki a,,,, shiru yayi don hannun da mutumin ya daga mai kafin ya dago kai yana fadin.
Taya zaku sakata tabi wanan motar na kaya ka tada driver ya sauketa gida a bata kudin aiki biyu tunda aikin mutum biyu tayi maku haka kuma ku bata duk wani hakkinta har na masauki tunda natane hakkintane.
To amma Bashi,,,, shiru ya sakeyi yana fadin shike nan ki kara signing a nan ki sauraremu mun gode da daman da kika bamu sai mun kara haduwa a wani karon nan ba da dadewa ba.
Na rasa wanda zanwa godiya a cikinsu sai in kalli wanan in kalli wancan lokaci daya kuma na juya ina fadin nagode da daman ku gareni Allah ya bamu alheri.
Na juya na fice daga office din suka bini da kallo yarinyar tana da kamun kai nayi mamaki data amince da wanan tayin namu a cikin sauki haka.
Yar talakawace fa komai zata iya indai zata samu kudin kula da kanta wanda baiyi magana ba tun shigowana sai bayan tafiyata yake wanan maganan.
Haba dai Yusuf ku fa kukaiwa yarinyar nan tayi aikin nan ba wai itace ta nema ba gareku da ace taki ba zakuji dadi hakan ba idan taki karban tayin ku don alherin da kuke ganin kun mata.
Ina mamakin mutane wani lokaci mu sanman kai Yusuf kai a zaton ka wanan yarinya tazo nan don kudine ko don wani abu ina warning dinga kan saurin yiwa mutum fassaran banza wani lokaci wanan halinkane .
In kunyi wanan tunanen kunyiwa zuciyar ku karya professor ya gaya min cewa saida yaga iyayyen yarinyar nan kafin su yarda tazo nan don ya dauka da sanina kukaje nemota.
Amma kuma yanzu kuna son ku fadi wani magana mara dadi akanta why why ai kuna sister meyasa baku dauko cikinsu suyi wanan abin ba sai ita ?
Kai Abbas shiyasa na baka warning cewa a samu wani family house a ajeta a gidan saboda tsaro ku yanzu kun fadi haka me kuma sauran mutane yan gari zasu fada ke nan a kanta ?
Tazo nan ne ta rama halarcinta garemu ba son abin duniya da kake magana ba koma meye kai Abbas ka sani kasan bana son hakan gaduk wanda zai bada gudumarwashi a company nin nan.
Shiru gaba dayan su sukayi don sun san yanzu zai iya zama masu matsala ya mike yana fadin.
Idan ka fito ka saukeni kaina ya matsa min da ciwo hutu nake son in samu na dan lokaci ya fada yana mikewa tsaye da sauri suma suka tashi suna mara mashi baya zuwa kofa kafin ya juyo yace wa Abbas din ina waje.
Koda ya sauko daga sama zaune ya hangoni na hada tafukan hannuna na dora fuskana sama kamar ina wani tunane ina jin ma,aikatan dake shawagi wurin suna gaidashi cikin girmamawa hakan bai kawo in sauke hannuna in gaidashi ba.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
3?? 6??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Zaune nake ina tunane na dora hannayena a fuska soja da bai kirani ba har zan koma gida don tunda mukai waya na fada mai inda zantafi da abinda zanje yi .
Mukayi dan tagadama dashi a karshe dayace saidai idan shi zai kaini nace ban yarda ba shine yayi fushi ya kashe wayan har nazo bai kirani ba gashi har zan koma ba kiranshi.
Haka yasa nake tunanen dama wani irin so sojana yake min ne zai zo gari musha hira yazo min da abin arziki donshi kyautan shi na bajintane ko yaushe.
Don in yazo hira kowa na gidan dama mutanen unguwa zasu sheda hakan don yan unguwa zasuga tsaro haka kuma wanda rabo ya ratsawa zai samu alheri a wurinsa haka kawai.
Musanman tsofi da yara har almajirai zaita basu dari biyu manya kuma dubu biyu wanda hakan ba karamin girma yajawa gidan gwaggon mu ba yanzu a layin don haka har dakon zuwansa akeyi ana tambaya yaushene zaizo ?
Koda yazo din kuma hiran duk barkwancine a cikinsa da zolaya har ya tafi ya barni ina mamakin ace sojoji basa dariya ga wanan shi ke saka mutum yin dariyan kuma ?
Ina cikin wanan tunanenne naji wani kamshi ya daki hancina tare da nauyin mutum ya tsaya a kaina lokacin hakan yasa na dago a hakali na fara tozali da takalman shi zuwa fuskanshi .
Hakan yasa da sauri na dan zabura ina gyara zamana ganin yadda mutane suka tsaya mashi a baya hakan ya kara tabbatar min da zargi a kansa cewa shi wani babbane a wajen.
Mikewa nayi tsaye da sauri na dukar da kai ina fadin sannu saida ya dan kalleni yace cikin harshen turancin any problem da sauri na girgiza kai .
Kin zauna kamar kina tunanen wani abu ko wurin bai maki bane ya fada yana tsureni da ido na yara na kara yi masa na kada kai ya fara tafiya yana fadin na biyoshi.
Na dan juya ba wani fuskan sani dana sani a wajen sai Mr Abbas dana hango yana saukowa daga matakala a lokacin shi zan iya cewa na dan waye da fuskanshi kaf a wanan wajen.
Tashi nayi hamar mara gaskiya nabi bayanshi har zuwa wurin da ake aje motocin ma,aikatan company idan sun shigo.
Tun kan ya isa ya danna remote motan ta dan kara kyau tana kawo danja wutan baya ta inda nake iya hangowa yana kaiwa ya bude ya shiga wurin mazaunin driver lokacin Abbas ya iso yana fadin iam sorry sir na tsaya dan bayani kafin infito da hausa yake masa wanan magana.
Baiyi magana ba sai nuna mai ya shiga motan da yayi ya taka zuwa dayan bangaren ya bude motan zai shiga ni dai ina tsaye a wurin naga ya dakata shiga ya bude dayan bayan yace min shigo muje.
Gabana na faduwa na dan dago kai na kalleshi tare da dan tunane kafin na taka zuwa inda ya bude din na shiga ya tayar da motan ya bar wurin kai tsaye.
Motan tsit ba wanda yai magana a cikinsu ina baya zaune sai binsu nakeyi da kallo tare da tunane kala kala a zuciyata lokaci guda.
Zamu sauketa tayi sayyaya kafin ka kaini gida naga kamar tana cikin damuwa lokacin naga Abbas din ya dan juyo yana kallona amma ai bamu bata kudinta ba sai gobe kudin zai iya fita.
Nan ma bai bada amsa ba bai kuma kara kallon Abbas din ba sai yaci gaba da kallon gabansa bai tsaya ko ina ba sai wani waje hadade nina dauka gidane k????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? o wani company a wajen.
Ashe shagone da iri mai sama da kasa da ake sayar da abubuwan bukata ga matune irin kayan masa rufi nau,in na turawa kayan shayi ,tufafi dinkaku kayan yara kayan kwaliya da sauransu gashina iya kallon mutum komai na bukatan rayuwa an baza a wajen.
Abbas ka fita kuje tare ina nan ina jiran ku ya fada komai take so ta dauka kada ka hanata ke kuma duk abinda yayi maki ko nawane ki dauka karbi katina kasan password dinsa ai.
Ya karba ya bude min motan yana fadin in fito muje ciki idan na fada maki duk abin nan ban san dani yake ba asalima bana jin abinda yake fada sosai dom haka na dauka badani yake magana ba lokacin.
Sai da naga Abbas ya bude motan yace min zo mu shiga mu fito na dan kallesu gaba dayan su kai ya gyada min alaman eh kuje na yunkura na bude motan har mun fara tafiya ya kira Abbas din yayi mai magana.
Tare muka zagaya shi Abbas din shiya fara daukan min kaya duk wani abinda yagani ya bashi sha,awa zai dauka kamar da gaiya yake daukan komai haka na dinga binshi zukai zukai ko ina yabi don wani abu ma bansan meye a cikinsa ba.
Da zai biya kudinne kuma naga ya koma gefe yana magana sai naga ya koma ciki hangoshi nayi tafe da dan trolley din mata mai launin pink y biya kidin komai muka fito zuwa motansu.
Idan muka samu wanan ogan ya kayar da kujeran mota ya dan kwanta aciki ya sake AC saida ya kwansa mai motan ta bude ya daga mai boot din motan aka loda kayan .
Muka zagaya muka shiga ina ta sake sake a kasan zuciyana don sai ina ganin kamar yaudarana suke sonyi alokacin.
Nidai gashi Allah yayi min farin jinin samun alherin maza sosai fiye da tsamanin maj karatu amma ko yaushe sai inga sallon yaudarane kawai hakan.
Don Allah ya hore min tunda na dan tasa din nan duk wani wanda zan hadu dashi ba ranke ranke bane gashi kuma ba wani dogon friendship nake dasu ba amma ina samun alheri a hannayensu sosai.
Wanda mutane zasu dauka cewa wani harkan banza nake zaman yi dasu yasa suke kashe min kudi hakana a banza wanda ba haka bane a yanzu na sheda cewa ba duk mazan yanzu bane mayaudara.
Kamar yadda ba duka mata bane suka lalace haka mazan akwai na kwarai na gari a cikinsu sosao har yanzu a duniya Allah ubangiji yasa mu dace ya Allah ka tsare ka kare muna zuria aduk inda suke amin.
Kauda ido da suka akan dan wani yana karewa mutum zurian shi idan dan wani yayi ba daidai ba ka bishi da addua da fatan shiryuwa a rayuwa shine alheri ga iyayye sai ubangiji ya juya adduan zuwa kan yayansu kona yan uwansa don hikimar ubangiji yana da yawa sosao.
Nan gaba zakiji dalilina na fadan haka yanzu gareku insha Allah don Allah iyayye mu kula mu kula sosai mu gyara rayuwan diyan mu aduk inda suka tsunci kansu a duniyan nan.
Har lokacin shike tuki mun dan taba tafiya kadan naji yace dani kece ta nawa a gidan ku yanzu kallon mamaki na jefa mai yadda ya juya harshe yana magana a cikin hausa.
Kallo daya zakai mai tundaga yanayinsa har zuwa shiganshi ka dauka shi din wani katon kabilane wanda bai iya ko zo inkasheka ba a cikin harshen hausa ba.
Abbas din ya dan juyo yana fadin fatima dake yake maganafa nace Pardon yi hakuri banji bane yace kece ta nawa gidan ku na dan sake kallon shi kafin nace ta bakwai a wurin babana amma a gun mahaifiyata ni kadai ta haifa a gidan mu.
Murmushi yayi ya murda sitiyarin motan zuwa wani kwana da zai kaimu wani unguwa yace Abbas ka yarda yanzu da abinda na taba fadama a baya.?
Duk wanda bai tashi tare da mahaifiyan shiba idan nagani zan gane da sauri wanan baiwane da Allah yayi min kan haddace abubuwa da dama danayi kan hakan.
Kwarai kuwa na kara yarda dakai amma ta yaya ka gano hakan please yace bai shafeka ba koda na fadama ba zaka gane ba yanzu so mu bar zancen nan anan.
Mun kara daukan wani kwana ya sake fadin zaki dai iya aiki damu ko don sai kin daure yanzu da abinda mutane zasu fada a kanki za a jefe ki da kalmomi masu zafi da farko amma daga baya idan kin daure zasu gane cewa kinyi gaba.
Nagode na fada Abbas ya jawo cigari daga aljihun shi zai kunna da sauri yace dashi don't please ka bari sai mun sauka ya mayar da sauri yana dafe kanshi.
A bakin wani gida ya tsaya da mota ya kallo Abbas din yace ka kaita gidan madam daga nan ka dawo min da motana ku bar komai a ciki gobe idan zasu tafi sai a mayar a motan da zatayi tafiya.
Ya bude motar ya fita ina ganin haka na leko ina fadin nagode Allah ya saka da alherinsa yace bakomai ya shige gidan kai tsaye shi kuma ya zagaya ya shiga motan muka bar wajen.
Mun dan taba tafiya naji yace Bashir ke nan Allah ya bashi kwakwalwa da zafin kai kinyi sa,a tun farkon ganinku yana mutuntaki ni har ina mamakin hakan .
Kodai bakizo nan ba saida kika danyi saddabarun ku na matane wai ya fada yana tuki cikin murmushi .
Ban gane na tambaya yace gaskiya nayi mamaki yadda kikai sa,a irin haka koda yake shegen inda ake zaton zaiyi tsiyarsa ba ban yake shukata ba wata kila mutumcin ki ya gani rubuce a goshinki don gaya har ya gano wani abu a kanki.
Abokinane tun muna yara mun hasu a secondary ne dashi munyi aboki sosai dashi lokacin yana abin tausayi amma yanzu kinga matakin da Allah ya kaishi shine shugaban mu don shi ya bani aikin nan yanzu.
Ba zan iya fahintar komai ba a lokacin don haka shiru nayi ina saurarenshi ganina a get din gidan mai masaukina yasa nayi ajiyan zuciya.
Yayi min sai anjima tare da bayanin cewa gobe idan munje office daga can zan samu driver yana jirana sai mu tafi idan na karbi takarduna.
Na shiga gidan na samu mai aikinta da yaranta tayi min sannu da zuwa na wuce dakinta shi kuma office ya koma saida aka tashi yakai mashi motarshi.
Washegari ina isa office na samu a hada min takarduna wanda shedan biyane sai opper na aiki tare dasu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login