Showing 336001 words to 339000 words out of 347556 words

Chapter 113 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8753

da yinsa da zaran lokacin yinsa yayi min idan banyi ba zan dinga jin wani iri a jikina.
Kwanansu uku a gari muka fita gidan maman ukku shiga mu gaida ita in nuna mata yar uwata da tazo ashe alherine ke kiran mu lokacin.
Don nan muka hadu da kanin mijinta da matarshi ta rasu yazo ganinsu bayan mun gaisane kan hassana din yana jin nace sister tace tazo daga gida nazo in kawo maki ita ku gaisa dama.
Sai ya dago kai ya dan kallo inda muken kafin ya mayar da kansa ga abinda yakeyi au yar uwarkice yaushe sukazo nace yau kwanansu ukku.
Maman ukku da yawan tambaya take fadin tana da aurene nace da saura Allah bai kawo mijin ba tukun anty ta nunashi tace gashi kuwa duk muka kallo inda take nuna muna din.
Wanan mutumin dai da muka samane a zaune take fadin Allah idan tana sonsa sai su shirya yanzun nan nagama masa korafin hakan ai .
Saidai mijin marigayiyace gaskiya zaki iya idan kinyi hakkuri ta kalli hassana tana fada likitane shi a nan garin yake zaune amma a maitama yake zaune shi ba unguwan nan ba yana da yara biyu da matarsa ta rasu tabar masa .
Muka tausaya masa dajin hakan lokaci guda mukai masa gaisuwa ya amsa da amin nan dai mukace zamu tafi tunda tana da bako ya dan kallemu yace No ku zauna abinku barin na fita daga waje insha iska ya mike ya fita ya barmu da ita
Tace haka yake baison magana iyayyansu daya da baban su big brother dinki amma yana da kirki sosai wallahi in zakiyi na tabbatar da zakiji dadin hakan sosai amma inkina da hakkurifa ?
Don gaskiya shi ba mai son hayaniya bane sosai kuma ki kula da yaransa don suna hannunsa har yanzun shike rainon abinsa baiba kowa ba shi ya zauna da abinsa sai mai renonsu tun uwar na raye.
Kinga ai wanan sai mai hakkuri ko don yaran amma wallahi yana da kirki sosai idan zaki iya balle gaki da zubi irin na matar nasa data rasu zaiso hakan shima nasani.
Bari zamuyi magana anty idan mun koma gida in har kin yarda dashi ai babu komai indai zasu amince tace gaskiyane kuyi shawara amma nasan zataji dadin idan hakan ya kasance .
Gashi tun farko yana da ra,ayin son mace haka ba baka sosai ba kuma ba gajera ba kice dan ka,idane dai tace ai kinsan halin likotoci dama mazansu da matansu.
Nan kuma muka dauki hiran wani dan garinsu tana bamu labarinshi muka sha dariya kafin muyi mata sallama mu fito don yamma daya soma a lokacin take tambayan Jamila na fada mata yadda muke da ita din .
Yana zaune cikin mota koda muka fito tace dashi to angon hassana zasu tafi fa gara ka dago kuyi sallama kada sai sun wuce kace ban fada maka ba kuma suka tafi.
Ya dago kai yana dan murmushi yace kun fito sun fito ko sunyi saurine tana mashi sherin kanin miji suna dariya nidai a sace na kare masa kallo don kada ya gane hakan.
Nace Anty har ya zama angon yar uwata ko tace me zai tsaya jira ai masa sakiyar da ba ruwa yanzune wani yazo ya rigasa ya dauketa in dai garin nan ne ta fada tana mashi sheri muka fito muka barsu.
Mun dan ba gidan baya nace ya Allah kasa wanan abin ya tabbata sister danafi kowa jin dadin hakan wallahi fatana a kullun shine kunyi aure kuma ku huta kamar kowa a gidajen ku.
Sister muma muna son hakan amma ya mutum zaiyi ko kafin mu taso korafin da hassana tayi min ke nan wai ko abubuwan dasu ya Altine keyine yake komawa kan mu yanzu.
Ya Altinece ta haifeku ko tayi wani sheri ai yayanta zaibi ba kuba na bata amsa daga hakan muka shiga gida bayan kowa yayi magana a dunkule cikin mu.
Bai dawo ba sai Jamal da Aliyu damuka bari a gida dake zaune suna faman kallo tun safe don basu san ko ina ba a unguwar sai cikin gida.
Malam Audi ne ya fara dawowa gidan da cefanen da yayo na kayan abinci kamar hauka zakice wani buki akeyi a lokacin haka sukai ta jido kayan suna shigowa dashi gidan suna jerawa store abinci kala kala na kwali kayan miya abinsha da ruwa .
Nan na fito ina gaida malam Audi ya amsa cikin girmamawa shiga matar Ogansa ya gani nace malam Audi da nasan zaka kasuwa aida kafita min da samarin nan nawa sunga gari.
Yace ayi hakkuri a can office Boss ya aikeni amma bai baci ba gobe insha Allahu zan shiga kasuwan in karbo nama zanzo na daukesu insha Allahu.
Bayan fitanshi na kalli samarin ina fadin to ga abinci nan sai wanda ranku yakeso amma don Allah kada a wahal min da iya wajen dahuwa kowa ya dinga girka wanda yake ra,ayi.
Sunji dadin hakan dana fada har kasan ransu don farin cikin da suka nuna na kula yarinyar nan jamila tana fama da wani lalura saidai rashin kula yasa kullun tana tsinbirewa bata girma kullun kwance ba lafiya ko zuwan nan nasu dai tayi ta mintan bata da lafiya ita ko yaushe zaku ganta kwance ta dunkule.
Boss ya dawo ya samemu a falo yake tambayan tana ina bayan mun gaisa ake fadin tana daki bata da lafiyane kalloni yayi yana fadin mekika bata tasha nake fadin haka take ko yaushe ai shiyasama bata girma.
Kukai yarinyar nan asibiti a dubata gobe zan turo suje da iya da Audi a dubata don mu zamu danyi tafiya ina jin dadin yadda mijina yake nuna kulawansa ga duk wani nawa hakan yasa na fara tunanen ni ta ina zan bullowa nasa yan uwan a koma daidai.
Ina son gwada karin maganan manya na uwar gida ran gida mace ke saita mijinta a hanyan alheri ko akasin hakan wani lokaci yasa nake aon nayi amfani na dan gwada damana akan ahalinsa nima amma na rasa ta ina zan bulowa lamarin.
Washegari kamar yadda ya fada yasa suka kai yarinyar asibiti aka barni gida dagani sai yan samarin nan ina daki dana tashi na fito na samesu a falo zaune suna kallo lokacin na samu zama dasu mukai hira ina fahintar damuwansu.
Tun safe sai bayan azahar suka dawo daga asibitin da labari mara dadin fadi wai sai an mata aiki an fitar da cutar a cikinta hakan ya tayar min da hankali sosai jin daga zuwa hutu ace yarinya kuma sai an mata aiki.
An bar yarinya na wahala datace ciwo in tayi arziki a dan bata paracetamol tasha zugin ciwon ya dan lafa bayan wani lokaci kuma ya dawo ta dinga wahala wanda ba mai kullah hakan asan da damuwabta don rashi uwa.
Wani lokacin idan ta fadi damuwanta a hauta da fada har duka tana samu ace ta faye ciwo da kirkire kirkiren fitina a kanta don bata son aiki wanan yasa nake godewa Allah da ba,a kaita wurin matan ubanta ba .
Don da Allah kadai yasan abinda zai faru da yarinyar a can dole muka jira daya dawo da yamma aka fada mai shikan amsan daya bayar shine an fadawa ubanta in ya yarda gobe akaita ai mata ta huta da wahala.
Hakan yasa na kira uban na sheda mashi yake tambaya suzo wajenki ne ko suna gidane nace suna nan sunzo hutu ya nuna damuwan shi yana ban hakkuri tare da fadin bari Fatima narasa meke damuna akan yaran nan gabaki daya lamarinsu saiya shafe min koda nayi niyar tunasu na rasa dalilin hakan wallahi.
Har yana tambayan ko nawane aikin nace ya bari mu gani dai tukun amsan dana bashi ke nan ina kashe wayan hassana tace munafuki kawai badole ya manta dasu ba tunda kasa ya rufe idon uwarsu yanzu.
Shi baikoji kunyar fadan hakaba a gabanki na girgiza kai ina fadin bari hassana na rabaki da sherin shu,uman mace wallahi.
Ni har yanzu idan ina tunane ina zargin wanan kawar anty din daga mutuwar ta ta aura mashi kanwarta kosu suna iya masa wani kulli ya manta da yayan ita kuma gashi yar iska ko bari a gidansa.
Tace ai Samira tace bata gidan ta dade tana garinsu nace yar iska nina san ko waye wasila itama tasan ai na santa farin sani.
Mun dai kira su hjy mun fada masu har hjy balaraba tana tambaya kota zone nace ta bari dai mu gani idan anyi aikin zan kira ina gama waya hassana ke fadin karsuzo su zauna ba gamu ba.
Hassana yarsuce fa dole suce hakan duk yadda muke son jamila sun fimu iko da ita suma suna kaunar abinsu aiko karene a gidan ka dole ka nuna damuwanka akanshi.
Washegari kuwa akaiwa yarinyar aiki bamu kira gida ba don jikin nada dama uban dai ya kira zuwa yamma yana tambayan lafiyanta nake fada mai gata kwance tana barci anfito da ita tunda rana.
Yaji dadin hakan yanata godiya kafin na kira baba na sheda mai halinda ake ciki su boss daga wajen aiki sukazo suka dubata su nabi suka saukeni gida lokacin don ni ciki ya hanani koyon mota a lokacin.
Cikin kwana biyu Jamila ta samu lafiya aka sallamota suka dawo gida a nan saiga yan gidansu sun bugo min waya inane gidan mu gasu suna shigowa Abuja nayi mamakin hakan nan da nan na kira iya bayan nayi masu kwatance nagama.
Iya tazo nace bakine damu iyayyen yarinyar nan Jamilace zasuzo dubata ya za ayi zancen abinci tace baida matsala ai hjy yanzu nan insha Allahu zan hada zamu daidai dasu don nakan soya nama ba aje dama akwai kuma markade dana kafe a cikin freeze.
Ba,a dauki lokaci mai tsawo ba na tura su Aliyu da jamal a junction suka jirasu sai gasu a gidan suka shigo sunawa Jamal sheri ya zama dan Abuja ko .
Na taresu sosai su shiddane maza biyu mata hudu Allah ya taimakeni ya hadani da mutumiyar arziki iya cikin dan lokaci ta gabatar masu da abinci sunga jikin yarinyar da irin gatan da suke ciki a nan din .
Wanda baki ya mutu murus ga ya Ibrahim dake fadan cewa don me daga zuwa hutu zamu kai yarinya a fasata don kawai mu nuna masu su ba kowa bane ko me ?
Shi inyazo sai yaci min mutunci kan abinda nayi zai taka min burki ga hakan kuma ya kwaso yaran tunda abin namu yazomo rainin wayau a garesu shi wallahi bai daukan wanan.
Tunda nace muna Aso yace what yaja bakinshi yayi shiru sai kuma dasu jamal suka shigo dasu get din gidan yaga motoci a fake yace wai gidan mijin Bantu din ke nan jamal yace ehh uncle ya jijiga kai suka shiga kuma yaga aljannan duniyan da Ubangiji ya jefani ciki ya saduda don baiga wurin jaba a nan.
Ni kaina na sauya masa matuka ga sanin da yayi min a baya ga cikin jikina ya saka nayi girma na kara kyau da zama babban mace a idanunsa gashi kuma hakan bai hana inyi haba haba dasu takar naga wa yanda muka fito ciki daya .
Ya dago daga inda nake zaune muka hada ido dashi yace hjy Fatima kice min kune nan kussa da baba kuke sha,anin ku kin manta damu a kaduna.
Nayi murmushi ina fadin ya ibrahin ni yaushema rabo dana ganka gun ina karatu fa yace ko dai tun da kika kimu zakice aka kwashe da dariya nace kai yaya baka manta ba ashe yace ina zan manta kuwa tunda kin kimu.
Kai ba wanan tsakanina daku ai don kune yayyuna dana sani nake tunkaho daku da zaku iya tsaya min ga komai a duniyan nan kuma ace wani halaka baya wanan ya shigo wa zan dafa kuma naji dadi yaya ,?
Gaskiya kan kin ma fisu tunane Fatima ai shine da Alh yazo yana fada muna zancen abin alherin da kukayi wa Mahmud nace Allah sarki Fatima akwaita dai da hangen nisa da sanin ya kamata ranan mun dade muna maganan ..
Muna da niyar zuwa har nan muyi maki godiya har an fara shirin hakan saiga zancen zuwa hutun yaran nan kin aiko shine Alh yace mu dage namu tafiya saiga kuma wanan zancen na Jamila ya fito.
Nan yaran nata ke mata kallon basu gane ba dagani har ita basar dasu mukayi ba wanda yai masu bayanin komai wuni sukayi damu karfe hudu sukai shirin komawa kaduna na hada masu abin arziki suka tafi.
Sun koma bakina fadi a unguwa irin daulan da suka sameni a ciki wanda bai sani bama ya sani a wajensu yanzu suda sukaje suka ganowa idanuwansu.
Wasa wasa maman biyu ta hada wanan halakan a tsakanin yar uwata hassana da kanin mijinta har yakai sun fahinci komai sai gashi ranan mijinta ya sallamawa Boss kan zancen yaji dadin jin hakan yayiwa mijin anty din alkawarin cewa zai bincika yaji sai asan yadda za,ayi.
Koda ya dawo bai mun magana ba sai washegari ranan ba aiki don haka mukasha barcin mu a tare sai shadaya da rabi muka tashi wanka na fito ina shirya shikuma yana kwance saman gado yana tura sako yake fadin.
Sister tana da saurayine dama a garin nan jin hakan yasa na juyo na dan kallesa ganin ya mayar da hankalinsa kan system din dake saman jikinshi yasa na juya ina kallonshi ta wayana nace a,a meka gani ?
Jiyan nan ma kwabcin nan nawa wanan bahaushen dake layin nan ya tareni yana fadin kaninshi yaga kanwar matana ya nuna yana sonta ko nasan da zancen nace masa a,a amma zan binkita naji kome kenan .
Don suna sob wai suga iyayye akan zancen amsan dana bash shi?e haka da sauri kuma zuwan nan natane fa suka hadu ranan mun shiga gidan a nan ya ganta.
Anty din tace matarshi rasuwa tayi da shine take son hadashi da ita sister din ranan ta bugo tace na tura mata number sister din na tura mata suna waya dashi yanzu haka amma ba wai sun wani dade bane haka.
Ok indai tana sonshi me za a tsaya jira tunda dama matarshi rasuwa tayi ai sai a turasu gida suga baba kome kikace nace hakane zanyi magana da ita kome ke nan zan fada maka insha Allahu.
Ba matsala ya fada daga inda yake kwance din nikuma nacigaba da abinda nakeyi muryanshi naji yana fadin matar Boss na kalloshi ta cikin mirrow din yace kinsan wani abu ?
A,a nace ina juyowa na mike tsaye yake fadin yanzun nan na fara sanin nima wanine wani mutum mai muhinmanci haduwana da family dinku yasa ina jin kaina a mutum yadda suke nuna min ina da muhinmanci ako ina.
Mikewa mayi na dauki rigan da zan saka ina fadin koda kai ai mutumne mai daraja da tsada da kima a idon kowa ya danyi murmushi yace kike gani ko nace kaidai kake daukan hakan amma ai yan uwanka kaf sun san gaskiya abu daine idan akace da yan uba kuma marasa fahinta sai abin yazo ta baibai amma ai dan uwa dadi garesa ga kowa.
Zasu nemaka nan bada jimawa zasu dawo gareka ko ince sun ma dawo din a yanzu haka fuskane basu samu a wajen kaba dai yasa suke dari dari dakai har yanzu basa iya sakewa dakai suna ganin kamar kana daukansu da wani ma,ana haka.
Amma ai dole yaransu su gane gaskiya a kanka su nemi shiri dakai sabanin iyayyensu tunda bakai masu komai ba bai kamata ace kayi masu dukan diyan kandanya ba da uwayen da yaran duk ka hade kana gaba dasu hakkuri ake da dan adam harsu iyayyen yakamata ka dan daga masu kafa a yanzu don Allah.
Sai lokacin ya dago yana kallona yama dakatar da rubutun da yakeyi kafin yace baki san wa yan na mutanen ba ko kina masu daukan wasane amma ninake zaune dasu nina san halaiyan kowansu kuma ko sunce maka sun tuba na ciki na ciki dakai.
Boss dama ba hakan rayuwan yake ba yawancin mutane duk a haka suke tafiya ai tare da makiyansu ana komai a tare wana abin naku yayi yawa kaida kake da a garesu kai zaka lankwaso dole sai a zauna lafiya.
Yanzu yadda ake shirin bukin nan sai ka saka kanka a ciki dumu dumu ba ka jaye gefe daya kana kallonsu ba idan ka dauki wani part mai nauyi tunda Allah ya horema abin yi ba baka dashi ba zakaka kun fara dan shiri da wa yan nan ahalin koda wani yayi niyar bataka a wajensu ba zasu yarda da hakan ba.
Kana dan kulla yan uwa da basu da karfi a cikin family kana jin matsalolinsu wanda baifi karfin kaba Boss ka taimaka da abinda Allah ya horema dashi.
Shiru yayi yana saurarena ganin hakan yasa naci gaba ina masa magana in a cool voice yadda nasan zai fahinta da abinda nake fada mashi nayi ta kawo mashi musalai karshe sai naji yace min zo nan.
Saida na dan juya ingani ko da wani a dakin bayan mu kadin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login