Showing 87001 words to 90000 words out of 347556 words

Chapter 30 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8793

aisai wanda ya matsu yazo muna.
Wanan maganan na mijin gwaggona ya kara min wani haske haka na kwana ina nazari a cikin raina washe gari na fice ranan ban dade ba na dawo don ba zamu shiga na rana ba .
Hakan ya bamu daman yin hira da gwaggo bayan mun dawo na tube na fito na gaida ita na zauna muna hira take fadin aifa jiya naje wurin malam yayi min bayanin komai.
Wani malam gwaggo na tambaya cikin mamaki take fadin malam dai da nace maki zani na unguwar Kusfa inda keda malamai nan ciki zaria .
Lah gwaggo saida kikaje ke nan bari yar nan abin na Suwaiba ba hankali dole inje in tsaya maki don Allahne gatan ki mune gatan ki in bamuyi makiba wa yayi maki fadimatu ?
Na rufe bakinane don malam dake gida tun jiya ba dama inyi magana yana ji daga can inda diyarta ke wanki ta kado muna baki tace zama da irin su mama dama sai ka zama jarumin kanka don ma kin rike Allah a bakinkine da yanzu taci galaban ki ko.
Allah bai taba bata ikon hakan ita daidata debo ta girbesa cikin kayan ta yanzuma malam yace min wai akwai rikicin da zai taso a tsakanin ku nan bada dadewa ba za a kara gane halinta sosai.
Yaban rubutu da zakisha yace hakan kawai ya datar dake abinda muka gani a koma a fada mai gashi can ina boyon shi tun jiya don kada malam ya gani ni zancen yankar zanin nan ya daga min hankali.
Don nasan da zaran an yaki zanin mutum abu biyune zuwa uku shine na farko koka haukace na biyu kuma ka kwata ciwo mara magani saina uku asakama tsana a idon jama,a kinga kuwa wanan abin daga hankaline ai.
Mikewa tayi ta dauko min maganin tana fadin karbi maza yanzu ki kurbe saura ki shafa a fuskanki insha Allahu kaikayi zai koma kan mashekiya ko wacece tayi maki wanan karan aikin haka.
Shuru nayi ina nazarin abinda gwaggo din ke fadi a lokacin kafin na nisa nace gwaggo unguwar nan idan nace zanyi sana,ata zasu dinga saya ?
Sana,a kuma yar nan yau Allah ya hadi da yarinya mai dabian yarbawa ke dai baki dorawa kanki girman kan zamanin nan ba ko kadan ?
Suyan zaki dingayi a nan ko wani abu kuma nace eh to gwaggo in ya kama nayi suyar sai in ware lokaci in dora tukunyana idan kuma sana,an danafi bada karfine yanzu na dauko buhuhunan hatsi ina bayarwa ga masu sana,an saina basu idan sun saida su dawo min da kudina na dauko wani bayan ko wani jumma,a don asabar nake zuwa kauye in dauko dama.
Hoh yan nema yarinya da dabara haka kamar yar kabila nace gwaggo na dolene idan na zauna ban nema ba karshenta babane zai wahala ga laluran gida ga kuma nawa dawainiyar abin zaiyi wuya gaskiya.
Allah yayi maki albarka wanan dabaran yayi saidai a nan kan zaiyi wuya gaakiya irin wanan sana,ar don gaskiya mutanen nan ka bawai sanin hakan sukayi ba.
Banki dai ace ko za,a sayo a dora kofan gida idan sunsan da haka kuma anga kwanon da sauki har nan cikin gida zasu iya zuwa su saya saidai matsala dayace shine wanda zai zauna a wajen .
Gwaggo ba gani ba asabar da lahadi in zauna ranan fita boko saida yamma idan na dawo in dinga zama da kaina kila hakan zai taimakawa rayuwana sosai don in na zauna a karshe wa zai dinga min lalura tace Allah ya zama gatan mu fadimatu muka amsa da Amin.
Gwaggo din ta dora da fadin yanzu saiki bari malam ya dawo na fada masa abinda yace zan bada maki inya yarda kinga sai ki soma idan kuma yace a,a kinga saikiyi hakkuri mu zurawa sarautan Allah ido kuma dama garesa maku dogora.
A sanyayye na amsa dato gwaggo in bai bari ba hakan ba matsala bace sai na nemi wani hanya kuma maisauki yadda kudi zasu diga dan juya min ina hada kudin karatun nawa.
Shi sana,a yanada dadine zama haka dip kana dan tallaka bayi bane tunda ko masu kudin ba zaune suke kudin na shigo masu ba haka kawai.
Munyi hira sosai a wurin kafin muka daga kowa ya kama aikin gabanshi don magariba daya gabato a lokacin.
Dakin nan na gyara tsab na gyara kayan dakin yadda ya dace saiga dakin ya dawo yadda nake nake son ingashi nafita nida bakuwan gwaggo muka ciki kayan gidan da ruwa tap da safe na huta da dibowa ke nan.
Bayan na gama komai na koma dakina don indanyi karatu saboda mijin gwaggo idan ya dawo sukan dade suna hiransu a nan tsakar gida har wani lokaci kafin su shige.
Wayata danake amfani da itace tayi kara na dauka Al,amin ne ya kirani muka gaisa yake fadin ya kira sau biyu wayan yana kashe.
Nace ina cikin school a lokacin yace lalai kin mayar da hankali sosai yan mata Allah yasa ki fito muna da first class nace wai da wuya Allah dai yasa.
Hira sosai mukayi dashi wanda hiran karatune karatun su nacen yana da bambamci sosai da namu karatun na nan Nigeria bayan mun gamane nake fadin idan ka biyewa diyan masu kudin nan sai ka fada daji baka sani ba.
Shiyasa nake abin a taka tsatsan yadda ba zan takurawa kowa kuma nima ba zan takura ba tunda banda wani jigo tsayaye da zai taimaka min a rayuwa zan dai iyacewa yanzu haduwana da yan saudiyane dai yasa nake jin kaina kamar nima ina da yan uwa a wani bangare.
Don ita samira akwai wata yar uwan haihuwan mahaifiyarsu datake taimakawa karatun ta don ko kudin farkon shiga da muka biya itace ta taimaka inda tabada fiye da rabin kudin su kuma suka cika saura.
Amma suk da haka suna kyashin ni yadda nake gudanar da rayuwata suna ganin wani shegen kudi nake dashi inawa mutane boyon kurwane don kada a gane hakan.
Safiyace don haka tunda safen dasuka fito masalaci yake zaune kofan gidansu don maganan da yake sonyi da mahaifisu saida ya daidaici yanzu ya gama shiri ne suka shiga cikin gidan shida Ibrahim kamar yadda suka saba shigowa gaidashi tunda yazo garin.
Iyayyensu mata suka fara gayarwa kafin su gaisa dashi Alh din bayan sun gaisane kowan su yayi shiru alaman da abinda ke tafe dasu a lokacin ke nan.
Lafiya dai Alh ya dago yana fadi Ibrahim ne yai magana yace dama Alh munzo da wani shawarane akan shi Mahmoud muke son a duba muna idan ya dace.
Murmushi Alhn yayi kafin yace to kasan fa shawaran mu ai irin na bayane bai cike da wayewa irin naku na yanzu sai nake ganin koma meye ai yanzu kuna iya ba kanku shawara ke nan ai.
Sun gane me mahaifin nasu ke nufi saishi Mahmoud din ne yace ayi hakkuri Alh a yafe min ko a baya kuskure aka samu Alhn yace aini na dade da yafema idan na rike da wani zancen a raina nima na cuta maka na cutawa kaina da mahaifiyan ka har yan uwankama.
Yanzu meke tafe daku don kusan zan fitane jin hakan yasa Mahmoud ya dubi Ibrahim sai Ibrahim din yace watau Allah shi Mahmoud ne dama yaga dacen wan ya dawo nan gida kaduna ya kara aure kuma ya dade muna wanan shawaran dashi tun yana can bai zo ba.
Shine yanzu dayazo muka yanke shawara akan zai kara komawa gidan baba Garba inda yayi auren farkonsa tunda akwai yan mata ya samu daya ya aura a cikinsu.
Amma dai mu shawaran mu yafi tsayawane kan Bantu don munga tafisu dama da saukin kai kuma ko banza har yanzu ita bantu din tana kula da yaran nan bata manta baya ba a garesu shine shawaran da muka yanke din mukazo.
Kallon dan nasa Mahmoud dattijon yayi sosai amma sai ya tsinci kansa da son baiyana masa abinda dake cikin ransa da dadewa game da hakan.
Ya gyara zama yana fadin kaiya ai Mahmoud kabar kyau tun wurin wanka yanzu me kake shirin fada min kan Fatima kai yanzu kasan ko wacece Fatima kuwa ?
Zama ya gyara ya kara lankwashe kafa yace a sanyaye kwarai Alh nasani sanin hakan nema naga ya dace yanzu ta maye gurbin yar uwata ta zauna tare da yaran nan.
Ido mahaifin nasa ya kura masa har ya gama kana ya sake sakin wani shu,umin murmushi yana kallon dan nasa yace tanan kuma ka fito yanzu ?
Mahmoud lokacin danayi maka sha,awan hakan kai bakaso ba don lokacin da naga yarinyar nan tadan tasa nayima sha,awan hakan a raina saika nuna min ban isa ba .
Don ko lokacin da yarta ta rasu ana iya saka yarinyar nan a dakinka ka reneta tare da yayanka gaba daya amma sai ka tafi ka share kowa da zaka dawo kuma ka dawo da wani zance na daban.
In har hakan zai kasance nina da kake ganina nafi kowa tayaka murnan hakan amma nasan yanzu yana da wuya hakan ya samu a gareka da dai watace a gidan ba ita ba zan yarda da hakan.
Amma itafa yanzu karatu ta koma tanayi zamu kashe mata burintane mu tauyeta mu hanata karatunta don naka bukatan a gareta kasan in munyi hakan mun shiga hakkin yarinyar nan yanzu.
Ibrahim dake gefenshi zaune ya dago ya kalleshi yana girgiza kai yace tabbas ka tafka wani babban kuskure a rayuwanka don gaskiyar Alh tun lokacin ya kamata ace kaga shakuwanta da yaran nan ka fara nuna ra,ayin hakan akanta.
Amma yanzu yadda idon yarinyar nan ya fara budewa hakan wani babban aikine kasani a garemu mu shawo kanta saboda hakan ni naga yafi tun wuri ka gagauta cire ranka a gareta ka zabi wata a cikin gidan zaifi maka saukin komai bisa ga ita don burin rayuwanta yanzu shine karatun nan nata.
Don mun taba magana da ita take fada min dal,,,,,,
A fusace ya juyo ga Ibrahim din rai bace yakece masa shut up don Allaj muddin ba zaka samo hanyar da za a biba to kaja bakinka kayi shiru ka barni da dabarana.
Yadda yayi maganan suka fahinci yayi zurfi ga abinda yasawa gaba ke nan lokacin don haka shi mahaifin nasu yace iya gaskiyan da zamu iya fadama ke nan a yanzu Mahmoud .
Don koda zamu shige maka gaba mu munsan da sanin wanan matsalolin sai ya biyo baya amma ai shawara muka baka a yanzu amma inkasan zaka iya aiga fili ga doki don dole dai mu tayaka nema tunda Fatima kowa na bukatan kasancewa da ita a cikin ahalinsa.
Kai yanzu dai bakaga wata ba sai Fatima a cikin gidan malam garba ke nan don kamar yadda Ibrahim ya fada zasu kai su shida nake gani ko biyar da suka dan tasa .
Ka duba cikin sauran mana ko zaka samu mai irin halinta kafin mu tunkari shi malam garba din da zancen kara hada iri dashi .
Zanyi shawara kan hakan Alh yace to Allah ya zaba muna abinda yafi zama alheri aka amsa da amin mahaifin nasa ya kara fadin yaushene tafiyan nakune ?
Ajiyan zuciya ya sauke tare da fadin zuwa gobe ko jibi zamu tafi amma in naje zan dawo don maganan wanan gidan man da nakeso.
Ok lalaikan ya kamata ka dawo da wuri don su san kana so da gaskene Ibrahim ya fada ya hade kafansa wuri daya.
Haka dai suka bar falon akan zaiyi tunane kafin ya wuce suna fita shi kuma mahaifin nasa ya mike don ya shirya ya fita saboda ya dan taushe hannu a zaman da suka danyi din dashi.
Baiyi maganan da kowa cikin iyalisa ba don bai son kananan surutu ya taso a cikin mata saida yammane daya dawo suka kara zama da Mahmoud din ya kara tabbatar masa cewa shifa Bintu din hankalinsa yafi kwanci da ita.
Yace to kaje zanga mahaifin nasu muyi maganan dashi yayiwa mahaifin nasa godiya a lokacin ne ya nufi masaukin su ya samu wasila zaune tana waya da Rita kawarta shigewa yayi don ya rage kayan jikinsa.
Ya watsa ruwa lokacin ya fito daga dakin ya sameta zaune a falon zama yayi cikin nuna yanayin gajiya ta dago kaida kyat ta dan kallesa.
Idan kin gama wayan ki ban abincina ya fada yana kallonta tace dashi gashi nan a cikin kulancan bai kiba ya mike ya dauko kullan ya bude.
Gani yayi bata taba abincin ba itama yasa spoon ya dibi nasa iya yadda zai iya ci a lokacin ya zauna yaci abincin sosai don tun karin safene a cikinsa daya karya a dakin hjyn su.
Mikewa tayi daga inda take zuwa ciki ya dan bita da kallo don ya fahinci tun jiya da sukai maganan tafiya take wan fushin dashi haka.
Saida ya gama komai har waya da mutanensa ya mike ya sskawa dakin key ya kashe wuta yashiga don ya kwanta .
Alokacin harta dade da barci ita don sanin yana tabata zata fara mashi mita da cin mutunci yasa ya kyaleta washe gari kuma ya fice zu masalci don samun sallah asubahi.
Bai fito da wuri ba saida haske ya gama gari ya fito don zuwa gida ya kara kwantawa kafinsu fita shida Ibrahim din zuwa ida suke zirga zirgab gidan man.
Don har lokacin banda ibrahim din ba wanda yasan da wanan zancen yana son sai abin ya tabbata zai sanar da iyayyen nasu.
Shiko Alh gidan mahaifina ya nufa daga masalacin yasa ai masa sallama da Abba din ake fada mai bai shigo ba har lokacin yana masalaci ke nan.
Don haka ya zauna jiransa a saman dan dakalin zaman da baba yayi a kofan gidan namu don zama irin haka ga bakinsa ko masu wucewa a lokacin su dan huta.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
[8/21, 8:16 AM] Maman Aslam: KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
2?? 7??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Tafe yake yana jan tasbaha a hannunshi ya doso gidan nasa tun daga nesa ya hango mutum a zaune yana jiran isowarshi saidai kan maishi a duke yake lokacin hakan yasashi tamtaman ko waye ?.
Saida ya kara karasowa kusane ya sheda ko waye duk da kansa yana duke a lokacin hakan yace a Alhajin Allah sai Alh ya dogo kai yana washe baki yace malam garba an karaso dama nasan kana kusa yasa nace barin dan dakanceka don nasan baka wuce masalaci yanzu daga nan ko sai gida.
Hannu baba ya mika mashi suka gaisa yake fadin lafiya dai ko na ganka yau kofan gidana da farar safiyan nan haka ga sanyi.
Lafiya lau wallahi sai alheri kasan ance me nema shike bi to yanzuma biyoka nayi gida mu tatauna kan wani zance da yaro yazo min dashi.
Kasan halin yaran nan idan suna son abu to ko kai daka haifesu baka da hutu sai sun ji matsayar abin nan garesu ,jin hakan yasa baba fadin Na,am cikin rashin fahintan ida zancen Alh ya dosa lokacin.
To magana kazo dashi ke nan bari nayi muna shimfida daga ciki ke nan yace a,a nan ma ya isa sai kace wani bako can malam garba ?
Dan shiru ya biyo baya kafin Alh yayi gyaran murya yace nasan zakai mamaki a yanzu amma in munyi duba ga yanayin abin tunda Allah ya halasta yin hakan wanan ba komai bane.
Kallon mamakin zancen sa da baba ke masa yasa ya dago da kyau yace watau malam garba har wa yau dai zancen gudane don daka surukinka Mahmoud baba yace na,am yace to shi ya kara turoni wurinka karo na biyu neman iri a gidanka.
Ikon Allah don kasan ance in abu bai kare ba ba mahaninsa sai Allah to jinyan nan dai ina zaune ne suka zo min da zancen cewa ya sake ganin iri yana sha,awa a gidan nan kuma tunda Allah baiyi marigayiya mai zaman duniya bace ita.
Allah babban sarki a nan gidan nawa kuma ya hango wata din kasan yaran nawa yanzu sun dan tasa da dama akwai su yan biyu kansu daya sai Samira da Fadima sai yahanasu kanwar samira din da itama kansu daya yanzu.
Murmushi Alh din ya kafin yace Fatima din dai ita yagani don kaf dinsu na dai sansu amma bani kawo sunayesu a yanzu itako kasan tuncan ai yar gidan muce dama.
Wani irin nisawa baba yayi lokaci guda kafin ya sake dan murmushin yake a fuskanshi yana fadin nayi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login