Showing 162001 words to 165000 words out of 347556 words

Chapter 55 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8755

Kuma na kara da wasu nau,in abincin larabawa dama na wani kasan bakaken fatan na koya a wurin ma,aikatansu don ni Khariya da salima mune tare da masu gudanar da abincin.
Sai zuwa dare na samu dan fitowa nima nasha kwaliyan abaya mai kyau da tsada wanda ummuvta sayo muna har ni khairiya da salima saidai kowa da kalan nasa don ma wanda ummu din ta saya min ainihi khairiya ta nuna shi take so na barmata na dauki natan wanda nake da yakinin cewa yafi sauran kudi ko a ido mutum ya gansa zai gane hakan.
Sai bayan mun saka kuma take korafin tana son nata din ummu tace bata isa ba kuma tunda har na rigada na saka saidai tayi hakkuri.
Ba laifi muma an dama damu a wajen duk da kusa ni ban ma fito ba don ni a kitchen nake ina kula da masu aiki yadda ake kai abincin sai kusan karshene bayan mun shirya na fito inda su hjy ke nasu taron matan zakice a gida Nageria suke wanan bukin ba a saudiya ba.
Tunda na fito wasu matan da kana ganin shigarsu batayi daidai da namu yan Nigeria ba don ko ina dan Nageria yake komai nasu daban ne.
Dan larabcin da nake ji nayi amfani dashi ina gaidasu suna amsawa matan dake zaune sai yaren su sukeyi suna dan hadawa da larabci nidai naga sun kira ummu sai ta kalloni tana dariya kamar tana masu bayani ne a kaina lokacin a zatona abinda ke hannuna suke so saina hari wurin nasu kai tsaye.
Kunan zakin ayane da muka sarfashi nau,in yadda muke hadawa a gida kayan kamshi da sanadarin kamshi na bature shine kowa ke mararin sha har larabawan dake wajen.
Ina zuwa na dire masu ina gaidasu hayya kamar yayi yawane ai wata ta fada kawai dai zamuce ita wanan yarinyace ita kuma wacan din ta danfita shekaru.
Ban tsaya ba na juya na wuce nakoma na dauko wani na fito zan fitone mukaci karo da wata mace a wurin na juyo da sauri ina bata hakkuri.
Larabci ta fara zubo min sharrr hakan yasa na danyi murmushi na juya harshe zuwa English nan dan Nageria yafi karfi dama nace sorry please.
Da kwatance ta fara min magana wai tana cigiyar dantane karami dan kimanin shekara uku kai na gyada don naga wani yaro a ciki don haka nace ta jirani cikin kwatance zuwa nayi na mikawa salima kayan na juyo zuwa inda nabar matan.
A nan na sameta muka shiga ciki tare can inda khariya take muka samu yaron zaune yana cin abubuwan da aka zuba mashi.
Ta sauke wani irin ajiyan zuciya tana kai hannu ta kama yaron yaki zuwa amma ina mika hannu yaron ya dago kai ya sake min murmushi kadan ganin hakan yasa na kara daukan wani packrd din da ba a bude ba na mika mai tare da dago yaron ya mike yana karba.
Nan dai yaron ya manne min khariya tayi mata larabci ta barshi a gurina ita kuma ta juya da hausa tana fada min naga matan ta juya ta fita tun lokacin nake faman dawainiya da yaron matan yana makale dani dama na saba renon yara nasan kan yara kuma.
Nadawo na dan zauna yaron ma ya zauna a kusa dani muryan ummu ne dake kwalla min kira na fito da sauri tare da yaron na sameta tsaye a corridor dinsu ina fadin mama gani.
Don Allah ki duba a store koda akwai ragowan sauran kunun ayyah nan ki kwasowasu Abbu da mutanensa yanzu ya aiko wai a karo masu shi.
Da sauri na juya zuwa babban store din nasu kai tsaye inda duk muka tara kayan da za ai waliman dasu na sunkuya ina duba inda muka aje katon katon din kunnu a cikin wani dip freezer nasu.
Ina sunkuye ina kirga wanda ya saura yakai kusan katon goma a ciki hakan yasa hankalina ya dauke bansan da zuwan mutum wurin ba a lokacin.
Tsaye yake daga bakim kofan ya zuba min nakassasun idanunsa a kaina yana min kallo mai kama da nakasa ko wullakanci ina dagowa tare da dan juyowa inga inda yaron nan yake kawai saina dora idona akan uncle din dake tsaye.
Kallona ya sakeyi daga sama har kasa yana tsaye kuma ya tare kofan yaki gusawa kuma yasan dole ta nan zanbi in wuce ai.
Nazo dab dashi kamar zanyi cikinsa da kayan a hannu daya ga yaron mutane da nake jaye dashi da dayan hannun ganin hakan yasa ya bude baki don dole yace.
Yau da kinsan baki da wayau idan kika kuskura kika bangajeni da kayan nan wai don Allah meya ku yayan tallakawa baku iya samun waje bane wai ?
Kalaman shi naji har kasan raina don sunyi matukar kular dani saboda kalman daya kirani dashi din a lokacin na yayan tallakawan daya ambata gareni.
Amma kai baka biyo mai sunan kaba gaskiya don bai dace da mutun irinka ba sam saidai kuma ni dakai din duk yan cin arzikine a gidan nan ai.
Koda kuwa karunane mahaifinka saidai kayi kuskuren labawa a innuwan wasu nagane kalan kallon da kake min ba yau ba ko baka fada ba nasan dama kallon raini kake min a idanun ka sai dai ka sani.
Don wace kake gidan nan nima nake yanzu a cikknsa kuma ina son ka sani daga yau kada ka kara gigin nema ka raina min wayau don abinda kake tunane ni bashi ya kawoni gidan nan ba a yanzu.
Don tun randa ka gani a gidan nan na hango bakin ciki da tsanna a idanunka don haka nima wani irin kunci nake ji idan na kyala ido na ganka kamar yadda kake jin nawa.
Muryan Hjy ce ya dakatar dani don ganin ban fito ba yasa ta leko tana kwala min kira da sauri na amsa ina nufan kofan kai tsaye yayi saurin jaye jikinshi yabani hanya.
Nan na barshi yayi kasake tare da wani irin kunci a zuciyarshi yayi tunane barkatai a wurin ya rasa yadda zai fassara maganganu a zuciyar shi.
Ji yake kafarsa bata daukanshi a lokacin ga zuciyarshi dake wani irin bugawa sosai kamar zata ballo gaba dogon jallabiyan dake jikinshi.
Da kyar yaja kafan shi zuwa dakinshi ya zauna saman kujera yana sake ajiyan zuciya lokaci guda don a rayuwan shi bai taba zaton wani mahaluki zai gasa mai magana irin wanan ba din sanin koshi waye .
Aliyune yajishi shiru ya biyoshi dakin yadda ya sameshi a zaune ya gane akwai wani abindake damun shi a lokacin domin kuwa kallo daya zakai mai ka fahinci hakan a tare dashi.
Aliyu ya san akwai matsala don ganinshi hakan saboda yasan shi farin sani don haka yasan yanayinsa idan ranshi ya baci ko kuma yana cikin walwala don haka ya tsura mashi idanu yana kaiwa zaune a kusa dashi din.
Don haka baiyi kasa a gwiwa ba ya soma tambayanshi da wai lafiya naganka haka jikin ka duk a mace ma,ana akwai wani abin bacin rai daya sameka ke nan yanzu ?
Uncle ya gyara zama yana kwantar da kanshi saman kujeran da suke zaune ya daga kan sama tankar zaiyi ihu a lokacin.
Ganin hakan yasa Aliyu din yin dan murmushi yana kai hannu saman kafadanshi yace wai duk rashin zuwan Nuriya din yasa rayuwanka baci haka kome ?
Cikin dan dakiku Aliyun ke jero wa yan nan tambayan sai yaji ya sake wani irin gajeren ajiyan zuciya kafin ya dago jajayen idon nasa yana kallonshi yace.
Yau mai rabani da yarinyar nan a gidan nan sai Allah don ko kiris ya rage ban ballawa shegiya kafada ba a yanzuma din kada in haka Abbu yace na kunyatashi na bata masa taron sa sanin yadda ya dauki taron nan da muhinmanci yasa na ragawa yar iska a yanzu din.
Aliyu yayi shiru yana mai kura mai ido yasan ko wacece ta tarowa rayuwanta mach babba mai ya kaita shiga shirgin uncle din nasu ma donshi a zaton Aliyu ko Salimaci don itace mai rawan kai a gidan.
Don ya wagance Aliyun yaja tsuki tare da fadin yanzu don wata sai ka kumshe kanka a daki kana hadiyan zuciya alhalin ita tana can tana damawan ta da walwala a cikin mutane ?
Haka kawai zaka bata wa kanka rai da shirmen wanan ballagazan salima din da anan ta dan fara waye ma ni sam yarinyar shiyasa ban sake mata fuska ai.
Kara kallon Aliyun yayi yace wace salima wai nifa ba zancen salima nake maka ba zancen wanan yar tallakawan dake ganin yanzu ta waye daidai take da kowa a gidan nan waye ita yar waye da zata bude baki ta fada min magana ?
Aliyu yayi kasake yana kallonshi tare da saurarenshi don yana son ya fahinci inda zancen nasa ya dosa kai tsaye don zancen da uncle din keyi ya matukar rudar dashi.
Huncin da uncle din yayi ya dawo dashi hankalinshi ya dago ya kalleshi yaga sai yaga har gumi yake wani tsatso mashi akan goshinshi tankar wanda aka watsawa ruwan zafi ko yayi gudun falfalaki lokacin.
Ganin haka da Aliyun yayi yasaurin fadin wai meke faruwane haka uncle ban fahinci wace yarinya kake magana akanta ba haka ?
Murmushin karfin hali ya sake wa Aliyu din yana fadin ba wata bace illa wanan yarinyar da Ukuty na ta dauko take ganin ta gama asirceta a yanzu a nata zaton har zata kawo iskancinta a kaina.
Ummm,umm uncle kada ka tafka babban kuskure don Allah lalai idan kace hakan gaskiya zaka jawo wani matsala mara amfani ga kowa .
Kasan fa halin ummu ba asiri bane illa tausayi da kaunar yarinyar nan daya shigeta farat daya har kake ganin hakan na fahinci komai nima da farko nayi wanan tunanen.
Amma daga baya kuma sai nazo na fahinci kaunace kawai da tausayin yarinyar da ummu ke yawan yi ya kawo masu shakuwa haka da juna.
Kaduba irin wahalan da yarinyar nan takeyi duk kuma akan ummu da Abbu take wanan ban dauke shi a komai ba yanzu din na fahinci tsakani da Allah take zaune dasu.
Ka duba fa har kasan nan tazo don ummu aiko ta gama muna komai don Allah kadai yasan irin takan da tasha kafin ta iso nan din a yanzu.
Uncle din ya katse masa tunane da fadin don ummu tana kaunanta shi zaisa har ta dauka tana da right din fadawa kowa magana yadda taso.
Uncle ka fahinceni don Allah koma ne tai maka kila sabanin fahintane ya kawo hakan amma ka jaye zancen duka don ita macece fa ka tuna da hakan.
OK k don tana mace bari ta rainawa mutane wayau a banza ko zan nuna mata cewa ita din ba kowa nace face yar tallaka tilis sai nayi maganinta ina fada maka kafin tabar kasan nan.
To ni dai shawaran da zan baka shine ka fita harka kawai tundama ba dadewa zatayi a nan ba dama program din nan yakawota kuma an gama shike nan.
Don haka ni shawaran da zan baka a nan shine gara tun wuri ka share wanan zancen koma metayi ma ka barta kawai don hakan zai iyasa zargin da Al,amin kema a cikin wasa a dauka yanzu da gaskene.
A fusace uncle din ya mike tsaye yana huci yace wai mesa kuke min hakane Aliyu na rasa wace zanso sai wanan yarinyar kankanuwa ?
Haka Al,amin yake min kallon hakan tun lokacin da ummu tasa na dauki yarinyar nan zuwa gidansu na zaria ni kuma saboda ummu nayi mata duk abinda nayi mata din a lokacin.
Meyasa kuke min wanan fahintar ne haka kuna dangantani da wanan kazamar yarinyar a rayuwata yarinyar da ko spelling bata karasa iyasa ba.
Mikewa Aliyun yayi yana fadin cikin taku daya zuwa biyu yace uncle yana dafa kafadanshi kayi hakkuri don iya gaskiyar da zan iya fadama ke nan a yanzu kayi tunane akai.
Lokacin wayan uncle din ya dauki kara amma zuciya ta hanashi ya dauka a lokacin kallonshi Aliyun yayi yace wayan ka uncle yana mashi nuni da ita a gefenshi.
Hannu yakai ya dauke wayan yana dubawa sunan Nuriyace ya gani a rubuce hakan yasa ya dan ja gutun tsuki yana daukan wayan ya kara a kunnensa.
Ganin hakan yasa Aliyu yabar dakin ya fita yana mamakin uncle din a zucuyarshi kai tsaye ya koma wurin taron nasu akaci gaba da gudanar da taron da tataunawa a tsakani mazauna saudiya yan aafrica


ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
5?? 1??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Da kyat na samu aka gama taron nan dani don sam ummu bata barni na zauna ba dana dan nemi wuri na labe yanzu zatasa a nemoni duk inda nake kuwa har na fara gajiya .
Ga kuma yaron mutane daya dafe min kamar uwarshi ko ina nabi yana bina a baya har yayi barci dole karshe na daukeshi na goyashi dana gaji sosai dole na koma daki na kwantar dashi saman gado.
Nima kwanci nayi lokacin ne maganan uncle mohammad yake dawo min sabo a zuciyana tambayan kaina nayi wai meyasa kallon farko ake min mumunan fahinta meyasa mutane basu ganewa akaina .
Ni dai nasan ban taba kebawa da wani namiji da sunan zai laluba min jiki ba haka kuma koda gigi ba namijin daya taba kai hannunshi a nawa da sunan jin dadin rayuwan shedanci.
Haka kuma saurayi ma na kwarai bandashi a rayuwana soja nadan ba fuska shi kuma nagane yaudarana yake sonyi yanzu ko waya sama sama mukeyi dashi duk ko da alherin da nake samu daga gareshi wanan baisa in zauna dashi hakana ba.
Hakan kuma wai har mutane kemun kallon wata gogagan yar bariki nake a yanzu Allah ne kawai shedana naba kaina amsa ina juyawa.
To me nayiwa bawan Allah nan da yanzu yake kokarin saka min kahon zukau a rayuwata a sanadinshi nasan zan bar hjy duk ko mutumci da halarci dake tsakanina da ita don ba zan lamunci cin fuska da tozarcin da dan uwanta ya bullo min dashi a rayuwata.
Koshi waye yace zai hada da iyayyena ba zan barshi ba ya tafi saina mayar mashi da amsa kwatankwancin wanda ya fadamin din.
Idan hakan ya faru kuma hjy ba zata soni tabar dan uwanta uwa daya uba daya ba ta kama min don kawai itace maj tausayi ko jin kai.
Salimace ta shigo dakin amma sam ko motsin shigowanta banji ba balle sallaman datake min sai lokacin data zauna kusa dani tana kai hannunta saman kafadana ta barin dama.
Ido na dago ina sakin ajiyan zuciya saboda zuciyan data lula duniyan tunane a lokacin na sauke kwayan idona da suke shirin sakin hawaye a lokacin saboda tsaban jin haushin zagin da uncle din yai min da bansan dalilinshi na hakan gareni ba.
Kallon salima din na sakeyi cikin wani irin yanayi ina kokarin dagowa daga kwancen da nake kallona tayi wani iri da alaman tambaya a fuskanta.
Kafin kuma inga ta bushe da dan dariya tana fadin lalaima sister badai wai kin gaji bane haka har kike batun kuka don gajiya ?
Kallon Salima din na danyi ina dan gyara zama nace Uhumm ke dai bari yar uwa wani abune da bansan dalilin shi ba ya shige min a kai kika ganni nan ina tunane.
Menene wanan din sister anyi wani abune kuma nace ban sani ba nima wallahi haka dai kawai yake son kawo matsala tsakanina da hjy nake gani.
Nan dai na fara bata labarin abinda ya faru har zuwa amsan dana bashi a lokacin da kuma tsaya min a rai da abin yayi yanzu don ina ganin amsan ma bata isheshi ba dana bashi.
A jiyan zuciya ta sauke tare da fadin ina ruwanshi dake to shifa haka yake a gidan nan da jiji da kai don kawai yana takama da saurata kome oho ?
Ni kin man daidai don kowa tsoronsa yake a gidan nan don haka yake ko yaushe muturku yana hadiyan bakin rai shiyasa kikaga ba ruwana da lamarinsa cikkn gidan nan.
Kema dai an kiyi kokarin fada mai magana don wallahi kin min daidai yasan koke wacece da zai fada maki hakan ko arzikin kikazo ci shima ai duk da yana dashi arzikin yakeci a nan tunda nan din ba gidansu bane.
Yar uwashice kawai take aure a nan ta dalilinta kuma yake zaune ba dalilin Abbu ba don haka ba ruwanshi da duk wani wanda zaizo nan in


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login