Showing 129001 words to 132000 words out of 347556 words

Chapter 44 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8744

san zaman da zanyi dashi yanzu Allah nagode ma da kake kareni ka bani zuciya irin hakan da bani da saurin yarda da kowa haka kai tsaye.
Haka na karasa wunin ranan sukuku dani a cikin dakin ban fita zuwa ko ina ba don banda gidan zuwa ina son zuwa gidan maman saudiya in duba iya dake zaune a boys quarter din gidan amma ban samu zuwa ba wata zuciya kuma na raya min cewa nakoma zaria kawai shiyafi min sauki.
Amma kuma na riga danayi alkawarin zuwa bukin sajida a lokacin haka kuma nayiwa yan uwana alkawarin zamuje tare dasu don haka dole in tsaya badon ni ba.
Da dare bayan karfe tara ina kwace a dakina hussaina ta shigo tana fadin wai kinga yar iskan nan yaya Mahmud ko take shigewa yanzu ashe.
Nina dauka ai shirmenta nason a sani takewa mutane ashe da gaske takeyi ita don nasan dai indon ta shine ba zai taba cewa yana son samira ba nemoshi dai sukayi kila ita da uwarta.
To meye hussai in yana sonta ai mu ba matsalan mu bane tunda ba mu zamuje mu zauna mata sai ta shirya zuwa gwabzawa da Wasila don yar iskace itama ta gaske.
Lalai Samira tayi gadon munafunci sosai wallahi ki dubafa da hassana akace za a hadasu amma shine samira ta zagaya baya tana ci mata duduniya kuma.
Samira da hassana ai duk dayane a gidan nan wace yaga yana so tana so sai ya zabi abinsa Allah ya basu zaman lafiya tayi shiru can kuma tace shegu da yasan sherine ai baizo nan kofan gida ba can ya tafi bayan gida wurin gidajensu ta sameshi ita kuma yar iska daya mara hankali.
Shiru nayi na nuna banson zancen tana fita na mike na rufe kofana don ni daya ke kwana a dakin saida naji gida yayi tsit na mike na bude wanan kayan da Mr Abbas suka saya min.
Nan nasha kallon mamaki na gaji zakice ko wani lefe za,ahada kayane masu kyau da tsada gaskiya matasan yanzu sun iya zabe idan sukayi zakice mace ce tayi sayayyan don sunsan komai da zaiwa mace kyau ya dagata.
Mayarwa nayi ciki da mamaki wurin rufe dan kit dinne naga abu cikin zip din kit din na ja naciro farin envelope da ba rubutun komai da farko na dauka irin tarkacen da mutun kan samu a cikin abune inya saya.
Amma kuma ina daukowa naji kamshi ga kuma abu a cikin takardan da sauri na sake dayan hannuna ina bude envelope din guest what kudi na gani sabi kal dasu yan dubu dubu wraffer guda saida na koma zaune da baya don tsoro.
Cikin su biyun waya saka min kudine na fada a fili Mr Abbas ne ko shi shugaban nasa inshine yaushe ke nan ya saka min kudin nan ban sani ba.
Tunda bada shi mukaje sayayya ba ai yana cikin mota zauneshi lokacin har muka dawo da sauri wani tunane yazo min na kiran da tayi wa Abbas bayan mu tafi sukai magana da kuma.
Cewa da yayi abar kayan a mota idan gari ya waye zan tafi sai a mayar cikin motan da zai kawoni gida din idona lumshe kafin nace wata sabuwa ke nan kuma ashe ?
Wani rigan dinkin Dubai na zabo na fitar a ciki wanda zanyi amfani dashi na mayar da kayan tsab na rufe na sakawa kit din security na aje inda na dauko zuciyana tab da tunane.
Nace Allah yana tare da bayinsa a duk lokacin dayake so Allah nasan wanan baiwankane da iyawan ka bana wani mutum ba can ya Allah ka kara tsare min rayuwata.
Ni dai nasan ban bin boka banbin malam saidai idan kuma dan abinda gwaggo ke ban lokaci lokacine shine amma wanan hikimar ta ubangijinmu ne Allah gareni.
Can cikin dare ina barci wayata ta dauki kara misalin sha biyun rana a lokacin nayi karfin halin bude ido na mika hannu na dauko wayan ina duban mai kiran nawa a cikin daren nam.
Bakon lambace ba suna nayi kamar in share amma kuma da nayi tunanen kila mai digital global ne sai kawai na dauka ims fadim sallamu alaikum.
Wslm aka amsa min a dayan bangaren yan mata ashe ana garin kin shigo break na zata ai yanzu kadunan gudunsa baki daya kikeyi ai don ni ?
Waye wanan wai na fada a dan fussace naji yayi murmushi yana fadin a lalai abinda naji akanki gaskiyane nace au wai ya Mahmoud ne dama ina wuni.
Yace sai yanzu ma kika sheda muryana ko ashe ni marowacine ban dauka Samarin ki yanzu sin buda maki ido da kudi haka ba har kika daukan mu masu sonki saboda Allah da kuma mutunci ai banza muke ba.
Kince ina da rowa ina da miskilaci da rainin wayau duka naji badai kudi kike so a rayuwanki a dinga maki karya dashi ba to yarinua kinzo gidan yanzu indai karyan kudine.
Malam na fadama kafita harkata wallahi ko inje wurin baba Alh mai mota dasu hjy inkai karanka su rabani da kai da girma da arziki .
Ka fitar dani cikin rigiman ku don Allah na rokeka kafita harkata kuma wanda ya fadama nace hakan kace dashi nafada yazo ya daukar maka mataki a kaina tunda taji haushin abinda na fada.
Na kashe wayan ina tsoki tare da furta Samira da badon wani abuba zataga tsiya amma mu zuba a gidan nan nida ita shege ka fasa tsakanin mu nida ita yanzu.
Haka ma kwana ina mita a zuciyana itin matakin da zan daukarwa Samira tun abin nata ba rawa bane tumamine dole sai mun fito yita kowa yaji.
Ina Allah Allah gari ya waye in fito da zancen idan baba ya fita Allah da ikon shi saiga mama ita ta kasa hakkuri ta fasa tun baba na gida ta fito tana fadin.
Ashe zaton wuta ake a makera sai gashi a masaka to munafukan Allah ta,ala masu zuwa lahira da kararawa asirin ku ya tono kega me ya kin dauki yarki data iya tanbadewa kinkaiwa mamudan Alh mai mota ta baya don ku kuka iya karfa wa mutane.
Kun sani sarai daga ke har yarki wanan ba abu bane da zai yuyu a cikin gidan nan gara tun wuri kiwa yarki fada ta fita cikin tsabagana tun kan dare yaiwa rayuwan ku sammako.
Haba haba wai memene menene hakan don Allah tunda asubahi din nan wanan wani irin dabi,an bazane haka wai kamar kin kwana da mutum a zuciyan shi.
Bawai ba don da zancen su na kwana malam kowa ya sani gidan nan an aje magana kan hassana da mamud amma muna fukan Allah nan da basu da kunya suka zagaya ta baya sunaci muna duduniya don ha,inci.
Wai wani zance kikeyi hakane ban fahinta ba illa kumfan baki danaga kina kina halako zaka sani don nasan da bakinka ke nan aka hada hakan.
Ta ya ga yadda mukayu yanzu samira take bin baya suna haduwa da mamud lungu kuma har itace mai fadin zaizo gari aji a bakin ta donta nunawa mutane ta isa kome?
Baba yace ita samira djn kin sheda hakan nace kwarai ababa ina fitowa daki kamar an turoni nace baba n abinda Samira ke mun a rayuwa ya fara isata ban shiga harkanta duk abinda samira keyi a Zaria ban taba zuwa gidan nan na fadawa wani ba in kuma akwai wanda na taba zama nayi dashi yau kada maishi ya boyeni don Allah.
Amma baba haka samira take kokarin ganin ta hadani fada da kowa a gidan nan bama gidan nsn ba kawai ga mutane hakan take min.
Jiyan nan fa baba jiyan nan fa mukai magana kan ya mahmoud dukkan mu .
Bata fadi kalamin kowa ba baba sai nawa shine ta kira layina cikin dare yana fada min magana baba niba wai nashiga zancensu bane don Allah ai mata magana ta fita harka don Allah nagaji da wanan abinda samira take min baba.
Samira yaushe kika koma haka kuma ashe da gaskene kina tare da Mahmoud ke nan ban sani ba ita yar uwanki da uwarku tace zata bashi kikewa zagon kasa ke nan kome ?
Baba ni abinda Bantu ta fada shine ya bata min rai don me zata nuna wai bashi da hali in ban tare dashi aiba zance zan amso muna motanshi muje gidan buki ba.
Sannan kuma baba hassana da ake zance yace shi har yau bai sanda zancen ta ba bantu yaso tace bata sonshi ya dawo wurina muka shirya dashi.
Yanzu kuma mama zatace don me wanda zatai hadin yace baisan da zancen nan ba amma kuma,,,, ke mara kunya fitsarariya ki rufa min baki ko in makeki a wurin nan yanzu.
Yace yana sonki ko kikakai kanki gareshi samira nasan abinda zaki iya da wanda baki iyawa gidan nan to ina dai nina haifeku dukkan ku daga kan fadimatu daya zo nema harku dukka kanku biyun ba zab bashi kowa ba a cikin ku kada kuma in kara jin zancen Mahmoud gidan nan hakan ya isheni wanan abin kunyar har ina zaku kaishi wai ?
Dagake har Ussaina da ita Fadimatun daya furta ba zan bashi kowa ba a cikin gidan in kuma kuna da wani uba bayan ni sai kuje ya daura maku aure dashi.
Zancen sherin da kikewa yan uwa kuma kici gaba in Alheri kike shukawa kanki komai kika shuka zai kare daga yanzu bana son i kara jin muryan kowan ku a gidan nan kuma.
Ya juya ya shige daki ban tsaya ba na shige nawa nan na barsu kowa nawa kowa kallon nakasa a tsakanin su sai zuciya ke magana don ba daman fadawa juna magana.
Gashi bayan fitowan baba yake kara jadda masu cewa duk wace ta tayar da zancen kuma bayan fitanshi a bakin aurenta gidan shi haka yasa zancen ya mutu.
Naje nagaida iya a nan na kusa wuni wurinta muna hira cikin gidansu yana kulle ga motocinsu nan rurufe an aje nake fadin yau da Al,amin nan nasan da dashi zamu fita zuwa wurin buki nake ba iya labari tace.
Ai akwai motan da ake amfani da ita ba kinsan bala driver ba makulun yana hannunsa saiko yazo ya kaiki aikin zama yar gida yanzu Fatima.
Nan ta kirashi tayi mai bayani yace ba matsala karfe nawa zamu tafi zai zo ya kaimu ai ba matsala bane na fada mai time yace sai yazo din.
Tunda safe danaje gaida baba na fada mai zamu wurin bukin wata yar makarantar a nan cikin gari yace Fadimatu ba zuwan ba magane banson a dauko min nace jnsha Allahu baba ba zamu dauko ma rigima ba da yardan ubangiji.
Mun shirya din a daidai lokacin banyi tsamanin cewa Samira zata bimu ba saida Nura ya shigo yana fadin Anty Bantu ga wanan driver gidan hjy saudiya yazo yace ku fito idan kun shirya nace kace muna zuwa yanzu.
Muryan Samira naji tana fadin an samu motan ne ashe wani kallo na juyo ina watsa mata nace ansamu to barince ya bari dama har yace akaimu ai.
Ban iya bata amsa ba na shiga daki ina shiryawa digon rigace yar super exclusive akaiwa aikin duwatsu tare da wani yadi da akaiwa gaban riga kwaliya yaji stone har ya baci a ganina.
Idan bana juya ko nazo kusa zaka gane yaddin da aka halaka na super din ba sai ka dauka cewa yadin ne zallah akaiwa aikin ba atamfa a cikinshi ko kadan .
Hussainace ta fado dakin tana fadinsaka wani shiga zamuyi ne sai kuma taja tayi tsaye tana bina da kallo kafin tace anya kuwa dama hassana ta fadi bamu iya binki don kin riga dakin tanadi abinda zaki sakake.
Wani shigane banda mutum ya saka abinda dake gareshi dai tunda ba cikin amare muke ba mu amma dai kan ta fara taba kayan tana yabawa nace malam gara kije ki shirya zaifi.
Ai na rasa abin fadane yanzu mu wani kaya zamu saka nace din Allah kije ki duba ni dai banzo da wasu kaya masu yawa ba kan hanya nake.
Saidai wa yan nan dana bari a nan ki duba ko zaki samu mai maki a ciki ta juya ta nufi inda na nuna mata tana budewa tace ga kaya kuwa ta shiga zabe dogon rigan lace da wani bakin riga na material ta dauka ta dunkule a cikin hijjab ta fita dashi.
Nasan ita da yar uwarta ne ta daukarwa bandaiyi mata magana ba tunda nasan nafi karfinsu yanzu Allah ya tallafawa rayuwana don me kuma zan tsayawa wani hassada a yanzu.
Nasan taje ta fadane yasa mama ta fito ta kafa kujeran rabo mai kafa hudu da baya a kofanta haka kuma sauran suka fito suka zauna kofofinsu har fitowan mu duk akan idon kowasu muka fito.
Ashw itama samira ta dinka wani material da zatazo shita saka tana wani laudi ta fito sai gashi taga kowa ya kure a daka yafito a take ta hade fuska mukai masu sai mun dawo muka fita daga gidan.



ZAINAB IDRIS MAKAWA



KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
4?? 0??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE TAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Wurine sabon wurin event ga kyau ga tsada amma wurin ya kawatu sosai kuma suna da kayan aiki ko kuma don zuwan mu na farkone irin wanan taron yasa mukaga hakan.
Don muna nufo wajen hassana tace wai dankari don yawan motocin data gani wurin daga can gefe muka samu wuri ya faka muka fito.
Samira tace anya Bantu zasu bari mu shiga wanan wajen kuwa nace mu daije idan basu barmu ba ai sai mu koma.
Driver maman saudiya yace zai dan shiga gari idan mun gama mu kirashi nayi mai godiya ya tafi muka nufi hanyar shiga wajen ga kida yana tashi sosai a wajen komai tun daga waje zaki gane a tsare komai yake.
Irin tafiyan nan nawa nakeyi wanda mutum zai dauka jan ajine hakan sam ban farga ba naji an jawoni na juyo ashe hussainace.
Bantu ki duba sojojine a get din fa kuma suna duba pass to sai yaya na fada ba tare dana tsaya ba naci gaba da tafiya cikin karfin hali.
Mai karatu shi ilimi yana da dadi kuma akwai waye kai don inkin tuna na fada maki na jefa kaina women's center anan na fara samun bude ido balle yanzu da muke gogaiya a cikin diyan manya da irin mu yayan kananun mutane.
Bansan hakan yana da ma,anaba gareni sai yanzu get din muka nufa with full confidence a tare dani nan sojan daya tsaya ya murtuke fuska ya miko min hannu tare da kallon wayan dake hannuna na ciro katin da aka ban na mika mashi.
Yanu da hannu yan cewa go na mika hannu zan karbi katin naga ya yaga lokacin kunnena yajiyo min wasu murya a bayana suna fadin.
Itace fa itace wallahi bakama bace itace jin abinda ake fadan a bayana din don su tabbatar ko nice din sai dayan tace miss A A digital globa na juyo don naga mai maganan wasu yan matasane zasu kai sa,an mu a shekaru tsatsaye da katinsu a hannu sun sha kwalliya.
Wallahi itace itace kuwa ta fada tana murna nayi murmushi tace don Allah muyi photo mana nan mukayi photo da ita sojan nan na bakin get yana kallon mu.
Muna gamawa nace mu shiga hakan ya bamu daman kutsawa a tare da yan uwana muka shiga ba tare da an samu matsala damu ba lokacin tan matan nawa sojan bayani.
Nice gaba suna bina baya wata masu uniform dana gani tazo tana fadin daga fannin amarya kona ango nace amarya ta nuna muna inda dangin amarya ke zaune muka nufi can din kai tsaye.
Munyi sa,a kujerun ba wani suna don haka muka samu table daya muka zauna mu hudu nan suka fara rabe raben idanu suna kallon wurin ba laifi gaskiya don shigar mu ba raini a kanmu wajen.
Takardan event din kus kus ne ya tashi a wurin inda har wasu suka zo suna fadin excuse don Allah miss AA digital na dago kai naji wacan da muka hadu ta farko a waje na fadin na fada maku ai itace wallahi.
Ashe dama yar garin nan ce ke photuna muke dasu wanda yaba yan uwana mamaki Sajida ce take fadin wai wa nake gani kamar FGK najuyo don haka nake sakawa a takarduna sheda


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login