Showing 189001 words to 192000 words out of 347556 words

Chapter 64 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8752

suka dawo gida bani gidan a lokacin ina gidan su hjy naje mu gaisa da iya don tun dawowana saudiya ban leka gidan ba ko yauma din don kawai in fito gida namune nazo nan in zauna don kada inje gidan su hjy Larba ace naje gulma a lokacin.
Nako samu iya mun gaisa taji dadin ganina da tayi nace mata ina zaria ne tun dana dawo yanzuma nazone don babana baida lafiya shine nazo in gaida ita.
Tayi min ya jikin baba djn nace Alhamdullahi gaskiya yanzu na zauna nan muna hira da ita take fadin wai don Allah in tambayeki mana amma kiwa Allah yarnan ki rufani kinji kada ki nuna munyi maganan nan dake.
Wani iri naji tun kan ta fada min koma menene don nasan ba alheri zanji a bakinta ba lokacin irin kallon da nake mata cikin mamaki sai naga dattijuwar ta tsargu saita koma fadin koda yakema dai barshi kawai.
Ke dai ki kula dan Allah kada kace zaka saka rayuwanka inda Allah bai kaika ba ki tsaya ko yaushe a matsayinki kinji.
Kallonta nayi nace iya don Allah ki sanar dani idan anyi wani abune ban sani ba kinga sai in gyara nan gaba tace a,a dama ba komai bane dai saidai da kika je saudiya anyi wani abune a can ?
Ina nufin wani matsala ya dan farune tsakanin ku dasu hjy don yadda ta bugo waya tana ban umurni a kanki da ko shigowa nan ki zauna ba zan yarda kiyi ba gaskiya.
Gabana naji ya fadi lokaci guda na tambayi kaina tome ya faru a can har hjy zata bada umurni haka a kaina mai tsauri ni dai a sanina bansan komai ya faru ba gaskiya.
Toko shiyasa idan na kira a yanzu bata daukan wayana saidai waya yayi ta ringing ba a daga ba sai naji iyan tace kada ki dauki wana wani abu ke dai ki kama kanki kiji yar nan .
Don a yadda take wayan kamar ranta ya bace sosai dake lokacin wanda akwai abinda kikaje can kika aikata mata daya sata hasala hakan nan.
To kuma sai naga idan hakane aiba zaki zo gidan nan bama yanzu ki dubani hakan ne ya bani mamaki sosai da lamarin amma dai koma meye don Allah ki dan yi nisa da lamarinta don dama baka sanin halin mutum saika zauna dashi.
Haka kuma wasu suke ba su son kazo ka shige masu sai suga kamar kai din ma ha,incinsune saidaga baya idan sun gane su koma kame kame.
Nan dai ba zata san kina shigowa ba a bakina din nikan baki muna komai ba balle ta raba ni dake naku daba nawa daban dake don Allah idan kina gari ki shigo mu gaisa na rokeki wanan alfarman a gareni.
A raina nace abi wani sarkin kuma ai kila nida gidan nan har abada insha Allahu badai Fatima bintu ba kuma ayi da wani kuma bani ba insha Allahu.
Ban nuna mata komai ba a fili dai cewa da ita nayi insha Allahu iya kuma ni harga Allah bansan abinda nayiwa hjy ba illa kawai kafi mu taso dai naga canji a fuskanta a kaina bama ni kadai ba har sslima da muke tare amma bansan komeye ba.
Kai duniya abu uku sa goma ke na kuma sai naji bakin ciki da danasanin shigowa gaida tsohuwar da nayi ma waini wani irin bakin jinine gareni haka wai.
Na dan zauna kafin nayiwa iya din sallama don yamma da yayi sosai a lokacin haka na dawo gida cike da tunane ina tuhuma kaina kan a binda ban san nayi ba.
Nan kuma nazo na samu su mama sun dawo hankali tashe baba na duba ban tsaya sauraron kowa ba na fada bandaki na gyara jikina na fito na dan zauna har akai kiran magariba da aka rarage na nemi wuri na kwanta abina.
Da safe ma kodana fito na duba baba nagama masa abinda zanyi na koma na kara kwantawa barcin safe duk hayaniyar da nake ji baisa na fito a lokacin ba sai can naji muryan Samira a tsakar gida sama sama.
Tsuki naja ina gyara kwanciyana yar banzan ashe kuwa ta dawo a daren jiya di kenan soja shi yaje ya taho da ita koma meye dai shikuma yaje can ya karata da matarshi babu ruwana ni da tsiyarsu yanzu kuma.
Tunane dai nayi tayi barkatai a wajen idan an leko an gani sai ace barci nakeyi don yadda na kwanta din na lafe saman katifan dakina .
Can naji an leko murya hassana naji tana fadin Bantu barci kikeyi ne gafa mutanen nan yan gidan matar soja sun zo suna kofan gida.
Ban kaiga dagowa ba Nurama ya shigo yana fadin gasu nan zasu shigo mm a gyarawa baba shimfida da dakin na dan fesa kamshi kuma don sunce baba suke son gani.
Na dago ina fadin ka fadawa baba din za a shigo yace na fada mai ai mama ma tana dakin tare dashi jin hakan yasa ban tashi nafito ba na kalli hassana nace ashe ta dawo jiya din ?
Ta dawo misalin sha biyu saura makaga yar iska ta shigo bata tankawa kowa ba suka shige daki da uwarta da safen nan kuma dazun dai naga ta fito tana waya babu ko kunya a idonta ta nufi kofan gida bata jima ba kuma ta dawo.
Munji shigowansu gidan sun dan dade a dakin baba din kafin su fito subar gidan Nura da mamane a dakin shiyasa ban damu da komai ba a lokacin.
Don nasan zamuji komai a bakinsu daga baya hakan ko akayi don har daki Nura yazo ya samemu yake fada muna yadda akayi da suka shigo din.
Yace sun tausayawa baba sosai yadda suka ganshi har suke fadin cewa sun dauka ai common zazzabine kawai ke damunshi kawai ashe abin yakai haka.
Sun bada hakkuri sosai tare da alkawarin hakan ba zai sake faruwa ba insha Allahu yara sunyi kuskure nan da kwana biyu kuma masu aikin gyaran gidan zasuzo insha Allahu.
Ya kare da cewa aimu gaba ta kai yar iska mai zuciyan shedanu wanan tafi kama ai da irin arnan dajin nan masu bautan gunki da basa sallah basu masan meye addini ba sai iskanci.
Ya zauna yakai wani lokaci suna zancen dasu Usaina ni dai ban iya magana ba don zuciyana ba dadi abubuwa sun min yawa a lokaci guda idan badon ciwon baba ba ba abinda zaisa in zuna gidan nan don kadunan baki daya ya isheni a lokacin.
Har na fara sabon Allah a zuciyata ina zargi nace kodai wani yayi min sherin bakin jini ga duk wanda na raba sai ya hango illata don gashi hjy ma da nake ganin banda kamar yanzu gashi wani abu ya shiga tsakanin mu.
Sai daya saura suka fita dakin nawa na mike ina gyaran cikin rashin kuzari wayata dake saman katifa ne ya dauki kara na kalli wayan kafin in dauka.
Sunan Sojana nagani rubuce wani tsuki naja ina jefa wayan inda na dauko ta naci gaba da aikina ba tare dana kara kula wayan ba ya dauke can kuma ta bada dan lokaci ya kara kira.
Nan ma ban dauka ba har ya katse na shareshi can naji sakonshi ya shigo min a wayana sai lokacin na duba naga abinda ya rubuta shine.
Why baby bazaki dauki wayana ba meye laifina a cikin zancen nan ki dauki wayata zamuyi magana dake don Allah.
Kashe wayan nayu gaba daya ina maijin zafinshi gaba daya a kasan zuciyana don sai nake ganin duk shi yaja min hakan ba samira bama.
Sai dare na kunna wayan ina kunnawa kira na sake shigo min a lokacin na dauka na duba Nuran gwaggonane a lokacin ya kirani muka gaisa yake tambayana jikin baba din nace da sauki yace gwaggonace ke son magana dani.
Na dauka muka gaisa da ita ta tambayi jikin baba din nace da sauki can tace Fadimatu meke faruwa hakane tsakaninki da bawan Allah nan ?
Ni dazun ina zaune wani yazo yayi sallama Aliyu ya fita yace wai waya ya kawo za,ayi magana dani nan dai take mayar min da yadda ya fada mata cewa wai an dan samu matsalane kuma yanzu yayi ta kirana naki daukan waya.
A sanyaye na fara kora mata abinda ya faru tsakanin mu har abinda samira tayi da zuwan mu station da dawowanta gida har zuwa ban hakkurin da sukayi gidan mu yadda aka tsara masu .
Tace amma Samira takai yar banzan yarinya a haka zata kare zan shigo ai wana karon za a yita a kare su sakar maki mara hakana ki sarara abin yayi yawa kishi aiba hauka bane don abin ya zama hauka kuma yanzu saidai shi kuma ?.
To meye hakan Fadimatu shi meye laifinsa cikin zancen nan yanzu ai yadda akeyi duk yayi maki tunda ya nunawa matarsa da yan uwasa kina da muhinmanci a zuciyar shi.
Ko ba zaki cigaba da zama dashi ba dai yanzu ki saurare shi don Allah tunda har ya biyo ta wurina baki san uzurinsa ba da yake son kuyi magana dashi ba.
Koma meye bawan Allah na yayi muna mutunci shi zaki duba kada ki mata hakan lokaci guda kiyi hakkuri har naku ya hadaki dashi don nima ban goyi bayan ki shiga gidansa ba matarsa tana haka.
Nagode gwaggo na fada tace in gayar mata da baba in fada mai yayi hakkuri tana nan zuwa insha Allahu ina jin muryan Aliyu yana fadin a bashi wayan tana fada dashi ai yaga aro wayan tayi ko.
Tana kashewa na kara kira aka dauka nace abawa Aliyu din mu gaisa aka bashi yana taxjin dadi nake tambayanshi yana zuwa makaranta yace ehh nace toka matsa don Allah kasan alkawarin da dai mukaiwa malam yace yasani.
Ina kokarin kashewa naji yace yaushe zaki dawo anty nace Aliyu kasan don jikin baba nake nan insha Allahu daya kara jin sauki in hutu ya kare zan shigo.
Yace to Allah ya dawo dake lafiya ya kuma bawa baba lafiya na amsa da amin yake fadin gidan ne ba dadi yanzu gwaggo sauran tuwo take bani.
Dariya nayi ina fadi Aliyu baka da dama bari dai tajika yace ai bata kusa na fito nan waje mukayi sallama muka kashe wayan na sauke ajiyan zuciya.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
5?? 9??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Jin karan rufe dakin yasa ta dago kai tana kallon saitin dakin nasa shine ya fito a cikin shiri kallon hamnusa dake dauke da jakarsa na tafiya tayi sai tayi saurin mikewa tsaye.
Yau akalla sun kai wata takwas koma fiye da hakan cikin wanan hali na rashin kula juna a tsakanin su duk yadda taso yaki ya sauko ya fahince ta shi kuma bai sake ta ba bai kuma yi maganan komai ba bayan hakan.
Suna dai zaman doya da manja a gidan saidai inda hankalinta ya kwanta shine yana kula da basu abinci da duk wani abin amfanin gida kafin ya kare zai sayo ya aje saidai kawai ta samu ya aje mata shi ba tare da magana ba.
Haka suke zaman wata da watani wanda hakan ya dan ja mata dan rama da baki ta fada sosai sai tsayinta ya kara fitowa fili sosai a yanzu din.
Nufarshi tayi kafin ya iso gareta kasa takai ta fara gaidashi tasan ba lalai bane ya amsa mata don haka taci gaba da magana tana fadin honey kayi hakkuri da abinda ya faru banayi haka bane son in yaudareka.
Hannu ya daga mata a daidai nan kafin ta kara fadin wani abu yana kokarin wuce ta yaji ta rike mai kafa ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciyan mai saurarenta.
Tsaye yayi wuri daya cak bai daga kafan nasa yaci gaba da tafiya ba yana sauraron kukan ta kafin can ya hade zuciya yana fadin ki sake min kafa kada ki yardani idan ma yaudarane koba yaudara ba kinyiwa kanki ni dai nasan ban zalunce ku ba.
Wanan kuma ya rage a tsakanin ku illa abinda na sani shine kin cuceni kin yaudareni kin bata min sunan ahalina nan gaba yanzu kuma abinki zaki girba da kanki.
Yana fadin hakan ya fisge kafanshi daga rikon darayi mai din yaci gaba da tafiya yana jin gumjin kukanta haka baisa ya waigo ba saida yakai tsakiyan falon ya tsaya ya ciro kudi a cikin aljihunshi ya dora saman dan table din dake wajen ya fice daga gidan.
Motarshi ya nufa ya shiga ya tayar ya bar unguwar kai tsaye sai yamma zai bar garin don haka baida bukatan komawa gida yasa ya fito da shirinsa baki daya daga nan zai wuce airport ya shiga jirgi zuwa Abuja daga nan yabi wani mai zuwa kaduna kuma.
Yayi ta kiran layin Samira a lokacin bai samu ba wayar tana kashe yaji haushin hakan sosai don yana sonyin magana da ita a lokacin gashi kuma bai sameta ba.
Har ya shigo kaduna yana trying din layin bai shiga ba sai kawai ya share bai sake kiranta ba sai da safe ne yana gwadawa wayan ya shiga yaji ta dauka tana sallama.
Fada ya hauta dashi akan me ta kashe wayanta bayan tasan zai kira suyi magana don hakane ashe tafi daga dakinsu ta fita wajen gida sukai magana dashi din da har naji muryanta a lokacin nasan da cewa ta dawo ashe ?
A dakin nawa nake kwance shiru ni kadai a cikin dakin kafin inji motsin shigowan mama uwa kwance ta hangoni saman katifa take fadin wai har yanzu barcine haka dai ai gara ki tashi ki karya kumallo ki watsa ruwa ta fada tana aje min kofin sliver mai marfi data zubo koko a cikinsa sai ledan kosai mai zafi don tasan shi nake sha ni ban damu da tea ba kullun indai zan samu koko din.
Na dago kai ina fadin sannu da aiki mama aina tashi tun dazun yanzunma na gama waya dasu gwaggo tana gaidaku tace tana nan tafe ta kara duba jikin baba din.
Allah sarki ashe ta bugo jiyan nan fa na kare zancen ta nace da tana garin nan abubuwa ke faruwa yanzu data dauki mataki ko murmushi nayi nace.
Da tana tsoron wani babba baba yakamata ace ta fara tsoro kafin wani amma bata ji tsoron hakan ba ko tausayin halin da yake ciki ta iya aikata hakan kai tsaye ba tare da tunanen komai ba.
Dolene jn barta ga Allah duk abinda tayi tayiwa kanta bani ba ni nasan zafin mahaifina da yan uwana ko uwata data barni har yau bata waiwayoni ba nasan zafinta don in aka zageta ina jin ciwon hakan har kasan raina.
Zata waiwayoki Bintu nasha fada maki zafin zuciyane na abinda akai matane a lokacin yasa ta kasa manta hakan a zuciyarta amma nasan kina ran Habbi har yanzu.
Insha Allahu zakice na fada maki hakan zata neman ki da kafafunta wata rana insha Allah.
Kaina dago nace idan tana raye ko mama don nafi sakawa a zuciyana bata rayene yan uwanta kuma ba zasu damu dani ba tunda kince basuso aurenta da baba a lokacin.
Bintu mubi lamari yadda ubangiji ya tsarawa bawashi duk abinda ya samu bawa da sanin ubangijishi Allah ta hanyan addu,a saimu magance komai sannu a hankali don ba abinda ya gagari ubangijin mu Allah.
Insha Allahu kuma Ubangiji zai duba maki don ziciyarki tsakakakene zuwa ga kowa dazun nan naji Lanto nawa Samira wanan fadan a cikin zafin rai akan hakan.
Wayata tayi kara yasa mama din yin shiru ta kara nanata min in tashi inci wani abu a cikina kafin na kwanta kuma na amsa da to tana fita na dauki wayan sojane a layin.
A sanyayye nayi sallama shi kuma ya dauka yana fadin haba baby na kin tayar min da hankali sosai wallahi why zakiki daukan wayana please bayan kinsancewa ina cikin damuwa a kanki wa??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????nan lokacin.
Dan murmushi na sake na takaici a bangarena da har yana iya jina a lokacin naji yace baki yarda bake nan baby don naji kina mussun hakan dana fada.
Nayi karfin halin fadin akan me ba zan yarda da hakan ba tunda ban shiga zuciyarka na gani ba kadai kawai muyi hakkuri da juna da kai kuma.
Wanan wani irin maganane haka kuma nace maganan gaskiya don nemawa kan mu fari ciki tunda matarka ta fara


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login