Showing 246001 words to 249000 words out of 347556 words

Chapter 83 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8718

Bamuyi maganan komai da Ammi din ba a ranan washe gari naje gidajen yayyena muka gaidasu ashe malam Audi din ya dawo kamar yadda suka fada bana gida saiga malam ya kawoshi inda muke gidan ya mustapha a lokacin bayan ya gama zagaye gidajen sauran yan uwa yana tambaya ko ina nan tare da fada masu ai driver nane yazo daukana kunsa mijinta yazo shekaran jiya.
Driver fa yace wallahi nifa gani nake dama tanada aure ta gudo zuwa nan saiya tsaya yana shaka masu karya sai gashi suna jin wani iri kan yadda sukaki sake jikinsu dani da farko.
Har yakai suna labartawa mazajensu abinda malam din ya fada masu game dani din sai gashi sunzo suna tambayan Ammi din wai ashe dama inada aure na boye masu.
Mamaki Ammi din tayi tace ina wanan zancen ya fito kuma wanda zai aureta dai yazo har nan ya gaidamu don mu sanshi ta kira maryama tazo tace ta dauko mata kudin da aka bata.
Maryama taje inda ta boye ta dauko matasu ta kawo nan tace ta mikawa Sagir ya gani yace kai Mahmud dake shiga Abuja zai karbi lambaka a wajen kanwar naka ku gaisa wata rana idan ka shiga garin.
Kudin ya kirga ya dago yace dari biyune cif tace shiya bani ya kuma ba malam da yan gidan nan harsu maryamu duk an basu tubarkallah masha Allah.
Yanzu haka motan nan na kofan gida donta aka barshi a garin nan dashi zasu koma gida mustapha yace wanan bakar jeep din ta waje kenan na ganta ina mamaki na zata ire iren bakin malam ne sukazo wajensa ai.
Cikin gidajensu da muka yawata matar ya Sagir din kuma da muka kwasa da farko tafi saki jiki damu don su sauran na kula akwai jinkai a tare dasu sosai shiyasa ko dadewa bamuyi a gidajen nasu ba muka fito.
Wanka nafito saidana shirya na fito falon ina masu sannu da zuwa nagaidasu ya Sagir din ne ya fara fadin sister kinsan zamuyi baki shine baki fada min ba in dawo ranan ?
Dan kunya naji kafin nace wallahi yaya nima bansan zasuzo ba son basu fada min suna tafe ba sai ganin su nayi kawai sunzo.
Daga kaduna suke ko Abujan kai na dukar kasa ina fadin inafadin ina ganin dai Abuja suka fito don bai faye zama kaduna ba sosai amma dai yan kaduna din ne.
Ok dashi za,ayi ke nan na dago na dan kalleshi ina murmushi kawai a tunda kaga har yazo gaida ummi ai kasan dashi za ayi ke nan No ta fada dai da bakinta muji zaifi ya Mahmud datun fara maganan baice komai ba ya mayar da hankalinsane ga wayanshi.
To kinji shidai ne za,ayi dashi ko nace ban yanke shawaraba tunkuna yaya don ba wani abu haka a tsakanina dashi sosai amma sun nuna min kamar komai ya kammala a tsakanin ku Ammi ta fada tana kallona.
Ammi ni gaskiya bawai ya kwanta min bane don bai a,a yar nan meyasa zaki haka da alama yaron nan yana da mutunci fa.
Ummi don Allah ku barta tayi magana zancen aure akeyi yanzu kada azo ai mata abinda za a dawo ana da ansani kuma karshe dan kallonsa nayi yace waye mashi tukun ya kamata ku fara tambaya ai ?
Kota fada muna shi yanzu zamu sanshine tunda ba a garin daya muke dashi ba ya mustapha ya fada kunsanshi shine wana me digital global din da nake aiki dasu a Abuja.
What ya fada wai kina nufin shidin da kansa kome yadda ya mustapha din ya tambaya yasa ya mahmud din dagowa shima da sauri ya dan kallesa yace.
Ummi wanan yar taki babbace gaskiya kinsan wanda ta kwaso maki har garin nan kuwa wani yarone dan manya masu fada aji shine fa yazo haba nikan nayi mamakin waye zai barwa mace mota irin wanan a nan garin .
Kudi yake samu na banza dole ya rasa me zaiyi dasu irin yan karyan matasan Abuja din nan kawai mayaudara masu bata mata ya Mahmud ke fadin wanan maganan.
Zuwa lokacin na fahinci yana kushe Boss don tun fara maganan nan dasu banji ya fadi wani alheri game da wanan zancen ba sai kokarin kushewan da yakeyi a kai.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
7?? 8??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Idan nace ba soyayya nake da boss ba ban fadi karya ba don banga wani sign din soyayyana a tare dashi ba a kaina asalin mutumin da ko kamanina akace ya fada ba zai iya fada ba kai tsaye don haka don yanzu nace ba soyayya muke dashi ba mutuncine ko mutuncin da oga Abbas bada shi din ba .
Mai karatu kin san alaman nuna soyayya ga da namiji balle wanan da yake tashen lokaci ako ina a kasan nan don me kike son na zure ga abinda bangani zahiri ba karshe in fada a ciki.
Muhawaran da akeyi yanzu a falon kaina tsakanin ya mahmud da ya mustapha shiya saka Ammi saka masu baki da sauri tana fadin ya isa hakan ke tashi ki koma ciki bana son kananan magana ya taso a nan don Allah.
Dakina shiga na barsu a falon bansan meta fada masu ba na daiji fitansu daga wurinta din don ba kara jin hayanitarsu ba hakan yasa na gane cewa sunfice daga gidan a lokacin.
Lafewa nayi saman katifan ina faman tunane a zuciyana don yanzu dole in koma gida ke nan a cikin satin nan din wanan tarkon da suka dana min na barmin malam Audi driver ya mayar dani gida.
Kknga ba zan zaunar da bawa Allah a garin mutane har tsawon wani kwanaki ba in kuma na koma gida a yanzu bayan kowa ya gama sanin cewa ina wurin dangin uwata sai su fara kus kus cewa banji dadin wajen bane na dawo yanzu ai.
Gaba kura baya karen daji nasan halin yan gidan mu wajen tsegumi da dane can baya da ban girmaba an samu abin jifana dashi da zaran nayi dan motsi kadan zakiji mama tace ke tafi wace ko dangin uwarta gudunta sukeyi nan kikaje suka koroki.
Yanzu ko dana girma cewa zasuyi ban samu abin kwarai bane yasa na dawo a fara dan kuskus ana tsegumi a tsakaninnisu yanzu ya zanyi da rayuwata ke nan.
Dole dai in koma donsun dana min tarko da bazan iya kaucewa ba a yanzu tunda na fara jin ya Sagir yana tambayan Ammi din yaushe zan koma gida ke nan tace sai sun zauna da malam mijinta.
Kwanciya na gyara don shigowa dakin da Fadila tayi tana fadin na dauka barci kikeyi ai Ummice take tambayan ki yanzu nace kinyi barci banyi ba barcin dai nake son nayi.
Jin cewa Ammi na nemana yasa namike zaune yarinyar ke fada min ta fita waje taga wasu don Ammi sana,an kifi take sosai a garin kuma sana,an ya karbe ta don tana cikin manyan yan kasuwan kifi a gashuwa din da sunanta yai fice.
Don haka ko yaushe cikin baki take masu daukan kifi wajen ta sai masu lalura zasuzo ta wajen malam daga nan shi kuma sai ya aiko a kirata ta fita falo din wurinshi inda bakin suke.
Barci na samu sosai sai wajajen yamma na tashi da wani irin ciwon kai nasan ba komai ya jamin shiba a lokacin don barcin da ban samu ba isashe ga kuma tunane a zuciyana.
Na idar da sallah na fito falon don in dan samu abinda naci kafin in kwanta Ammi tana zaune waya takeyi a lokacin a cikin yarensu don haka bansan me take fadi ba a lokacin.
Na bude kulan abinci na dan diba kadan a cikin plate nasa dan miya kadan a sama na zauna a nan kasa gefen kujera ina ci.
Muryan Ammi dince dake kallona naji tana fadin gata a kusa dani ma ta fada da hausa jin hakan yasa na dan juyo na kalleta ina kawar da kaina gefe daya lokaci guda.
Sai naji tace karbi waya Fatima ki gaisa da mahaifiyarki dama an katse layukan kasan ne don rikicin zaben da sukeyi yanzu kuma an maida masu don an dake zaben.
Kokarin miko min wayan takeyi na girgiza kaina nace ki gaida ita Ammi bansan me zance da ita ba kona karbi wayan a cikin murya mai rauni kuka nazo min lokaci guda.
Kanki daya kuwa mahaifiyarkice fa a kan layin yanzun nan ta kirani zakice ba zaki karba ba fushi kike da itane kome na girgiza kai ina fadin a,a Ammi bandai san me zan fada bane.
Kara wayan tayi a kunnenta tana sauraren abinda take fada mata a bangarenta kafin naji tayi yaren a cikin kakausar murya ta gama ta miko min wayan.
Dole na karba na kara a kunnen sallama naji tana mun na amsa da wa,alaikis sallam muryanta rarara a wayab zakice a fili take sai dai hausanta a yanzu ya juye ya koma da harshen yarensu don jin abinda take fada nayi kamar yaren nasu tana fadin.
Kuna lafiya ya wajensu iyayyen naki lafiya kalau suke na fada har lokacin muryana yana nuna alaman kuka da kuma rawan murya a gareni.
Murmushi naji tayi tana fadin kiyi hakkuri wallah ba mantawa nayi dake ba kina raina nasan muddin kina raye wata rana zaki nemeni alkawari nayi a lokacin ba zan taba taka kafana kaduna ba gidan mahaifinki da sunan ganin ki shiyasa kuma,,,,.
Nagode ina gaida mutanen gida na mikawa Ammi din wayan saina fashe da kuka mai tsuma zuciya cikin mahaifiyata da baba na rasa me laifin daya wofintar dani haka a cikin duniya na koma kamar marainiya a cikin mutane.
Na taso a mara gata mara asali saboda fushin zuciyar dake tsakaninsu harni abin ya shafa yanzu tunda gashi ta fada da bakinta cewa tayi alkawarine akan hakan ba zata taba waigena ba muddin ina gidan mu idan na girma zan kawo kaina duk inda take.
Gashi yanzu din na kawo nan na mike nashiga na barsu suna yare da Ammi din a falon kuka sosai nayi saboda na fahinci wani abu da Ammi din ke boye min a yanzu.
Tunda na tashi da safe na fara shirin komawa kaduna ba tare da sanin Ammi din ba su maryama dai sunga ina hada kayana kila watace a cikinsu ta fadawa Ammi din kamar tafiya zanyi fa sunga ina hada kayana.
Saigata dakin ta shigo lokacin ina rolling din gyale a kaina jin muryanta yasa na dan juyo ina amsa mata tabini da kallo kafin ta saukw idonta akan yar jakata dake gefena a tsakar dakin.
Ya haka Fatima me nake gani hakane kanki daya kuwa an fada maki ana fushi da iyayyene kome ke tsakaninsu ai badake acikin matsalansu ba balle ya shafeki a yanzu.
Na fada mamaki matsalan da aka samu ko tayi maki wani maganan da ba daidai bane jiya din na gurgiza kai don kuka yaci karfina a lokacin.
To ba inda zaki tunda kinzo nan ni da kaina zamu maidake gida albashin in mahaifiyar taki sunzo sai mu zo tare da ita har gidan naku mu dubaki a can.
Bazata zoba Ammi bazata taba zuwa ta dubeni ba nasani yanzu na hakkura da son ganinta zan koma wurin mahaifina shida ke kaunata akul akul kada ki kara fadan haka Ammi din tareni ga fadin abinda nake fadi lokacin.
Duk maison ki wallahi bayan mahaifiyarki yake ita datayi wahalan cikinki kuma ta haifeki ba zaki san hakabi yanzu don zuciyarki ya rufe da zargin hakan da kike ganin shine gaskiya amma kin taba jin inda uwa ta guji yarta a duniya.
Bacin raine na yarda suka rabu da mahaifinki shine yake taba zuciyarta ta kasa mantawa da hakan muyi magana sosai a jiyan da ita zata zo nan muje har garin naku insha Allahu.
Don haka ki kwantar da hankalinki kada fushin zuciya ya dibeki ki fada ga halaka wanan zancen bai shafeki ba kinji diya itama nayi mata fada sosai a jiyan tagane kurenta ta ban hakkuri hakan kuma saikece zance kiyi ki kasayi Fatima ?
Jin hakan yasa nakai gurfane daga inda nake tsaye da dankwali a hannu na sake wani kuka cikin sauti mai gumji wanda zaiba na kusa dakai a lokacin tausayin mai kukan.
Dan takowa tayi zuwa inda na zube din ta kama min hannu zuwa dakinta a bakin gadonta mai tarkace a nan ta zaunar dani takoma gefe daya itama ta zauna har lokacin kuka nake ta zuba min ido na dan wani lokaci kafin naji ta dafani tana fadin.
Fadima kukan ya isa haka nasan irin zafin da kike ji a yanzu shiyasa ban hanaki kukanki ba kokya samu sauki a zuciyan ki amma kukan ya isa hakana yanzu.
Na dauka aikinsan abinda kikeyi tunda Alhamdullahi kina da ilimin ki wadattace akanki naboko dana alkur,ani don me ba zakiyi koyi da sunna ba ki rugumi kaddaranki kamar yadda kika saba din.
Kuskuren fahinta kikaiwa mahaifiyarki bawai tana nufin bata kaunarki bace a,a har yanzu haushi da takaicin yadda mahaifinki da yan uwanshi da matarshi suka rabaku da juna take tunawa wanda kuskurene ana son bawa da yafiya a zuciyanshi dama hakan rubutacene a gareku gaba daya.
Alhamdullahi tunda mahaifiki bai wofintar dake ba bayan ya raba tsakanin ku din keda bakinki kika fadi hakan kuma ga zahiri mun gani baki tare da wahala ko kadan a tare dake sai hamdallah da godiyan ga ubangiji.
Don wani idan kinji labarinsa naki din nan ba komai bane haka kuma gashi ubangiji har wayau din nan ya hadaki da yaro mai hankali da sanin ya kamata wanda insha Allahu da alama karshen kukanki yazo a yanzu din.
Duk da kin nuna bai kwanta maki ba wanan ba komai bane yau duk wanda ya nuna damuwa a gareka har ya kula dakai haka yadda yaron nan ya bar komai naki yazo har nan don ya tabbatar da inda kike ai baki da babban masoyin daya wuceshi a yanzu.
Da farko nayu kwadayin zmanki da daya daga cikin yaran nan na nasa cewa ba zan barki ki koma gida ba kinzo kenan kusa damu ba zamu kara barinki zauna a cikin maraici ba a rayuwanki.
Amma zuwan yaron nan garin nan da irin gatan da na hango zai gina maki yasa a yanzu na janye wancan manufar tawa a kanki don haka ni da kaina zan kaiki gida har gaban iyayyanki.
Don su kara sanin kina da gatanki har yanzu ke din ba marainiya bace yadda wasu ke daukan ko Nuratu tana raye kota mutune a yanzu ta barki haka shiru ba waiwaya.
Zanje mu zauna dashi muyi magana kuma a kanki din don haka don Allah kome ke cikin zuciyarki a yanzu ina son ki janye hakan a ranki ki fahinceni.
Nasan a cikin yan uwaki nan da akwai wanda suka nuna ra,ayi akanki kai na dago da sauri na dan kalleta tace kwaeai cikin kada kai tare da fadin nasanke baki fahinci hakan ba dama amma yanzu duk ki jaye wanan suma a yanzu sun san ke ba sa,ar aurensu bace ai koga iliminki kowama yasan da hakan.
Don Allah ki kwantar da hankalinki ki fahinci yaron nan dake sonki donshi din masoyinkine na hakika duk na fahinci hakan a gareshi a cikin dan zaman da mukayi a falon nan.
Kina jina yata ba zanso abinda zai cutar dake ba a yanzu don jinki nake wallahi tankar nice na haifoki ga cikina tun ranan da kikazo garin nan .
Fadawa nayi cikin jikinta lokaci guda ina sake dan kuka mai sauti sai naji ta shafo kaina tana fadin kiyi shiru fadima kukanki ya kare a yanzu ba gani a kusa dake ba a yanzu ko Nuratu tana kasan nan nidin ce dai uwar taki ko yaushe.
Kai na gyada alaman gamsuwa da abinda ta fada din daga nan ta fara share min hawaye naji ta kwalawa maryama kira tazo tayi mata yaresu na somalia larabci da surki haka taje ta hado min shayi na daiji shayin a cikin zancen.
Muna nan tana ta min nasiha har maryama dinlb tadawo dauke da kofin shayi yana tururi a hannunta ta aje a gabana ta koma ta dauko bread ta kawo na kada kai ina fadin shayin ma ya isa ai don ban iya cin komai a lokacin saboda safiya yayi da yawa ga kuma zuciyana daba dadi a tare dani.
Haka na daure nasha shayin Ammi na zaune ta kura min ido tana cigaba da ban baki ta hanya karfafa mi zuciyana tana fadin saina yaba da halin mahaifiyata duk


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login