Showing 84001 words to 87000 words out of 347556 words

Chapter 29 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8745

a dakin hjy zaune ok bari muje muyi sallama ya fada yana mikewa tsaye.
Tare suka shiga dakin mahaifiyar tasu tsohuwar ke fadin ashe yana kusama da ake zancensa ya amsa da fadin muna daki tare da Alhne akai masa sallama ya fita.
Kafin ya duka yana fadin ina kwana hjy ta amsa tare da fadin ina ita matar taka maijin kyamar yan uwanka don taki sake jiki da kowa a gidan nan ita a dole ga yar birni ko muko kauyawa.
Haba yaya kaf gidan nan wa tafi ko wa takai da zata rainawa mutane wayau wanan iskancin ya tsaya can washi da ta raina tayi masa amma ba nan ba gaskiya.
Yazo yayi aure a gida cikin mutunci ga yaran arziki nan masu tarbiya da rikon addini amma yaki yaje yayi yadda ransa keso yaje ai gata nan gashi mu dai ido muka zuba masa ai yanzu kuma.
Ayi hakkuri hjy ai na kusa aure a nan din yanzu insha Allahu ku dai tayani da addua nan bada dadewa ba zan gabatar maku da wace zan aura din idan mun shirya.
Kadama kayi din uwar nasa ta kara fada zakayi aure ita wanan ka kaita ina lokacin da muke hanaka ba ki kayiba kaje kayi son ranka a can don haka da kayi da karkayi a yanzu dukka uwarsu daya a garemu.
Hjy da gaskiya yakeyi fa ku bari dai komai ya daidaita zakuyi alfahari da hakan kuma insha Allahu sai hjyn rigachikum din tace yar nan din ka samu baiyi magana ba sai ibrahim dake tare masane yace.
Yar nan makwabtane ma yarinyar jira dan lokacin kadan zajuji ko wacece kuma zakuyi marnaki da kuma farin cikin da haka ya kasance komai dan lokacine fa hjy.
Allah ya nufa akwai aure a tsakanin shi da ita wanan din kinga abinda Allah ya kaddarowa bawansa babu mahalunkin daya isa ya hana hakan gareshi.
Ai dama kun saba da zaben tumun dare waiku ala doe kun girma ba ayi maku dole kuje in muna raye ai maji ko meye insja Allahu hjyn rigachukum ta fada .
Shine dai bai samu zuwa gun wasila din ba sai wajajen azahar koshi yaje yayi wankane don ya sauya kayan jikinsa zuwa wasu na daban.
Tana zaune a dakin duk da tana cikin dakin hakan baisa ta kunna haske a dakin ba don dakin koda ranane wani lokaci sai kayi amfani fita haka take zaune tacika tayi fam sai wani huci data keyi saboda bacin rai da take a ciki lokacin.
Yana shiga dakin da sallama yakai hannunshi a makunnin wutan dakin haske ya haska ko ina na dakin can ya hango ta zaune ko kai bata dago ta kalleshi ba.
Shima haka dakyat yake daga kafanshi don zuciyar shi datayi mai nauyi a lokacin yake jin kansa ba dadi a lokacin don haka shima yanayinta bai ko kula da hakan ba.
Ganin batayi mai magana ba yasa ya nufi uwar dakin kwanan zai shiga nan yaji muryanta tana fadin amma dai honey kasan baka kyata min ba yau.
Kasan tun jiya na shirya kayana akan yau zamu koma saika shiga gari kayi zamanka ka barni nan ina zaman jiranka ni gaskiya baka kyauta min ba kasan fa na baro mimi a gidan Rita.
Juyowa yayi yana kallonta kallonta kafin yace me kike nufi da hakan munyi dake cewane yau zanu koma ko kafin muzo na fada maki iya kwanakin da zamuyi a nan ne ?
Ko kuma kin manta nan din wurin iyayyena nazo ba wani waje ba ke har inkina da adalci kinsan darajan iyayye aike mai fada min gaskiyane idan ma nace yau zamu koma.
Yaushe rabona dasu da zanzo inyi dan wanan kwanakin kuma ana gama buki washe gari ince zan koma kin daukeni wani sgagalale ke nan kome don ban gane me kike nufi ba ?
Ganin yadda ransa ya bacine yasa tausasa murya tace dashi ni ba haka nake nufi ba naga buki mukazo ai ba ganin su ba kuma bakace min ga iya kwanakin da zamuyi ba idan munzo na dauka da an gama bukin ne ai zamu koma a yau.
Don hakane nabar mimi a gidan Rita ban kaita gidansu anty ba yace wanan kuma matsalan kine ai kinsan gida zamuzo ba wani wajen shakatawa ba don me baki daukota mukazo da ita ba.
Yana fadin haka ya shige ciki ya barta a zaune inda ya sameta wanka ya shiga ya fito ya shirya a cikin wasu farareb kaya nasa yana fesawa jikin shi turarene ta sameshi a dakin .
Kallonshi tayi tana fadin ni dai gaskiya baka kyauta min don wallahi ko kayan kirki ban deboba iya na kwana uku kawai na dauko da niyar yau zamu juya mu koma.
Mahmoud din ya dago ya fara magana cikin daga murya yana fadin ban gane me kike nufi ba wasila kina nufin sam baki son gidan mu da yan uwanane kome kike nufine wai ?
Na kula don dole kikazo gadin nan har yakai baki iya boye meke cikin zuciyarki tun zuwan mu har yasa mahaifiyata daga zuwan mu ta fahinci manufanki.
Yanzu na tabbatar da ace son gaskiya kike min da kinsoni da kowa nawa koda kuwa ace gidan mu a cikin dokan daji yake inda ba mutane zaki soni a yadda nake ashe ke ba hakan bane a zuciyarki.
Ganin yadda yake maganan ransa abace komai zai iya faruwa a tsakaninsu a lokacin data danyi mistake din fadin wani kalaman da ba daidai ba yasa tace kayi hakkuri nina dauka ai yau dinne zamu koma .
Baiyi magana ba ya fita ya barta a dakin bai dawo ba sai dare ya shigo ya samu har lokacin bata wani sake ba ya fita batun ta sati daya ya nasa cewa zasuyi don hakan sai sunyi zasu koma ke nan.

Baba ya dawo gida yana zaune yana cin abincine shiru baji na shigo gaidashi ba yake tambayan mama Lanto da cewa wai Fadimatu ta fitane banji motsin taba tunda na shigo.
Ance sabo turken wawa don danaji motsin shi nake lekowa in masa sannu da zuwa lokacin baya kuma da nake suya a kofan gida daya sauka zan taso inbawa mai mashin kudin mashin ingaidashi.
Yanzuko dana bar harkan suyan awara yana shigowa gidane zan fito in masa sannu da zuwa hakan yasa yau yaga har yadawo sallah baiji motsina ba.
Kamar ba zata amsa mashi ba saida takai ruwan daya wanke hannu waje ta watsar take fadin bata fadama yau zata koma zaria bane halan ?
Zaria ya fada cikkn mamaki yace takoma zaria din ne amma bata sheda min hakaba da safe da muka gaisa da ita ai mun dai gaisa tayi adawo lafiya kawai.
Kowa haka ya gani don ko yarinyar nan bata fadawa cewa zata tafi ba yau don ta dauka sai gobe ko jibine zasu koma sai gashi tace zata tafi wani yazo nan kofan gida ya dauketa suka yafi.
Wani kuma baba ya tambaya cikin mamaki tare da karawa da wani wa kuma tace ni ina zan sani andai ce wani mutum fari mai kama da balarabe ne yazo gida ya dauketa.
Ta dauki kayan abincin zata fita baba ke fadin inkinje ki turo min uwa yafita ba tare da amsawa ba taci gaba da tsabgoginta sai zuwa can ta leka mama uwa take fadin malam na magana dake.
Mama uwa ta shigo ta sameshi zaune kasa inda mama Lanto ta barshi yana shan bbc a yar redio shi ta kara gaidaashi ya amsa ya dago yana fadin wai yarki ta koma zaria yau ?
Ayya wallahi malam tace in fadama aikin can ne yasa na manta nima bansan yau zata koma ba ai sai gashi ta sameni daki tace min wai zata tafi.
Sako nanan ta bani in bakama ya katseta da fadin ance wanine yazo har kofan gidan nan ya dauketa ai tayi salati ta sanarwa ubangiji kafin tace malam bafa wani bane.
Wanan yaron dan wanan hjyn da take mutunci dashine ya bugo mata waya a gabana yake fadin mamansa tace wai yau zata koma har ta yafine ko yazo ya kaita har take mai wasa da bata so yace Allah mama tace in kaiki zaria.
Shinefa yazo ya dauketa bayan ma ai harta shirya ta fito da kayantane ya kirata shine za,acema wani kuma kai gidan nan dai munafuci da son kai yayi yawa wallahi.
Yarinyar nan bata tafi ba aidata dibar muna duk dan abinda matan nan ta hada mata ta bamu kafinta tafi din kuma ni tafiyan nata ai ina tunanen akan babatun da Altine tazo gidan nan tayine da safe yasa ta tafiya yau ai.
Barin daukoma sakon naka ta fada ta tashi ta fita tabar baba zaune cikin mamaki har ta dawo yana zaune a yadda ta barshi leda ta miko masa yana kallo yace meye a ciki ?
Wallahi malam ban sani ba yadda ta banshi na aje sai yanzun nan dana dauko maka shi na kara tabawa bansan ko meye a cikinsa ba nima.
Kai Allah ya kawowa yar nan miji mai albarka tayi aure ta huta da kace nace din gidan nan shine fatana a kullun wanan abu kamar cin kwan mahaukaciya ?
A toh wanda yace bai bari ai shima ya haifa duniya ce fadine da ita in wani yakika da kwana wani da wuni yake neman ka ai.
Don yanzu kan muda ganin bintu gidan nan sai wani ikon Allah kuma don ta kwashe kusan kayanta kaf ta loda ta tafi kaga sai wanda ya ganeta kuma ke nan.
Ban fahince ki ba tace ah malam da can ba dan daukan wanda zasuyi amfani dashi sukeyi ba idan zasu dawo su dawo dashi su canza yazo ko gaba daya naga ta kwashi kayanta ta tafi dasu.
Da nayi mata magana cewa tayi zata dan dinga zuwa don kai tana dubamu kaga kenan ta koma zaria din da zama take nufi ke nan baba yace haba uwa tana komawa zaria gaba daya ba tare da sanina ba.
To alama dai ya nuna hakan gaskiya don kusan kayan amfaninta kaf ta dauka sai yan kadan ta bari a nan din koshi ba wasu abin azo a gani bane.
Tace kuma Nura ya zauna dakin nata da zata tafi kag??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a ke nan ba lalai bane zamanta ya dawo nan yanzu kuma ?
Wai me Altine din tazo tace matane tace a irin dai maganganunsu na nuna isa da gadara tayi tayi nan a tsakar gida tana zage zage tana sake haibaici shine kawai .
Bari naje na karasa aikina ta fada tana fita lokacin baba ya jawo ledan yana budewa dambun namane da maman saudiya ta bani sai wani leda dana cusa baki a ciki ya bude kudine sabbi kar yan dari bibiyu ya gani acikinsu.
Idan baki manta ba mai karatu wanan kudine da maman saudiya tasa yayanta su bani shine na sakawa babasu a cikin leda na kulle.
Ido ya lumshe lokaci guda shi kadai yasan yanayin da yake ciki a lokacin baice wa kowa kalla ba illa da gari ya waye zai fitane ya leka dakin nawa nura na kwance yana barcinsa har lokacin ya tayar dashi yana zagi da fadin wanan ai tabi,an banzane namiji dakai kayi kwance haka kana barci har wanan lokacin.
Dole yaron ya mike yana kame,kame yace baba ina kwana yace kayi sallah asubah yace tare fa muka jera dakai muna bayan ku sanan ya sake labule ya juya yana kallon mama dake aikin koko tana wani fisge fisge baice mata kalla ba ya juya ya fita.
Yana fitane suka hade da Alh daya fito shima zai shiga gari a lokacin gaisawa suka tsayayi inda Alh din yace ya shigo ya saukeshi kasuwa yace a,a Alh kada in takura maka dana kai nan bakin titi zan samu abin hawa yace assha muje kawai in saukeka ai.
Baba ya shiga suka dauki hanya yake kara masa bangajiyan buki yacewa baba sai hamdallah kasan yanzu buki na yarane kuma ai .
Donsu su sukai kokarin su a wanan sha,anin mu namu shawara ai in fadama malam garba shi dan yau da kake gani idan ka fahincesu bisu da adduan fatan alheri kawai a rayuwansu.
Don inda duk suka dosa ta ba wani mahalukin daya isa ya karkatosu sai idan sunkai sunga ba daidai bane suda kansu zasu gane kuskurensu akarshe.
Shiya ban dauka komai da yawan zafi kan yaro a yanzu donshi Mahmoud lokacin da muka hanasa auren wanan yarinyar ya zagaya baya yaje yayi yanzu lokacin dana masa baki kona furta wani kallama da bai dace ba a kansa kaga tayi cikin mu ga baki daya.
Don hakama uwarsa na taushesu na hana kowa maganan a lokacin yanzu ba gashi an zauna lafiya ba malam garba.
Baba yace kwarai kuwa Alh kaika fahinci dan yau a yadda suke kuwa amma ni iyalina sun kasa gane hakan kullun kokarinsu da jahilcinsu akan yarinyar nan bintu yake su daiga sun mata tabo a cikin rayuwanta shine burinsu akullun.
Inka debe uwa yanzu da suke dasawa da ita kaf dinsu gidan yanzu har yaransu basu kaunar yarinyar nan a rayuwansu.
To ai baka sani ba malam garba wanan Fatima da kake gani kamar taki suke zuba mata ai a cikin rayuwanta don lamarin yarinyar akwai al,ajabin rayuwa a cikinsa saidai me hankali zai gane hakan.
Duk fa bukin nan da akayi gidana wani ci dasha wai ace yar karamar yarinya kamar Fatima itace ta tsara masu komai kuma tayishi yadda ya dace ba a samu matsalan komai ba wanan kawai ai ya zamo abin mamaki gaskiya.
To su basu gane hakan sun kasa gane ko wacece fadimatu a cikinsu ita dai uwar biyu kishin nan na uwar yarinyar ta rike a ranta har lokacin nan ta mayar akan yarta.
Ita kuma Lanto yanzu akan yarta take yaki da fadimatu don fadin gaskiya a,a don me zata fadi gaskiyan abinda yarta keyi a can wanan ya zama sheri kada ka kara donshi ta daura danmara da fadimatu.
Kuma wallahi Alh ba fadimatu ta fada min ba ita da kanta tazo min da zancen wai tana son yarta tabar gidan kanwata ta koma wurin masaukin dalibai da kwana.
Hakan yasa nagano da wata akasa don na tambayeta hujja bata dashi shine ni kuma hankalina bai kwanta ba naje na ganowa idona komai na dauko yar na dawo da ita shine ta dora laifin ga fadimatu akarshe.
Abin mamaki saiga fadimatun ta baro karatunta ta biyo sani Allah sani ma,aiki harta shawo kaina na yarda suka koma tare kagani basu gane yarinyar saboda mugun nufi da suke dashi a zuciyarsu.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

[8/20, 10:17 AM] Maman Aslam: KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
2?? 6??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI AKANKI YAR UWA, , , , , , ,

Washegari sammako nayi na shiga school don nasan an dan wuceni ga karatu ina son in danyi covering din haka nafito gida da sassafe nazo na karbi handouts a hannun Ezekiel don yana shiri dani sosai a ajin mu.
Gashi ba kunya kowa ke nuna mashi kyaman zaman tare dashi niko ba wani zama bane sabon da nayi dasu a canne har nake danjin yaren yasa muka dan shaku dashi .
Saiya kasance ashe shima mayen karatune sosai in bai fahinci abubu a fara naci sai ya gane me haka yake nufi zai bar mutum ba yabon kaiba dama karatu naci da kwakwafewa yake so tare da mayar da hankali.
Don hakane na kara yankewa kaina shawaran in tsaya in fuskanci karatu na a yanzu shine mafita a gareni ba zama zanyi ba ko nan zaria din don zan fara dan buga bugana saboda biyan kudin makaranta.
Ban dawo gidaba sai gap da magariba na shigo a gajiye na samu gwaggo ta gama hada abincin dare don shi kadai sukeyi a gidan.
Saiko abin karyawa idan ya sauwaka idan babu kuma kowa ya nemi abinda zai danyi kallaci dashi a waje idan ya fita duk damu bamu damu da abin karinsu ba tunda da safe muke barin gidan kafin ma gwaggo ta hada mun fita ko.
Tuwon masara miyan kuka tayi shina zauna naci bayan na idar da sallah don dan cock da meat pie kawai naci da safe shine kuma a cikina har daren .
Ina jin baba ya dawo dana fito na wanke hanni gami da kurkure bakina na nufi wurin baba din mijin gwaggo ina gaidashi ya amsa tare da fadin ashe kin dawo tun jiya saidai na samu kinyi barci.
Na dawo baba ya kasuwa baba ya washe baki yana fadin Alhamdullahi kasuwa yanzu sai a hankali yanzu masu abinci kawai ke samun kasuwa don su dole aje masu amma irin namu marina


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login