Showing 174001 words to 177000 words out of 347556 words

Chapter 59 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8777

dakin na samu ya zauna na kara masa ina kwana ya amsa.
Yana min ya hanya ya na barsu hjy a can kuma na amsa maibda Alhamdullahi suna gaida ku har mijinta yace ai masa godiya a wajen ka idan nazo.
Muke da godiya nida suka rikewa ya amana ai anyi aiki lafiya Allah yasa makasudiyace na amsa da amin baba ina dukar da kaina a kasa.
Yace sai kuma kika dawo kika samu zance ya canza Allah dai ya nufa yaron nan samira zai aura a cikin ku don nasan an fada maki komai yanzu kan.
Nace haka naji baba Allah sanya alheri yace amin yar albarka abinda su Suwaiba da diyanta suka kasa ganewa ke na har yanzu sai tsuki burutsu sukeyi kan zancen auren .
Sunki su gane Allah ne maiyi ba wani ba Fadimatu yaya zanyi yaran nan sun kai mu ga manya unguwa sukai kara mu ai dole in yarda tunda ba shedani nake ba.
Nace kwarai baba ai gara ayi tunda sun shirya da junansu mekuma za a tsaya jira Allah dai ya basu zaman lafiya yace amin tare da dora fadin.
Hankalinki da fahintar ki Fadimatu yasa nake yarda da lamarin ki tun kina karama amma uwayanki kaiya su gasu manya sun kasa wanan hangen a zuciyar su.
Ayi hakkuri baba na fada cikin ladabi yace hakkuri ai dolene Fadimatu in banyi hakkuri ba dukansu zanyi ko ita wanan data fita ai ita ta kaini kara kan ba zata zauna gidan nan ba muddin nace sai samira ta auri yaron nan Mahmoud.
Baba ai da bakabi ta nata ba tunda bacin raine yasa ta hakana kayi hakkuri don Allah na sake fada yace haka fa ta zabawa kanta barta aiga gidan nasu nan taje ta zauna tunda haka yafi mata.
Zata dawo ba don Allah inma zuwane baba kaje kabada hakkuri mama ta dawo dakin ta hakan ba girmanku bane irin wanan har yakan shafi yaya yayi shiru kafin yace dani.
Ba matsalan komai a yanzu wurin karatun naki ko nace dana dawo shine na tsaya gyara komai yanzun ba matsala insha Allahu.
Mun dan taba hira kafin na mike yace Allah yayi maki albarka ya baki miji na gari na amsa da amin na mike na fita na barshi yana shirin fita daga gidan.
Mama Lanto kan iyakana dasu gaisuwane daga ita har yarta samira nima ina ganin hakan na kama kaina saikuma habaici dake biyowa baya naji Samira na waya tana fadin makka dai yanzu da ya zama ruwan dare.
Muma muna tafe ai kwana nawa ya rage muma muje mu taka arfa da mukaman ibrahima muma da zamu ta hanyar gaskiya bana yaudara ba mama uwa ta kalloni na girgiza mata kai don mutum biyu ke fada ai.
Rashin kulasu yasa ba wani fitina dana huta na fita zuwa kasuwa da yan canjina duk da nasab su kadaine a hannuna lokacin amma haka nayi kundunbalam zuwa sayo abinci dashi.
Sai ganina akayi na sayo buhun shimkafa galon manja maggi gushiri masara da geron koko na aje a gidan ban tafi ba saida na kara yiwa baba magana akan dawowan mama na komane washe gari Usaina ta kirani tana fada min cewa mama ta dawo mun kuma san aikinkine hakan bantu.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
5?? 4??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Nan nake labartawa gwaggo abindake faru a gidan namu ashe bata da labarin abinda ke faruwa a gidan namu ranan tayi fada sosai da baba.
Ina muna mata hakan ba komai bane don harga Allah ba zan iya auren ya habibi ba dama amma gwaggo tace ko bazan aureshi ba aini ya fara nema ba samira don me baba zai yarda a bashi samira din.
Da kyat na lalasheta ta hakkura ta daina zancen banyi wasa wurin cikawa Aliyu alkawarinsa nakaishi wani makarantan gwaunati a unguwarmu na dinka mai kayan makaranta.
Ban ankara ba sai gashi na tashi da dubu biyu kawai a jakata Alhamdullahi tunda muna da abinda zamuci a gidan mu da gidan gwaggona.
Sai hakan bai dameni sosai ba don zanyi manejin kudin motan da zan dinga zuwa makaranta a haka da maneji har gwaggo tasa min hannu data kula banda kudi ga Almajirin mu kullun sai nabashi dari na cin tara a school.
A dadafe har sati uku ina cikin kan bandashi gida balle waje amma ina hamdallah ga Allah idan na tuna da rufin asirin da Allah yayi min don ko ba komai ina fita tsab ba tare da wani ya gane gazawata ba sanan ina iya cin duk abinda na samu a lokacin ba tare da duban inda Allah bai kaini ba.
Duk da raban gidan masu arziki da nayi idona ya bude da ganin abin duniya a yanzu hakan baisa na jefa kaina yanzu cikin damuwa ba ina hamdala ga hakan dana tsunci kaina.
Tsorona da fargabana a yanzu shine inji cewa abincin gidan mu kona gwaggo da muke dan maneji ya kare shine kawai fargabana a yanzu din.
Yau ya kasance asabarce don haka bamu fita yasana shaki barcina nasafe a ranan duk da ina jin motsin gwaggo tana ta dan aiyukanta na gida amma na kasa tashi in fito a lokacin .
Don tunda na dawo ban samu barci irin wanan ba sai a ranan nakuwa yisa sosai ashe soja nata kirana ban sani ba don sau daya mukai waya dashi ymtun bayan dawowana Nageria.
Saidana tashi naga kiransa dama na Usaina wanka na fara yi dan wake da maida yaji gwaggo tayi shine abin karin kummalon safe har abincin rana sai dare a girka abinci kuma.
Bayan na shirya na zauna inci duk da yai danyi haka nake hadiyansa don yunwa nake ji sosai a lokacin.
Muryan wani yarone daga kofa yayi sallama tare da fadin wai ance ana sallama da Fatima a waje ?
Shiru nayi ina saurare kafin naji muryan Aliyu na fadin muje inga waye suka fita da yaron sai hakan ya bani dariya saidana dan murmusa a raina ina fadin Aliyu hoo.
Sai gashi da gudu ya shigo yana haki yace anty wallahi mutumin nan ne mai zuwa bakiga motan daya zo dashi ba yau harda sojoji yazo yana waje.
Hannu na tsame daga abincin na fita na debi ruwa a randa na wanke hannuna daki na koma na dauko mayafi na dan gyara fuskata tare da dan fesa turaren saudiya a tufafin da gyalen na saka takalma na fita.
Yana zaune gaban motan daya bude kofan kafafuwanshi duka biyu suna waje tunda na fito ya tsura min idanu har na karaso inda yake.
Gaidashi na fara fuska daure amma kuma sai naga ya tsura min ido kawai bai amsa min ba nima dan kallonsa nakeyi saidai nakasa ido da ido dashi na dukar da kaina kasa.
Nace haba malam kayi sallama nazo ka wani kura min ido kamar yau ka fara ganina a hankali naga ya lumshe idanunsa tare da danyin murmushi ya na bude idanunnasan.
Kallon meye haka wai kona sauya makane suffane daga fatiman daka sani zuwa fati yanzu ?
Yace kwarai kuwa don gaba daya kin sauya min wallahi kin koma wata irin classic baby din nan ko wata hjy fatima hakan nan saboda tsabar haduwa.
Lalai ruwan saudiya daban yake Allah na yarda da fadin mutane da sukecewa ko ya kake idan kaje saudiya saika canza.
Murmushi nayi har hakorin gold din dake tsakiyan fararen hakorana yadan baiyana yace ehhye ashe dai har sheda kika saka amma hakorin nan ya karawa fara,anki armashi.
Na karkada kai mai nuna bakada dama din nan nace saidai kuma duk kyan danayi akwai wa yanda suka fini ai don nasan bani kadai aka fara fadawa hakan ba.
Yayi dariya sosai yace badake wacece na fadawa hakan kuma nace waya san iyakanmu mata da yawa a gari kamar jamfa a jos.
Murmusawa ya danyi kada kai yace shedan da zaki min kenan kuma baby na ki yarda dani daga Salbiya saike banda wasu yan mata kamar yadda kike zargina.
Trust me salbiya a gida ke kuma next to be insha Allahu ko baki yarda sani bane jn rantse maki na gane me kike tunane tun lokacin da kikasan ina da aure gaba daya kin canza min kin hana zuciyata sukuni.
Na dubeshi a wani irin yanayi nace ni bansa ka rantse ba tunda nasan matsayina a yanzu wajen ka din me zan tsaya saika rantse min.
Yace to shike nan amma dai kinsan ni musulmi ne ba dan auren zobe ba don haka me zaisa gabanki ya fadi da hakan akwaiki da yawan tsoro gaki amaryan soja.
Dariya ya bani nace kai wallahi baka da dama ina kataba ganin soja yayi mata biyu inba akanka za a fara ba yanzu.
Yace Ahaf haka dai kuke fada saunawa akayi soja har mai mata hudu akwai gasu nan kuma suna rayuwansu lafiya lau ke bari kiji nifa ba ragon maza bane nasha fada maki.
Nace wai zance ni dai yau ya akayi ka tuna dani ko madam dinka ta koma kasan wajene ka samu tunawa dani yau ?
Kai ya kada yana fadin zan baki mamaki kuwa Allah zaki gane ni din bana wasa bane nan dai mukasha hira sosai dashi da zai tafi yai min alheri ta ban girma damashi gaskiya hannunsa a sake yake.
Wanan zuwa kan kamar ya tsomani aljanna naji ga kudi ga sayyaya yace yar makarantace ni saida sayayya kullun donshi dan ba,ane ko yaushe tun wanan zuwan muka koma kamar yadda muke baya dashi muna waya lokaci lokaci.
Ban bari abincin su baba ya kare ba na dan aikawa nura kudib ya sayo masu abinci a gida gashi kome akayi sai su Usaina sun kirani sun fada min wani lokaci harda mama idan tana kusa don bata da kunya.
Usaina dince ta kirani tana fada min cewa rikici ya barke tsakanin mama lanto da baba wai yayiwa yarta kayan daki marasa kyau don an rainasu za ayo masu tsohon yayi a jibge mata.
Dariya nayi nace ai yayi kokarima da har ya samu yayi masu kayan dakin da har suke rainawa in basu so su sayar su cika suyi mai kyau.
Ance rana bata karya saidai uwar diya tayi kunya buki saura sati biyu shiri ake gadan gadan ban shigo kaduna ba tun zuwan danayi dawowana makka har lokacin ban koma ba.
Ban kuma fasa danyin akke gida ba ga baba ta hannun Nura ranan baba ya kirani yana fada min yadda suka kwasa da mama Lanto don yakan dan kirani kwana bibiyu a waya mudan yi hira dashi.
Nina yarda rashi nasaka bawa komai a rayuwa shiyasa idab kaga mutum a cikin wani hali kabarshi kawai kada ka yanke mai hukuncin daba daidai ba .
Don irin hakane a gidan mu yanzu gashi dai baba yasan ni mace ce ba namiji ba amma yana min kyakyawan fahinta da halaiyana.
Mun gama waya lafiya da baba ya kashe wayan ina jin tausayinsa da safe saiga wayan Nura hankali tashe wai baba baida lafiya ya fadi.
Ina kuka nakira soja ina fada mai koda taimakon da zai min kafin inzo yace ba matsala zai tafi kafin nazo yakoje asibitin ya duba gaskiya sauki sai gun Allah.
Don baba baisan wanda ke kansa ba baisan wanda yazo koya tafi ba hakan dai yake kwance zuwan sojanane yasa aka canza mashi daki aka kaishi amenity room a ward din maza .
Haka muka iso hurjajan tare da gwaggo harda Aliyu daya matsa zai biyoni yaje ya roki malaminsu mukazo tare da niyar in sun wuni sai su koma a ranan.
Sai dai ina yadda mukaje muka samu baba din ya tayar da hankalin kowa don haka gwaggo ta tsaya zata kwana dole soja yayi min kokari sosai akan baba don tun yana turowa har yakai yazo da kansa yagani yakuma ga likitan dake duba baba din shine har yasa aka canza mashi daki.
Dare kuma bayan na isone yazo kara duba baba din nan suka shigo da likitan dakin akasa adan rage yawa a dakin yayi yan aune aunesa ya kara rubuta wani magani da za a sayo shine har muka fita dani dashi da Hassana muka tafi.
Da kyar muka samu maganin sai tsada yasayo zamu dawo kuma ya tsaya wani shago ya sayo muna kayan tea dasu bread har gassasu kaji dasu abinsha.
Koda muka dawo mun samu matan gidan mu duk su ukun sunzo harda samira a lokacin muka shigo da sayayyan Hassana ta aje da Nura a gefe daya bai tafi ba saida akaiwa bana allurab da wasu abubuwa kana yai muna sallama zai tafi.
A nan ne na taso na rakoshi yake kara kwantar min da hankali yana ban magana har ya tafi ashe kuma bayab fitan mu Samira ke fadin ashe ina tare da wanan mutumin har yanzu ?
Nura ya amshe da fadin ai kinsan halin Bantu ba yarson hayaniya bace ita balle ta kama fafawa mutane ta nuna ita itace yanzu ba gashi hali ya nuna kansa ba.
Kai kuma Nura ba zancen ka bane wanan da zaka karba don naga idan ,,,, ke ke kirabamu da diban albarkan na naki bashi ya taramu a nan ba zaku kawo muna sakarci a wurin nan.
Wanan wani irin halin rashin tarbiyane haka mahaifinku yana kaance a cikin wani yanayi da damuwa zaki kawo muna wani zancen banza a nan yanzu kuma.
Dakin yayi tsit gwaggo ta fara binsu da idanu tana kallonsu takara da fadin koma wayeshi mun gode masa ga taimakon nan da yai muna ina dai ai ba mutumin banza bane dai ?
Wanda yasan darajan mahaifin na tare dashi aiya gama muna komai a rayuwa yanzun kan don haka banson in kara jin wani zancen banza kuma a nan.
Nikan nashigo dakin na samu rayukansu a bace har hankalina ya tashi na fara bin kowa da kallo na juya na kalli inda baba yake kwance har lokacin yana numfashin nan sama sama baisan inda yake bama.
Nace lafiya dai ko a cikin damuwa ba komai Usaina ta fada rai bace na danje wurin da ake karawa baba din ruwa na duba na dan tsaya ina kallon yadda yake faman bautan Allah idona ya cika da hawaye na juyo na koma wurin bango na rakube ina kallonshi tare da tunane .
Yau in baba ya mutu ya barni ni fadimatu yaya zanyi da rayuwata a duniyan nan cikin yan uwana dasu kadai na sani a rayuwata yanzu ?
Bintu zoki zauna mana mama uwa ta fada na dan motsa ina sauke ajiyan zuciya alaman dawowa daga tunane gwaggo tace yarinyar nan tun safe komai bataci a cikinta ba.
Fitanta ke nan sai gata ta dawo min da mugun labarin nan na ciwon yaya muka dungumo zuwa nan tun lokacin banga taci wani abuba a cikinta tana tsaye tun dazun akansa.
Bantu ki bude mana kiga ko akwai abinda zaki iyaci kici zaki zauna da yunwane haka ai gara ki dan sha naga kamar drink's ne a cikkn wancan ledan.
Waya kawo mama ta tambaya hassana din tace wanan saurayin nata ya sayo muna shi da zamu dawo ta mike tana fitar da kaya nan kowa ya mayarda hankalinsa yana duban abinda ke cikin ledojin.
Kamshin dakwalan kajin gassasu ya dauki daki lokaci guda ko ina ya dauka a nan kuma ta kara budan wani tsirene mai zafi yaji hadi a saman shi sai su kayan tea da sauransu a wajen.
Takowa nayi zuwa bakin tabarman da gwaggo take zaune na dan takure a bayanta cikin damuwa ina dukar da kaina kasa motsin hassana naji a kusa dani tana aje lodojin a gefena ta koma ta dauko dayan tazo ta zauna a kusa dani ta kara bude ledan.
Na dago nace bari a dibarwa gwaggo dasu mama sai muci sauran naga ta fara diba kadan nakai hannu na raba biyu na aje a gaban gwaggo.
Na kara dauko wanan na hada da daya da ban baraba nace basu mama wanan saimu muci wanan ki raba shi yadda ya dace kowa ya samu.
Ba kunya nan kowa ya shiga ci wanda na dan faraci na tuna da Aliyu dake waje zaune yace zaije sallah bai shigo ba nace wai gwaggo ina yaron nan ya shiga ?
Duk abinda mukeyi samira bata dago kai kota kalli inda muke ba saida taji gwaggona fadin kici bari in raga masa wanan ai yayi min yawama ni kadai.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login