Showing 198001 words to 201000 words out of 347556 words

Chapter 67 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8781

zuciyata don a dan takin nan kallo daya zaki min ki gane ina cikin wani yanayi na tashin hankali.
Don yadda yanayi ya koma zai nunawa mutum banda kwanciyan hankali a tare dani ko kadan karfin hali kawai nakeyi ina wayancewa da mutane.
Tun da naga lokacin da suka fada ya gabato hankalina ya tashi sosai don maganan ya Ahmed ya zauna min a zuciyana dayace hakan ya zama kafirci ina tsoron wani abu yazo ya samu mahaidin mu yan uwa suyi kuka dani daga baya.
Hakan yasa na fito daga dakin na zauna a wajen haraban asibitin ina kallon masu fita da shige cikin asibitin yayin da kasan zuciyana yake fal da damuwa da tsoro tare da fargaba.
Lafiya kike wanan tunanen haka muryan Oga Abbas ne ya ratso dodon kunnuwana a lokacin kafin in kai ga dago kai kamshin turare ya sanar dani tare suke da Boss din mu lokacin.
Don wanan kamshin garesa kawai nake jinsa don shi kadai na sani mai amfani da wanan turaren dake da matukar dadin kamshin gamai shakarsa.
Lafiya meke faruwa kika zauna a nan ke kadai cikin tagumi wanan karon a cikin harshen hausa yake min tambayan a hankali na dan girgiza kaina garesu alaman ba komai a tare dani.
Wanan maganan nasa da nake mamakin yana tare dsshi suke saurin fahintar meya fada har su gane da sauri abinda yake fadi saboda yawan saurin maganansa mai kama da i,i,niya da yake.
Ko yanzuma din shi yayi min yana tambayana babu dai wani matsala amma rashin sabo da wanan yasa ban fahinceshi ba da sauri dayace.
Ko wani abin ne ya samu baba din kuma kika dawo nan kika zauna Oga Abbas ya fahinci ban gane ba yasa da sauri yace yako farfado tun dazun din nace ya farfado ya koma barci ina mikewa tsaye daga zaunen da nake.
Sai a lokacin na samu daman gaisawa dasu ya amsa a cikin irin yanayin maganarshi kafin yace ina dakin da yake din ?
Yana daga ciki na bashi amsa ya dan fara tafiya zuwa cikin suka bishi a baya cikin girmama a gareshi duk da kusan duk sun girme masa a shekaru.
Amma dole tasa suna binsa a baya yanzu saboda girma da arzikin da Allah ya bashi suna bayanshi a yanzu don suci arziki gasu zasukai kamar su bakwai zuwa takwas dake tare dashi.
Sun sami likitocin akan baba ashe sunzo tafiya dashi dakin awon nasu inda zasu sakashi cikin ijin dinsu na gwaji su gano ainihin abinda ke damunsa din.
Nan suka tsaya suna dogon turanci da doctor din yana masu bayani abinda suke son ganowa akansa muna kallo aka gara baba duk hankalin mu a tashe muna masa fatan fitowa lafiya cikin tashin hankali.
Za a gara shi ya lumshe idanu ya bude kuma yana fadin abinda ba kowa ke ji ba nida ya Ahmed muka matsa kusa da sauri yaya duka yana son gano me yake fadi lokacin .
Ya dago yace dasu godiya yake maku yace waye babba wanda ya dauki nauyinshi din cikinsu aka nuna masa shi ya mika hannu yazo kusa ya tako shida Abbas zuwa wirin shi har lokacin lik???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?itocin suna tsaye.
Yace nagode da alherin ku gareni kona mutum a haka ga iyalina nan ku kula min dasu don Allah na baka Fadimatu da zuciya daya kayi hakkuri ka karbi alherina nasan zakayi alfahari sosai da hakan.
Ba zaka taba danasanin auren Fadima a duniya insha Allahu duk wanda ke wajen ya gane me baba ke nufi hakan yasa naji wani kunya da nauyi da bacin rai ya ziyarceni lokaci guda.
Saidai halin da baba din ke magana ciki bai bari na koma takan hakan ba sai rakiya da mukai mashi har zuwa kofa iya inda zamu iya tsayawa ke nan.
Ko kafin mu dawo mun samu sun fita daga dakin harsun juya sun bar wajen sai Oga Abbas da ya tsaya muna tare dashi kuka nakeyi sosai a lokacin tun lokacin da baba din ya fara maganan.
Sorry wanan ba komai bane adduan ku yake nema kawai a yanzu don avbin yazo masa da sauki oga Abbas din ya fada wanda wayanshi da yai kara ya hanasa karasa maganan daya soma din.
Sai cewa da yayi OK sir yanzun nan zamu bar asibitin dasu insha Allah ya sake fadin OK sir ba matsala insha Allah.
Duban ya Ahmed yayi bayan ya kashe wayan ya tura aljihu ya dago yana fadin yanzu zan kaiku masauki don kuda ganinsa sai nan da kwana uku masu zuwa insha Allahu.
A firgice kowan mu ya kalloshi yace ehh don kafin su fito dashi dare yayi sosai don haka kuma a ICU zasu ajiyeshi ba kuma zasu bari kowa ya shiga wurinsa ba tsawon wanan kwanakin.
Don haka yanzu muje a dauko kayan ku a kaiku a masauki ku huta don kuma akwai gajiya a tare daku ku huta don ko kun tsaya a nan din haka zaku zauna cikin fargaba a wajen asibiti don ba yarda zasuyi a kwana masu a ciki ba don haka mu tafi yanzu in sauke ku.
Nasan don mama data fara fadin a,a gara dai a zauna a nan din aga halin da yake ciki zaifi ta ya za a barmai jinya haka shi kadai cikin wanan halin ?
Gidane mai kyau gidajen wajen duk irin ginasu dayane yadda ya wacin ginan garin yake wanda ko gidanjen tsarinsu kafin kakai wajensu sai ka wuce masu gadin get din gidajen sanan ka shiga.
A house number thirty seven ya tsaya da mota a bakin get din gidan kafin ya fita yasa key ya bude gidan ya dawo ya shiga motar ya jamu zuwa cikin dan karamin packing space din dake a ko wani gida na wajen.
Ya tsaya yana fadin bissimillah ku fito mama kuyi hakkuri kun gaji ko ga gidan mun iso ai a nan zaku zauna har zuwa lokacin da Allah zai bashi lafiya ku tafi.
Amma ke dai ba zama zakiyi nan din ba ai na wani lokaci don karatun ki ko tunda akwai wa yanda zasu tsaya dashi a nan din.
Ehh dama so nayi muga yadda abin zai kasance saina koma Nura yazo don yaya yaji saukin abubuwa shima da sauri yaya din yace a,a basai yazo ba meye a ciki tunda bama asibitin zamu dinga kwana dashi ba.
Gidan ya bude ya shiga muna biye dashi a baya yasa hannu ya kunna wutan gidan haske ya kama ko ina tar kamar rana a lokacin gida mai kyau lafiyayye zakice akwai wani a cikinsa da yake rayuwa a cikin gidan dama.
Dakuna ukune da wani spare ta falo ga kitchen ga backyard mai girma ruwa ko available ko yaushe gaskiya tsarin gidan ga baki daya ya ban sha,awa.
Ga kuyeru na alfarma lafiyayyu masu kyau na alfarma ga tv bango babba a falon gaskiya gidan zaici lokaci idan na tsaya bayani iya tsaruwa dai ya tsaru gaskiya.
Nan yayi muna sallama yace zai tafi dare ya soma ya fita tare da ya Ahmed ya dan jima kafin ya dawo da ledojinsa a hannu lokacin na idar da sallah ina duban wayana naji muryanshi a falo don haka ban fito ba sai bayan dana dan rage na fito zuwa wajen su a falon.
A daidai dan karamin corridor din da zai sadaka da falon gidan dan dogon corridor din naji muryan mama na fadin wanan ai son kaine ya nuna.
Muna tsaye a gaban mu zai furta hakan kaga ke nan yai mata gata koda bayanshi bata da wallah ni malam ya ban mamaki yau sosai wallahi wai ya mayar damu mutanen kawai zaice ga Amananta nan wai,,,,
Da sauri na juya na koma dakin na kwanta don nasan dani suke ke nan wanan zancen da baba yayi cikin zafin ciwo ya batawa ita mama rai ke nan.
Shirin kwanciya nayi nabi lafiyan gado na kwanta na laife zakice nayi barci a lokacin don yadda nake kwance sun dade kafin mama din ta shigo don a daki daya zamu kwana da ita.
Sai can bayan wani lokaci naji shigowanta dakin tana fadin ita wanan har tayi barci ashe to Allah ya kyauta gamu dai kamar ba jinya mukazo ba kuma mun koma jin dadi kuma a nan din mu kadai.
Duk abinda take fadi a kunnena ban motsa ba har ta gama ta kwanta a gefena don gadon babban gadone ko mu hudu zai iya dauka sai dai bata kashe wuta ba can naji ya Ahmed din yana rufe kofofin waje dana cikin gidan.
Sai da naji ta fara nasarin barci na tashi naje nakewaya na fito na kashe wutan dakin na dawo na haye gadon na kwanta bansan lokacin da barci ya dauke ni ba sai gashi badon Allah ya gyara ba ranNdana na makara sallah asuba don dadin barcin dana samu zuwa safe din.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

.KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
6?? 3??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Washegari koda muka tashi ba wani abinda zamuyi tunda munji ka,idan asibitin don haka bamu wani damu da saurin zuwa duba baba ba saidai hankalin mu yana yajansa.
Muna tunanen ko wani irin hali yake ciki a lokacin don tun idar da sallah mama ta fara magana har yakai yanzu da nake gyaran gidan ta kara magana kuma da ya Ahmed ya fito tana fadin.
Tir da irin wanan rayuwan nasara din shiyasa akace komai na nasara ragagene ta ya za ace kana jinyan mutum ba zakagan shi ba kuma ?
Wanan kan ai halin kafiraine har wani abu yazo ya cika da dan uwanka wanda ba,aso shi yayi kuka dakai kan ka zaluncesa.
Inda munsan hakan ne tsarin yake gaskiya da bamuzo ba jiya ko barcin kirki banyi ba don fargaba ta ya mutum mai jin jiki kamar malam zaka barshi a hannun wasu can da bai hada komai dasu ba suna jinyar sa a kafirce don ba zancen bissimillah ko kalman shada a wajensu ai.
Gaskiya dai wanan taimakon a yanzu ya koma min ciki gaskiya ba zan boye ba nagane inda zancen ta ya dosa a lokacin don dani take wanan maganganun nata dai a lokacin.
Kasa hakkuri nayi a karshe nace amma mama naga hasaran baba a yanzu na kowace ni kaina bawai na taba zuwa bane wajen nan balle nasan ya tsarinsu yake tun farko asalima bansan wajen nan ba ni .
Taimakon nan kuma da akai muna ta dalilina ba yin kaina bane na dauko baba zuwa nan a yanzu ni kadai asali saida na nemi shawaran kowa a cikinku akace hakan yayi kyau azo don yanzu munzo mun samu wanan matsalan meye laifina a cikin hakan ni ?
Bantu bar zancen nan don Allah ki kyale mama tun jiya da kika fara maganan nan naja maki burki amma bakiji ba ki duba irin kulan da baba yake samu tun jiya da mukazo can a gida da koke magana wa zai bashi shi a cikin mu kaf ?
Yarinyar nan duk yadda akeyi tayi iya bakin kolarinta da mahaifin mu bai kamata kan wanan tsarin nasu a bata mata ranta bakuma tunda lafiya mukazo nema kuma ana kan neman insha Allahu.
Iya ka dai in zaman nan dinne bai maki ba sai ku koma gida keda ita azo da Nura da mamansa mu zauna tare ya Ahmed ke wanan bayanin daga tsaye inda yake tun fitowan shi a dakin daya kwana din ciki.
Ba dole in fadi haka ba jiyan nan ko runtsawa banyi ba fa saboda da tunane da sauri na dago kai na kalli mama din cikin mamaki .
Matar da ko motsina bata ji duk tashin da nakeyi bata ma san nayi shiba sai nasarin ta take har nazo na tayat da sallah amma duk bata sani ba ko sallah asuba saida na tayar da ita da kyar ta tashi kada ta makara.
Kofan get din gidan namu ake duka alaman wani yazo gidan ke nan wurin mu kallon juna mukayi ni da yaya don ita mama bata dauka gidan ake duka ba lokacin.
Nan nefa ya fada yana kallona nace ehh nan ake nocking waye zaizo wajen mu yanzu ya fada hankali a tashe ya bude kofan falon zuwa waje.
Nikan addua nakeyi a cikin raina Allah yasa ba wani abu bane ya faru da baba don hakali yana wajen shi dama gashi ba wanda zan kira in bincika halin da baba din yake cike balle mu sani.
Sai gashi kuma anzo ana dukan kofan mu da safen nan dole hankalina ya tashi a lokacin bayan tunawa da maganganun mama a garemu.
Kofan na zurawa ido kafin naga shigowan ya Ahmed dashi da wani mutum a bayan shi dauke da basket din abinci da sauran ledoji farare daya riko again.
Bayan mun gaisa dashine yake gadin madam breakfast na kawo maku daga gidana oga ya ban kwangilan daukan nauyin hakan gareku.
Godiya nayi mai ya gaisa da mama ya tafi mama kan ganin kula har yawunta ya tsunke balle da aka bude taga abinda ke cikin kulan .
Mikewa nayi na shiga wanka kodana fito na samu suna karyawa nace ya idan kun hada sai muje asibitin muji lafiyan baba ko ?
Kada ya shiga damuwan rashin ji daga garemu tunda tun jiya bai ga kowa daga cikin mu ba gara dai yana dan ganin mu jefi jefi zaifi.
Nima dai yanzu nagama wanan tunanen a zuciyana mama ta fada tana kai cibi a bakinta da take faman hanbudawa cikinta lokacin.
Sai can ya Ahmed din ya dago kai ya dan kalleni kafin yace dani ke ba zakici abincin wai ya fada ya tsureni da idanuwan shi yaji amsan da zan bashi lokacin .
Dan murmushim yake nayi kafin nace dashi sai mun dawo zanci yanzun safiyace sosai idan na karya yanzun zai iya zama min matsala.
Cinyar kaza mama ta dauko tana tusga kafin tace mu kan ai idan ba,aci yanzu ba shine matsalan saidai idan kina da wata manufa a kasan zuciyan ki naga tun jiya bakya cin komai tunda muka sauka garin nan.
Haba mama wani manufa kuma ke a zuciyanta kuma kallansa tayi tana hade naman data tara a baki tace nasani ni tunda ban shiga zuciyarta nagani ba amma meye mutum bai iya yi a yanzu.
Mama ke nan aiko ina cuta ba zan iya cutanku ba idan na cuci uwata kuma da dan uwana waya rage duniya da bazan iya cuta ba ke nan kuma ?
Kawai dai halin rayuwace kawai haka akidana yake bana cin abinci da wurini na gajarce zancen kada yai muna nisa nida ita don ta dauko zancen da zuciya bai iya dauka a lokacin sai Allah ya gyara ban dauki zancen da zafi ba a wajena.
Karfe tara muka fito muka nemi abin hawa sha daya muna cikin asibitin sai dai bamu gane komai ba don kuwa ko likita bamu da mukamin gani balle baba don basu bamu daman hakan ba tunda bamu muka kawo baba asibitin ba duk da sun sheda fuskokin mu muma mun sheda nasu.
Amma ganin baba bai yuyu a garemu ba ranan saima da zamu fitane wanan ma,aikaciyan bahausa bahausa da mukaita sintiri da ita akan baba din ta hango mu tai min hannu naje wurinta muka gaisa.
Itace ke fadin dama basu fada maku ba zaku ga baba sai nan da kwana uku masu zuwa na dauka ai zasuyi maku bayanin hakan a jiyane don kaidar asibitin nan ke nan .
Amma baba ya nasamun sauki sosai don koda safen nan na shiga nagaidashi jikin nasa kuma yana samun sauki sosai Alhamdullahi gaskiya aiki za ai masa naji yar uwar aikina ta fada min dazun nasan zasuyi maku bayanin komai.
Godiya mukai mata sosai zamu tafine na karbi number wayanta don na sake kiranta muji lafiyan baba wajenta daga nan mukai mata sallama muka shigo Nape ya sauke mu har bakon get din gidan namu kowan mu fuskan shi babu dadi a lokacin.
Ya Ahmed ya bude gida muka shiga falo mama ta zauna dashi suna maganan tsarin garin hakan ya bani daman shiga daki na dan kwanta har barci ya dan fara daukana na tuna banci abinci ba lokacin.
Na taso na fito don in karya muryan mamace kamar tana rada tana fadin ni dama tun farko saida yaya ta fada min cewa yarinyar nan zata zamo muna ciwon ido ta saka mata suna karan dafi.
Gashi kuwa sunan ya tabbata mata don ta zamo karan dafi a cikin mu yanzu wai ace yau


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login