Showing 24001 words to 27000 words out of 347556 words

Chapter 9 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8726

abinda ke faruwa bai dauki lokaci ba don ba nisa yaje ba dama.
Ya shigo kai tsaye yana fadin lafiya dai meke faruwane wai ina hjy laraba ta amsa daga ciki tana fitowa tace gani Alh mu isa part din hjy mairo don Allah.
Lafiya wai ina hjy mairo din hjy Laraba din ta tareshi da fadin ka hadu dasu Ibrahim a waje ya juyo yana fadin ban ga kowa a wajen gidan nan ba ai.
Ya sakai zuwa cikin dakin hjy mairo din bata falo amma a nan ya zauna hjy Larabace tace hjy kizo ga Alh ya dawo itama saita samu wuri ta zauna din suna jiran fitowan hjy mairo daga uwar dakin.
Tafito idanunta ya kade yayi jawur a lokacin din kukan da tayi duk da taba kanta hakkuri ta daina don zubarwa da da hawaye ba karamin mayar da yaro baya yakeyi ba.
Waime ya farune tun dazun ina tambaya kunki fada min Alh ne daya tambaya karo na barkatai bai samu amsa ba shine ya kara tambaya cikin hasala.
Sai hjy laraba din tace tou Alh zancen ne baya da dadin ji an riga da anyi kuskure sai hakkuri yanzu kan tunda an aikata.
Kai ni wanan kwanaye kwanayen ya isheni daji haka kuskuren me aka aikata anki fada sai hakkuri kuma ake bani ita wana kuma tafito min a haka yana nuna hjy mairo da hannunsa.
Alh ba wani abu bane yaran ibrahim da usman suka dawo yanzu suke fadin wai Jos suka fito an daurawa baba aure da wanan yarinyar dayazo muna da zancen ta.
Daura aure shi baba din ya daura aure bada sanin muba to shike nan ku barshi Allah ya basa zaman lafiya ni yanzu me zance kuma ?
Hjy mairo ta dan dago tana fadin amma Alh haka za a zuba mai ido ana kallonsa yayi abinda ba daidai ba kuma a kyaleshi.
Me zamuce dashi lokacine duk yadda zan tsaya yanzu in nuna bacin raina kan hakan aiya sani rainane zai baci a banza don haka ai gara a sakamai ido baidai da wasu iyayyen bayan mu.
Yana dasu kan ai kaji yaya Audune ya goya masa baya tare dashi suka tafi daga tambaya aka daura auren dayani a can suka dawo.
Shi Alh Audu din shifa da kansa yaje masa neman auren to ai shike nan Alhn ya fada yana mikewa tsaye yace kowa ya saka mai ido barkice ai gashi nan gata Allah ya sauwaka.
Jinkin kowansu yayi sanyi tundai hjy Laraba don bata dauka Alhn zaiyi sanyi hakana ba ita a zatonta ta dauka zaici mutuncin hjy mairo yaci na dan ga baki dayansu sai taga ba hakana ba ta sare.
Shikan ya fita ya barsu nan zaune zugun zugun kowa da abinda yake tunane a kasan zuciyar shi a lokacin kafin can hjy laraba din ta mike tana fadi a fili Allah yasa hakan alheri ne.
Wai wai muka fara jin cewa wai yaya habibi ya daura aure da wata yar bariki a can kowa yana mamakin hakan har zancen yasha ruwa a zukatan mutane.
Yanzu kan gaba daya bani shiga gidan don abubuwa da sukai min yawa saboda sana,ata ya dauke min hankali wanda yanzu bani kadai bace a gidan mu dake wanan sana,an ta bakin kofan gida har su samira da yan biyu sunayi yanzu.
Don haka sunan gidan namu ya dawo gidan yan awara muna sarrafa waken suyi ta hanyoyi daban daban kuma duk nice me dauko yin abubuwa dana dauko yi kowa zai kamayi don banzama neman kudine kawai a gabana sai karatu.
Baruwana da wani zuwa gidan kawa ko wani didiman buki koda yaushe ina bakin sana,ata kuma saina sayar sauran zasu sayar sainaji tausayin wace naga nata nada yawa na debo na zuba a wurina a sayar mata.
Allah da ikon shi kome nataba yazama kudi har ya kai na fara dauko jarkokin mai ina sayarwa duk unguwa har bayan mu da gaban layin mu suna zuwa wurina daukan mangyada na asali kauye nake zuwa duk sati in dauko.
A haka na fara budawa tun ina dauko jarka biyu uku yau har yakai mota ya tsaya a kofan gidan mu zai sauke min kaya.
Ganin yadda aketa shigo min da jarkokin mai din cikin gida mama Ladi yar maman biyu dake zaune suna kallon ikon Allah ta tambaya wai duk kayan nan na malam ne ko nawa ?
Wani malam na yarsa daine yar kasuwa ita ke zuwa ta dauko a kauye yanzu zuwa gobe da yamma idan kin shigo sai dan wanda zamuyi amfani dashi a gidan nan kawai zaki samu inji mama uwa ke bata amsa.
Wai wace yar kike magana tace bintu ce maishi yanzu ai zakiga ta shigo don dawowanta ke nan daga kauyen yanzu.
Ikon Allah ban fada maku wanan yar zata zamo maku karan dafi a cikin gidan nan ba nan gaba gashi ko kun gani tun ba,aje ko ina ba ta ta fara baiyana kanta gareku.
Aiko mun gani kedai yarinya kamar me sihiri sai bakin wayaun tsiya da iyayi muna kallo yarinya karama tazo ta gwada muna barkadon duniyanci.
Nice na shigo cikin gidan masu buhun wake da suka dauko min suna bayana tafe nace ku kai wana kofan maman biyu wancan kuma kai Ado kofan mama uwa zaku aje matashi.
Masara kuma na mama lantone nagansu da sauki a can na kamo maku yafi wanan sayin da kukeyi guntu guntu hakan zaifi ku samu riba sosai sai ku hada min kudin koda baikai ba zuwa wani sati saiku bani dan abin daya samu a karo wani.
Kai amma Bintu kin ko kyauta muna da wanan dabaran da kikai muna nace hakan naga yafi don yadda kukeyi din nan bai kawo riba gareku sai faduwa amma ku gwada wanan ku gani ko zaifi.
Na juya na nufi kofata na saka makulin na bude nan da kaina na fara jidan kayana ina sawa a daki kanina na kira nake ce masa yazo don Allah na aike shi gidansu hjy mairo.
Yaso yaki zuwa ina jin uwar tayi cikinsa da fada sai gashi yazo nan ya zo na bashi sakon nace ya kaiwa hjy din yace injini shi kuma nace jeka dawo na baka tsaraba .
Wanka nayi nayi shirin islamiya na dauko kayan kauye dana sayo masu danfin kayan miya dana dan icce na fito masu dashi a lokacin nasamu su maman biyu sun shiga daki da yar uwanta.
Mikawa mama uwa nayi nace ni zan tafi islamiya ga wanan abaiwa Audi idan ya dawo daga gidansu hjy dana aikeshi nan na barsu suna ta faman yi min godiya daga kofa na tsaya na sallami maman biyun dake daki da yar uwanta.
Daga fitana ba a dade sosai ba suka fito yar uwa mama dince ta fara fadin yanzu uwa kuna zaune kuna kallo za,a sakaku kwana a cuceku ?
Tace cuta kuma to inba cuta ba wanan yarne za ace tana da wana kudin kayan ai wannan abin a tsaya a tambayane gaskiya.
Wai kina nufin lamarin Bintu tace shi mana to ai a gaban mu take sana, anta duk mun sanina a sati tana rika riban kusan dubu bakwai a hannunta.
To yanzu mace bamu san yaya akayi ta samu kudiba kuma mama Ladin ne ta karbe da fadin ikon Allah fin yayanku tayi ko makari tafisu da zata fisu kasuwa.
Dole akwai dai wani abinda yake boye kunyi sakaci kuna zaune kuna kallo har ku bari tazo tana yar kankanuwa tafi diyan ku kuna zaune kun zuba mata ido haka kamar wasu sakarkaru.
To maganace bata yiyuwa a yanzu da kafada sai malam yaji ya kama cin mutunciwa mutane shi anwa yarshi kazafin sheri amma yanzu ai dole mu saka ido akanta mu gano gaskiya jifa wanan sayayyan wanan ai kudine aka kashe yafi dubu dari barkatai a wurin nan.
Haka ta tsaya tayi ta zugasu har tayi masu sallama ta fita duk abinda take fada Samira na daki tana jinsu don ranan basu da garin masara fara da suke sayarwa kuma tana danjin ciwon kai.
Na dawo daga islamiya na hada wuta na tattara kayan sana,ata na fita na dora suya saiga masayana suna zuwa saya wasu tun daga wani unguwa suke zuwa saya don gaskiya na iya yinsa sosai don na gwane a cikin harkan .
Saura min kadan a lokacin ne na tuna da samira bata da lafiya nikansu babu mai kai masu wani dan matashi da muke shiri sosai dashi yana zama wurin Isah mai shago.
Shina bawa dari biyar na lalashe yaje yakaiwa mama lanto nikanta yana murna yana godiya yana fadin hjyta angama ai dari biyar ma yayi yawa da kin ban ko uku aiya isa tunda nan bayan mune manikan.
Ya shiga gida ya samu mama lanto yana fadin hjyta ta ban dari uku nazo nakai maku nika haka ya dinga cicibo buhun zuwa injin yakai masu aka nika ya dauko koda ya dawo yasamu har na shigo gida.
Ni na tayasu aikin har suka jika masaran na koma daki ina karatu baba ya shigo gida ina jin muryanshi na fito.
Yana tsaye ya dafa bangon dakinshi yana fadawa matanshi yadda akayi yakai dare haka bai dawo da wuri ba don rashin abin hawa dayai karanci a gari lokacin.
Na gaidashi yace a,a fadimatu yaya kauyen kaya da sauki ko nace baba saidai ace Alhamdullahi amma kayan sai kara kudi sukeyi ko wani kasuwa haka dai aka matsa aka sayo su.
To Allah dai ya kyauta kawai zamuce amma rayuwa a yanzu tsada yakeyi tundai a wajen mu masu iyali daki na koma bayan mun gama gaisawa dashi.
Kasancewa lahdine washegari ina son nayi fashin zuwa islamiyan safe a ranan naje kitso don kaina a dankare yake har kunyan budanshi nake ji don banda lokacin gyaran kaina gaskiya neman kudi kawai nasa a gaba.
Amma wai a hakan harsu maman biyu keson jefa min zargin ina bin maza nake samo kudin da nake dashi bayan a gabab su nake wahalan neman kudi ruwa da iska suna kallo.
Washegari tun gama sallah asuba nake zaune ina banyan kaina na samu da kyar na gama sai lokacin na fito na gaidasu na samu mama biyu na aikin madaran wake da takeyi tana sakawa a fridge idan yai sanyi a fita dashi.
Shine dalilin dana dauko mata wake a kauye donsu samu amma kuma ban tsira ba saida suka bini da sheri ita da yar uwarta don kawai hassada da kyashi irin nasu.
Ban zauna ba aikin waran mu da mama uwa keyi a yanzu shina kama mata itama mukayishi a tare dasu duk da kudi zan biyasu amma banyi kyashin saka hannuna a aikin ba lokacin.
Kai jama,a yanzu don Allah mama ku duba boyar Allah nan duk dai tana iya kokarinta a zauna lafiya komu da kuka haifemu bamuyi maku irin aikin wahalan nan.
Amma wai a haka kuke son ku kulla mata sheri bayan mama kin sani da badon ita ba satin nan ko sana,an da ba zamuyi shi ba don babu kudin saro garin nan gareki.
Samirace kewa uwarta wanan maganan tace aiko ya uwa haka ta fada min dazun da badon ta taimaka mata ta sayo mata gero a wanan satin ba ba zata samu na sayan geron da zatayi kasari ba har a sayar din.
Nidai na fada maki mama ku bar wanan halin don Allah yanzu ya kamata ace kun fahinci anbinda maman biyu ke nufi da Bintu cikin mu komu don ana ganin kune ake muna ragowa.
Na fada maki yanzu ban fahinci komai bane na zaman gidan nan itafa yaya idan ba ita da yaranta ba babu kowa a gabanta nagane taimakon da Bintu ke muna shine yake bata mata rai don bata da ikon hana yarin hakan garemune.
Nagama komai nazo zan fita wurin kitso naji maman biyu din tasa min kira hakan yasa na juyo na tsaya take fadin kin kawo buhun wakw kin aje min ban fahinci na meye ba.
Cikin mamaki na kara kallonta nace mama ina munyi wanan bayanin daku jiya a kauye nasa kudina na sayo don naga can yafi sauki nan kuma sai kun dauko a wurin wasu karshe azo ana tijara daku yasa kudin adashena da aka kwashe min na sayo maku don ku daina dauka a waje.
Hakan ne ai bani so don ban rokeki ba kimin hakan ki barni in dauko da kudina na halak yafi min karban kudin da bansan mafarinsu ba.
Mamaki sosai naji a lokacin amma don kada zancen yayi gaba nace kiyi hakkuri mama banyi hakan gareku ba don naga gazawan ku sai kawai don na taimaka wa zama tare.
Ke bintu ki fita idona don tun warki bata san duniya ba nasanta aa zakije waje kina talan cewa kekike daukan dawainiyan mu dana diyan mu .
???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Kudin ki kudin haram da ba wanda yasan yadda kike neman abinki ki dauki buhun wakeki daga kofan nan tun ban watsawa dan baza ruwa ya lalace a wurin nan ba.
Ni mamaki ma ya hanani fadan komai a lokacin sai kawai na amsa da mamakiyi hakkuri nayi kuskure ba zan kara ba insha Allahu.
Haba dai yaya wanan ai kamar taimakone binta tayi muna kinji dalilinta na sayo muna ai kaji sakarai ke idan zaki dauka ki dauka nikan badani ba cin kudin haramun.
Kudin haramun saboda idon ku ya rufe da son abin duniya har za a zolayemu da kudin maza ita kadai ke wanan sana,an ko mu yaran namu basu iya neman kudi bane da basu taraba ko don su basu iya zuwa lungu da maza ba.
Wa,iyazu billahi mama ni kikewa zargi da maza dama kallon da kike min ke nan ashe ta tareni da fadin an maki ko waye baisan abinda kike shukawa ba a gidan nan.
Hawayene yazo mi lokaci guda na dago kai na kalleta nace mama ke mahaifiyatace amma kikai min wanan zargin Allah ne alkali a tsakanin mu dake ai ina juyawa naji ta shakoni ta baya ta fara kai min mari a haukace.
A lokacin karfina ya kawo koda nace zan rama zan iya kai mama kasa amma haka na daure tayi min maru takai biyar masu kyau a fuskana wanda saida mama uwa ta shiga tsakanin mu ta kwaceni daga hannunta fitan da banyi zuwa kitso ba ke nan.
Zazzabi mai karfine ya rufeni lokaci guda naci kukana a dakin ni kadai na kwanta ina tunanen duniya meye laifina a cikin wanan abin don kawai na taimakawa zama tare.
Koda baba ya dawo baiji motsina ba yake tambaya nan mama lanto take fada masa cewa banda lafyane ina daki kwance baba ya mike a rude sai gashi a dakin nawa yake fadin.
Fadimatu meya sameki haka da kyar na dago kai zanyi magana sai hawaye tarrrr ya zubo min da kyar na iya fadin banda lafiyane baba.
Ban fada mashi komai ba sai washe gari dana fito zai kaini kemis ne yaga yadda fuskana ya kumbure da sauri yace subbahanallahi wai me yasameki haka kamar bugu a jikinki ?
Kafin nayi magana dan wurin mama lanto yace maman su biyuce tayi mata duka jiya sosai kallon yaron kowa yayi shiko baba kallona yayi yace wai fadimatu dukan Rakiyace haka a jikin ki nake gani ?
Kasa magana nayi sai kuka dana fashe dashi wi wi wi na juya na koma daki na fada saman katifa niba dukan nata datayi min ne ya dameni ba ya tsaya min a rai sai cewa da tayi wai ina biyan maza dashi nake hada kudina.
Nida ko saurayi banfara tsayi dashi ba komai iskancin mutum indai sai yaga fuskata zai sai sana,ata saidai ya fasa saya don ba zai taba ganin hakan ba a gareni amma ban tsiraba a wajen mama don ga wanan zargin da tayi min.
Ai kuwa ranan dai sun kwasa sosai da baba bayan ya gama ji ba,asin dukan yayi mata Allah wadai yafi a kirga a ranan yace komai tsafin ki da shiga malaman ki va zaki taba ci galaba akan yar nan ba dama kin sani ki zauna lafiya da ita.
Wanan kalamin shiya kara batawa mama rai sosai a cikjn fadan take fadin cewa wai baba yaiwa yayanta baki sabodani son haka ta fara jami mugun kaba,i iri na bakinta tare da aibantani da uwata.


ZAINAB IDRIS MAKAWA


[7/29, 2:36 PM] Maman Aslam: KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
9??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,

Alherin dake cikin wanan ranan ta jumma,a ya Allah


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login