Showing 324001 words to 327000 words out of 347556 words

Chapter 109 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8825

barki da tsinuwar uwarki a kanki yau.
Rakiya kuzo ku fice min daga gida dama haka kike so daga ke har suwaiba din taje na saketa saki daya ta kuma kwashe har yaran nata taje dasu ina dana sanin hada jini daku.
Gida ya barke da kuka har hassana din danasani ya darsu cikin zuciyarta akan sanadin dakatar da mama ga saki ya shiga tsakaninsu da baba yau ita ya makomar rayuwanta zai kasance ke nan a yanzu.
Su mama uwa da sukazo gaidani da rana suke ban labari yau abinda suka tashi dashi ranan sun dai baro gida baba ya dage kan sai mama ta kwashe ta bar masa gida ita kuma tace ba inda zata tafi zata zauna zaman yayanta gidan.
Inna lillahi na ambata yare da karasa fadin meyasa baba zai yanke wanan danyen hukuncin haka kan mama a inda suka kai din nan ga shekaru.
Bai kamata baba yayi saurin furta saki akan mama ba ai aike Bintu ba kowa bane da irin rayuwanki yaya ba karamin abu takeyi a kan kowa ba gidan nan i kin debe yayanta .
Na tare da fadin mama meta zama yanzu don Allah ko mama din ta canzane bayan tafiyana jifa yadda ta koma dan kwanakin nan danayi banganta bayan buki da mukaje sallama daku.
To ai gara dama da yanzu don duk ta zube don mugun abinda ke cint a zuciya kan yayan wasu ni nan cewa tayi da mutuminki Nura wai ya fara sata yana kawo min ina jin dadi nida ubanku.
Mace tace bata son dan kowa sai diyanta ko diyan nata ta raga masune maman Amira aiko diyan nata bata barsu ba cewa tayi hassana fa haka zata kare tana maku fadanci don kawai itace mai dama a cikinsu yanzu.
Ni hassana din ma tausayi take ban wallahi da gani yanzu abin duniya yana damun yarinyar a zuciya bata dai da yadda zatayine.
Ai dole duk sa,aninsu suyi aure mugun abin uwarsu ya hana anemesu da mutum ya fara zuwa kwana biyu sai ya dauke kafanshi kamar abin baki amma ta kasa gane hakan.
Suna dai maganane amma na kasa fahintar me suke fada har mukai sallama suka tafi inda na tsuke saida Boss dina ya fito min da zancen dalla dalla lokacin nasan gidan akwai camera amma ta ina na tambayi kaina.
Karshe yake fadin bari kiji bazan yarda ba muddin wani abu ya samu cikin nan na jikinki naje na fadawa baba yace Allah ya fita na kuma saka ai muna addua da sauka kur,ani.
Shiru nayi don na suma a zaune na kasa magana a lokacin sai tunane nakeyi a inda camera din yake wanda yake ganin komai a gidan da nakeyi in hakane shi har dakine ko iya falone kawai cameran ya tsaya.
Na tsargu sosai da har ya gane hakan amma matukar zanyi siri da yan gidan mu ko kawayena kenan komai mukeyi a kunnuwansa kenan yake zuwa ko idanunsa.
Dole in dakatawa hakan burki sannu a hankali ciki hikima na fara neman camera din inayi ina basarwa har na ganshi can makale gefen home theater din da bamu amfani dashi an dai saka kawai don kawa a falon.
Igiyarshi nabi a cikin tako naga yayi dakin shi hakan yasa na katse shi daga sama nabi na dakin na batar dashi shima na fuske ina jiran yai min magana aka hakan naji shiru bai min magana ba.
A bangaren mama kuwa hankalinta ya tashine sosai akan wanan abin don ganin irin kudin da suke kashewa a tsakaninsu Altine tayi ita tayi yayan tudun wada tayi amma yau duk a banza don gashi yin baiyi amfani ba da girmanta da shekarunta malam ya dankara mata saki a gaban kowa.
Gaban jikoki da yaran gida da kishiyoyi kalam Nuratune a baya ya fado mata a rai bayan iri hakan ya fadu da ita take fadin yaya kinsa malam ya sakeni ki zuba ruwa kasa kisha amma ki rubuta ki aje.
Komai dare dadewa insha Allahu sai irin haka ya sameki zafin danaji sai kinji wanda ya fishi a rayuwa dadi abin ma ni da kurciyana zan iya aure keko ba halin hakan gareki a lokacin.
Ta Allah ba taki ba gaiyan tsiya nida gidan malam mutu ka raba takalmin kaza nan kika ganni nan zaki barni tama dutsen sihiri duk abinda kike takama dashi Nuratu nadamaki nashanye yar gudun hijiran dake labewa kuna cuta.
Yarki kuma ku karbe min ita malam ba zamu bari taje da ita ba ta koya mata mugun abu acan don haka a nan zata tashi cikin dangi keda ita har abada wallahi middin ina raye kuwa tunda kince ke tantiriyace mu zuba mugani nidake a gidan nan.
Tana kallon yadda su gwaggo sa,a a lokacin suke kwantan yariyar a bayanta tana hana musu har sukaci karfinta suka kwace yar ta juyo tana fadin kin kwace min ya Suwaiba kina ganin kin kuntata min a kanki zai koma wata rana wanan abin insha Allah tasa kai ta tafi ko juyowa bata yiba sai wanan ganin da tayi mata a cikin daula ta firgitata abin ya tsaya mata a zuciya haka kuma.
Yau kuma sai gashi saki ya hau kanta da tsufanta a sanadin yar Nuratu din ta hanyar yarta data haifa da cikinta hassana wace ta dauki son duniya na Bantu ta makalawa zuciyanta akan bata yarda suna cutawa yar uwarsu.
Ke nan bakin Nuratu ya kamata ashe don yau Bantu ta zama mata matsala a rayuwa kamar yadda uwarta tace kuma ta rabata da yarta hassana datafi so a cikin yayanta har sunyi sanadin igiyar aurenta.
Duk da irin taka tsatsandin tayi tayi a kan yarinyar tana kashe zarahinta da karfinta wajen ganin jini Nuratu din bata zama kowa face yar kallo a cikin gidan duk hakan a yanzu ya tashi a banza kudinta da wahalanta sun tafi a banza ke nan ga baki daya.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

@KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
Pagen karshe labarin Bantu yar baiwa
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Kallin matar nasa yayi rai bace yana fadin wani zancen banza kike min yanzu don Fatima nada ciki nina hanaki haihuwa kome koda kika aureni kinga ban haihuwane wai?
Wanan matsalan kice Samira tareshi tayi da fadin ai dole kace hakan tunda baka da hasara kai kana da wasu diyan da kake gani a matsayin naka a duniya.
Juyowa yayi cikin mamaki yana kallonta kafin ya furta ashe baki da kunya haka samira koda yake banga laifinki ba don kinyi hakan ai duba ga yadda kikazo min.
Yau keda bakinki kike fadin haka ranan da kika fara approaching dina mekice min ina cewa kikayi kina son na aureki don kawai ki gushewa su Jamal maraicin dake zuciyansu na uwa idan fatima taki tausaya min ga hakan ke gaki duk daya kuke da fatima.
Fada mi tunda kikazo gidan nan idan kin nunawa yarana wani kulawa ko damuwa akansu banda makircin da kike kulawa a rayuwana dana wasu babu komai a zuciyanki samira nasani .
Ko kina daukana bansan komai ba bansan abinda kowanku ke ciki ba bari kiji ni dukkanku biyun nan kun isheni kun kai min ko ina a yanzu don babu kwanciyan hankalin dana auro ku akansa nagane abin hannu kawai kuke bukata kuci.
Kallon shi tayi shekeke kafin tace ina abin hannun da kakewa mutane burgan aiki dashi ina abin hannun Mahmud nace ina anbin hannun yake yanzu makaryacin banza makaryacin wofi nan kace makka sainace ban zuwa ina makkan yake yau babu.
Ko sutura tun na aurena dashi nake maneji sai gwanjon iyamurai da kake jibgo min wai kai sutura ka kaini asibiti a duba lafiyata kaki don kada kwandalan ka ya tabu sai karyan arzikin bamza dana wofin arziki da,,,,
Ta ta ta ya waketa da maru ako wani gefen kumatun ta saida taga wani wuta ya gitta a gabanta ta duka bashiri yace ashe karamar yar iska kike ke har kina da bakin magana.
Tunda na aureki hasara da kaddara kebina wai kece zaki bude baki kice min ina arzikin yake don baki da kunya yar iska mai farin kafa tsiya mugun halinki harni ya shafa dama saida aka fada min keba alheri bane gareni kika matsa min da mita kika yaudareni na auroki.
Yar iska mara tarbiya wace ta fita zakka a cikin dangi ke din nan badon wani abuba sai ince ba malam garba yai ciki aka haifeki ba don baki da halin diyan malam garba ko kadan.
Nan tayi ta maza ta dago dafe da gefen haba tana fadin kaifa aikaima din bakai kama da dan Musa driver ba aiko yayi cikinta da bugu da shuri tun tana na maza har yakai ta fara ihu don duka iya karfinsa yake mata.
Da kyar ta samu hanya tafito daga dakin tana ihun neman ceto bai barta ba ya biyoota da zagi da cin mutunci yana fadin taje ta sake ta tabar mashi gidansa har ya bar gidan yana auna mata zagin cin mutunci ya dawo ya wurga mata kudin mota yana fadin kar in dawo in sameki gidan nan na fada maki.
Bayan fitanshi tayi tunane kala kala tasan inhar ta bari ya dawo ya sameta kila kasheta zaiyi da bugu don haka ta tashi ta hada duk wani abinda take so ta shirya ta fito wasila bata gidan dama takai sati uku bata nan ashe gara wasila da ita don salin alin tayi tafiyanta kuma bai bita ba sunyi kira yaki daukan waya balle yaje.
Na tashi da dan karfi don haka na shirya don inje in duba gida tunda nazo gidan mami nayi karfin halin zuwa ranan tare dashi don zuwan mami din biyu tana dubani da jiki.
Don haka nasa ya kaini kada ya zama rashin kunya tana zuwa ni banje na gaida ita ba idan ita ta dauka hakane wasu zasuce izzace hakan nakeyi.
Tare da iya da sadiya muka tafi wuni gidan mu gaida babana wanda ya kasa boye farincikin shi a lokacin da ganina mun yadda yarshi ta koma lokaci guda yan watani da aurenta.
Dakina nada nayada zango don nan su hassana din suke na samu Usaina bata nan su mama uwa da mama Lanto suna daku nan su koda na shigo sai baba zaune shi kadai zaune yana gyangyadi saman faran kujera ya makala dan redion sa yana sauraren tashan kaduna.
Da mulkin azzalumi Obasajo yanzu ya rage masa karfi don kawai yaga ya gurgunta dan arewa gidan redion da ada ko ina kake kana iya kamosu sai gashi yanzu wasu jahohin na arewama mutun ba zai iya kamasa ba sai yayi mamare akansa.
Da murna ya taremu bayan ya bude ido da farko yana bin mu da kallo saida nace sannu baba kai kadaine a gidan ya sheda muryata yana fadin ikon Allah fadimatu kune tafe sauki ya samu ke nan masha Allahu.
Har ina cewa nan da gobe zuwa jibi zan gaiyace mai mota muje mu duba jikin naki ashe sauki ya samu tunda gaki kinzo masha Allahu lokacin yake kwalawasu mama uwa kira su fito gani.
Ta fito tayi tozali damu take fadin a,a su Bintuce sannunku da zuwa mama lanto ma ta fito muka gaisa nake fadin mama fa yadda suka amsa min nagane akwai wani abu.
Don cewa da sukayi a dadare tana ciki sai baba ya amsa da fadin tana ciki tana ci kanta bakar manya ke ai ba manya bace gadai manyan ta ainihi nan muna gani mace mara zuciya an koreta tana kafe wai tana zaman yayanta gidan.
Ko da kudin yayanta na gina gidana idan tayi min tsiya nasan ta hanyan da zan fito mata dama gidan yanzu aiba nawa bane nakine donke mijin ki yayi sabin gina sai in amshi kudin kangona daya rusa inciye abina tun ina da rai inga tsiya inga ta inda munafuka yar asheri mai yukan yanke kauna zataci gadona ita da diyan nata.
Tundai wanan bakar haihuwn Altine ko mutuwa nayi a yau din nan ku sheda ba Altine bacin gadona a gidan nan don na tsameta a cikin diyana.
Altine yar sherice na karshe tun lokacin da munafukan nan Rakiya ta dauki rikon Altine da yaye suka shayar da ita mugun abu har yanzu tafisu iyawa na tsani in bude inji sallaman Altine gidan nan don zuwanta gidan nan ba alheri bane a kullun.
Jin yadda baba din keta zuba cikin bacin rai yasa na nisa daga inda muke zaune ina fadin baba kayi hakkuri don Allah bacin raine su kuma Allah yasa su gane su daina abinda sukeyi ba alheri bane garesu.
Yace ashe tunda kince Allah ai shike nan amma wa yab nan bakaken maguzawan har yanzu ba musuluncin gaskiya a zukatansu saina fir,auna da hamana da suka gada.
Ina su hassana na fada ina kallon mama uwa don ina son in kaucewa fadan baba tunawa da nayi iya da sadiya na wajen baba keta fadin wanan maganganun haka kan iyalinshi kada suyi masa wani fassara na daban kuma.
Nace sadiya ta ajewa baba manyan kulolin da muka shigo dashi gaban shi na mike naji mama Lanto na fasin abin arziki muka samune tana bude kulan ta kasa sadiya ta tsaya ta bude suka saka shewa don gani abinda ke cikin kulan farko na kara fadin su hassana fa mama ?
Cewa tayi suna dakinsu kedai hankalinta kan dayan kulan da yarinyar ke budewa na mike na nufi dakin nasu na mama tace bacan ba dakinkina da nan suka koma aida zama yanzu to bari mu gaisa da mama na fada ba tare dana juyo ba su iyama suka biyo bayana.
Sallama yakai uku a kofan dakin tana uwar daka bata amsa min ba jin tana nan yasa nayi kundun balam fadawa dakin da sallamana suma suka biyoni mama mama na fada naji muryan ta can ciki tana fadin wayene ?
Nice mama mun sameku lafiya na fada daga kofan shiga kuryan dakin nata tace wai Bantu ce lafiya lau tana daure fuska su iyama suka gaida ita muka juyo muka fito tabbas mama ta rame kuwa na fada a raina .
To meke samunta haka ta zube lokaci guda duk ta zabge kamar ba mama mai ishashen jikiba ga tsayi ga haske amma yanzu duk ba wanan a tare da ita.
Dakin mu na dosa a can na samu hassana kwance ta lafe lamo saman katifa nace jin dadi sister wai duk jin dadine haka nayi zaune ina kai mata maka a baya.
Ta dago da karfi ashe barci takeyi duk abin nan nan muka zauna muna hira nake fadin wai ina big sister ta tafine gashi har yanzun bata dawo ba na tambaya dace Usaina.
Ta wani yamutse fuska tana fadin wai mama ta aiketa gidan maman tudun wanda tun da safe tana can kinsan yanzu itace yar gaban goshinsu tunda tana nuna goyon baya a kansu basu san yar iska bace tama fini kin halinsu.
Akai kiran sallah azahar mukai sallah sadiya taje mota ta dauko muna abinci don ban yarda ko ruwa insha ba saboda tsaron lafiyata don kada su sa min baki nacewa mama uwa ganye nakeso nasan da wuya a samu.
Allah sarki saiko ga ganye gudan me yawa ganyen na zage naci na koshi na bar masu abincin yaran gidan mu duk wanda ya dawo cin abincin rana ya ganni sai yasa ihun murnan ganina.
Sadiya tashi kije kice driver nan ya shigo muna da bag din nan biyu tsarabace naso sai Usaina na nan in raba don ban iya jinininta gashi har yanzu bata dawo ba .
An kawo min tsaraban zan fara rabone saiga Usaina din tayi sallama tashigo tana ganina ta saki ihu muka hade muna murna nan suka tayabi fitarwa kowa da nasa ana kiran masu shi suna karba kowa na murna.
Sai nayi niyar wucewane mu dauko wani hira can mukaji gidan yayi tsit lokaci guda kafin muryan mama uwa ta jera kiran sunaye mu tana fadin mu fito babu lafiya fa ga samira ta iso a cikin wani hali.
Innalillahi muke fada muna rige rigen fitowa daga dakin kowa ya hangonta sai muja muyi turus don yadda shedan duka yake jikinta Samira hatsari kukayi inashi Mahmud din kuma mama uwa ke tambaya.
Kuka kawai takeyi nace babu lafiya akaita asibiti baba zaifi da abarta haka a gida cikin wani yanayi na wahala ai wa zai kaita asibitin Fadimatu niko ke babu ko dayan ku da zai kaita asibiti aiba bakuwa take a garin nan.
Ita da uwarta sunsan hanya dama wanda baiji bari ba akace zaiji hoho gashi kuwa wanan da gani dukane da zana yayi mata ta dauko wahala tundaga kasan iyamurai zuwa nan karshen ruwan ido ke nan ai.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login