Showing 282001 words to 285000 words out of 347556 words

Chapter 95 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8760

yake baitin uwa mamana mamana mai share hawayena su kuma su hassana sai rawa suke tika zuwa kujeran da zan zauna.
Ammice ta riko min hannu tana kuma rugume dani yayin da diyar ya Mustapha ke rike da gyalena da aka yafa saman lafayan da sai a jikin indiyawa ake ganinsa a film.
Hjy Maryan wacan kamar Matar Abbu Sifyanu na jodan mana nima ita nake kallo wallahi inba ita bace kamar nasu yayi yawa gaskiya amma dai kamar mutanen kasansune don shigarsune wanan.
Bullowa su maamah yasa tace wallahi sune ga wa yan nan yan uwan nasu da muke haduwa dasu lokaci lokaci kuwa tabbas babu tantama su din daine kuwa meye hadinsu da yarinyar nan kuma ?
Yana yuyuwa suzo mata sha,ani haka ba halaka har kasan nan kuma gaba dayansu har suka kai kujerunsu suka zauna suna zancensu don sunganesu kuma sunsan kosu suwaye tunda mazajensu a karkashinsu suke ko a can din don sun san akwai kudi ba karya.
Nan suka fara kallon juna hjy lailace tace kinsan bashir dan iskan tantirin yarone zai iya daukosu suzo su haska masa bukinsa kai ummu ta kada tana fadin bani tunanen hakan gaskiya.
Har lokacin tana kada kai kafin tace idan ba zargi nakeyi ba duk yadda akayi sune uwayen yarinyar nan don sai yanzu nake ganin kamarta sak dasu wallahi.
Waiko ita dince ta jiyo tana murmushin karfin hali tace kina tantaman haka duba can ga Fadilan Sa,an daura can kuma a gidana suka hadu suke kawance da juna ashe har yanzu suna tare tunda gashi har tazo nan bukinta amma bataje gidana ba.
Shiru kowa yayi na dan lokaci suka tsurawa Fadilan idanu na dan lokaci suna kallonsu cikin wasu kaya pink color wanda yai shige da shigan jikina.
Gaskiya tsayi bayani bata lokacine yar uwa ki kiyasta yadda wanan abin zai kasance a idanuwanki idan kina wajen haka abin ya kasance don ya kawatu anyi shagalin da ba ai tsamani ba both side sun taka rawa anga karyan naira don dolars yan Somalia suke watsawa wanda ya ruda wurin ba a bari nakai magariba ba har su muka koma gida cikin dadin rai ba abinda nakeyi sai hawayen hamdallah ga ubangiji a lokacin.
Gidan mu muka nufa dakin mama Uwa nashige na kwabe kayan jikina don ban sababa Ammi tana fitowa bayi ta ganni take fadin baki saba dasu ba ko zaki sabane don yanzu kin shiga sakasu ai tunda uwarki ta jibgo maki su don shiga taro.
Murmushi nayi sai daga baya tana sallah na tuna abinda Ammi ke nufi nima sallah na mike nashiga bayi na dauro alwala nazo na tayar muna idarwa Ammi ke fada min ga motanan zamuje gurin mahaifiyata can masaukinsu kafin su hajiya Hanifa su koma gidansu don da a can gidan wasu yan kasansu zasu sauka sai ga wanan gidan kusa da gidan mu suka zauna anan din.
Bata fita dani ba saida ta fadawa mama uwa har mama da take tsame kanta cikin sha,anin nawa ta fadawa don baba baya gari yana sokoto kwana biyu ke nan amma ya bugo waya suna hanya tafe harda wasu yan uwa daga can.
Don musanman sukaba baba mota malam Audi ya kaishi sokoto din wajen yan uwasa daya dade bai tafi akan shirin daurin aurena a can yasa a yanzu din ya tafi.
Tun daga haraban gidan mukejin muryoyinsu cikin yare su kuma matan yayyena na gashuwa suma suna nasu maida ba,asin kan taro dakinsu na fara lekawa basu sanda shigowan mu ba sai jin muryana sukayi ina fadin haram haram a dinga tausAsa harshe bima,ana ayi koyi da sunna.
Dariya suka kwashe dashi suke fadin bari yau munsha kallo wallahi abin yayi kyau sosai wallahi yar ya Mahmud dake kuka na karba a hannun uwarta ina fadin meya dameta suke fadin murne iskan mota da kuma canjin yanayi ya saukar mata da mura.
Nura na kira ina dan jijiga yarinyar na fada mai don Allah ya karbowa yarinyar magani a chemist nan sauran ke bada sakon magani suma ina fada mashi yasayo idan ya kawo ya kawo dakin matan yayyena a nan masaukinsu.
Na kashe wayan son Ammi dake jirana a waje suke fadin naje nadawo mu zasuyi magana dani ina dan dariya na fice daga dakin muka nufi dakin da mahaifiyata din suke.
Bamu dade da shiga ba saiga su Amira kanwata sun kawo masu abincin dare suka aje ana masu godiya su fadawa iyayyensu.
Nina san komai amma babu halin magana tunda da tsigar alheri don haka a tafi a hakana amma ba zan tashi gidan yawa na kasa sanin halin mutane wanan wani baiwa ga duk wanda ya tashi gidan yawa zai taso mai hikima da nazarin mutum farat daya.
Sun dauka wani abin Ammi tazo dani nan ai min a bayan idanunsu sai gashi nima waya suka samu lokacin inayi da Nura a kofan dakin ban kuma shiga dakin ba sai bayan wuce wasu da dan lokaci na shiga dakin su Ammi din.
Nasiha ne sukai min don sunce ba lokaci a cikin yarensu inda wani lokacin Ammi ke fassaramin ko hjy Hanifa sai kuma ita mahaifiyata dama take kwance tana waya lokacin.
Uwa Uwace don kuwa nasihan da take min babu wata uwarda ta zaunar dani ta lurar dani abinda ke cikin aure irin wanan da yanzu din suke min.
A don sunce ba lokaci daga ranan zan zama busy yasa suka zaunar dani Ammi ta debo abinci ta sakani gaba saida naci fiye da rabin abincin nan kuma wata ta debo wani abu a kofi mai kama da nono da tun jiya isowansu take dinkira jin shi a cikina na karba nasha.
Muna gama cin abincin mahaifiyar tawa da nake kira da maamah ta miko min waya a cikin hausanta da baso saiba tana fadin ki karba mijinane maigida ko zai gaisa da ku.
Na karba nayi sallama naji mutum ya fara zubo min larbaci nayi shiru nikan bansan me yake fada ba ko in kasheki bansan me yake fadi ba ga yaren nasu nasan yaji shiru ya tuno ban fahintarshine ya juya min zuwa turanci.
Nankan nafi dan auki a gurin don ina fahintarshi saboda turanci yake min sosai cikin gwanewa ina kuma fahintar abinda yake fada min din tare da dan amsa mashi.
Yana ban hakkuri akan yaso zuwa aurena da kansa amma kuma saboda aiyukan dake gabansa ba zai samu zuwa ba ya dan min nasiha na biyayyan aure nayi mashi godiya na mika mata waya.
Kula da nayi basa iya cin abincin namu don abin miyan kawai naga suna tsamewa suna ci ya dan daga min hankalina don kada su zauna da yunwa.
Wanan yasa na dan tambayi ammi me zasu iyaci naji sai take fadamin zasu sha shayi sukace akwai gas dasu flas har cup a kitchen din yanzun mai aikinsu zata sayo masu bread.
Fita nayi waje na kira Hassana mukayi magana.
Bata jimaba kuwa sai gata da bread dayawa Nura kuma ya shigo masu da nama gassasa leda biyu manya aka aje daya a wajensu daya nakai dakin matan yayyuna.
Suka hau min shewa lokacin hassana ke fadin Bantu meyasa ba a debo masu nama bane a aje nan don su ba saboda buki da baki aka yanka bane.
Murmushi kawai nayi nina isa na tunkari wani a gidan mu ince adebowa uwayena nama a kawo masu a canza min magana zuwa wata nan take yasa nayi murmushi kawai taci gaba da fadan haka take fadin zata koma gida wajen kawayen mu.
Nan ta barni ina jiran Ammi nagaji lokacin yasa na koma dakin matan yayyena na dan kwanta sai barci don gajiyan dana tara a jikina.
Saida ta gama suka tayar dani muka dawo gida akwai barci a idona kodana shigo nasamu kawayena sun kwanta hakan yasa na nufi dakin mama uwa nan ma akwai bakin sokoto dasuka iso a bayana .
Na tsaya muka gaisa dasu hakan yasa na nufi dakin mama lanto dogon kujeran falonta na haye na kwanta lokacin idona ya dan bude sama sama nake ji muryanta.
Sai daga baya na fahinci da yarta samira take wayan saidai bansan abinda samira din ta fadi ba na daiji ta hauta da fada tana fadin nasha fada maki banson baki biyu a yanzu.
Yarinyar nan bata kimu ba bata nuna muna komai ba don me ke baki son a zauna lafiyane ko kizo ko kada kizo buki dai za ayisa cikin mutunci yarinyar nan ta wuce duk iskancin da kikeji a rayuwanki.
Muryan gwaggona nane data shigo ya katseta da gwaggo ke fadin Allah sarki wai Fatimana nan tazo ta kwanta dama ake nemanta dama uwarta tace barci take a can gidan ta tayar da ita taga dakin ya cika shine tazo nan ta kwanta ashe.
Lokacin ta fito daga kuryab dakin nata tana fadin banko san shigowanta ba dakin nan ba gwaggo tace tun dazun ta shigo har tayi barci ai yadda na lafe zakace barci mai nauyi nakeyi lokacin.
Nan suka tsaya suna zance da gwaggona kan bukin da kuma abubuwan dake faruwa wandama ban sani ba har barcin gaskiya ya daukeni a hakan ban sani ba a wajen.
Sai can cikin dare naji tana tayar dani akan na tashi na shiga kuryanta mu kwanta da fadila da maryama da suka biyoni a nan din nan muka kwana dasu har safe sai asuba muka tashi sallah.
Gari ya dan haska muka fito nida hassana da maryama zuwa wani shago da ake kira da shagon Madina a nan kasan unguwar mu don kayan saudiya komai zaka sameshi shagon har daga wani unguwa suna zuwa sayayya.
Wayata dake hannuna tayi kara nake dubawa Oga Abbas ne a layin na dauka muka gaisa dashi sai naji yana fadi ina zaki haka da safen nan abin ya ban mamaki yake fadin gani a bayab ku ina binki ai har da angonki duk muna tare dashi.
Jin hakan yasa na dan juyo na waiga naga wata jar mota karama mai kyau kamar kifi tana bin mu a baya a hankali nace nashiga uku da sauri su hassana ke tambayana meye ?
Nace wallahi gasu a bayan mu ashe suna bin mu da mota lokaci daya suma suka juya do??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????le mukaja muka tsaya har suka karaso wajen kamar kasa ya bude in shige in rufe kaina a ciki naji a lokacin.
Don rabona dasu haka tun a Gashuwa dasuka sameni sai yau din nan da suka rutsani haka duk kuwa da ina cikin zulunbun hijjab a jikina na mama Lanto dana saka tunda nayi sallah ban cire ba har lokacin.
Gab damu ya tsayar da motan yana sauke glass yace sai ina kuma da safe haka kinsan fa ba,a son amarya na fita gudun tsotsayi inji manya ko ango Fatima.
Ya Bashir ina kwana sai lokacin ya dago ido don jin ana gaidashi a cikin sanaiya don yadda Family dinsu ke kiransa ke nan ya amsa kafin su hassana da maryama su gaidashi.
Nikan ta inda bai ganin fuskana na dan labe son ba zan iya jure hada ido dashi ba don ko Abbas din ma kunyarsa nake ji balleshi da yanzu ya zama dodona.
Abbas din ne ya sake tambaya sai hassana ke fada mai zamu shagon can ne mu sayowa baki bread da dabino da sauran abubuwa ta fada kai tsaye babu kunya wanda niko hakan haushi ya bani gaskiya.
A rasa wanda zai tafi sai ku don Allah ku daina fita da ita idan ba wani event zaku tafi ba saboda tsaro akwai abubuwan dake faruwa shine dalilin fitowan nan namu da mukai ayanzu .
Bani kadai ba don sai ince kowan mu ya tsorata da zancen shi don ya gani ga idanun mu a zahiri tunda mata muke bamu raina abin tsoro a kanmu.
Ehh aiya wuce koma meye ku dai kiyayye don Allah don bamu san shirinsu na gababa kuma amma an gano barayin ai suna can tsare ki koma gida ke Fatima bari wa yan nan su biyo mu sai a sayo komai din.
Nikan kafin ma yayi magana har na juya a cikin dan sauri don nabar wajen kada in fadi suka suka wuce tare dasu nikuma da Fadilan gashuwa muka koma gida a cikin tsoro.
Sai bayan sun dawone da kaya kamar hauka zakice bread din shagon suka kwaso da dabino mai yawa a buhu da butter jam milk katon katon da drinks masu tsada.
Hakan yasa nagane Hassana ta fada masu bakin Somalia basa iya cin abincin mu na nan irin su tuwo da fate da mutanen mu suke ta kwasa suna sha a dakin mama Lanto aka zube kayan.
Nan nayi hikimar cewa Hassana ta kwasa ta kaiwa mama sai a raba akai ko wani daki wa baki da sauran mutanen dake nan sai naga ta dan kalleni tasa yaran su kwasa suka fice har takai kofa kuma nake fadin kada ta manta ta fadawa mama zancen naman da za a dibawasu Ammi akai can gidan.
Wanan abin da nayi yasa mama dan sakewa bayan sun kwasa dasu hassana din tace ba zata karba ba aje wajen uwa da ake ganin ta fita ta raba din nan yaran suka sakata gaba har ta amince shine a karshe ranan ta gyagije ta fito ana gudanar da abubuwa da ita ta dauki girman ta na uwargida.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
9?? 0??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Kwance take don ta debo gajiya a jikinta a wajen taro jin gashi kuma basu dawo gida kai tsaye ba sai da sukaya da zango gidan hjy Halima akai zaman gulma da kuma kitsa sabon tuggun da za a bullo dashi.
Don tun a wajen taron ta fahinci ba zata samu yadda takeso wajen su hjy maryam ba tundai hjy Battula da yanzu take ganin mijinta ya saye zuciyar ta jan abin harin nasu ta fara boye mata wani plans dinsu akan Bashir din.
Shine nan ta zagaya gidan hjy Halima su idda nufinsu akan Bashir din donta rantse sai yayi kunya akan bukin nan tunda aka nuna masu bambamci a kansa tunda kurciyansu don kawai sun haifi yara mata su da farkon haihuwarsu duk da har yanzu ita din da daya namiji ta haifa a rayuwanta shine kuma na biyun karshe a haihuwanta.
Sunyi nasaran dana masa tarko don wanan bashi kadai zai shafa ba har bukin da suke ganin sunzo masu daga wata uwar duniya wanan tuggun nasu saiya shafi kowa.
Da zaisama a karshe ya tsiyace don ina yake da halin biyan wanan kudin duk karyan arzikinsa tasa ba zai iya biyan wanan ba yasa ta tura yaran da suke masu irin aikin nan suka tsara masu yadda suke son aikin .
Sai gashi hjy haliman ta kirata yanzu da farar safiyan nan tana sanar da ita an samu akasin aikin don yan vigilantes din unguwan sun darkakokusu har sun kama yaro daya a cikin yaran nasu.
Wanan mumunan labarin yasata mikewa saman gado tana fada tare da fadin wanan unguwar matsiyatan yaushe har suka samu wani security haka na tsaro saidai idan wani yai masu cune a wajensu har aka gane plan dinsu din.
Bata tsaya nan ba don ita komai bata taba barwa Allah lamarinta take fadin duk yadda akayi daga cikinsune wata ta zame jiki ta labarta wanan zancen har yafita.
Ta rantse da Allah sai taga bayan maishi kuwa su saka wando kafa daya da maishi kai karshema cewa tayi tasan wasukai mata wanan sherin son kawai suga bayanta saboda kyashi da hassadanta data kulla sunayi yanzu don kawai sunga ta darasu ga komai suka fara mata bita da kullin sheri.
Haka taita fada a daki ita daya bayan kashe wayan tana zage zage da tonawa yan uwa asiri don tasan komai nakowansu saboda bala,in saka idonta akan mutum ko yaushe.
Kai kai kai gaskiya mutumina kayi dacen mata wallahi Fatima tanada tarbiya ga mutunci sosai da girmama na gabanta wanan nacikin abinda yasa nake kara maka sha,awan yarinyar.
Kai kaga wanan din ban tabbatar da hakan sai idan ta shigo gidan nawa nayi nazarin hakan da kaina zan fadi wanan amma ba irin wanan yabon da kake mata yanzu ba.
Insha Allahu zaka tabbatar da hakan dana fada wata rana zakace na fada maka hakan don duk abinda kake tsamani ko zato ban hangoshi a wanan yarinyar bani.
Don nafika sanin mace don wallahi da watace ai ba wani kunya ko raba da zata nuna wai don ta ganmu koda kurciya da halin kwarai a zuciyanta sosai wallahi kasan wani abuma.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login