Showing 63001 words to 66000 words out of 347556 words

Chapter 22 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8798

ashe itakuma bata iyaba ta kwabe abin.
Nayi masu sallama na fito zuwa gida ina shan kwanan gidan mu na hango taron jama,a sun fara cika kofan gidan Alh mijinsu hjy mairo.
A raina nace mutane basu raina harkan buki da maikudi da tallaka kowa sai an nuna mashi kara idan harkan buki ya samu mut mussanman ma mata akwaisu da kara wurin sha,anin buki gaskiya.
Gidana shiga adaidai lokacin wayata ta dauki kara ina dubawa naga ashe hjyce dana baro gidanta take kirana na dauka take fadin mamata kin manta kin tafi baki karbi kudin da zaki hado kayan ba.
Gobe idan zan shiga kasuwa zan biyo tanan kafin in tafi tace Allah ya kaimu goben lafiya na amsa da amin ya Allah muka kashe wayan na fada gida.
Mama sannu da gida nace ta amsa daga inda take aikin nikan ban tsaya sauraren amsanta ba nasaka makuli ina bude dakina na shiga gyaran dakin nayi dana fito haka na daure na share filin gidan namu naje nayi wanka na kwata.
Ban dade da kwanciyan ba aka kawo muna wutan Nepa kallo na kunna mbc Bollywood suna wani film a cikin yarensu na indiyanci duk da banjin yaren haka na kurawa tv idanu ina kallo.
Saida darene da akai sallah magariba na samu shiga gidan bukin bakinsu na nesa sun fara cika gida lokacin don haka da kyat na samu shiga dakin hjy mairo dakin nata da dandama don bamutane sosai a dakin nata sai diyanta dake aure a cikin gari da sukazo wunin buki.
Muka gaisa dasu sukayi kamar basu sanni ba sai ga hjy tana fitowa daga kuryan dakinta take fadin a,a Bintuce saukan yaushe ina yaranki sunce dani ai baki gari.
Sunje gunki ki saya masu anko suka samu wurin nakima wai an daina suyan yanzu ko karyansune oho haka dai suka dawo suka fada min shekaran jinyan nan.
Hjy wai ana nufin yaran nan basuyi anko din bane kome wata yarta ta tambaya daga inda suke zaune da yan uwansu suna hira.
A banda abinki sadiya nice zan tsaya sayawa yaran nan anko din ina fama da kaina shi ubansu me yake daba zai saya masu ba har fa waya sukasa hjy laraba ta kirasa ta fada masa bai aiko da kudi ba.
Kai nikan kaina yana daurewa da lamari irin na yaya Mahmoud ace har yara baka iya kula dasu shi wani irin rayuwane wai dashi ni yanzu ido nasaka mai dama abinda Alh ke gudu ke nan ga auren nisa gashiko ya faru.
Don tun bayan aurenshi duk lamarinsa ya dambale sam ba a gane kansa yanzu in anyi magana yace shi daidai yake abubuwane sukai masa yawa a yanzu din.
Shiru nayi bance komai ba ina saurarensu saiga jamal din ya shigo dakin sun dawo daga inda aka aikesu yana ganina ya sheko da gudu ya rungumeni yace eh anty Bantu ashe kin dawo ?
Na dawo jiya jamal ina sister cewa Jamila don haka muke kiranta dashi yaron yace suna can gidan baba Ibrahim suna kallo namike ina fadin hjy bari naje nagaida mommy naja hannun yaron muka fice daga gidan ban biya dakin mommy din ba.
Tambayanshi nayi abubuwan da suke bukata yaron ya fada min na sallamoshi ya dawo gida ni kuma na koma gidan mu cike da tunanen irin maganganun da naji suna fadi akan ya habibi di yanzu.


ZAINAB IDRIS MAKAWA


[8/12, 8:33 AM] Maman Aslam: ,KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
1?? 9??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,

Wanan karon tafiyan mota yayi tundaga Fatakwal din suka shigo kaduna a cikin motarshi dake dauke da tsaraba daya shako mota dashi irin na abin marmari da ake samu a can kawai.
Ba wanda yasa rai da zuwanshi saiji akayi yara na kururuwan shelan isowanshi a cikin wanan daren dakin mahaifiyar nasa tab yake da yan uwanshi lokacin da wa yanda ke ciki gari da masu aure nesa tare da bakinsu kuma.
Hjy Mairo ta dan kore yara aka samu wuri kafin suka shigo sai lokacin aka san tare da ita akazo saidai hankalin yan uwansa yana kanshi don haka ita wasila din take ganin anyi mata wullakanci.
Ta samu kujera daga gefe takai zaune dama a gajiye take lokacin sosai tana zama kuma ta harde rai kamar bata taba dariya ba a duniya.
Ganin hjyn tasu ta zaune ya dan zamo yana gaida ita nan kuma yan uwan nasa suka shiga gaidashi suna masa ya hanya wasila kamar ba zatayi magana ba sai data bushi iska can tace hjy ina wuni a wani lalace kamar mai magana da sa,arta.
Duk yan dakin suka kallota cikin mamamaki hjy ko gaita girgiza tana gyara zama kafin tace wanan ce matar taka yace cikin jin nauyin uwartasa da eh hjy itace.
To sannu da zuwa yau Allah ya nufa ashe zamu san ki kunzo lafiya ya hanya da yan uwa a can ta kara daure fuskaka tana fadin duk suna lafiya.
Tana zaune dagwas saman kujera ba wani alaman girmama uwar miji bashi ba har hjyn duk kunya ya kamasu agaban mutane duk da ba bako duk yan gidane dakin amma hakan da nauyi da kunya gaskiya.
Hjy balaraba ce tashigo da murnanta jin sun samu zuwa bukin suma an kuma fada mata harda matarshi yazo hakan yasata tasowa don ta taso don ta taresu da zuwa.
Tana murna tace ashe dana yana hanya ban sani ba ko kai waya a sanda zuwan ku kaiko baba yayi murmushi yace mommy kona fada gamu tafe ba za a dauka gaskiya bace yasa na barku sai munzo din.
Suka gaisa tana basarwa tace ya matar taka take can yace mommy ai tare mukazo gata nan ta juya inda yake nuna mata ita tace a,a sannu da zuwa kunzo lafiya ya hanya ?
Lafiya kawai ta fada ta kawar da kanta gefe daya haushi da takaicine ya kara kamashi yayi dana sanin zuwa da ita dayayi a wanan tafiyan.
Hjy laraba na gani hakan tace tou irin wata sabuwa din nan saita juya tana fadin akwai abinci nan ne ko aje a dora masu yanzu tana kallon hjy mairo din ?.
Tace anya amma maryam duba ciki koda sauran abinci ki hada masu No a barshi ta fada da sauri tana wani yatsune fuska matan su ibrahim sai mamakin hakan sukeyi don sunga bakon abu a gidan yanzu.
Ba zakici ba me kikaci da za,ace za akawo abinci kice a,a ya fada a fusace ka barta don Allah ai ita duniya a sannu ake binta.
Duk yadda kike daukan mu mun wuce nan a gareki yanzu don shi mijin naki mudai muka haifeshi a nan kuma ya taso tare damu .
Kingasu nan ta nuna matan su Ibrahim su uku dake zaune suna kallon ikon Allah tace duk daya kuke a garemu har wa yan nan din da muka haifa.
Basu ko taba nuna cewa su din sun fito daga babban gida bane ko su nuna sunfimu ko wani komai a tare mukeyi dasu idan sha,ani ya tashi.
Amma ke da zuwan ki kin nuna kina kyamar mu harda abinci ma zakiwa kanki kyata kice ba zakici abincin mu ba gaisuwama jira kikayi mu fara gaidake kafin ki gaishemu.
Amma kinzo kamar wace mukaiwa wani abu sai yatsune yatsune da hare hare kikeyi tunda kuka shigo dakin nan kamar wace bataso zuwa ba ko kuma irin kinga wullakantatu din nan .
Har in wanine yai maki wani abu saiki fada amma ba kizo ana murnan da zuwan ki ba ki ki kuma dinga kallon mutane a hankade don ban rainaka ban kuma son rainon hankali a rayuwata gaskiya.
Hakkuri yan dakin suka shiga ba hjy hjy balaraba tace kinsan yaya kowa da irin hankalinsa nima nayi mamakin hakan gaskiya amma dai don Allah ayi hakkuri ke kuma ki saki jiki nan gidankune ai yanzu.
Wasilako ko ajikinta don zakace bada ita ake magana bama a lokacin don hankalinta na kan waya tana dakila hankali kwance.
Aka kawo masa abincin tuwon shimkafane da miyar bussasan kubewa yaji kifi da manshanu sai kamshi ke tashi a ciki zauna kasa yaci saida ya koshi yana hira da yan uwanshi cikin wayencewa.
Hjy ce ta kalleshi tace ka tashi kuje masaukinku hakana dare ya dan ja yanzu gobe ka shigo ku karasa ai tunda suna nan yanzu kullun a nan dakina zan sauka ai ita ta zauna nan cikin gida wurin ku.
Wani kallo ta watsa masa a fakaice hjy tace ina hakan zai yuyu kuje dai can kila can sin tafi sakewa don ba kowa yace to shike nan hjy yaci gaba da hiransa saidata kara magana ya mike tsaye.
Itama tayi saurin mikewa batacewa kowa komai ba ta fice a dakin duk suka bita da kallo, harshi da ransa ya gama baci sosai a lokacin saboda tagama badashi da zuwansu.
Ya juyo zai masu saida safe yaga hjy din tana girgiza kai cikin takaici nan jikinsa yai sanyi ya kasa fita daga dakin tace zabin naka ke nan ko yanzu ?
Wanan nan kan ya zama wajibi a gareka dole ka kara aure insha Allahu karaf wanan zancen ya shiga kunnen wasila data leko taga meya tsaya yi kuma a dakin ya barta tsaye waje.
Kasa daurewa yayi yana fadin anyi hakkuri hjy don Allah hjy mai data fito part din Alh ne ta hangota a tsaye take fadin wai har zaku tafi ke nan eh ta fada ta juya don a hasale take lokacin.
Ya fito yayiwa mommy saida safe tunkan yakai wurin motan ya bude tana zuwa budewa tayi ta shiga har suka kama hanya zuwa inda zasu sauka ba wanda yai magana a cikinsu don tare da ibrahim suke lokacin.
Yana shigowa dakin nasu ya tura kai kenan ya hangota zaune tana wani karkada kafa a cikin masifa ta mike tsaye tana fadin yanzu gurinka ya cika ko dama ka kawoni gidankune don kawai aci min mutunci.
Kana zaune kana kallo komai baka iya furtawa ba dama kun shirya aimin hakan a tasani a gaba a tozartani yasa ka tillastani zuwa dole.
Inbashi ba dolene sai nazo har ana wani sani agaba wai ana min fada nayi yadda kowa keyi har ana wani fadin dole ka kara aure wai an fadane don inji haushi kome ?
Ko kuma tana ganin wanan zaisa in,,,,,
Tass tass ya dauketa da marin dayasa saidata duka ta dafa kujeran data tashi akansa lokacin don wani wuta data gani yana mata yawo a idanunta a lokacin saboda zafin marin nasa dayai mata.
Ya nunata da yatsa yace ahir dinki wallahi duk iskancinki da wautanki rashin mutuncinki ya tsaya iya kaina karya kaiga uwata ko dan uwana.
Ko don kinga ina kyaleki bana kula iskancin da kike min kike tunanen zaki wuce kaina har kiyi watau fadin kallaman banza kan mahaifiyata.
Sai yau nasan tabbas baki da hankali da tarbiya mara wayau wace bata da tunane kawai tunda nake dake kinga ina aibanta wani naki dayazo garemu ko kin taba jin na fadi kallaman banza akan yan gidankune ?
Ko me sukazo dashi guna kin taba ganin koda musu nayi dasu kan hakan sai nawa uwar don ta tsawata maki kanki daina wullakacin kibi duniya a sannu saboda kin rainani kin mayar dani dan iskan da baisan abinda yakeyi ba zaki dinga zagin yan uwana kina muzantasu a gabana yadda kike so.
Idan kinji ba karya ta fada ba don wallahi ko hjy batace ba aure zan kara nan gaba kadan tunda na fahinci badon Allah kika aureni ba wasila don wani manufa nakune kawai kike tare dani.
Jin hakan tana dafe da kumcinta ta dago tana fadin ka mareni to wallahi baka issa ba dakai da duk wasu masu zugaka akaina sai kun raina kanku kayi kadan wallahi .
Ya daka mata tsawa dasaida ta kadu yace saina takaki na karkaryaki a nan na karya banza ke wacece me kike ko yar wa kike mara mutunci da tarbiya kawai zaki gane kiyi nadaman fadin hakan da kikayi very soon indai nine.
Yasa kai ya shige uwar dakin yana sauya kayan jikinshi taci gaba da zage zage tunda ya shiga bakin ciki da takaine suka hanasa fitowa falon inda take yana dana sanin zuwa da ita cikin ahalinsa a lokacin.
Nida hussai muka shiga kasuwa don taji ina fadin zani kasuwa tace in tsaya mata muje itama tana son sayo gyalen da zata saka da kayanta don taji ance har dinner za ayi na bukin.
Yawon neman ankon yaran na farayi Allah ya taimaka na samu mai kyau dama yafi wancan yadin nasu tsada amma kala dayane na saya tare da takalama shina mijin harda hula da cliff da agogo sai mace da takalma da gyale anan na bada dinki cikin kasuwa express za ai masu muka wuci na sayo garin alabo da kayan miya ganyen ayoyo na sayo da egusi sai naman kai da aka yanko min na dubu uku.
Dan kudin hannuna duk na karar dasu ban sayo ma kaina komai ba munyi da masu dinki da yamma zan koma na karbi kayan koda kuma ban samu zuwa da kaina ba suka ban kati naba wanda zaizo ya karba min.
Ban koma gida direct ba nace wa hussaina ta wuce kawai zan shiga naba hjy sskon ta ta juya ta tafi tana shiga mama tace ai na dauka zaku dadene naga kinbi wanan gantalalan inci maki mutunci yau gidan nan.
A,a mama ni dai ina hanaki fadin haka kan yar mutane yawancin fitan Bantu kasuwa fa mama duk akanki ne amma kinki gane hakan son nakkn cikin da kikeyi mata.
Ko yanzuma fa don su jamal da iyayyensu sukaki yiwa anko taje kasuwa ta hado masu komai har dinki ta bayar ta biya meye gantali a cikin wanan wanda yaje wuri don jininka mama ?
Ke rufa min baki ko nasa tayi masu anko din ne ni in tayi hakan ma bata kyauta min ba tunda mutanen banzane daga dan har iyayyenshi nan nace su nan ko yar macen ne suka rufe ido suka hana min su .
Don yanzu sun gaza dasu shine zai dameni ko inji zafi ita ta saka kanta yin wahala ba wanda ya aiketa don haka ki rabani da zancen banza.
Duk data fadi hakan sai kuma zancen ya tsaya mata a rai sosai tunma dataji hussai da hassana suna maganan a dakin dole tausayin yaran ya dan shigeta abuda naka dai.
Niko ina shiga gidan hjy basa falo amma falon a gyare yake yana kamshi kitchen dinsu na nufa anan na samu iya tana wanke kayan miya nagaida ita nan nake fada mata cewa cefane na kawo wanda zamuyi girkin abincin rana dashi tace kingako hjy ta manta bata fada min ba Allah ya taimaka kin shigo da wuri wallahi da anyi tsiya ai yau.
Ruwa na dora a gas kafin na dauki naman na wanke tas na tsoma a cikin ruwan don in zauka na kawo dan gishiri kadan da kayan kamshi na zuba na rufe na koma anan tsaye na gyara ganyen miyan na yanka.
Na hada ruwan zafin yin tuwon amala din Iya tana nata aiyukan a lokacin tana kuma kallon abinda nakeyi lokaci lokaci wurin tuka tuwonma tare mukayi tana gani don ita ba yadda nayi takeyinsa ba sai yayi mata ruwa idan tayi talge.
Leda na dauko na kwashe saidana ciki kulan abinci na sakawa iya dani don ba zan tsaya ci ba a nan na gama na koma wurin miyan don naman ya dahu lugus saboda silver spoons dana saka a dahuwan har kwara hudu.
Hakan yasa ya dafe a cikin lokaci nan na hada miyan attah na agushi wanda na lemawa manjan dana soya daga baya bayan miyan ya hadu na daure na kawo soyayyen manja na lema a sama na dan rage gas din don ya hade na koma na hada miyan yaukin zalla daga ruwa sai dadawan eru dana zuba a cikinsa yayi kore zalla.
Muka gama misalin karfe biyu har nabar gidan ba wanda yasan na shigo nayi aikin a get na hadu da Aliyu yai min horn ina fita yana shigowa gidan lokacin.
Na shigo gidan ina sallama mama Lantoce a tsakar gida tana aikin girki don itace da g???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?irki ranan ina gaida ita na fada dakina na aje kulan abincin kwantawa nayi indan huta saiga Jamila ta shigo dakin.
Na dago ina kallonta sai naga ta danyi rau rau da idanu tana son kuka nace meya faru jamila tace ba hjy bace tace bazata ban kudi ai min irin kitson su hussuna ba.
Ke kuma irinsa kikeso ko ta gyada kai nace wani irine kitson nasu tace


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login