Showing 75001 words to 78000 words out of 347556 words

Chapter 26 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8792

na kura masa su.
Da kyar ya iya budan bakinsa cikin kyarmar murya ya fara magana tankar zaiyi kuka a lokacin saboda bacin rai yace don na auri wasila a matsayinta na kanwar kawar matata hakan ai kinsan ba laifi bane.
Na kada idanuwata tare da rausaya kaina gefe daya cikin yanayin yatsine fuska nace wanan kuma shine ba zan yarda dashi ba kun dai kasheta don ka auri wasila indai wasilace har wasilan dana sani a baya sunan aurenku sorry wallahi don ba zaka taba gane komai ba a kanta sai ragowan katar iyamurai da yan iskan gari.
Lah Bantu kefa mommy tacw nabi na kira mata ke dan aikin dazun yace tare kuka kamo hanya ashe ke kina nan kin tasa ya Mahmoud a gaba.
A hanzarce na juya na nufi cikin gidan na barshi tsaye anan yana bina da kallo cikin mamaki da taksici har na shige cikin gidan lokacin ibrahim dake cikin mota zaune ya fito yana fadin akwai magana ke nan a kasa gaskiya tunda kaji yarinyar nan ta fara fadan haka abin ka tsaya kai nazarine sosai akai gaskiya.
Don wanan zancen idan ta fasashi ko mutanen gidan mu yarda zasuyi da hakan don ba wani mahalukin daba zai dauka gaskiya bane zancen nan.
Nisawa yayi yana fadin ni ba wanan bama Ibrahim sai Ibrahim din ya dago yana kallonshi yace ban taba tunanen haka ba a rayuwa amma wai abin mamaki ibrahim .
Shin kasan zuciyana ya kamu da son yarinyar nan Fatima kuwa a yanzu ban taba kawo faruwan hakan ba gareni amma tun zuwan nan namu kallo daya nayi mata naji ta shiga raina fiye da tsamanin mutum.
Ibrahim ya saki guntun murmushi yace ai wanan mai saukine kaima kasan na bangaren da za a samu matsalan hakan dan dama dama dai a wurin yarinyar ko ita nasan ba wani mai yawa bane idan ka jajirce mata.
Mahmoud din yace kai dadina dakai saurin yanke hukunci kai yanzu ina fara tunkaran wani da zancen nan ba tare da nayi tako ba akan hakan.
Ya sake wani huci tare da gumi akan goshinshi yana fadin ko an samu matsala akanta za a kuma samu a cikin gidansu ma don nasan maman biyu bata taba yarda da hakan.
Ibrahim din yayi shiru yana tunane akan zancen dan uwan nasa Mahmoud din ya katse shi da fadin bana son in rasa Fatiman ibrahim ko don in samu yaran nan su dawo kusa dani da zama.
Don ita kadaice zata iya zama dasu ta rike min su amana kuma dubada yadda ko yanzu take fama dasu din nan har yanzu bata yarda ta watsar dasu ba dukko da sukan da kakan yaran keyi mata.
Ibrahim din yace kayi kuskure tun farko yadda ta taso a hannunka bai kamata ace ka watsar da itaba daga baya don inda hakan ya kasace a yanzu baida wani wahala ka shawo kanta gakiya.
Don haka ni shawaran da zan baka in zai yuyu gara tun wuri kada ka furta hakan gara kayi hakkuri ka cireta a ranka ko banzama kaji abinda ta fara fada akan matarka yanzu ai.
A dan fusace ya kalli dan uwan nasa kuma aminsa yace wai meyasa baka ganewa idan nace zanyi abune na dauka kaine na farko da zaka mara min baya hakan ya yuyu.
Ibrahim din ya dafashi yana fadin dan uwa ni duban abinda zaije ya dawo cikin maganan nan nake maka amma kayi hakkuri domin hakan wani babban aikine na hango maka cikin maganan nan kuma ita fatiman kana ganin zata yarda ?
Lokacin ne wayanshi ta dauki kara kira amma sam bai kula da kiran da ake masa ba a wayan har saida ibrahim din ya dafashi yana fadin kirankafa akeyi a waya bros.
Sanna yakai hannusa ya fiddo wayan yana duba Wasilace take kiransa a lokacin baisan lokacin dayaja wani uban tsukiba ya kashe wayan cike da dacin rai gaba daya baya da bukatan jin wasu kalamai daga bakinta.
Saboda jin kalamanta ba zai haddasa masa komai ba sai bacin rai domin shi a yanzu duk fadin duniyan nan babu ya macen da yake son gani da jin muryanta kuma irin fatima.
Don ita kadaice yake ganin zata wanke masa zuciyarshi a yanzu har komai nasa ya daidaita ya koma daidai yadda iyayyensa suke masa burin hakan.
Kayi hakkuri dan uwa kabani nan zuwa gobe don kaga yau bamu da lokacin hakan saboda masu daurin aure zuwa gobe insha Allahu sai mu nemo mafita kan wanan zancen .
Yanzu dai abinda nake so dakai shine ka kwantar da hankalinka saboda tun farko dai ka riga da kayi kuskure yanzu kuwa sai neman hanyar gyara.
Ina shiga hjy ke fadin wallahi fatima an samu matsala don yanzu Alh ke zancen yan daurin aure yanzu ya zamuyi ke nan dan shiru nayi kafin nace mommy me zai hana muyi amfani da wanan farin shikafan na wurinki inyaso ke a dafa maki wani yanzu.
Anty hafsat tace nima abinda nake son fadi ke nan nace bari a tura Nura yaje ya sayo kayan hadi a kasuwa yanzun nan sai a hadashi ko nan gidan ne tunda akwai markade nikake ku kuma nan sai ku fito ku fara hada take away din mazan don aikin yayi sauri.
Muna tsaka da aikjn girkinne can a bayan dakunan su hjy naji ana kiran sunana na juyo naga wasila a tsaye bayana din tana fadin Bantu nace ko kinga min honney don Allah ?
Waye honey na fada ina dagowa anty hafsat tace mijinta wai nace ya habibi wai da zan shigo na barshi a kofan gidan nan ai ina fadin hakan na juya naci gaba da aikin gabana na barta wurin .
Saida naji anty hafsat na fadin angama muna habibi an dawo muna da honey kuma yanzu nace saura sugarcane kuma ko nan gaba duk suka kwashe da dariya.
Cikin yardan Allah mukayi komai yadda ya dace hjy tana ta saka muna albarka karfe biyu aka daurawa zainab aure da mijinta mansur .
Komai kuma yayi kyau sosai wallahi don anci ansha saboda ya habibi ya bude aljihunsa an fita kunya a gidan nasu saura takwas na dare da zamuje cin dinner da fannin ango suka dauki nauyin yi.
Gida na koma don inyi wanka in huta ina wankan na fara kafin nayi sallah saida na fitone na fara tunanen zancen mu da ya habibi.
Wani takaici da bakin ciki naji lokacin nace dama nasani ba iya amsan dana nashi ke nan ba dan rainin wayau kawai.
Dama shedan bai zuwa mutum sai lokacin da yaga mutum mm a shirin yi ibada zaiyi kokarin shagal da mutum daga barin aikin ladan don kada ya samu rahaman ubangijinsa alokacin.
Daidai lokacin da nake idar da sallane mama uwa ta fado dakin tana fadin Bintu ashe kin dawo na dan kwanta fa shine barci ya daukeni nace wallahi mama aiki mukayi a can gidan nan nake fada mata abinda ya faru da kiran da sukai min din.
Tace ai kuwa ko malam ya dawo da ledanshi na dauri aure wanan abin yanzu kuma ya zama al,ada a wurin maza suma duk wanda yaje dauri aure saiya dawo da dan kumshin leda kamar mace.
Nace mama ko inane fa wanan al,adan don in bakayi ba sai ya zama maka abin fadi a cikin abokai wani dazun ko fitan nan da yaya tayi anya ba wani abin sheri taje yiba a can.
Ta fitane na tambaya cikin mamaki tace ta fita mana kuma bata fadawa kowa inda taje ba na dauka ai gidansu hjy taje da zancen jiya din kinsan yaya bata da hakkuri haka take kamar zawo wani lokaci.
Wayana yayi kara na dauka ina dubawa maman saudiya nagani yadda na rubuta mata da sauri na dauka ina sallama ta amsa tana fadin yau buki ya hana mu ganki ko ?
Ga autana nan kwance wai shi wanan tuwon amalan nan yakeso yau ya hanani sukuni tun dazun da zancen banza nace barin kawo masa akwashi kuwa wanda mukayi na buki gashi nan da zafinsa yanzun zan kawo masa mama ya rabu dake don Allah.
Kulan na bude yana da zafinsa nayi tunanen hakan yasa na dauki leda biyar na dibi miya kuma na saka nama sosai na aje da niyar na aika masu sai kuma hjy ta kirani.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

.KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
2?? 3??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,

Don Allah kada wani ko wata yace zai juya novel din nan zuwa Audiovisual don na sayar dashi ga yan S Zaria duk wanda ya juyashi zuwa hakan akwai sharia tsakanin mu dashi da fatan za a kiyayyen don Allah.
Ni kadai na dauka zuwa gidan yamma ya soma don haka akwai haske ko ina na gidan don suna kunna haske tun karfe hudu mm a yamma kullun a gidan.
Nayi sallama na shiga yana ganina yace amma mami yarinyar nan yar albarkace da kina fadin hakan ban yarda ba sai yau din nan.
Dan hararanshi nayi don saboda yawan wasan da yake jana dashi yanzu mun saba dashi sosai kuma ko banza shine karami a cikinsu .
Sai naji hjy tace indai ka wuce aita huta da sherin nan naka yanzu ba gashi ta taimakeku ba kaida uncle din ku don kiri kiri yaki cin abinci waishi wallahi da za a samu sakwara ko wanan tuwon shi yake son yaci .
Kinga min yara da tsiya suna son dauko min rigima ni ina zan iya wanan aikin wahalan yanzu mama zaki iya ai tunda ba mai yawa zakiyi ba.
Mamata kinsan yaushe rabona da shiga kitchen da sunan aiki kuwa ai naso ace mun tafi dake wallahi Alh yaci girkin nan naki jaji Al,amin yace wai da munga boni mama don kullun irin abincin da zaisa ai muna ke nan.
Don tana karatune da na biya mata wallahi mun tafi da ita ta huta a can wallahi mami ta huta da wa yan nan munafukan gidansu din da sauri na dan kalleshi.
Mama din tagane mamaki nake ya zagi yan gidan mu haka tace aina manta dazun wata matar babakin tazo gidan nan da safe .
Matar gidan mu mama na tambaya cikin mamaki tace wallahi tazo bincike kan wanan kayan wai idan ba daukar muna kikayi bamu sani ba shine mahaifin ki ya turo ta bincika.
Innalillahi na ambata nace daga gidan mu mama Al,amin ya tare da fadin ga recording nan ma mami tayi don kada tayi mussin hakan sai hjyn tace musu akan me ai ba zatace da ita komai ba tunda bataci riban hakan ba.
Nayi shiru ina dan tunane sai can na gane maman biyu ce fitan da mama uwake zargin tayi donni ke nan ashe dama donni din kuwa ta fito gidan lokacin donta kulla min sheri ke nan ashe.
Lalai mama uwa ko tasan mama da kyau tunda harta fahinci meta fito yi a lokacin harta iya gano abinda ya fidda ita a gida lokacin.
Yanayina ga baki daya ya canza lokaci guda son wanan abinda mama tayi min har abin yakai ace mama tana min irin haka ai wanan shine zagon kasa.
Ina an gama bukin dai nadago ina sauke ajiyyan zuciya nace eh mama saidai karfe takwas za,aje wurin dinner shine ya rage muna yanzu.
Ok akwaiko wani lace a cikin kayan nan naki wani haka sky colour da adon dark blue a jikinsa wani me ratsin adon tsone wurin dark blue din adon ina ganin shi zai dace sosai da zuwa dinner.
Bari na dauko maki mahadansa nan ta mike ta shiga ciki sai gata da dan madaidaicin leda bandai san meye a cikinsa ba na karba nayi godiya sosai .
Kofan aka turo aka shigo ya Aliyune tare da uncle kaina saya ina masu sannu da dawowa Aliyun ke fadin kai ina ka samu wanan abincin yana kallon abincin da dan uwan yake ci.
Da yatsa ya nuna masani ma,ana a wurina ya samu ke nan ina dai namu ne a nan sai shi Al,amin din yace badaku ta kawoba wanan idan naci zan kara ko Fatima ?
Ke zuba min don Allah yunwa nakeji dama inji uncle din kai amma yaran nan baku da hali wanda yaji sai ya dauka bamuyi abinci bane a gidan alhalin ga abinci nan girke ba wanda ya kula dashi.
Marmarin wanan din dai sukeyi don baku dashi a can sai shinkafa koda yaushe dole shinkafan ya fita ransu ai ansan akwaishi mama na fada ina shiga kitchen dinsu na dauko plate da cups din shan ruwa.
Saidana zuba masu nakoma daga bayan kujera don ba zan iya tsayi suna cin abinci ba Al,amin ne yace amma uncle kana ragewa abincin nan dadi cinsa da hannu yafi ci da cibin nan da kakeyi ai.
Kaima kasan Mohammad ba zai taba cima abinci da hannunsa ba saida cibi nan gashi ko mamata dake dan shigowan nan tasan da hakan.
Dago kai yayi ya kallo inda nake yace badon naga kin rike wanan sunan ba Ukuthee ba abinda zai kaini cin abincin wanan kada ki dauka kin iya wani girkine ake yabon ki haka shi wanan har yanzu baisan wani dadi bashi kawai yaci abincine yasani.
Lah uncle amma kuma kake wanan loman kaima baka san dadin ba ke nan Al,amin ya fada saiyace dashi yunwa nakeji yasa nake cinsa ai kawai.
Mama kinji ko in hakane kuwa ba zan sake girka masu abinci ba sai sun tafi na dinga zuwa kullun ina girka maki abinda kike so koma meye zan dafawa mamashi.
Don Allah ka bari kada kaja muna gashi gobe mama tace zatazo tayi muna Danwake mai mai da yaji a gidan nan gaskiya mama a bari saina dawo idan sun tafi.
Haba dai maman mu yi hakkuri da wasa nakeyi ko wanan din ai yayi dadi sosai sherin wanan mai yawan magananne Al,amin yasa na fadi hakan .
Basu ba harni saidana dara mama tace to ku dakata duk mai son diyata tayi mai girki gobe nagani a kasa ta mika masu hannu alaman su bada wani abu.
Da sauri nace Lah mama don Allah ki barsu basai sun bada wani abu ba hannu ta dago min tare da fadin kyalesu mamata aike ba boysrsu bace.
Da kike ganinsu nan manyan ma,aikatane ina zan kyalesu su dinga shammatanki indai zakiyi masu wanan dan waken mu gani a kasa don ba zan yarda ba.
Mama wallahi su barshi nina yafe sai naji mama din tace ni ban yafe ba ai wurin dinner zaki yanzu kuma dole ki bada dan kudin manni a wurin don haka su baki tunda suna da kudi.
Mama ai uncle ya ban tunda ya hadawa yarshi provision mai yawa don haka a cikin ladansa zan masu wanan din ya wuce na yanzu dai zasu bada.
Ina danwaken sai kin hado abubuwan yisa a kasuwa nace ban ma san ko na wake zallah kona filawa suke so ba wanda yafi dadi zaki muna muna dan gwal danyajin nan da mai don Allah.
Aina fulawa gaskiya yafi shiga sosai amma zan dan hada da wake kadan ba mai yawa ba a ciki to naji Allah sai kunyi wani abin tundai kai Aliyu mama ta sake fada.
Mikewa Uncle din yayi zuwa gaban mama ya tura hannu a aljihun wandonsa sai ga wraper ayan dubu ya zaro ya dorawa mama a hannunta yana fadin wanan din yayi ko ?
Saura kai ta mikawa Aliyu hannu yace mama ai abinci nakeci a bari na gama dai ko an bari kai kawo sai Al,amin din ya kalloni nace nayefe ai yace kinji mama tayafe fa.
Aina fadama ban yafeba ni sai kowa ya bata cikin ku haja kawai yarinya zata bar aikinta ta dinga zuwa tana hada muna abinci zikau baku tunane.
Mama ai uncle ya badanamu kada mu kara mata yan gidansu suce ta,,,, kaima sherin zakayi mata don karka biya da sauri ya sa hannu ya debo yan dari bibiyu ya aza mata a hannu yana fadin na daina saka albarkan tunda yanzu abin na biyane.
Oho dai dama aiba albarkanka take nema ba ya Aliyun shima ya dora nasa yan dari biyar biyat kar dasu yace mama mun biya shike nan ko aje dinner lafiya nasan wanan dai yarki kikewa bara da wayau.
Ai basai munyi bara ba kono na wadatar da ita ko ita kanta da kake ganinta tana da sana,anta wayau dai naga kuna mata shiyasa nace ban yarda ba gaskiya.
Haka mama ta hada kudin ta miko min tana dariya nace zan tafi Al,amin yace kinada wanda zai kaiku wurin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login