Showing 330001 words to 333000 words out of 347556 words

Chapter 111 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8735

a gidan nan inba ita ba dama ?
Daga kofa Usaina tace akan meko za a bayar tunda bata tuna da kowa ba lokacin da take cikin dadin rai a gidan mijinta ai mantawa tayi da kowa gidan nan sai yanzu daya cika da itane zaka dauki kudinka ka bata ?
Haushi ya kara kamata ta shiga balle ballen magana tana fadin dama tasan ba,a sonta kaddara daine da ila ya kaita auren Mahmud akai mata sheri kada su zauna lafiya don kowa yarasa a cikinmu.
Gashi na bar maku hassana kuje ku aurenshi indai mahmud ne ai nima kaddara ta kaini aurensa ai daga daki hassana ta fito tana fadin Samira sunana ya fita daga bakinki don Allah.
Waye Mahmud ana zancen mazan arziki wake zancen wani Mahmud can yanzu ke dai da kikaji kika gani kije kiji dashi ni nafi karfin Mahmud a yanzu kema kin sani aini wallahi ba sheri kikai min ba taimakona kikayi a hakan kuje can ku karata dashi keda kikaga kina iyawa din gaki gashi.
Ni Mahmud ko daura minshi a kafa akayi yanzu na yafe indai wanan mutumin ne don ki sani haba nan dai gida ya kicime da hayaniya fada sosai sukayi suka taru a kanta suna tonawa juna asiri.
Baba yaji hayaniya yayi yawa ya shigo gida nan ya samesu da tsina yana fadin tir tir da halinku wallahi yan banza ko wace ra fito da miji nan da wata uku idan ba haka ba wallahi na auraku ga wanda naga dama shegu masu gadon bakin jini ga iyayyensu mata.
Ke Samira ki tattara ki koma dakinki inkinje yayi gunduwa gunduwa da namanki ya sako min a kwali ingani ya cika dan duniya na fada maki ba rabuwa dama tun farko ai saita saka kuka cikin tashin hankali.
Ba dai dadi a gidan ranan cin mutunci anyi shi harda mama da zama daki ya sama a yanzu saida ta fito tana kare yayanta tare da yiwa aurena da baba tace yake kuri dashi don yaga kudi ayanzu sun rufe masa idanu a yanzu har yake aibanta mata yara.
Kai gidan mu gidan danja abu kamar almara haka mama uwa ta kirani ta saka min muryan mama ina sauraro tana sababi lokacin mu har mun shiga garin Abujama muna gida muna hutawa a lokacin.


ZAINAB IDRIS MAKAWA


KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Muna da sati daya da dawowa Abuja na samu na kira mahaifiyata mun dade muna magana a waya da ita zakice ba ita bace a yanzu idan kinji muna waya yadda takan dan sake muna hira duk da akarshe zakiji tana ban hakkuri kan abinda ya faru a baya.
Idan naji hakan nakan kaucewa zancen ince Ummi wanan ai rubuttacene a kaddaran mu baki daya abar tuna hakan tunda haka ubangiji ya tsaro tun farko saitayi dan murmushi.
Na sheda mata zamu shigo karshen wani wata kamar yadda naji yana fada don ma bukine da zasuyi a family dinsu yasa ba zata ganmu ba da munzo mukayi sallama bayan tayi muna Allah ya kawomu lafiya.
Ban dade da aje wayan ba ina wajen kwance kiran hassana ya shigo min na dauka ina fadin big sister ke nan ta kwashe da dariya tana fadin karan dafi ya akayi ne shiru kwana biyu bankira ba ke baki nemini ba.
Dan dariya nayi nace kinsan in bashir na kusa komai nawa ragagene ai yau dai na samu yayi tafiya yanzun nan muka gama waya da ummina sai ga kiranki kuma.
A cikin hiran mu take fada min bari ke dai baba yana nan ya dora muna takunkumi a gida yanzu kedai mukan zuwan Samira bai tsinana muna da komai ba sai wahala.
Ai Mahmud din baizo ya dauketa bane na tambaya take fadin yo ina zaizo kiko yar iskan yarinyar nan ashe sakinta yayo tundaga can bayan ya linkida mata dukan tsiya kuma ya saketa amma bata fadawa kowa ba.
Saida taga da gaske baba keyi zai mayar da ita take fadawa maman Amira cewa ta koma bayan ya sake ta ko ita wallahi saidai ta barwa baba gida idan yace sai ta koma gidansa.
Gashi ba dadi tsakaninta da uwa ranan da kuka tafifa ba dadi ranan da ita da uwar har taja muna tsiya wata uku kacal baba ya bamu sai mun fito da mazaje koya auramu ga wanda yake so.
Dariya na kwashe dashi ina fadin ashe kice mu shiga kasuwa neman miji ke nan kafin baba ya kwafsa muna ta danyi dariya tana fadin aike kin huta bantu.
Mama Lanto ta fada ai tace Allah yana sonki sheri ya zamo maki taki a rayuwa ke kan taciwa Samira mutunci sosai ranan tana fadin ita a yanzu ba zata sake yarda ta hadata da kowa ba.
Nace kinsan Allah ni tausayi matan nan ke ban yanzu da ganinta zancen zuci yana cinta duk kuma nasan akan samirace in kin bincika.
Kema kin sani ai tasan komai dake faruwa ita uwan boyewa kawai takeyi sherintane yake cinta kinji samira samira ba karamar makira bace bantu ki barta kawai inda kika ganta hassanan take fada nace .
Sheri har kaiwa kanka kina matakin mai tsawo a jami,a ki tuma ki bari don kinga kudi sai naji hassanan na fadin ina kudin suke yanzu ke aini na auna arziki da mama taso hadani dashi banso banso har maman tudun wada ta ciwo kaina na yarda da kitsawansu a lokacin .
Da yanzu kece a hakan ni tun farko nasan waye shi zan yarda in jefa kaina cikin zuciyan nan nasa waceni aima abin kunyane hakan a gareni bar dan iska ta fada.
Yanzu fa baida komai yadda Samira din ke fadi wai an masa damfara an karbe kudadenshi ko tayi damfara na masu kudi sin karbe kudin su na bata amsa.
Yace Samirace ta shigo masa da farar kafa har hakan ya sameshi shi tun haduwa da ita arzikinshi ya koma baya son haka su rabu kawai tunda bata da halin kwarai ya fadawa baba a cikin waya.
Don dole baba ya nemoshi yaji ba,asin abinda ya faru tsakaninsu shine yace bai iyawa tana da kyashi da hassada a rayuwanta don kawai taji kina da ciki ta aza mai fitina sai ya kaita kasan waje an dubata yace baida halin hakan shine ta shiga zaginshi shi kuma ya linkida mata duka ya sakota yace ba zai iya ba ta dawo gida.
Kinsan halin baba ai nan yazo tsakar gida yai mata tas yace indai akankine saidai ta mutu don duk wanda ya daura dammara da ajiyan Allah karsheshi wahala.
Nice ajiyan Allah na tambaya tace ai kinsan haka yake ce maki yanzu na danyi dariya ina fadin oh ni Fatima nasha suna a duniyan nan nikan tun daga jamal sai naji tace.
Take fadin ke nama tuna ko jiya jamal yazo yana tambayana wai kince zaki turo a daukesu in anyi huta na tuna maki don Allah.
Nace ban manta ba sister zancen yana raina kilama tare zakizo dasu don naji Boss yana maganan zuwa ki ko kan ya tafi din nan saida yayi magana a kanki.
Tace Allah sarki in-law ashe bai manta ba nace nakune yazo daya yace duk kin fimu hankali da natsuwa a gidan mu ta kwashe da dariya tana fadin ni din nace ai a raina nace baisan ke din kaifi daya bace sai ranan daya fada tarkonki zai sani tace ba za akai can ba ai insha Allahu.
Munyi hira sosai kafin mu kashe wayan mukai sallama ta barni da tunanen zancen ya habibi da naji a wajenta gaskiya akwai kamshin gaskiya a zanceta don gidan mai da yake ginawa nan kaduna ya saida naji daga baya.
Haka kuma ya dai barkace gaba daya lokaci guda kariyan arziki ya taso masa nina rasa meke damunsa ya barkace a dan shekarun nan kuma ni dai sanin da nayi masa a lokacin yana son zancen iyayyensa amma yanzu ba zancensu bana diyansa gabaki daya duk ya barkace wallahi.
Allah ya gani ban manta da rikon da yai min ba son a wajensa da matarsa na fara samun saukin rayuwa da har yanzun nake a cikinsa na aje a raina zan bincika muyi magana dashi ta fahinta in fahinci halinda yake ciki idan ina iyawa in taimaka masa.
Don abune mai zafi da ciwo kariyan arzikin matashi lokaci daya hakan abin yakan zamo matsala har yazo ya shafi kowa a karshe a koma da ansani da anyi kaza.
Allah ya gani iyayyensa basu min komai ba har yanzu kuma suna sona da arziki da mutunci don nikan dafasu inji sauki alokacin da nake neman taimako a rayuwa nima shiyasa bani son jin wani abu mara dadi a tare dashi.
Shigowan sadiya dakin ya katse min tunanena a lokacin ta fada min ga bakuwa nayi wai tace ace min maman yan uku makwabciyatace da sauri na daga na fito don na tuna da ita.
Wanan matarce datazo wani lokaci yaran dai nata sunzo sau biyu tun lokacin bamu kara haduwa dasu ba kuma na fito tana fadin a,a amarya shiru haka koda yakw na fahinci kamar ku bamaau zama bane kamar mu ko yanzu yaran suka matsa min inzo sunga kamar kuna gari.
Ayya anty kiyi hakkuri bamu zauna bane munyi tafiyane mun dawo kuma muka wuce gida na fada ina kaiwa zaune na gaida ita take fadin masha Allah aure yayi albatka ashe su yan uku zasu samu abin dauka.
Kullun su dameni mama ki haifa muna baby mu dauka muma niko yanzu basu san tsoron haihuwan nan nake ji ba tunda nayi uku bayansu yaran basu zuwa da rai saidaga baya aka gane shuga gareni yasa haihuwan ma ya fice min a rai yanzu su dai din Allah ya raya minsu.
Na kalleta nace Allah sarki Allah ya yaye wahala anty aiba daga nan yake ba komai daya samu bawa da sanin ubangijinsa sai kuma kiga anzo an dace daga baya an samu rayye a cikinsu.
Tace bari ke dai baki ganewa ne yanzu haihuwan ma ba dadi babansu ma yace in huta hakana Allah ya raya minsu din muyi dan hira sosai da ita kafin tayi sallama ta tafi ina tambayan yaran take fadin sunje nan islamiyan malam khalid acan suke hadda yanzu.
Sai naji sha,awan na tura sadiya itama ta karu damu nace aiya aikuwa da mun tura yarinyar nan ta tare damu dama nayi tunanen hakan har boko idan akwai kusa mai dan saukin kudi nake aon in turata.
Kin dauko yarinyace take tambayana nace eh jikan iyace dake tayani zama sukazo tare to zamanta hakan yana damuna tace aiko dakin taimakawa rayuwanta zanyi magana da driver mun donshi ya kai muna yaran can zaizo ya amshi komai da za a bukata sai yayi mata registerer.
Nayi mata godiya ta tafi abincin da ta sama iya ta hada nasa sadiya din tabita dashi har gida sai ga sadiya din da turare ta bata tare da number wayanta tace in kirata.
Na kira take fadin haba haba dai amarya don kawai nashiga zaki biyoni da abinci haka son Allah kada a kara min hakana nace kiyi hakkuri anty nasan kinfi karfinsa hakkin makwabtakane da alhakin ido da hanci na saukewa kaina badon kin rasaba.
Dariya na bata tace to Allah ya karba yasa mufi karfin zuciyan mu na amsa da amin muka dan taba wani hiran a waya kafin muyi sallama da juna.
Karfe takwas bayan na idar da sallah kafin na fito na gwada layin ya habibi dake a tsohon wayana saiko ya shiga ya dauka yana fadin Fatima kece ?
Muka gaisa a cikin mutunci dashi kafin na soma fadin yaya habibi sai nake jin maganganu marasa dadi suna fito don Allah kayi hakkuri kafin naci gaba sai naji yayi murmushi yana fadin.
Fatima ba zaku gane irin hakkurin da nayi da Samira bace bata da dadi wallahi kin sani saidai abinka da dan uwane kawai zaisa ba zakiga laifinta ba sai nawa a yanzu.
Nace yaya ba hakana bane ni yanzu ba son samira na kiraka ba na kirakane muyi maganan daya shafi rayuwa tsakanina da kai kuma da zuciya daya wallahi na kirane muyi magana na yaya da kanwarsa kan abinda ya shafi rayuwan yan uwa don ban taba manta alherun ku gareni kaida yayata Safiya har abada .
Don kune silan zama komai a rayuwata a yanzu don me zan manta halarcin ku gareni idan ba na zama butulu ba har abada bani manta taimako ga wanda yai min a lokacin da nake cikin halin neman taimako a baya.
Jikinshine yayi sanyi nagane hakan ta muryanshi daya sauya lokaci guda yakw fadin ya akayi Fatima kina da matsalane da mijin ki kome na danyi murmushi nace ko kadan wallahi yaya lafiya kalau muke dashi.
Kawai dai in ba zaka dauki zance na da wani fassara ba da abinda zan fada yanzu ya habibi ka daukeni tankar kanwarka ta jini ya zamo siri a tsakanin mu ba sai kowa yaji ba a duniyan nan.
Mekikeso dani Fatima ki fadi maganan ki kai tsaye matukar baifi karfina ba kai tsaye insha Allahu ni Mahmud nayi maki alkawarin zan maki ko menenw matukar bai sanawa sharian mu ba.
Nagode yaya dama nace idan na baka kudi a wajena ko zaka karba kaci gaba da business din ka normal basai kowa ya gama fahintar ka ba a yanzu don Allah yaya kada kace a,a ka fahinceni don Allah.
Shiru naji yayi na dan lokaci har saida na daga wayan ina dubawa kafin naga yana online din nace yaya bakace komai ba mana kayi shiru.
Fatima me zance dake kina da kudi a wajen kine da har kike min tayin haka ko kuma mijinki zaki turasa ya taimaka min nace a,a wallahi yaya ina da kudin kaina matukar milayan goma dai zasu iya daga ka sai ka dan fara Allah yasa masu albarka dul lokacin daka samu kuma sai ka mayar min shine kawai nakw so da kai naji ya kashe waya nayi mamakin hakan.
Na dan bada lokaci na sake kiranshi ina fadin ya habibi ko maganan bai maka dadi bane ka kashe wayata ?
Yadda naji muryanshi yana amsa min yasa na fahinci kuka yake a lokacin yace Fatima ba hakana bane tunane nakeyi na duniya kawai shiyasa ake son kayi duk abinda Allah da Annabinsa suka fada idan kabi baka tabewa a duniyan nan.
Duk cikin yan uwana fatima ba wanda ya taba kirana haka yaji damuwa ko halinda nake ciki tun bayan rasuwan yar uwarki safiya sai ke ayau ke da kike ganin na taimakawa rayuwan ki taimakon da baikai cikon ludayi ba ma ko rabisa a lokacin.
Sai gashi yau kece kika san zafina kika san damuwa tabbas safiya bata fadi karya ba a kanki da takan fada min idan bamu taimaka maki ba wa zai taimakeki a lokacin kema wata rana bamu san me Allah zai zamo dake ba ki taimakemu ta wani hanya gashi kuwa nagani ayau din nan.
Fatima ke mace ce hakan ba zai yuyu tsakanin muba mu biyu dole sai wani naki ya sani tare da wani nawa nima na jini abune na amana kike son mu kulla a tsakanin mu dake wanda shedan na iya biyowa baya ya bata halakar tamu ta hanyan yaudara na naci amanan ki kinga ban kyauta maki ba kuma.
Don haka ki bari zan tuntubi baba garba da baba mai mota cewa yadda muke kiran mahaifinsu gidan mu ya fada inji ra,ayinsu zankiraki daga baya in sanar maki da duk yadda mukayi dasu din insha Allah.
Ku kema ina son ki fadawa mijinki ya sani don kada daga baya yaji zancen ya zamo maki matsala dashi tsakanin ku nagode fatima Allah ya baki zuria masu albarka da zasu rama abinda kikewa mutane ya kashe wayan.
Shiru nayi ina tunane ta yadda zan fitowa Boss da zancen duk da nasan bada dukiyanshi zanyi amfani ba nawane amma ina duban yadda zan fito mashi da zancen kai tsaye haka.
Mai karatu nasan zakiyi mamakin ina na samu kudi haka cikin dan lokaci a,a kada ki manta wanan sarkan nawa na daham da muka sayo da Fadila a saudiya da wanda mahaifiyata ta zo min dashi da kudin da nake tarawa tun farko suna haihawa a banki sai kudin da mahaifiyata ta saka min ga account ita da yan uwanta bissa ga al,adansu idan an aurar da yarinya dasu nake son yin amfani wajen daga ya habibi a yanzu nima.
Bayan kwana biyu ba kiran ya habibi har boss ya dawo daga Accra ghana dayaje don haka hankalina ya dauke da dawowanshi din duk wayoyina na kashesu muna daki ana shan dinner.
Sai daya huta ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login