Showing 108001 words to 111000 words out of 347556 words

Chapter 37 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8788

uwar biyu yaushene zata girma tasan Annabi ya faku ?
Gara da bakisa rai akabsa ba kibar zancenshi suje can su karata dashi mu gani in zai yardashi don so ai a zuciya yake data hakkura tunda keya furta yanaso dayafi mata saukin hadin nan da takeson yi tsakaninshi da yayanta.
Wasu yayama zata hada dake yaran nata jiki a soye irin na uwarsu ina za a hada dirinsu dake Allah dai ya kyauta wani hassada takine ga bawa.
Balleni gwaggo baya gabana indai wanan ne nafa sanshi don na zauna a gidan shi kuma naga yadda ko yayanshi yanzu ya watsar ya auri kanwar kawar matanshi .
Me zai kaini shiga gidanshi da hankalina Allah dai ya tsareni wallahi niko zancen ma banson ayi na kuma fadawa baba gaskiya ya fadamai ya fita harkata don Allah karatu nakeyi ni.
Allah dai yayi maki zabi na alheri amma wanan abin ya bani mamaki ita Altine da take fadin hakan wani tsiya take a gidan mijin nata ?
Gata nan kullun jiya wa yau ba gaba ba baya duk hakan baisa ta gane ta daina sherin nata ba har yanzu ?
Kada zancen yasaki wani hali tunda basuyi kamar Allah ba ai sherin su kuma akansu zai koma insha Allah ni yayama yafi ban mamaki daya kasa maganin wanan matsalan shida gidan shi.
Baba yana kokarinshi fitinanar mace kawai Allah ya hadashi da ita don ita kowa bata bari ba gidan nan inba diyan cikinta ba.
Har akai kira na koma daki zuciyana yana cike da mamakin wanan kyautar sojan a kaina don irin alherin dayake min dinnan ya fara sakani a shakunsa .
Sai nake gani kamar tarko yake dana min yana son rudina da abin duniya don yaga na shagala na sake jiki a hakan ya samu ya yaudareni karshe ya gudu ya barni.
Don mafi yawan maza masu yaudara haka suke zuwa,wa yan mata da tsigan nuna kudi a karshe sai yaudara ya biyo baya don haka zanyi taka tsantsan dashi har in gane manufarshi a kaina.
Haka rayuwa ke tafiya gwaggo kuma sai yan magunguna take ban tasani a gaba insha ko hayaki da sauransu kuma dole inyi tunda tayi bugun gaba ta nuna ita uwane a gareni.
Yadda ta rikeni nima hakan na riketa ban bari tayi wani abu kuma duk abinda ya dace ayiwa uwa ina matashi haka mama uwa itama nakan dan mata sako idan na dan samu kudi .
Don ban manta da halarcinta gareni ba haka samira ta dawo mukaci gaba da zama saidai wanan karon ba kamar daba da komai mukeyi a tare yanzu kowa harkan gabanshi yakeyi.
Lokacin data dawo taso matsawa yaron nan Aliyu dan almajirin mu sai ta bashi wanki idan yayi kuma ta kama zagin shi wai bai wanke mata da kyau ba.
Ganin yaron ya fara takura yasa na fadawa gwaggo sai tajawa abin burki tace kada ta kara ganin wani ya nashi aiki a barshi da diban ruwa da aiyukanta.
Ranan ina jin tana ta faman jan tsuki tana kananan magana lokacin ne na bata amsa nace haba samira da daba yaron wake maki wanki ko wani abu ko a gida ai naga keke abinki.
Ta juyo tana fadin malama banfayi da kowa ba nasan dama bakin ku daya don kawai anga ina bashi dan wankin nan ne dai nasan gwaggo tayi magana.
Nace saiko ki wanke abinki ko kikai wanko tunda baki son magana tunda shima dane ai ba fadowa yayi daga sama ba ki tausayawa yaron nan mana don Allah.
Yanzu na fahinta nagane saukin abin dai nima ina da kanne balle a gwada min tausayin kani nace ni da banda ai Allah ne bai nufa in samu baya a tare dani ba kuma hakan bai hanani rayuwa a cikin ku ba.
Mun dai yisa ba dadi da ita muka gaji na kyaleta nasan kuma gwaggo tana jin mu tankawane kawai batayi ba don gudun magana ace tafi son wani a cikkn mu.
Duk wanan abin samira bata san mun kula da soja ba gani take itace mai farin jinin wanda bayan malam dake daukata bata da wani na gwadawa shi kuma yanzu ya dan fara ja baya da ita.
Don ya samu sabbin yan mata dama halinsane hakan idan wasu sunzo ya bar wace yayi yayi da ita ya koma gun wata.


ZAINAB IDRIS MAKAWA





KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
3?? 3??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Zaune suke gaban abinci har kowa yaci ya tashi bataga dan uwan nata ya fito ba a ka,idansu kuma karfe goman nan indai kana gida zaka fito a gaisa da yan uwa aci abinci tare adan taba hira kafin kowa ya kama tsabgan gabanshi.
Sai ta kula tun dawowanta dan uwan nata baya cikin sukuni asalima wanan zaman duk yanzu ya daina idan ya fito zai fita zuwa wani waje ne .
Wanan yasa hjy ta danshiga damuwa don ita macece mai kula akan ahalinta sosai don sune rabin rayuwanta a yanzu.
Babban abinda yake damunta a yanzu shine halin da kaninta kuma danta ya shiga a gashi kullun ta tambaya sai yan uwa suce mata ummu kinsan haka yakefa dama shi.
Kai takan girgiza tace wanan na dabanne gaskiya don har rama ya danyi da baki ina dai ba matsala yake samu ba a wanan aikin nasa yanzu.
Gashi idan ta tambayeshi sai yace ba komai Uktee aikine kawai ke dan min yawa daga hakan bai dora komai yaja bakin shi yayi shiru.
Don haka wanan zuwan nasa tasha alwashin sai ta titsiyeshi taji menene damuwan dan uwannatane ko matsalace babba ya shiga zurfin ciki ya hanasa fadawa kowa ?
Abincin dare za aci a lokacin gaba dayan su sun mayar da hankali akan abincin suna ci in ka debe shi dake zaune ya kurawa waya ido yana dube dube a ciki. tsura masu ido yana kallonsu sai ta daga muryanta da dan karfi ta kara kiran Mohammad da dan karfi.
Firgigit yayi ya dago kai yana kallon inda take zaune kafin kuma ya juya gefen shi ya ganta tsaye ta zuba mai ido cikin mamaki tana karemai kallo yace.
Ummh ummu Ukteeh da kyar ya samu ya saita kansa daga kame kamen da yakeyi na ganinta tsaye a kanshi ta zuba mai ido cikin zargi ya samu ya daidaita haruffan da yake son fadi yace Ukuteeh banjiki bane wallahi.
A hankali ta dafa Al,amin dake kusa dashi zaune ta nuna mai inda ta taso kusa da Abba tace yaje can ya zauna cikin nune ya gane me take nufi don hakan ya mike baki alaikum ya nufi inda ta taso din ita kuma ta gyara kujeran ta zauna kusa da dan uwan ta.
Tana masa duba irin na tuhuma duk sai yabi ya tsargu da irin kallon da hjy din take ma don haka ya dukar da kanshi kasa kawai don gaba daya wurin sun zuba masu ido.
Sunansa ta kara kira tana fadin Mohammad ya amsa cikin murya kasa kasa yace na,am ukteeh ba tare daya dago sun hada ido da ita ba a lokacin.
Itama din ido ta zuba mashi tace wai me yake damun rayuwankane gaba daya ka canza a cikin kwanakin nan tun bayan dawowana ina kula dakai ko abinci baka sonci sai abu mai dan ruwa.
Duk kabi ka rame kayi duhu sai kai daka tara suma kamar wanda ba shida lafiya nafa gaji da wanan kwanaye kwanayen da kake yi min ?
Shiru yayi na tsayin lokaci yana cigaba da abinda yakeyi a lokacin ganin hakan yasa ummu ta daga murya cikin fada da nuna bacin rai zuwa gareshi tace.
Ko bakaji abinda nake fada bane wai ta sake fada a cikin bacin rai Abbu dake zaune yana cin abincin shi bai tanka masu ba ya dago kai yana kallonsu donshi drama yaga sunayi don yasan ba zai taba fada mata koma wani abune ke damunsa ba.
Yana mamakin hjyn data kasa fahintar waye kanin nata har yanzu don ya kamata ace zuwa yanzu ta fahinci halaiyan dan uwan nata ai.
Shiko Mohammad din ya dago kanshi da yake duke ya dubeta ya sake wani guntun murmushi a fuskanshi yana fadin.
Na fada maki babu komai Ukuteeh ki yarda dani da ina da matsala da tuni na sanar dake ko Abbu ai ba komai normal nake ni ya sake mayar da hankalinsa a wayan shi.
Ganin hakan yasa ummu ta hasala ainun dajin abinda ya fito daga bakin kannin nata tace ban yarda da abin daka fada ba mohammad ta kira sunansa kai tsaye jin hakan yasa ya dan sake kallota don ya fahinci ranta ya gama baci ke nan.
Taci gaba da fadin domin tun bayan dana dawo nake kula da yanayin nan naka idan anyi magana kuma kace ba komai kai kullun dan ba komai ne wai ?
Duk mai hankali ya dubeka a yanzu ya san da komai akwai abin da yake cin zuciyar ka a yanzu din nan kake boye hakan.
Ka sani babu wanda ya kamata ka fadawa damuwarka a yanzu wanda ya wuceni din nan don ko nafi kowa yanzu kusanci da kai.
Saboda haka ni nafi kowa sanin halinka da kyau don ba haka kake ba gabadaya a yanzu ka sauya rayuwan ka ko abinci ace sai mutum yaga dama yakeci ?
Ta karashe zancen da zallah bacin rai a zuciyanta tana kawar da kanta daga kallonshi shiko mijin nata sai murmushi yake famanyi daga inda yake zaune din yana kallon drama.
Da sauri ya dago a cikin marairaicewan murya yace Ummu na fada maki babu komai babu abinda yake damuna illar cikin yan kwanakin nan sam bana jin dadin jikina.
Hjy ta sake duban shi tace wai aikin ke nan kuma in ace kaje asibiti kace ai ba sai kaje ba amma koma meye tunda baka fadawa mutane aikai ka sani ta fada tana mikewa daga wajen nasa.
No Ummu kada kiga laifin uncle fa ta ya zai fada maki cewa yayi missing din abincin Fatima ne a yanzu can da muke Nigeria tana dafa muna ba yana ci sosai ba.
Aikin banza ke nan umma ta fada Abbu ya dago yana aje abinci tare da fadin wai waye Fatiman nan don Aisha ma taban labarin wanan fatiman data iya girki.
Dan murmushi hjy din tayi tace in abincinta yake so ba saiya koma nageria ya zauna ba ko kuma ya daukota ya kawota nan ga baki daya tunda zai iya hakan.
Ya tashi a harzuke yana fadin shut up ya fada yana nuna Al,amin din da hannu wallahi zan sabawa Al,amin rai yanzun nan idan bai fita harkata ba yanzun nan nina fadama donshi nake haka ko munyi dakai nace ma ga dalilina.
Dariyan mumuke kowa na falon keyi sai Abbune ya samu karfin halin fadin yanzu dai tunda na hannun daman ka ya fada muna meke damun ka ai yanzu mun fahinta.
Ke Hajjara zaso mu gaiyaci wanan matar mai abinci idan za ayi taron shekara tazo tayi muna irin girkin nan nata mai dadi muci ina ganin hakan zai yuyu ai sai a gaiyato tadan zo muma nan zamu so mu dadana abincin ta muma muci girkin nata muji.
Anya uwata zata samu zuwa nan kuwa don gaskiya karatu takeyi a yanzu kaga ko za a takura mata ke nan don ba zatace bata zuwa ba koda hakan zai ja mata mata matsala kuwa.
To shike nan Abbu din ya fada yana kokatin mikewa Aliyu yace no ummu don Allah a gwada tambaya aji don zuwantan nan zai kara muna daraja gun mutane sosai saboda ta iya abinci mai dadi gaskiya.
To yanzu dai idan zata zo a tuntubeni na saka maki kudin komai nata saita zo di ai na dan lokacine tunda ba dadewa zatayi a nan din ba ai kuyi yadda duk ya kamata ace anyi din idan da halin hakan.
Wani lokaci samira na zaune zataji muna shan hira da sojana amma bata san ko dawa nake wayan ba wanan yana matukar daure mata kai gashi a yanzu sama sama muke zaune don gaba daya na fita sha,anintani.
Haka kuma muddin zata zauna a daki toni ina waje ina wani aikin cikin gida don itace ta fara nuna min wanan halin a yanzu kuma nace nafita iyawa.
Don haka rananma shigowan ta daki ke nan ta dawo wurin kitso duk da bata fada min kitso zata tafi ba amma sai na gane hakan don haka kafin ta dawo naje wani saloon aka ragada min kitso mai kyau mai daukan hankali.
Kuma cikin ikon Allah na rigata dawowa gidan har nayi sallah azahar da la,asar kafin ta shigo gidan karan takalmanta naji suna gaisawa da gwaggo daidai lokacin ina wayan .
Don tunda naji muryanta ra shigo tana waya na dauki waya na latsa flashing wa soja karo na farko don ya kira nake fadin ina wurun gyaran kai zan kiraka idan nagama.
Shine yanzu din ma nace bari na kira ya dauke min hankali don ban son abinda zai jawo muna cacan baki a lokacin don Samira akwai sakin habaci ga mutum.
Adaidai lokacin data shigo din tana waka mata ku sanya shadda atamfa lace awarwaro, daidai lokacin dadadiyar muryanshi ya ratso dodon kunnena yake fadin
Baby nayi missing muryan kin nan na kwanaki fa nayi murmushi tare da lumshe idanu na dan gyara kwanciya ina jawo filon dake gefe na dora kaina a sama.
Duk wanda ya gani a cikin yanayin kallo daya zai min ya san ina cikin farin ciki da nishadi a lokacin don yanayin da nake da yadda nake murmushin zai nunawa mutum hakan.
Naji yace naji kinyi shiru mana koda akwai matsalane ko kina tare da wani kusa yasa baki son amsa min yadda ya dace.
Jin hakan yasa nayi murmushi mai hade da sauti tare da lumshe idanuna nace bana tare da wata matsala ai muddin ina tare dakai yanzu.
Shima murmushin yayi yana fadin nagode da nuna kauna a gareni shiyasa nake matukar ji dake a rayuwata fiye da komai yanzu.
Fiye da komai fa kace yace kina mamakine na amsa da a,a hhaa meye na mamaki a ciki kuma yanzu yace da kyau.
To ya lafiyan jiki ?
Na amsa da lafiyata kalau sai alheri.
Yace, Da kyau kinsan wani abune ?
Nace A,a saika fada ?
Yace fatima kinsan yadda nake jinki a cikin raina wallahi ko kadan bani fatan koda kuda ya sauka akan fatan nan naki don ina ji a jikina ke wata abace mai matukar muhinmaci a tare dani yanzu anyway kada ma dai in cikaki saidai mun hadu zakiji a bakina.
Dan murmushi mai kayatawar na saki nace to shike nan sir yadda kace zanci gaba da kular maka da kaina ko kuda ba zan yarda ya hau gyalena ba.
A,a lalai sabon shiga wai shege da hauka dan baka sababa anyi new catch ke nan ake wanan zumudin haka can gasu gada inji yan ganye.
An daiji haushi na fada daga bangarena shi kuma a rude naji yace meya faru kuma ?
Nace a hankali da akai me fa kuma ?
Yace wani magana naji kin fada nace ayyah sorry bada kai nakeyi ba wata nake ba amsa a nan ai .
Yace datayi maki me nace cewa tayi wai dan baka sababa ke nan dagani har kai bamu saba ba ke nan take nufi.
Yace munfi gwani kuma iyawa ko fada mata a nan zata sha haushi a kanmu idan tana saka muna ido nace ai tana jinka.
Sister ne ko ki fada mata haduwan mu da ita ta shirya amsan quarry na kan sakawa masoya ido tsuki taja mai karfi.
Yace what fada mata yanzun nan inta kara zata kwana a cell jin hakan yasa samira ta kalloni cikin mamaki ba kuma daman tambayan waye .
Yaci gaba da shakiyancinsa har nakai ga fadin Mohammed baka rabuwa da saka mutum dariya zan ajiye wayan nan kasan yau a saloon na wuni kai kuma kana sa mutum dariya haka ?
Yace korata kikeyi ne ?
Da sauri nace nina isa ka rufa min asiri kawai dai zan fita na nemi abinda zancine a cikina.
Haba dai wa kina nufin dahuwa zakiyi yanzu kome nace haka nake so yace to ki huta ga yarona tafe zai kawo maki take away yanzun nan.
Nace kash saidai kuma anyi rashin sa,a niba maison dahuwan waje bace nafi son na girka da kaina inci hankalina yafi kwanciya da hakan gaskiya.
To indai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login