Showing 123001 words to 126000 words out of 347556 words

Chapter 42 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8764

dan hanyan da zai sada mutum da cikin gidan mu.
Fadimatu ijin ba wani laifi kikai masu a can ba don hankalina ya tashi yadda mutanen nan suka kirani hankali tashe na razana ainun da kiran nan.
Dan dukawa nayi ina fadin baba ba komai bane shine sojan da nake fadama wanda yake zuwa wajena ikon Allah shi din ne ya biyoki nan ke nan baba ya fada cikin tambaya.
Dama garin nan yake shi ga wanan yace a baka a gaida kai wanan kuma yace inbawa su mama su raba da yara ikon Allah wanan kudin me yawa haka to Allah ya sanya alherinsa na amsa da amin .
Yace kai masu tunda suyabawa ai da sauri nace hamsin ne nake gani ga dai ashirin ka kara a cefane ashiri su raba goma abawa yara su raba.
Allah yai maki albarka fadimatu Allah ya baki zuria masu albarka da zasu rama maki Allah ya tsare ya kareki daga sherin shedan nace amin baba nagode.
Na shiga ciki ina kallon lokacin da mama lanto tazo ta gitta mu a wurin tana leken mu nasa kai na shigo na samesu kowa zaune a kofanta suna zaman jiran tsamani jin ko ta kwana a gareni.
Mama uwa na nufa don in mikawa kudin ina mata bayani tace sun tafi ko nace eh dama office zai tafi ya biyo nan mu gaisa .
Kai amma bai iya zuwa hira ba shikan zakazo sai kayo muna gaiyan sojoji a kofan gida kamar hauka ?
Mama lanto ke fadin haka ita ko mama sai cewa tayi idan baiyi hakan ba ai ba asan koshi waye ba kai kuna wani zance dai kan wayaki hakan a kayansa mama uwa ta basu amsa.
To sani in fika agola da rabon gida ai ba bakin ciki mukace munyi ba magana daice mukayi tunda ya tsorata mu haka.
Gashi na mika mata na fara mata bayani tace dan albarka kaji wa yanda suka san darajan hiran rana ke nan wanga kan ai bamu bari ya kurce muna gaskiya.
Murmushi nayi na hussai na fadin jiya koda na dawo kinyi barci ashe zaki shigo gari dama ko munyi zancen shigowanki da friends dina akwai bukin shemau da zamuyi fa.
Nace to gashi ko nima akwai bukin wata kawata da za ayi shiyasa zan kai har sunday don ta hadani da Allah inzo mata amma ba laifi ai zamu leka dai.
Daga haka na juya zuwa daki daga cikin dakin ina jiyo muryan mama tana fadin dari biyar zai rage sai a kacan canashi.
Hassana ta leko tana fadin sister waiko shine wanda muka taba haduwa nace bashi bane wanan ai yace muna likitane shi wanan kuma Mohammed ne sunan sa dan yolane shi amma kowa nasa na garin nan zaune yace.
Ana dai ta magana can na leko nace shine fa ya saya min wanan kwalin naman dana aiko kwanaki shi komai zaiyi haka yake yin bajintansa.
Jamal ne ya shigo yana gaidasu sama sama yace ina mama ga kudin zobonta da nasha na samu naji mama lanto na fadin yau an samu kudi ke nan yaron ya washe baki yace mijin anty Bantu ya bamu har dubu goma.
Kai makaryaci mama ta fada yace wallahi mun kaiwa hjy ta kirga ta nunawa maman su Faisal itama ta kirga akace dubu goma shine hjy ta bamu dari biyu biyu muje school dashi.
Ina anty Bantu din kota tafine ya tambaya tana dakin ta naji an bashi amsa daga cikin gida sai gasu dakin suna sallama suka shigo kwance nake nace jamal nagaka kara min tsawo mana ?
Yayi dariya yana fadin fadin kema ai hjy tace yanzu kin girma kin gujesu rabon da kizo gidansu tun auren anty zainab wai don kawai babanmu yace yana sonki ?
Kai Jamal dama babanku ai yana son mu tun muna fatakwal ko yace ba yace min wai ke zai aura yanzu ba ki zauna makwafin maman mu ba mu kuma can wurin shi fatakwal.
Nace ba gaskiya bane ai dai yau kaga mijina ko ya gyada kai alaman eh nace toshi zan aura sai mu tafi bariki ka zama soja in saka makarantan sojoji kaida Jamila dariyan jin dadi yayi yace .
Ehh har naji dadi wallahi ai su hjy sunce wai baban mu yanzu ba zai aureki ba tunda maman biyu tace Daddy mu anty hassana zai aura shi kuma dasu baba mai mota sunci a,a dadai kece.
Ranan mafa har gidan mu taje akai fada sosai sosai da ita shinema hjy tace kada mu kara zuwa gidan nan yanzuma ba,a san nazo ba Jamila nacan tana son zuwa hjy tasata aiki tana kuka.
Amma fa ni nakanzo dama nakanzo na in sayi zobo wurin maman biyo idan banda kudi ta hana min ko ranan saida Anty hussai tasa ta bani bashi wai idan na sami na kawo mata shine yau dana samu na kawo mata kudinta.
Jamal kada ka kara cin bashin kowa don Allah baka san saboda bashi Allah na saka mutum a wuta ba ya kona shi ka bari kaji kada ka kara zance kullun abaku zobo ni zan dinga biya idan nazo na bari ba zan kara karba yace.
Hjy dama tace maman biyu muguwace ba zata kara hada komai da ita ba tayiwa daddy mun fada sosai tace mashi ya rabuwa mama da yaranta yace shi ba ruwanshi da yaranta dama.
Ranan da yazoma maman biyu tace in kirashi kada in bari hjy ko wani gidan mu yaji dana fada mai yace bai zuwa kuma baizo ba din har ya tafi.
Ga yaro ake jin komai akace gashi ina zaune yanzu jamal yazo har dakina yana fada min abinda ban sani ba wanda suma suke ganin ba wanda zaisan da hakan kenan .
Watau dai mama tayi amfani dashi yaron ya zama mata makami tana turashi a asirce ya jawo mata hankalin babansu yanzu zuwa gareta da yarta ke nan .
Ganin yaron yanata zuba nace kagane Jamal kada ka kara fadin komai nasu kaji ka barsu fadansu tsakaninta da hjy ba ruwan kai yarone a cikinsu kowa nakane don dukkansu kakanin kane kasani ko ?
Ya gyada min kai shigowan mama uwa dauke da kula tana fadin ashe wanan yana nan ban sani ba bari na karo maku doyan ashe zata juya nace a barshi mama wanan din ma zai ishemu ai nidashi.
Tana fita na mika mai dari biyar nace jeka karbo muna cock mai sanyi a wurin isah da ruwa yana fita na mike na dibi ruwa na shiga wanka koda ya dawo ina bayi nan ya zauna har nafito.
Kallonshi nayi nace dauki abinci kaci mana ka dauki cock daya daya kuma sai ka kaiwa Jamila gida itama tasha jiki na rawa ya shiga bude dan kulan doya da miya da kifin icce fish tayi lokacin.
Jiki na rawa yake ci duk ya ban tausayi gara ni lokacin ina kamarshi ina gidan mahaifanshi ina samun abinci sosai ina ci lokacin suko yanzu lamarin sai a hankali don Alh dai yanzu karfinsa ya kare ba kamar da yake ba.
Don ada shine mai kudin unguwar mu gidansune gidan yan birni a cikin unguwa kaf kowa yasan da wanan amma yau jikokinsune suke wahala haka rayuwa ke nan.
Kafin in gama in juyo har yaron ya gama ci abincin yana lashe robo wani haushi da takaicin ya habibi naji a raina bansan lokacin dana furta Allah waddaran naka ya lalace ba waishi ya habibi wani irin makwadaden mutum ne wai ?
Tashi muje ka rakani jamal na fada yace inbar cock din anan ne nace baka sha ba yace idan nasha naje hjy zatayi min fada dauki kasha barin shiga dakin mama in dawo.
Dakin mama uwa naje neman basilin na samesu zaune suna cin abinci da yaranta tace doyan nan akwai kyau wallahi nace dana sani in sayo mai yawa kuyi ta amfani dashi ko kuma ku dauki wanan na gwaggo idan naje tashe sai insaya masu wani a nan idan zan tafi.
Manja daine wanan yana da kyau abar muna shi sai a karo wani a nan ai dana nasan zamu samu kudin nan yau sakwara zan muna a gidan nan kowa yaci.
Ko maman ku yanzu dana leka inkai masu abinci na samu sun baje dakin ana shan gara ansoyo abinda rai yake so ana ci.
Mama niko hakan bai dameni ba haka yake kawo muna abubuwa mai yawa saidai samira dasu gwaggo su dinga amfani dashi a gida ni irin haka bai gabana wallahi.
Mukan nan sai maneje yau kan ai ansamu nayi dakincan kodana shiga din zancen sukeyi ko ina kika hadu dashi haka ana ganina aka bar maganan don sunsan ba kyalesu zanyi ba.
Dagowa nayi ina fadin mama zan dan fita da jamal muje kasuwa daga can kuma zan biya gidan su hjy in gaidasu saboda suna korafin na gujesu yanzu ban shiga wurinsu idan nazo.


ZAINAB IDRIS MAKAWA


KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
3?? 8??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Shiri nayi sosai na fito na rufe kofana muka fita da jamal mama lanto na wajen amma kala bance mata ba don na gama fahintar ta ita da yarta a yanzu dama badon Allah suke zaune dani ba tun farko.
Hassada da bakin ciki yayiwa zuciyarsu yawa sosai har basu iya boyewa a zuciyarsu sai sun fitar fili saboda bakin ciki kuma bani kadai sukewa hakana ba da kowa haka suke sai yanzu na fahincesu sosai.
Isah mai shago yana hangoni ya taso yana fadin yau na shiga rudu a wurin nan lokacin da sojojin nan suka zo sukace ke suke nema.
Haba isa duk da ba a mamaki da kaddara amma ai zakayi mamakin anzo kamani ai nace zamu fita in na dawo zan ganka yace to to to sai kun dawo ke nan ai shiyayiwa mai Napep hannu daya sauke wasu yazo ya dauke mu.
Kasu mukaje nayi wa yaran sayayyan duk abinda yace min yanaso ita macen har kayan kwalliya da man shafi na hado mata muka ciko ledoji sai la,asar muka dawo gida kofan gidansu muka sauka.
Muka shigo da kayan ciki niki niki da hajiya balaraba muka fara cin karo take fadin a,a,a dankari ehwa ya,i yau Bintace gidan namu ashe yau za ayi ruwa kuwa.
Nayi murmushi na karaso ina gaida ita jamal yaje yakai ledan dake hannunsa ya dawo ya karbi biyun dake hannuna ya kai wurin hjysu ya aje ina bada baya hjy balaraba ta bini da kallo tana rike baki don mamaki wai lokaci guda na juye na goge haka.
Hjy na hango zaune saman kujeran dakinta dake facing din kofan shigowa gidan tana tabe baki tare da kallon kayan da yaron ke ta murna a kansu.
Sallama nayi na cire talmana na shiga dakin da dadene kasa zan zube amma yanzu saidana zauna saman kujera nace ina kwana hjy ta karba min kadaran kada ham .
Da lafiya Binta ashe kin shigo gari jiya saiga dan sako yazo muna da tsaraba nace ehh Abuja na fito yin wani course to ai naga alama tunda naga wanan tsaraban nasan sai hanyar Abuja dama.
Dazun kuma saiga danki ya shigo da kudi yace wai mijinki sojane ya basu Allah ya umfana angode murmshi nayi kafin nace ina jamila hjy tace yanzun nan ta fita zuwa islamiya shima an nemasa an rasa ashe yana tare dake.
Nace can yaje sai na daukeshi mukaje kasuwa yanzun muka dawo gashi nan ai yana rawan jiki maza ka shirya kaje islamiya ta fada a tsawace.
Sai naga yaron ya dago yana wani iri nace kaje har ka dawo ina nan ba inda zani ai sai dare zan koma gida daidai lokacin hjy balaraba ta iso wajen take fadin wata sabon gani hjy yau kinga yar gidan ki ta gama guje gujenta ta shigo ko ?
Naganta ai ko yanzu ai sarkin nacin nan yayo muna bikonta nasan nace a,a dama wanan zuwan ina son shigowa in gaidaku yanzu bana zama nan ne hjy shiyasa.
Ai munji ance kin koma zaria da zama baki daya sai lokaci lokaci kike dan shigowa dada dai kinki dana ko Binta wani kallo nayiwa hjy larba din sai kuma nace kai hjy .
Hjy ina abincina Jamal ya fada watau ba zakaje karatun nan a cikin lokaci ba ko nace yunwa yakeji hjy kasuwa muka fito dashi gashi can ka dauka kasan table ta fada ya jawo kwanon doyan dana aiko masune suka dafa da manjan da aka soya sai gishiri da aka zuba.
Shi yaron ya dadatsa ya fita muka dan yi hira dasu kafin in mike na dauki tsintsiya na fara share dakin tana wai in bari nace bari na gyara dai haka na gyaro daki tas na daga har kujerun na gyaro ko ina saiga dakin ya fito fes dashi.
Kame kamen abinda zasu dafa akeyi wurin isah na fita na amso cus cus da kayan markade na shigo dashi nacewa hjy laraba hjy a dafa muna cuscuses din nan yau na tuna da irin dafuwanki ta amsa cikin jin dadi ta nufi dakin hjy famfo na tsaya na wanke kayan dake wajen tas na kife lokacin aka fara kiran magariba nayi alwala na koma dakin hjy na tada sallah.
Muna idarwa yaran na shigowa jamila a guje tana leke kona tafi naji hjy na fadin gata can bata tafi ba tana sallah shiko Jamal yana shigowa dan kale kale ya farayi kafin yace wai hjy dakin nan yau yayi kyau sosai tace aikin uwarkace wazai tsaya ya gyarashi haka yanzu idan ba ita Binta din ba ?
Hjy balaraba ta shigo dauke da kula biyu a hannunta na tashi da saur????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
i na kama mata nakai inda take aje abinci a dakin kinji Alh yanzun daya shigo wai ya gane anyi gyaran wurin famfon nan yau ?
Nace masa ai yarsa ce yau ta shigo ita tayi wanan aikin haka yake mamaki nace bari naci abinci naje na gaidashi nan muka zauna da yaran baci abinci a gidan muna dan taba hiran rayuwa da hjyn akan karatuna a yanzu.
Take fadin na daure idan na samu nagama watarana sai labari halin matan gidan mu kuma aina saba dashi tun ina karama kada yanzu ya dameni naje mun gaisa da Alh yake min fadan rashin shigowan da banyi idan nazo garin.
Inda yake fadin ko akan zancen Mahmoud ne nadaina shigowa nace ba haka bane kawai dai bani shigowa kaduna sosai yanzu nafi zama a zaria koda munyi hutu.
Karfe goma nabar gidan na dawo gida nan na samu Samira tazo a wurin mama uwa nake jin zancen zuwanta din duk da ita taji muryana bata fito ba don na leka dakinsu ina gaida mama lanto kafin in shigo nan dakin mama uwa.
Maman uwan ke fadin nasan tazone don uwarta ta fada maki dawowanki da kuma zuwan sojan nan yau nasan don shi tazo taga gulma.
Zata iya don ban yarda ta ganshi ba har yau din nan tayi kwakwan ta sanshi Allah bai nufi susan juna ba dashi nima dama ban son ta san komai a kansa din.
Dakina na nufa na ina tube kaya Nepar suna hasko wuta na dan gyara na fito nayi alwala nakoma na rufe kofan nakwata ke nan wayata na tsuwa na daga soja ne yake kirana.
Yana fada min ba zai samu fitowa ba don matarshi ta dawo naji gabana yabada dam na dake na dauka wasa yake min nace ina mata sannu da zuwa naji muryanta tana fadin honey a ina ka ajemin ,,,
Ban tsaya naji ba na kashe wayan haka na kwana da tunane kala kala a zuciyana don shakuwar mu da zaman mu sam ban taba kawo cewa yana da mata ba ashe.
Washegarma naso saka abin a raina don haka na tashi zukuku ina tunane akai karshe dai na dake na share zancen a zuciyana naci gaba da har kokina.
Sai zuwa shadaya na fito daga dakin ina gaida mutane nan naga ashe yar mama din nan dama taso tafi mama samin kafa tazo gidan namu ashe tana ciki lokacin tare da mama da su yan biyu adakin.
Bayan na gaidasu na juya naji tana fadin ke suwaiba dama haka yar takoma ashe lalai na kwana biyu ban gane taba ban fada maki idan bakuyi da gaske ba zata zama maku karan dafi a cikin gidan nan ba.
Yanzu ga zancena nan ya fito wa zaiga yarinyar nan haka yace itace a yanzu zon Allah kinga ya yardata bunkashe lokaci guda haka lalai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login