Showing 105001 words to 108000 words out of 347556 words

Chapter 36 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8773

alakan saita zumuci da mutunta juna a tsakanin mu don har gobe kai yayanane kuma marikina a zuciyana.
Ina fadan haka na doshi cikin gida gadan gadan jikinshi ya dauki karkrawa lokaci guda yana fadin na gane me hakan ke nufi a yanzu.
Amma zuciyata da ruhina akanki ke fatima ya tsaya ba a kan wata ba a gidan nan jin abinda ya fada yasa na juyo na tsaya na tsura masa manyan idanuna akanshi wanda sukai matukar firgitashi a lokacin nace.
Wanan kuma ruwanka yanzu don duk yadda ake bawa mutum girmansa da mutumtawa nayi maka sauran abinda ya biyo baya a yanzu kai kaika ja kuma idan baka daina wanan maganan ba tsakanin mu na juya nasa kai cikin gida.
Naji muryanshi muryanshi yana fada tankar zai shekeni ko ya rungumoni a lokacin cikin daga murya yace ban amince da abinda kika fada ba, kinji na fada maki nike nagani kuma nake so a gidan nan kamar zai biyoni zuwa cikin gidan a lokacin.
Tsaye na samu kowa cirko cirko a tsakar dan gidan namu suna sauraren abinda ya habibi yake fada kallon samira da muke takon saka da ita tun jiyan nayi daga ita sai shimi a jikinta kai babu dan kwali a lokacin.
Dakina nasa key na bude na shiga ba tare da nayiwa kowa magana ba na turo kofan da karfi ya rufe yana bada kara a daidai lokacin kuma naji tayar da motarshi kofan gidan namu.
Tau dada gaskiya tayi halinta yanzu kan kowa yaji gaskiya ke nan mama uwa ke fadan hakan tana tafiya wanda kowa yasan abinda take nufi.
Koda baba ya dawo ranan na daiji ya kira matanshi saidai ban san kan me ya kirasu ba don ba wanda yace dani komai akan zancen.
Tun daga ranan kuma ban wuni a gidanmu da gari ya waye inayi wanka ina shirya ina gidan hjyn saudiya bazan dawo gida ba sai wajejen magariba zan shigo gidan na dan kaiwa mama uwa dan abindana riko masu su raba duka gida.
Haka kuma wata rana inje da kannena wata rana kuma ina can zasu sameni don dai a tabbatar da inda nake ne nasan sukan samemi a can din.
Ba karamin alheri rashin girman kaina yaja min a wurin wanan matar ba don iya samu na samu kuma na karu da zama da ita sosai.
Don alheri kan mun sameshi a wurinta ga kuma idona ya kara budewa sosai har yan gidan namu sun lakaci wan arziki tun dai ma mama uwa da take dauka a matsayin uwa a gareni a gidan namu dkn komai na samo zance mamata.
Sati biyun ma bai cika ba saura kwana uku tashin su yazo muka rakata har kano inda zataje ta shiga jirgi nida wasu yan uwanta,
Haka na nade kayana bayan tafiyanta da kwana biyu na juya zuwa zaria don na karasa hutuna a gidan gwaggo don hakan yafi min sauki saboda yanzu gidan namu ya fita raina ga baki daya.


ZAINAB IDRIS MAKAWA





KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
3?? 2??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NA???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?KU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Na dawo zaria cike da kadaici amma haka na daure nake zaune a gidan gwaggona nake rayuwa da dadi ba dadi bani da zabi hakan yafi min dauki bisa ga zaman hattaran da ake min a gidan ubana.
Gashi yanzu kullun cikin damuwa da kadaicin rashin mahaifiyata nake tundai idan ina daki ni kadai tunane barkatai nakeyi game da ita wani lokacin insha kuka wani zubin kuma naga laifinta fiye da wa yanda akace sun mata sheri sun koreta.
Misalin karfe goma sha biyun rana ina kwance a daki ni kadai gwaggoma tana nata dakin tana sauraren redio wani yaro ya rangada sallama har sau biyu.
Lokaci daya muka amsa masa da gwaggo din kafin in fito ta fito yake fadin ance nazo na sallamo Fatiman gidan nan idan bata nan wai Samira tazo.
Fatiman dai ke nan Samira tana kaduna gwaggo ke fadawa yaron jeka kace tana tafe lokacin na fito daki da mamaki nace wai ani akewa sallama yace gwaggo ?
Eh haka ya fada nace yace gaki tafe yaron ya dawo yace wai ance to fatima din tazo don Allah Mohammed ne yaron mai rararan murya dashi sunan na maimaita ina fadin waye hakana kuma.
Jeki mana ki gani idan kaji ance anawa mutum sallah aida dalili gashi kuma har ya fadi sunan sa in kin fita ki shedashi ai.
Dole na koma daki na saka wani dogon rigan assh color tare da gyalen shi na dan fesa turare na dauki wayata na rike na fito wata farar mota kal kiran land grosser mai manyan tayu da dan tsayi na ban sha,awa.
Ba karya motar ta hadu sosai a lokacin dana hangota sai nayi saurin kawar da kai gefe daya don bansan wanda ke ciki ba kada yaga zakewana ina dan ya hangoni.
A hankali nake takowa saika dauka akan kwai nake tafiyan ina gudun in taka da karfi ya fashe a zahiri kuma hakan tafiyan nawa yake ba kari don mutane da yawa na min magana kan hakan sai daga baya su gane yanayin tafiyan nawa ke nan dai dama.
Yana zaune a bayan motan daga can yake hango yadda nake tafiya ina dan waige waigen neman wanda ke min sallama din a lokacin a haka ya kare min kallo tsab don ranan farko bai samu hakan ba a wurin.
Bude bayan motan yayi fuskanshi dauke da murmushi yana saye da kananun kaya a jikinshi sai banin ranan dayasa dinkin maza na yadi a jikinshi.
Kansa saye da facing cap tsintsiyar hannunsa na hago yana daure da agogon Gucci ta maza fatar agogon kalar rigar jikin sai takalman sawunsa ma kalar rigar daya saka ajikinshi.
Dirowa ya karasayi ya fitowa daga cikin motan yasa hannu ya cire hular dake kan nasa ya shafo sumar knsa mai laushi yana murmushi yace.
Da fatan baki fushi ba kuma kin shedani zaki tuna da haduwan bayan dan lokacin dana dauka bamu sake haduwa ba sai yau Allah ya ban ikon zuwa gareki.
Shiru na danyi tare da saurin dago kai ina kallonsa ina son tuno inda nasanshi a baya hakan daya gani nanuna yasa yayi saurin dan takowa izuwa inda nake tsaye.
Ya tsaya da kyau tare da tura hannayenshi cikin aljihunsa yana murmushi yace mai turarenkine na ranan wanda baki aikaba na zabo maki ko Allah zaisa ki tuna da muka hadu shago.
Yadda yake magana kamar mai rada yasa bansan lokacin dana murmusa ba ina dan kawar da kai gefe daya yace good kin tuno dani ke nan baby ?
Ban tuno ba na fada ina dan tsuke fuska sai naji yace ohh No please ki tuna da dan bawan Allah nan mana da fatan dai fushin naki ba mai tsawo bane ?
Don naga kamar har yanzu fushin turaren kikeyi tunda bai maki ba yasa banji kanshi ko yanzu a jikinki ba kada ki damu fada min duk wanda kikeso zan nemo maki shi a yau din nan duk inda yake.
Haba malam nifa ban shedaka ba har yanzu kana min zancen daban sani ba murmushi yayi yace au aina manta kedin tagwayece .
Amma dai ni tawa Fatimance nan nake tsaye da ita please baby kada kiyi fushi haka don muddin kikai fushi dani hakan na iya jefa zuciyata cikin kunci a yanzu hannunsa akan saman chest dinshi.
A hankali na lumshe ido yace koke fa baby nasan ba zakiso hakan ba ai ko yana kallona tare da son jin abinda zan fada a lokacin.
Wai dama ana samun soja mai raha haka yace kwarai kuwa bagashi kon gani ba a gaban ki kuma saidai kuma a gaban mata kawai muke hakan yanzu da nabar nan zan juye na koma sojana sak.
Na danyi dariya naji yace nagode tunda an hakkura har naga fararen hakoran da suke boye kai na girgiza nayi tsaye na kura mashi ido yace baki yarda ni din bane ko ?
A,a nace ina girgiza kaina nace sannu da hanya da alaman yaji dadin hakan yace yawa baby ya bayan rabo nace sai alheri.
Kinji ni shiru ban sake neman ki ba ko wallahi tafiya mukayi zuwa waje yin wani mission shine muka dauki lokaci a can ya wanan yar uwar taki kuma ?
Samira tana kaduna taje hutu nima ban jima da dawowa daga can ba au dama ashe ku ba yan garin nan bane ko ?
Kaina girgiza nace a,a karatu ya kawo mu muke aune da gwaggon mu a nan ok wanan gidan ke nan nace eh an dawo lafiya?
Yace ga zahiri kin gani kuwa har nazo wurin ki in ji sanyi a zuciyata nashiga ukku na fada a hankali sai naji yace .
Ina ina tare dake beauty ba zaki taba shiga ukku ba ai nifa din nan ko a cikin jarumai daban nake baki sanin hakan sai kin gani a fake fama ina fatataka arna dole ki tafa min.
Kallonshi da kyau nayi na gyara tsayi ina murmushi tare da fadin kai din dan akwaika da abin dariya ko mutum bai tashi ba sai ka sakashi yayi hakan.
Masha Allah dama shine burina naga na sakaki dariya da jin dadi yadda zan tafi ina tunanen hakan nima a zuciyana.
Can ya nisa yace yaushe zaku koma school ke nan koda yake hakan ba matsala bane tunda a gida kike zaune yau nazo na duba idan gaskiyane nan ne gidan ku dama.
Don kinsan yan matan yanzu da iya yaudara har mazan na yanzu ai mayaudara sunfi yawa na bashi amsa yace harni ke nan ko nace to abu a duhu wazai gane hakan ?
Murmushi yayi ya rausaya kansa kwarjininsa da kyawonsa ya fito fili yana min wani tsadaden kallo irin na mazan da suke cikin shauki yace naji tsoron wanan kalamin naki beauty .
Duk da yanzu ban da lokaci ya dubi agogon hannusa yace zamu sake haduwa wata rana saidai kafin nan ina son inba damuwa ki ban layin wayanki don na dinga kira ina jin lafiyan ki.
Saboda ni signal army ne ba ko yaushe zaki rika ganina nan ba, don aikin mu busy ne ko yaushe ina cikin aiki don haka sai a waya zamu dan dinga gaisawa dake koshi ba kullun ba.
Na bude idona da suke lumshe na dubeshi mukayiwa juna kallon ido da ido da hanzari na jaye nawa ina fadin aiko hakanmana gode .
Masha Allah na dauka ai dana fadi hakan zaki fushi sai kuma naji sabanin hakan gareki lalai tafiya dake baby zai min dadi tunda kinada saukin kai haka da sauri.
Haka dai mukaita ba,a har yai min sallama akan zai tafi ban bari ya shiga mota ba na juya zan shiga gida yace dan turo min yaro ya shiga maki da tsaraban Paris gida mana.
Jin hakan yasa na jiyo ina fadin haba dai kada ka damu koba tsaraba hakan ma nagode ai kuma ai nikadaice yarinya a gidan nan yanzu.
Murmushi yayi daga inda yake zaune a cikin mota kafan shi daya yana waje yake fadin kai ba zan ba gibiyata daukan komai ba aike kamar sauraniya kike yanzu.
Dariya na danyi don barkwancinsa yayi yawa yana matar da mutum damuwarsa in kana tare dashi na juya na daga mai hannu na shige cikin gida kai tsaye.
Ban samu gwaggo waje ba tana daki nima dakinmu na nufa na shiga ina kwabe kaya naji yaro yana sallama na leko ta labule na amsa mashi naji yana fadin wai Mohammed yace a shigowa fatima da wanan.
Bin kayan hannun yaron nayi da kallo nace kawo nan yana ajewa ya sake fita ya kara shigowa da wasu kayan yaron yace yace in fada maki ya tafi sai kunyi waya.
Yaron ya juya zai tafi nace tsaya don Allah na zaro dari biyu zan bashi yace ai ya bani dubu daya gashi nace to karbi wanan din tunda nayi niyar baka.
Nagode Allah ya saka maki da alheri yasa akai cikin mizani gwaggo dake fitowa daga dakinta ta amsa da amin da albarka har ya juya zai fita sai kuma yaja ya tsaya yana fadin.
Don Allah kuna daukana aiki na dinga zuwa ina maki aiki da aike ni almajirine har na juya zan shiga dakin na dakata ina kallon yaron cikin tausayi.
Da ganinsa sabom kawowane don yana da sauran tsabtanshi har lokacin sai naji gwaggo tace kai yaro yi gaba mena tsaye yaci balle yaba na zaune ?
Gwaggo don Allah inba laifi a barmin shi zan dinga bashi dan abu sai yazo ya dinga muna shara da diban ruwa da dan aike ai basai kin basa ba yaci abinda mukaci tunda kin yaba a daukeshi.
Yaran ne yanzu basu da tabbas wasun su sun bata yan uwa ka dauki yaro yazo daga baya ya cuta maka nan yaron yace insha Allahu ba za a samu hakan a gareni ba gwaggo yadda yaji na kirata dashi.
Yana tsugune har lokacin tace ai saika fara da debo ruwa mu gani na kasa danne mamakina nace yaci abincine gwaggo ?
Ina nasani fatima ya debo kafin a gama ya kara cika randunan ruwan can bari na bashi ko bread ne yaci na fada na juya zuwa dakina rabin bread din dana tean safe na dauko na bashi ya karba yana godiya.
Ya mike yana fadin ina roba ko bucket da zai debo ruwan gwaggo tace bari na baka dan markade mai hadi kaci dashi inka gama ga robanan ka dauka kaje can kasa Bohol na nan ka dibo muna can.
Ta juya zuwa daki ta dauko dan markade a wani tsohon roba ta mika mashi ya kara godiya ya juy har ya fara tafiya ya dawo yana fadin gwaggo ga kudin nan ki ajemin kada inje dashi makaranta a sace ko yan gulma su fadawa malam ina da kudi.
A,a to da alama kana da gaskiya tunda har kabada kudin nan ajiya da har inajiwa bahona don dayawa haka kukeyi da an baku kubarwa mutum kayansa a can sai in rabone mutum yabi yaga abinsa.
Yaron dai yayi murmushi ya tafita lokacin na koma daki kayan nagani na sauke ajiyan zuciya zama nayi na duba kayane masu kyau da tsada dagani naira tasha kashi wurin.
Dogayen riguna masu kyau da tsada don laushinsu kawai zai nunama hakan sai kananan kaya suma kala uku sai kayan makeup na mata dayan ledan kuma kayan makulashene irin na turawa dayan ledan na jawo set din dan kunne da sarka sai bag guda biyu masu kyau gaske.
Ido na tsurawa kayan ina mamaki wai haka maza suke da kyautan bajinta ko dai nice mai sa,an mazan dai haka masu sakin hannu ?
Shiru nayi ina cigaba da tunane sai zuwa can na nisa na mike na fara kawar da kayan na adanasu nasan akwai kyashi da hassada idan samira ta dawo don haka na yanke cewa ba zan nuna mata bama saidai tagani dasu.
Gashi donta na tsaya har naba da kai bori ya hau na tsaya na saurareshi don maman saudiya data lurar dani kuskuren danake tabakawa iyaka dai in kula da mutuncina don wasu bada alheri suke zuwama ba.
Wanan yasa yau din har na tsaya da soja mai ban dariya muka danyi hira wanda barkwancinsa yayi ya tafi don ba zance ga halinsa na gaskiya ba yanzu.
Nagama na tsinkayi muryan yaron nan yana fadi hakan yasa namike na fito don lokacin dora girkin mu ma yayi a lokacin don tunda na dawo nikeyin komai a gidan yanzu.
Nafito ina fadin ka aje roba kaje ka dawo lokacin angama sai a zubama yace idan ban koma da roba makaranta ba manyan dukana zasuyi.
To kaje idan an tashi saika dawo na fada har lokacin gwaggo tana daki yayi muna sai anjima ya tafi tun ranan kuma nake kula da lamarin yaron.
Bayan na gama abinci na kwashene na gama komai na debi ruwa naje nayi wanka na shirya a cikin wani wando da riga wanda a gida kawai nake amfani dashi ganin gwaggo na waje yasa na fito na debo mata drinks na kawo mata ina fadin.
Gwaggo gashi wanda yazo dazunne ya kawo min su na duka ina ajewa gabanta tabi kayan da kallo tana fadin ikon Allah su kuma samarin yanzu kayan zakine toshin nasu haka.
Nan nake bata labarin shi har sherin da samira tayi min akanshi da abinda ya faru tsakanin mu da mama zuwana gida.
Gwaggo tace amma anyi matar kawai wurin nan wai ita


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login