Showing 234001 words to 237000 words out of 347556 words

Chapter 79 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8796

kika daina cin abincin ?
Na koshine Ammi sallah nake sonyi akwai salloli a kaina ta kalli yarinyar tana fadin Fadila kaita wajen ku tayi sallah kafin ta huta inji daga ina take don na kasa tuno fuskanta gaskiya.
Na daga tabini da kallo har lokacin kokarin tuno inda na fito takeyi don ita dai bata san kowa ba a kaduna danace na fito don hakane take mamaki.
Wani daki aka kaini nan cikin part dinta daganin dakin na yan matan ne ya nuna min ban daki nashiga nayi alwala na fito na tayar da sallah nagaji sosai ina idarwa a wajen na dan kwanta sai barci ya daukeni.
Ashe ta leko suka samu nayi barci a kasan kayana tasa aka shigo min dashi dakin can naji muryan budurwan tana tayar dani in hau katifa.
Nace ta bari nan yayi min a nan na kwana hakan ya kara min tsamin jiki gana gajiyan hanya gana kwana a kasa danayi tunda ban saba kwana kasa haka ba.
Washegari na rigasu tashi daga barcin natashi nashiga nayi alwala motsina ya tayar dasu suma suka tashi sukai sallah tun wanan tashi basu kwanta ba nima haka don na tsaya na gyara dakin bandai fita waje ba ina gamawa na watsa ruwa a jikina don ina jina wata iri ko kafin su shigo har nayi wanka na saka kaya ga daki a gyare sai kamshin manshafina da tureren dana murzawa jikina yakeyi.
A cikin hausan nan nasu mai suna Fadilan tafi sakin fuska ta kalleni tace dani har kinyi wanka ashe ga gyaran daki kuma keda kika kwaso gajiya haka aida kin bari mun gyara.
Ba komai na fada tace Ummi na falo kije ku gaisa da ita yanzun take tambayana ko kin tashi jin hakan yasa na fita zuwa falo din da sai lokacin nafarayiwa gidan kallon tsaf.
Nayi sallama nashigo falon tana zaune a kasa saman carpet din sallah ta juyo tana amsa min sallamata na karaso har kasa na durkusa ina gaida ita da kwana.
Tayi min ya gajiyan hanya jiya gajiya ya hana mu gaisa kodana shiga kina kwance kina barci nace wallahi tun safe na bar gida ina hanya na gaji sosai ki zauna ga abin karyawa nan kafin naji daga ina kike don gaskiya ban shedaki ba har yanzu.
Na dan dago kai na kalketa nayi murmushi kafin cikin rawan murya nace ba zaki shedani ba Ammi tunda baki taba ganina ba ni yarkice yar wajen yar uwarki Nuratu bin Dauda,,,,,
Kafin na rufe baki sai salatin ta naji wanda hakan ya jawo hankalin mutanen dakin dama na waje dake aiyukansu a sakar gidan suka fito zuwa falon nata.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
7?? 4??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN
JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Hannayenfadinta ta bude alaman inzo gareta da sauri na fada jikinta sai kuka ni kuka ita kuka tana ki gafarce mu ashe kina raye baki mutu ba wallahi yadda Nuratu ta barki a kaduna mun dauka baki rayene a yanzu.
Ohh innalillahi wa,inna alaihin raju,un ta dago ta dubi fuskana dake cike da hawaye a lokacin sai kuma ta kara rungumeni cikin jikinta itama tana kukan, yare naji an mata take bayani yaren dai kamar larabci kamar kuma wani yare can ni sai wallahi nake ganewa kawai a zancen nata ashe da yan matan nan su Fadila suke yaren .
Yadda take nunawa suma basu san ina raye ba wani dogon dattijune ya shigo dakin yana rike da sanda dogo dashi har ya dan duka duk daya tsufa yake tambayan abindake faruwa a dakin.
Nan ta dago tace Alh yatace daga kaduna tazo neman mu amma ban shedata ba sam ban gane cewa diyata bace yace yarki yar waye yana min kallon kwan don ya gane fuskana dana dago fuskan ina kallonshi.
Tace ga kama nan a zahiri kagani yar Nuratuce fa yar data haifa a kaduna a lokacin datayi aure a can ashe tana raye sai tsohon yace ikon Allah lalai ga kama nan sosai kuwa.
Ashe dama yar tana raye kuma a cikin kasan nan ashe ba wanda yasani sai naga ta fashe da kuka mai tsuma zuciya.
Tana mai bayani tace lokacin da Nuratu tazo nan ta fada min cewa fisgan dasu akaiwa yarinyar yasa ta fado daga bayanta tana ganin ta mutu don ko kukanta bataji ba bata kuma tsaya ta bincika ba a lokacin ta dai barsu suna salatin cewa ta mutu a lokacin.
Yan gidan suna tsaye cirko cirko suna sauraren mu yace Allah bai kasheta ba aiba mahalukin daya isa ya kasheta sai Allah yanzu ba kuka abinyi ba kuyi hakkuri ba kuka ya kamaci kuyi ba a yanzu ai.
Sai ku godewa Allah daya hadaku a yanzu harta gano inda kuke tun kuna a raye har kuka sheda hakan da numfashin ku sai ku godewa ubangiji Allah amma ke kuka ita kuka kin manta da hawan jininki ne da kike fama dashi ajikinki halan ?
Dole in kuka Alh yarinyar nan Allah kadai yasan a halin data rayu a gidansu itama Nuratun kanta idan ta tuna tana hawaye balle ita datayu rayuwa a cikin gidan nasu tare da wanan muguwar macen Suwaiba.
Kaina girgiza nace Alhamdullahi Ammi babana yana sona ya tsaya min ga komai a duniyan nan baya bari su cuta min ko a bayansane .
Ya dubeta yace to kinji dama haka abin yake ku kuna tunanen wani abu daban shifa shike da yarsa yafiku sanin dadinta don yarsace.
Kaita dago tana fadin maryamu zoki bugawa su Mahmud waya kada su fita wurin aiki basu san da zuwanta ba suzo ga yar uwarsu tazo daga kaduna da cewa yayanta na cikinta data haifa saip naji maryamu tace to ummi.
Nan yan gidan suke gaidani wata mace dattijuwa a cikinsu take fadin halan har aure kinyi ko tunda naganki nan ke kadai ta fada tana kallona na dan girgiza kai ina mikewa tsaye daga inda nake don in danje in wanke fuskana son idan nayi kuka nauyin hawaye yakan damu idanuna idan ban wanke da ruwa ba.
No banyi aure ba tukun nagama karatune a yanzu na fada a sanyaye ina shigewa ciki nabar hajja din tana masu bayani a kaina ga wa yanda basu sanni ba a gidan.
Ina bayin ne na fara fargan rashin jin komai game da mahaifiyata da banji sun ambata ba har lokacin gana yayi wani mumunan faduwa don na nasa a raina kobata rayene dai ?
Addah wai kifito gasu yaya sunzo ku gaisa wanan fadilan ta fada daga kofan bandakin na amsa da toh ina goge fuskana da habar hijabin dana saka a jikina saida na tsaya na dan gyara na fito falon suna zaune saman kujeran hankalinsu na gun mahaifiyar tasu dake magana.
Kallo daya zakai masu ka gane bambancin da suke dashi da sauran mutanen garin don suna da wani baiwa ko nasaba na kwarjini a idanuwansu daka kallesu wanda wanan baiwan shine a jikina da nake saurin shiga ran mutane wanda ba a ganeba.
Sallama nayi cikin yar siririyar murya suka juyo zuwa gareni da kallo naji wani nauyi da kunya ganin yadda suka kafamin idanu suna bina da kallo.
Cikin yar murya nake gaidasu suka amsa da anzo lafiya ya mutanen gida kallon mamaki nake masu don da ganinsu ba sai an tambaya ba don suna da zubi da larabawa sosai.
Don dan sajen dake kewaye a fuskansu yasa sun kara fitowa da larabawan asali meye sunan ta sai Ammi din tace ni zumudi ai bai barni na tambayi sunanta bama.
Fatima nake tace hakkun fatima kuwa haka sunan ta yake waya fada maki Ummi na nan dayansu mai dan hasken fata sosai a cikinsu ya tambayeni .
Nace last week na dawo daga service na shiga makwabtan mu nagaidasu sai ya katseni yace har kinyi karatu haka kike nufi na gyada masu kai dayan yace a ina kikai karatun ?
A B U zaria lalai yar taki babbace Ummi har tayi karatu a wanan makarantar tayi bautan kasa na zata zasu tambayeni mena karanta a lokacin sai naji Ammi din tace waya fada maki ina nan .
Wata kawar mamace tayi min kwatance ta fada min cewa tana da yan uwa garin nan inzo na duba ko Allah zaisa in dace idan tana nan shine na taso nazo jiya din.
Kina da aurene dayan ya tambaya nace banyi aure ba tukun har yanzu sai naga ya mike yana fadin zan tafi sai na dawo anjima zan shigo amma ai ba a nan zata zauna ba zan tafi da ita gidana zatafi sake jiki a can wuein Bas,ma .
Ina jin hakan da sauri nace No a barni nan kusa da Ammi zanfi jin dadi na fada kai tsaye don ban yarda in bi kowa gidansa ba don bansan halinsu ba balle na matansu din.
Da kyau yar albarka ku barmin ita nan kusa dani ban gama ganin abata ba zakace zaka dauke min ita tun yanzu Ummi ai muma muna son muga yar uwar tamune shiyasa tace ban yarda ba kubarta a nan duk maison ganinta yazo nan .
Nina tafi ya fada tace dakata yaja ya tsaya tace wanan shine mansur wanan mustapha wanan kuma na tsayen Mahmud yake sai karaminsu yana yobe yana karatu a yanzu sunansa Mohammad shi su hudu Allah ya ban a gidan nan su kuma ke nan nake dasu a duniya.
Banda diya mace yanzu kece kanwan su ke nan kece cikon ta biyar dinsu sai na danyi dariya har dan sign din dake lutsawa a kumatuna idan nayi dariya suka fito fili.
Lalai wanan jinin kuce Ummi dariyanta irin naku sak wallahi har dimple din nan irina su Sagir tana dashi suka mike lokaci guda tana masu adawo lafiya tare da addua.
Bayan na karya har lokacin mutane na shigowa gaidani har daga makwabtansu da wasu yan cikin gidan gaskiya suna da mutunci da karamci sosai yan garin nan.
Wajajen shadayan rana na shige na kwanta don barcin da nake ji a lokacin sosai a idona ina kwanciya sai barci mai nauyi yayi gaba dani harda dan mafalkina wai ance ga mahaifiyana tazo ina barcin natashi na yanka da gudu da hakan na farka wani irin zafi sosai naji lokaci guda ashe Nape sun dauke wutan dake dan kada famka a lokacin .
Ina son in duba time lokacin na tuna da wayata da tun zuwana ban duba ba sai lokacin na tuno da ita namika hannuna na jawo jakata da fadila ta dora min a gefen kaina.
Lokacin na tuna ashe a kashe take na kunna ta kawo na duba time din ashe har biyu ta gwauta a lokacin da sauri na mike zuwa bandakin su haka nake kewaya don Allah yayini da jin kazanta a rayuwata nasani wanan halittace hakan jin saurin kazantan abu.
Ina fitowa na samu wayata tana ringing alaman wani na kirana lokacin na dauka Hassanace ina dauka take fadin wai har kinsa hankalinmu ya tashi wallahi tun jiya fa muke kiranki wayan yana kashe.
Wallahi na mantane ashe tana kashe ban kunna ba yau tace kin isa lafiya nace Alhamdullahi sai gajiya akwai nisa sosai da kaduna muka dan taba hira kafin ta kashe na aje na tayar da sallah.
Waya take ta dealing a lokacin yaki shiga saida kyar ta samu ya shiga ta fara fadin waini kina ina haka ina ta kiran wayan ki baki dauka ba saidana tsamaci hakan kedai bari.
Muna nan Dubai dankine ko kanin ki ya bamu aiki dana wani dan nawa ciki tace bashir mana bashir dai naku daya taba zama a gidan ku.
Wai Bashir din yaya dan galadima ko wani bashir tace shifa kinsa wai aure zaiyi shine ya turo min mahaukatan kudi bari saidai matsalan a account din Oga ya turo kudin kuma tare mukazo sayayyan dashi a nan Dubai.
Aure fa aure kikace tace wallahi muma kwatsam ya kiramu wai yana son a hada masa lefe zai turo da kudi kuma baya son lefen ya wuce nan da sati ukku ai kinga ya bamu aiki babba.
To shine muka taso tun shekaran jiya zuwa Dubai din gashi har mun fara sayayya a yanzu zuba takeyi amma bataji an bata amsa ba yasa ta dan cire wayan a kunnenta tana fadin sherin network ko sai kuma taga tana saman layin amma batayi magana ba a lokacin.
Don haka ta kashe wayan taci gaba da abinda takeyi Al,amin dake gefenta ya dago yana fadin Ummu wani abu ya farune sai lokacin ta dawo firgigit a cikin hankalinta.
Meya farune Ummu ya maimaita tambayanshi gareta a cikin kidimewa da aon jin abindake faruwa don ganin yadda tayi din nisawa ta danyi kafin tace dashi wai Bashir ne zaiyi aure.
Bashir wani bashir ke nan ya sake tambayan ta bashir dai bashow na gidan yaya dan galadima wanan ne abin mamaki ya fada yana mayar da kansa kan abinda yakeyi din.
Ita kan zama bai ganta ba lokacin don zama a falon tayi waya baiyi don Al,amim dake wajen zaune don haka ta mike zuwa ciki shi baiko san ta daga daga falon bama lokacin.
Tana shiga dakin ta kira hjy Tantano aminiyarta ta fara fadin kai mutum wai kinji hjy Kaltume suna Dubai sunje yiwa Bashir sayayyan aure ita da Isma,il.
Wani Bashir wai tace Bashir dai da kika sani na gidan dan galadima wai Kaltumece me zuwa yi masa sayayya a yanzu kuma don yana ganin shi yakai a yanzu.
Yakai man idan baikai ba hjy Kaltume zata bar London zuwa Dubai yiwa wani Bashir can sayayya yakai kan tunda sunje har Isma,il din sun tafi zuwa yi masa sayayya din.
Sun dade suna gulmansu dama sune suka bata masa suna a wajen mututane sune kuma mazajensu suke uwa daya uba daya da mahaifin Bashir din.
Kansu kawai suka sani tun zaman da akayi kafin kowa ya zama wani abu irin kishin saure din nan shine kiyayyan bashir din kasancewa shi uwarshi ta fara haifa jika namiji a gidan sai aka nuna masa gata a wajen kakanin a lokacin wanan yasa basa sonshi ko kadan.
Alokacin harda dan shige shige ake masu akansa shida uwarshi don kawai ya koma baya ya lalace sai Allah yai nasa ikon mazajensu suka samu aiki lagos suka koma can daga nan kuma cigaba yazo suka bar Nageria din kwata kwata.
Tun Lokacin kuma mahaifiyan shi bashir din bata kara haihuwa ba karshe ma ciwo ya sakata gaba tazo ta mutu tabarshi shi kadai ba a dade ba kakan nasa sarkin ya rasu dole ya koma wurin kishiyoyin mahaifiyar shi matan babansa ke nan.
Sai kuma zaman yaki dadi dasu don ta biyun data saka mai kafa sherin duniya ba wanda batayi masa ba wanda hakan ya kara ja masa bakin jini a wajen mutane ya zauna wurin yan uwa da dama amma haka kawai zasuji sun kishi ko matar gidan ta samu sherin data laka masa.
Har Allah yazo ya hadashi da amininsa Abbas mahaifiyar Abbas din mutumiyar arziki ta hada da danta ta rugume har ya zama wani abu ayau ta sanadinsu Abbas din.
Malamai sunsha fada masa cewa sherun makiyane tun yana karami yasa yakejin baiaon mata amma bai yarda ba shi abinda ya yarda dashi shine hakan yasamo asali daga matan ubanansa da sukayi ta gana masa bonin duniya a lokacin.
Ba abinda yafi tsaya mai arai kamar yadda hjy Malka tayi mai kazafin kutse dakin yan matan gidan inda yarantane datazo dasu aure suke kwana tace wai yana shiga dakin da dare yana kokarin bata mata diya.
Har hakan yayi sanadin da mahaifinshi yayi mai kashedin shiga masa gidansa daga lokacin wanda har ya zama sarkin nan ko bai taba shiga cikin gidan ba don ya kasa mantawa da hakan a ransa.
Yanzun ma koshi Isma,il din da matarshi don sun nemesane sun roki yafiyansa tunkan ya zama wani abu don su komai bai taba hadasu dashi ba kawai don sunga kowa baisonsa ne a family din suma sukabi ayarin mutane.
Daga baya kuma suka gane duk sherine ba halinsa bane hakan kazafine kawai sai suka nemi shiri dashi amma sauran sun kasa gane cewa shidin ajiyan Allahne fa wata rana a nan din da suke ganin sa.
Yanzu kuma da zancen aure ya taso masa shine hjy mami tayi tunanen cewa kada yan uwansa suga ta mallake masu da su dauka wani abune shine ta bashi shawaran ya tura masu kudin sayayyan suyu masa in yaso idan an


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login