Showing 111001 words to 114000 words out of 347556 words

Chapter 38 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8738

hakane kice min na dace da mace ta gari data san ciwon kanta ashe kada ki damu yanzun nan zai shigo ki bani minti talatin don Allah nace nagode na kashe wayan ina tunanen me zaiyi a lokacin yace in bashi mintoci kadan.
Kashe wayan nayi ina murmushi nace an gama mai sir ina ajewa naja tsuki tare da turo baki alaman gajiya a tare dani lokacin .
Wanan kuma sabon kamu akayi haka naga an zake ana wani marairaice murya har da ciki baki ?
Maimakon in bata amsa sai nayi murmushi kawai ina fadin wanan kuma bai shafeki ba ko yaya yake matsalatace yanzu.
Ta mere baki don bataji amsan kwarai a bakina ba gashi yanzu ko kewaya zanyi zan dauki wayana inkai kofan gwaggo in aje inna fito in dauko abina din ban yarda da samira ba ko kadan ayanzu tun kan abinda tayi min .
Yaron nan Almajirin mune ya shigo yana fadin wai ga sako inji oga Muhammed a kawowa anty fatima kafin na fito samira dake tsaye kofa tana kallon mirror har ta daga labulen dakin namu.
Ya aje kofan mu ya juya ya fita sai gashi ya sake dawowa duk dauke da kaya a cikin kwali tau lalai abin nayine susan kai da galma samira ta fada.
Mutum dai ya iya bakinsa na fada ina fitowa daga cikin dakin don ganin me aka aiko min dashi kwalin farko na bude saida gabana yayi mumunan faduwa saboda tarin naman dana gani a cikin kwalin.
Gashi har lokacin Aliyu almajiri sai shigo da kaya yakeyi gidan hankalina ya tashi na rasa me zanyi don haka na kwalawa gwaggon mu kira ta fito.
Itama kayan tabi da kallo cikin mamaki take fadin ina sallah yanzu nake jin yaro nan na fadin wani ya aikoshi ko waye da wanan kayan hakane ?
Gwaggo saurayin nan nawa mai zuwane fa da wanan haukan don nace dashi ya barni zan fito inyi girki shine ya turo min da wanan kayan haka.
Ta nufi kwalin tana budewa idona ya sauka a kaji figgagunsu an yanka anyi komai bayan dayan na farko dana bude mai naman shanunu ne kona rago oho ?
Wanan kifine ko ta fada tana bin kwalin da kallo tace wanan kuma kayan miyane ko ba a bude ba ga alama mun gani tana taba buhun da hannu taji.
Lokaci daya muka juya don jin karan shigo da buhun da Aliyu ke kokuwan yi shi kadai shimkaface yar gwaunati ya shigo dashi ya fita wuri na samu saman dakalin kofan dakin mu nakai zaune lokaci guda tare da dafe kai.
Sai gashi da tsirin kwalayen taliya cuscuses da tumatur dan gwangwani ya shigo da kyat ta saukeshi haka aka baje kayan muna bi da kallo.
Bari dai mu fito muga ikon Allah samira ta fada daga cikin dakin tana fitowa tace wai rangas duk ke kadai haka gwaggo tace wanan yar da arziki kika fado duniya.
Ko yaushe kafan ki da alheri yake fita gidan nan ya dawo da sa,a da rabo ke din uwarki ta iya haihuwa a cikin duniya da ace haka ko wace uwa take da sa,an haihuwa da mata sunji dadi a wurin yayayen su gaskiya.
To gwaggo aiko wace uwa ta iya haihuwa duniya saidai kawai ace wanda mutum ya gani zai fada kawai ko don kowa bai iya kissa ba.
Haba yar nan ba haka nake nufi ba don Allah ku din gaba dayan ku daya kuke a gareni babu bambaci a wurina kawai dai harkan maganace kawai ya kawo hakan na fada.
Kai Aliyu dauko robancan ka juye naman nan don Allah kada yayi bashi a gyara yaron yaje da sauri ya dauko roban yazo ya juye dauko dayan mu juye wanan.
Yana murna da jin dadi nan akai aikin dashi na gyara na dora komai a wuta bayan ya sawo muna icce samira ta soya nikan girkin abinci na hada muna lafiyayye na zubawa ban kara kallon kayan ba don data gama gwaggo muka kaiwa a dakinta.
Samira can taje ta debo mai yawa tazo dashi dakin mukaci ina mamakin yadda take iya cin nama haka da yawa ta kora da drinks tana gyatsa na kallota nace kinci saura baba dasu mama lanto ko ?
Waini kina ban mamaki waya fada maki irin wanan ana nunawa gida shi ai sai su koma zargin mu da harkan banza a nan ko gwaggo ai don ana lasa matane kikaji ta shiru.
Haba dai samira sam ba hakana bane suda iyayye daban suke idan ka boye masu ka nuna cewa harkan banza kakeyi ke nan .
Gaskiya nikan ban iya hakan da kikeyi gaskiya danice yau wallahi fita zanyi in sayar da kayan nan baki alakum ba wanda ya sani.
Ke daya kawo min wanan kayan gara ya ban kudina na tura jakata baki alaikum yafi mun kallonta nayi kawai nayi dariya naja filo na kwanta ina tunane.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
3?? 4??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Komai na hada tsab nayi package dinshi yadda ba mai budewa na rubuta nomban Nura ni da kaina nakai tasha acan na kira nura nayi mai bayanin komai.
Bayan yaje ya karbo sakon ya aje dakin mamanshi saida yamma yayi baba ya dawo gida ya dauka ya kai mashi tare da bayanin cewa nice nace yaje tasha ya karbowa baba shi.
Uwa bude muga meye a ciki ya fada ta shiga kiciniyar budewa duk wani abinda ya aiko min na tsakurawasu babashi alokacin.
Daya bayan daya suke shigowa dakin bayan fitan mama uwa don gaida baba da dawowa yana fadin ga duk wace ta kalli kayan sakon mutanen zaria ne nan fadimatu ta bayar akawo.
Budan bakin mama lanto sai cewa tayi ikon Allah ashe abinda yar nan ta fadi dagaskene kuwa don ga zahiri mungani.
Tace suna shan gara a gidan tun shekaranjiya wani ya kawowa Bantu kayan makulashe kamar hauka a zamani don rashin kunya ba kunya ba tsoro shine ita ga issasa ta debowa mahaifinta don asheda abinda takeyi can.
Lanto baba ya ambata da dan karfi ta dakatar da abinda take fada tana kallon shi yace yata ba yar iska bace bata da gadon hakan da ace kuwa harkan banza takeyi a can na tabbatar da ba zamuji kamshin wanan ba harma mu ganeshi haka.
?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? Ban auro uwar Fadimatu wurin iskanci ba asalima tarbiyanta da hankali irin nata nabi na aureta kuma shedan hakan ne gidan nan don haka kada ki jefi yata da shedan banza.
Yau na tabbatar da ace harkan banza take aikatawa ko kanwata da suke zama bata fada min gaskiya ba zan iya ganewa da kaina ta hanyar fahinta.
Don na tabbatar da bazata kawo wanan gida garemu ba har mu gani ke in uwar kwaraice ya kamata ki fahinci wani abu cikin halaiyar yarinyar nan zuwa yanzu ai.
Malam bakai ka fahinta ba ai shike nan gamu gani dai inji tsohuwa da,,,,,baba ya tare da fadin kuga alheri insha Allahu irin wanan halin naku na zargin banza akan dan wani shike kawo nakasu a rayuwan bawa.
Nina fahinci abinda ku kaf dinku baku fahinta ba shiyasa kuke ganin kamar nasakawa Fadimatu ido na daure mata gindi take abinda ranta keso da kuke dauka fitsarane irin nata nan gaba zaku gane insha Allahu inda rai da lafiya kuma zaku fada ai.
Yanzu malam wani yace wani abune kuma yace ko baku fada a fili ba nasan zaku fada a rayukan ku amma ku rike ku aje a ranku cewa ranan na tafe da gaskiya zatai halinta tunda kun kasa fahintar halin yarinyar nan har yanzu.
Uwa ki dauka a raba wanda zaici yaci da zuciya daya wanda baiso kuma tun yanzu ya fada kada a raba dashi tunda kayan haramun ne.
Ai da wani harkan banza take acan da tuni aji a nan ina zaria ina kaduna in wani baiji ba wani zaijine a cikin mu ita dai halinta taci da dan uwa kawai ba wani abu ba.
Yace kin fara ganewa ke nan ke muje dai zuwa wata rana zaku gane hakan ke lanto da kike kokarin fadan wani kalma mara dadi kina da sheda ke nan aka yarki dake can yanzu ?
Shiru tayi don abin nason zama wani magana don bata zaci hakan ba da farko data dauko zancen ta zata baba zai hau yayi ta fada akan hakan.
Wayan baba yai kara ya dauko yana fadin yar halak ya dauka duk suka kasa kunnuwansu muka gaisa nake fadin baba kaga sako ko ?
Wani sojane dake nan wai yana sona shinefa ya kawo muna wanan kamar hauka naga na debo maku tunda yana da yawa haka kaima kaci.
Allah sarki na zargi hakan tunda nasan ba zaki saya ba haka Allah dai ya tsare ya kare a kara kula da mutunci da kima ayi abinda akaje nema .
Ajiyan zuciya ya sauke bayan ya aje wayan yace Fadimatu Allah ya tsare ya kare yayiwa rayuwa albarka ni dai uwar nine uba don haka nake son abata.
Duniya wanda yace yaga bayan ki Allah ka fara ganin bayanshi ka tsare min yata a duk inda take ya Allah ka shige mata gaban lamuranta da yan uwanta baki daya.
Mama uwace ke mayar min da duk abindaya wakana a lokacin nace watau mama Samira ba zata bar sherin ta ba ke nan komai sai ta gida ta fadi karya da gaskiya.
Barsu kawai da halinsu idan ta fada kinji ki dinga nuna mata kinji zata gaji ta daina nace haka zanyi yanzun nan zan kira na fada maki yadda mukayi anjima.
Ina zaune ta dawo da dan leda tana zama ta bude bread ne ashe ta sayo ta jawo roban data dibo nama daga dakin gwaggo ta fara ci na kalleta nace.
Samira kin kira mama kin fada mata muna nan munacin gara da saurayi ya kawo min amma baki iya tunawa ki dan dibar mata ba itama ta lasa.
Ke kanki kawai kika sani baki tunanen iyayyem mu dake gida idan dama ya samu irin haka kallona takeyi cikin mamaki nace eh kin fadawa mama muna nan muna shan harka koba ke kika fada ba a gida.
Don na fada laifine nace amma yanzu baki buga ki fada mata kin sayo bread zakiyi danke dashi ba ai kin dauka hakan wai zaki bata min sunane kin gyara naki Allah ba azzalumin kowa bane.
Allah ne shadata ban taba fadawa wani wani abuba game dake tun zuwan mu garin nan karatu har yau amma ke duk motsina sai kin kira gida kin fada masu.
Da yake banda amanan ki a kaina sai gashi na raba wanan din biyu na aika akai masu tunda ban iyaci basuci ba din nasan mahaifin mu baida halin hakan.
Ashe ke kin rigada kin gulmata masu zancen cewa wani dan iska ya kawo min banza kuna nan kuna ci zaki sheda wanan bawan Allah dan iskane shi ?
Alaman kyautan ban girma a zamanin shine kyauta na bajinta da kowa naka zai sheda shine so nagaskiya ba wanda zai saya maka makulashe ba ya koyama kwadayi karshe ya lalataka ya tafi ya barka daga baya koma wahala.
Bantu kada kika a sanadin ki aka sami abin nan kice zaki fada min maganan banza a kai don ba kyaleki zanyi ba nace idan baki kyaleni ba dukana zaki yi ?
Ta san fadana baida dadi don sun gwada dukkansu har su yan biyu basu sha da dadi ba don saina bar masu rauni a jiki sunyi jiya don haka sai ta tura min roban tamike wai tayi fushi .
Nace yafi nono fari don haka mutum yabar gulmata ko nayi nasa don nasan komai yanzu ban kara kyale mutum kada kiga kamar ina tsoronkine ko wani yasa ban fadan komai .
Hakan yasa tayi ta fushinta dani kwana da kwanaki niko in Aliyu ya shigo zai tafi nake daukan tsoka in bashi don gwaggo ta aje na wurinta tace zata dinga tsankwarawa a cikin miyan gida aci.
Zaman gidan yana min dadi don iyalin gwaggo ba masu zaman gida bane su sai dare har mijin nata yake dawowa gida don hakane bamu da takura ko kadan a gidan.
Monday ce ranan kowa na dan kure adaka don haka na bude akwati na ciro wanan rigan da soja ya bani don banson kiran sunansa don nauyin suna ga musulmi shiyasa nake kiranshi da sojana haka nayi serving dinsa a wayana.
Rigar purple ce daga gaban rigan sai mix da baki da duwatsu da akai mai ado dashi daga sama kadan dogon rigace har kasa mai kyau ga daukan ido.
Yar jakkarta na dauko na hada da wasu takalmana bakake masu ado kamar kwalliyan lace a sama half cover na mata dana saya da kudina a kaduna.
Na fito naje kofan gwaggo nayi sallama tace fadimatu shigo mana aikinsan baban naku asubancin fita yakeyi shi kullun.
Nace gwaggo dama ajiyan wayan nan nake son karba yau tace to tana mikewa ta daga can kasan kaya ta dauko min tana miko min nace nagode na cire kwalin nace saina dawo.
Saidana fita na tuna ba caji amma ba full ba don nakan karba nasa caji lokaci lokaci tare dan mashin mukai jinga na tafi ya saukini a inda muke sauka.
Na tako zuwa department din mu gab da zan shigane wata yarinya da yanzu take yawan son shige min take miko min card kallonta nayi take fadin na auren sister dinace don Allah ki zo.
Kallon katin nayi nace nagode Allah ya ban ikon zuwa ta amsa da amin idan kin karanta zaki ji komai a ciki mukai sallama na shiga idanu ya dawo kaina cikin biyu zuwa uku narasa me suke kallo gareni saida naji wani shakiyin ajin yace rangas.
Kaga matan manya dole ayi dake ko rai baiso dama na fada maku wanan kayan sai manya ko manyan ma nacan sama sama ba irin kananun nan ba.
Yarinya yi hakkuri mu danyi solfi dake don Allah ko gp dina zai daga nima koki ban aron wanan laptop din naki na dauka a fara gani a wajena ban kulashi ba na nufi inda nake zama kusa da Ezekiel na zauna.
Ya juyo yana min kallon mamaki tare da fadin friend how comes baki fada min zaki sai wanan ba ai shigowan lectura yasa muka natsu aka fara daukan darasi.
Mun fito a gajiye kowa ya nufi inda zai tafi masalaci na nufa don sallah inyi sallah na bar kayana hannun Ezekiel da Victoria dake zaune a innuwar bishiya suna nazari.
Na sallame na dawo na samesu ina zama Victoria ke fadin anzo nemana daga office din H,O,D namu na science mamaki ya kamani nake tunanen mekuma ya hadani dashi har yake nemana.
Banyi sanyi a gwiwa ba na mike kafin mu shiga aji na nufi wajensa nan na tsaya jiransa saida akai min iso na shiga dattijon matashin mai zubin kamilai yana duke yana rubutu a cikin wani takarda na gaidashi bai amsa ba saidaya gama rubutunsa ya dago ya amsa min tare da fadin.
Fatima Abubakar kaduna nace yes sir yace ok zauna yana ciro wasu takardu a table din shi yace zan iya cewa you are lucky ko kuma dai bansan yadda zan fada akan hakan.
Don wani lokaci al,ada yana shiga gami kuma da addini har ya hanamu samun ci gaban mu ya dire min wani takarda a gabana yace wanan takardan neman yardan kine .
Company Digital global suka kawo min na son ki zamo daya daga cikin customers care dinsu na nan kinga idan Allah ya taimaka zaki dinga samun albashi na dan lokaci daga garesu.
Don su company ba mutane bane da zamuce na dindindin don haka a yanzu dai sun zabeki a nan makarantar kancewa suna son yardewan ki ma,ana ki saka hannu a takardan nan ki zamo cikin yan arewa da zasu tallata masu manhajarsu ta sabon company su.
Amma fa sai inkin yarda zaki iya don abune da duniya ko nahiyar mu ta Africa ga baki daya zasu sakin ta hanyar yadda fuskanki a wanan tallan da suke so.
Da sauri na kalli malam din yace yes don abune da zasu kaiwa tasgoshin redio da talabijin talla su haska a duniya don hakane suke neman yardan mutum kan hakan kafin ka cika komai dasu.
Da sauri na katse shi da fadin gaskiya malam ba zan iya wanan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login