Showing 171001 words to 174000 words out of 347556 words

Chapter 58 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8734

mijinta tun safe salima kuma tana daki tana barci don haka zama ya isheni na fito falo na kwanta saman dogon kujera ina duban sakonni a wayana.
Na gaji da duban wayan na dauki hannuna na dora saman fuskana ina tunane a yadda nake kwance gashi falon yayi tsit babu kowa a cikinsa.
Ban san shigowan mutum ba don nayi nisa a cikin tunane ba komai nake tunane ba sai yadda zamu kwashe da makaranta idan na koma don sakon da samuel ya turo min nagama karantawa lokacin na fada a tunanen.
Tsaye yayi yana karewa kyakyawan surana kallo yadda na kwanta rabin kafana duk suna fili ya hango hakan ya tsaya yana bina da kallo cikin shagaltuwa.
Saboda yadda ya hango ko ina yayi sumul gasu lub lub dasu tankar wace bani taka kasa dasu ga farina ya karu halittana ya ciko ta ko ina saboda hutun dana samu a nan sosai ban cikin wani damuwa idan ba wanda na dorawa kaina ba lokacin.
Koshi ban yarda na nunawa hjy cewa na fahince ta sai sharewan da nakeyi saboda banson inyi mata butulci gashi kuma bansan dalilinta na hakan gareni ba lokacin.
Bansan lokacin daya tako har zuwa gab dani ba a inda nake kwancen sai jin muryanshi nayi a kaina yana fadin abinci nakeso don Allah ko zaki taimaka ki dan hada min wani abu inci yanzu.
Daga cikin tsakiyan kaina naji maganan kamar daga sama wanda ba tantama muryan uncle ne nake ji a lokacin gefena don haka nayi saurin sauke hannuna ina bude ido da sauri.
Uncle din na gani a tsaye kaina yazo har inda nake yana magana da sauri na yunkura na tashi zaune ina jefa mashi wani fitinanen kallo a fuskan shi.
Ya kara fadin yunwa nake ji ki dan taimaka ki hada min wani abu don Allah inci fatima wani dogon tsuki naja masa na mike tsaye nace saboda ina yar tallakawa bansan ciwon kaina ba zan shiga kitchen yanzu in dafama abinci ko me ?



ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
5?? 3??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Murya ya mairaraice zakice ba uncle bane mai jiji da kansa da girman kai yace fatima har sai yaushe zaki gane don Allah bar zancen nan yanzu ki dafa min wani abu.
Wani banzan tsoki naja nace ai gidan ba bakonka bane kana iya shiga ko ina kayi duk abinda kakeso ni yar tallaka dani me zai kaini shiga harkan yayan manya kuma ?
Na rokeka ka fita daga harkata don Allah sai naga yayi min wani kallo kalan tausayi ya kama gefen cikinsa ya dafe yana kaiwa zaune saman kujeran dana tashi tare da dukar da kansa yayi shiru a wajen .
Tausayi ya bani lokaci guda na juya na shige na barshi a wajen kamar in wuce dakina in kwanta sai kuma nayi shawara a zuciyana na nufi kitchen din kai tsaye.
Don nasan ran hjy ba zaiyi dadi ba don da alama kamar baida lafiyane ma yadda naga ya rame din nan ya fada ya danyi duhu sosai.
Cuscus da ganye na dan dafa mashi cikin dan kankanin lokaci sai gashi na hada na kwashe na nufo falo don ina sa rai har lokacin yana nan falon inda na barshi.
Kwance na hangoshi a inda na tashi na jawo dan karamin table na dora mai akai na koma na dauko ruwa kodana dawo na samu ya tashi ya zauna.
Zan aje ruwan yace sorry bana shan ruwan sanyi a wanan yanayin jin hakan yasa na dago na juya don in dauko mara sanyi da yace ina kunkumi a raina.
Uncle ya dago kanshi dake sunkuye yabi bayana da kallo a cikin zuciyarsa yake tunane tare da jerowa kanshi tambayan da baida amsan shi a lokacin.
Kafin in dawo da ruwan na samu hjy zaune a kusa dashi tana tambayan abindake damun shi na aje ruwan ina mata sannu da dawowa ta karba tana fadin sannu mamana abincin ya saura ki debo min nace ehh mama na juya na tafi.
Na hado mata na kawo zuwa lokacin ya dan fara cin abincin a yangance suna magana da ita wani dan table din na jawo na aje mata a gabata.
Na juya zan tafine take fadin don Allah ko akwai wanda Abbu zaici a yanzu nace ehh ummu akwai don na dan rage wanda zanci na juya naje na shirya masa.
Ina bada bayane hajiya ke fadin yarinyar tana da saukin kai da sanin ya kamata amma kuma na fahinci wani abu daya a kanta shine idan ta rabi mutum zata iya finsa nan gaba.
Yayi murmushi a tausashe yana lumshe ido yace ummu ke nan sai yanzu kika gane hakan a kanta na fahinci baiwantane hakan don ta????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
na da saukin kai da sanin ya kamata.
Kallonshi tayi cikin mamaki yace kwarai umma baki tunanen yadda akayi bashir yake tare da ita ba duk zanfin kansa kuwa da saurin hasala irin nasa amma ya ganta a nan ya nuna yasanta .
Mohammad bansan iya adadin tausayi da nakewa yarinyar nan a baya ba amma yanzu sai nake jin tana fice min a rai don zata iya kawo min matsala nan gaba nake gani.
Yan gidansu basuyi karya ba a kanta da suke kiranta da karan dafi don ko taci wanan sunan gaskiya wai kasan sarkan data sayo a makkah kuwa wanan zuwan namu ?
Wani dan murmushi yayi yA rausaya da kai yace baki tambayeta inda ta samu kudi data saya ba sai ganinta kawai kikayi ta sayo sarka ?
Kallonshi tayi tana jawo abincin zuwa gabata tace ta fada min akwai kudi a jikinta har sau biyu amma banyi azancin in karba insan nawane yawan kudin ba.
Ummu kece kikai min fadan daya ratsa zuciyana baki mamaki da yarinyar nan takai matsayin tsayawa da bashir ba sai wanan sarkan data sayo.
Meye na mamaki a ciki don tasan bashir hjy ta fada ta dauki spoon ta dibi abincin takai a bakinta ta kalloshi ta ambaci sunanshi .
Ya amsa cikkn murya kasa kasa tace ba zaka fita zancen Bashir ba hakana bako, ko kishin hakan kakeyi don yasanta nafagane wanan kwanaye kwanayen da duk kakeyi akan yarinyar nan.
Shiru yayi na tsayin lokaci yana cin abincinsa ummu ta kara daga murya cikin bacin rai tace ka sani sarai abune wanda ba zai yuyu ba a gareka duk zancen da Al,amin keyi nima na dago hakan akanka kan yarinyar nan fatima.
Wani kallon mamaki yayi mata yana dagowa sai kuma ya mayar da kansa kasa yaci gaba da cin abinci yaci kamar rabi ya mike daidai lokacin da Abbu ya shigo falon.
Yadda ya ganshi zai shige shi yasa ya kalloshi ya koma ya mayar da kallonshi ga ummu yace lafiya dai itama ta hau a lokacin don haka da kyat ta bashi amsa da fadin lafiyan ke nan dai.
Zama Abbu yayi take fadin ga abinci nan yace meya hadaki da mutumin naki kuma naga kamar ransa a bace yake da zai fita.
Ka barshi kawai magana yakeson ya jawo min bayan yasan aurenshi dan lokaci ya rage nayi masa magana kan kada ya soma abinda yake niyar yi shine ya fita yana fushi yanzu.
Murmushi Abbu yayi yana kaiwa zaune inda uncle din ya mike tare da jawo plate din abincin gabashi ya bude ya fara ci can ya dago yace aikin fatimane wanan ko ?
Saida hjy taja aji kafin tace itace ta dafawa wanan dan rigiman bayan ya gama ci mata mutunci waishi so ko an fada mai haka ake soyayyan da hauka oho ?
Soyayya kuma son fatima din ke nan yakeyi kuma ko me tace waya sanar mashi nidai na taka masa burki kar ayi kar a fara don ba zan yarda ya mayar dani mutumiyar banza ba a nan.
Bai kara magana ba yaci gaba da cin abincinsa karshe kuma ya tsaya yana waya bai kara maganan ba saida ya fitane ummu ta kira salima tazo ta kwashe kayan da sukaci abincin.
Saidana kara kusan wata daya kafin hjy ta shirya komawan mu duk hakan da tayi min baisa nayi mata magana ba don bansan abinda take nufi ba dani.
Saukan dare mukayi kano don haka muka kwana gidan wata yar uwarsu Salima sai washe gari muka rabu ita ta nufi katsina ni kuma na nufo zaria don a nan zan fara sauka.
Kafin mu dawo har an fara shaguben cewa na koma makka ina takari a can don karin karya har cewa akayi wai sana,an abinci nakeyi a can din.
Ban shiga kaduna ba saida nayi clearance din komai a makarata naga komai ya koma min daidai ka ranan wani jumma,a naje masu weekend.
Kwatsan suka ganni don ko baba baisan na dawo don wayanshi da akai blocking dina koya kira sai yajita kashe har ya soma zargina a lokacin kan naki dawowane.
Sai gani don ban samu fitowa gida da wuri ba don haka nayi dare a hanya kayana yaro ya fara shiga dashi don na tsaya yin magana da isa daya taso bakin shagonshi yana min sannu da zuwa.
Tambaya yaron samira tayi kai wake da kayan nan haka yace wata hjy ce tazo isah yace in shigo mata dashi ciki ashe duk da darene yaron yaga hakorin gwal din da salima tasamu sakawa a madina.
Kai ko dai Bantuce Nura dake cin abinci ya fada yana mikewa da sauri ya nufi waje saurab ma suka biyoshi a baya da gudu.
Muna arba sukayo kaina da ihu nima nabar isah na rugumi yan uwana muna murnan ganin juna dasu muka kwasa zuwa cikin gida da murnan mu.
Ashe baba na gida lokacin sai gashi ya fito yana fadin ikon Allah Fadimatu kece tafe yanzu yaushe kasan jin muryan baba yasa na sake hannun hussaina na tunkaresa da murna na kai kasa tare da fadin ina wuni baba mun sameku lafiya ?
Yace fadimatu shiru haka har alhazai sun dawo muna ta saka ido muga dawowanki shiru ni har abin ya fara tsoratani ai hankalina ya tashi matuka da rashin jin duriyan ki.
Gashi kuma ko kira nayi bana samunki amma sai yan uwanki sunce suyi waya dakw lafiya lau amma a wayata inyi ta gwadawa baya shiga.
Wallahi nima haka baba ina yawan kiranka baya zuwa ko dana dawo din nan nayi ta kokarin in sameka bai shiga ba sai baba din yace ikon Allah.
To ya haka a,a baba wata kila dai an shiga block ne a number ta yasa baka samunta wani abune hakan ni dai zan iya tunawa tun lokacin danaba Samira wayan ta duba min tun ranan na daina samunki gaskiya.
Yana fadin hakan nagane inda matsalan ya fito na kawar da zancen da fadin ai gani na dawo baba ya gida ya jama,a ya kara amsa min cikin jin dadi.
Yau din nan kuka saukane ya tambaya nace ba yau bane baba na kusa sati biyu da dawowa na tsaya makarantane nayi wasu yan gyare gyre yace ikon Allah to wajan ita hjy din nace suna lafiya suna gaida kai na fada.
Dakin mama uwa muka nufa don dakina baiko shakuwa saboda rashin gyara da bai samu a yanzu duk dakin ya kazance sosai .
Na muka zube da yan uwa ana hira banda Samira tunda na shigo tace mutanen saudiya an dawo nace Allah ya dawo damu lafiya.
Mama uwa tace min hjy ga ruwa naji daga gefensu ance a,a naga ta mike tashiga dakin su bata kara lekowa ba kuma duk zama hiran da mukeyi don ma nayi saurin barcine saboda nagaji sosai a ranan.
Don ba karamin wahala nasha ba a school don ma ina da daurin gindi a wajen H,O,D din mune abin yazo min da sauki da kila spell zasu bani a lokacin nan.
Ni kaina nasan hjy ta kuntatamin data tsayar dani kuma tasan ina karatu amma bata duba hakan ba tayi ta dage muna dawowan mu wai sai Abbu ya dawo ya sallamemu.
Washegari da safe saigasu jamal sun shigo su suka tayar dani daga barci zuwansu yasa na fara raba tsaraba a gidan mu kowa ya samu har wasu makwabta da muke shiri dasu haka .
Do mun tsaya kano nida salima muka canza dan kudin hannun mu da Abbu ya bamu muka karo tsaraba dashi duk da a can ma muyi ta sayan tsaraban mu a hankali mun tara.
Na aikawasu hjy maman ya habibi dashi nace a fada masu ina nan shigowa gidan idan nan mama uwace daba kowa a dakin take dan gulmata min yadda abubuwa suka faru akan auren ya habibi da samira da baifi wata daya da kwanaki ba a yanzu.
Allah ya basu zaman lafiya nace kafin na dora da fadin baba bai kyauta ba dayasa mama tabar gidan nan a wanan shekarun da suka kai.
Nima dai haka nace tunda ya saba da halinta kuma yayi niyar bada samira din meye abin saki kuma a cikin zance mama uwa ta fada.
Nikan wanan abun kunyar ina za a kaishi mama baba baiyi saki ba sai yanzu da duk tsufa ya kama kowansu kuma saki zai shiga tsakanin su aiko don yaran zaiyi hakuri da halinta.
Nikan idan da sauran aure gara kawai baba ya dawo da ita dakinta ta zauna yafi mai sauki nake gani.
Sai mama uwa din tace dani, ai kinsan halin malam idan ya kafe akan zance don ba yadda bamuyi dashi ba akan yayi hakkuri ranan.
Shigowan Usainace yasa mama fita daga daki ta barnu tare Usaina din ganin mama ta fice yasata zauna tana fadin kinga dai har yanzu mama bata dawo ba nace wallahi zancen da mukeyi ke nan yanzu da mama don gidan ya koma ba dadi ayanzu.
Kai Bantu hoo ke kike ganin hakan sukan ai mutanen gidan dadin sune haka don basu boyewa sai shirye shiryen bukinsu suke faman yi.
Ana son ayi karya da bukin ba halin hakan sai karyan banza da takewa mutane da ita da uwarta don karya ankon lace aka fitar wai shine ankon bukin duk sai muji haushi.
Nace a,a ashe abin babbane tace na karyaba ni garama daba hassanace zata auri dan iskan ba duk ya fice min a raina dan iskan banza kawai mayaudari.
Shiru nayi kafin nace Allah dai ya kyau yanzu dai zancen dawowan mama zamuyi musan ya za a bullowa baba da zancen don barin mama gidan nan a yanzu baiko taso ba a yanzu .
Bantu ina kika san hakan ai sai ance dake safiya yayi kowa na neman abinda zai karya a gidan nan muna kallo sai mama uwa itace mai dan bamu koshi ba kullun ba sai idan tana dashi.
Nace subbahanallahi tace kwarai kuwa don baba komai yanzu sai yace zancen auren samirace a gabanshi gamu dai munsawa sauratan Allah ido mu gani.
Wai baba ko yana cikin hayacinsa Usaina ta yaya har hakan keta faruwane wai tace ai munyi maganan ranan da mama uwa take fadin dama kece karfin abincin gidan nan gashi ko mun sheda hakan da baki kusa yan watanin nan da kikayi a Saudiya.
Ki bari kawai Bantu munga abu sosai wallahi bayan tafiyan ki yanzu ai kin dawo kya gani kema ai hassana ke fadin ashe haka kikai fama da rashin uwa a gida.
Har mun yanke shawara mu fara sana,a akofan gida shekaran jiya don na sabuluma yana kokarin gagaran mu a yanzu balle abinda zamu danci dole sai mun jira an samu muci.
Wani iri naji a raina lokacin da take wanan bayanin ina mamakin ya akayi gidan namu ya koma hakane kuma don nasan baba yana da dan kokarinsa wurin kula da iyali.
Amma kuma ba mamaki kila zancen Usaina din gaskiyace don auren nan dake gabanshi ne komai ya jagule mashi a yanzu kai saboda mutum daya zaka ba rayuka kusan goma sha a cikin wahala na tambayi kaina.
Muryab baba din ne dake kirana ya katse muna hiran mu na daukama ya fita a lokacin ashe yana gida bai fita ba na dago da sauri na yafa mayafi a kaina wanda bai gama rufe min jiki ba na fito ina amsawa.
Tun daga nisa yake fadin fadimatu ai kyazo mu gaisa ko wallahi baba bansan kana gidan nan ba na dauka ka fita tun dazun kasuwa.
Ya juya yana fadin kasuwa basaida abin saidawa ba ya shiga daki nabishi a baya zuwa cikin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login