Showing 288001 words to 291000 words out of 347556 words

Chapter 97 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8795

matane a zaune suma dagani lokaci yanayinsu dayan ta kalli Basma tace wai kuwa kin gane amaryan nan kuwa Basma ?
Kallonta tayi ta kada kai tace a,a saidai ina ganin kamar na santafa a baya wani waje kallon da nake mat ke nan amma gaskiya ya samu mata ai wanan ko ina ana shiga da ita don ta hadu sosai wallah Basma din ta fada.
Dariya mai tambayan tayi kafin tace kinsanta mana budurwan man dinkine fa wanan yarinyar da kukayi case da ita kwanaki yar unguwar malali mana ko har yanzu baki yarda ita bace ?
Exactly itace itace wallahi itace, ta kusa da Basma din tace ke kibari don Allah wllahi itace, lokaci daya suka maida kallonsu garemu a daidai lokacin muna tare da matan yayyuna ina dan murmushi suna min sheri ni kuma abin yaban dariya na murmusa har duple dina ya dan lutsa kadan.
Basma kice muna kin auna arziki irin wanan zukekiyar yarinyar haka tace bardan iska ni zai sakawa hawan ruwa ina zaune kalau ya jawo min rigima nina rasa inda man ya zakulo wanan yarinyar.
Shigiya Basma sai kikai masu na mahaukata ko kika kakabata jikinshi tace ba dole ba ke bari man ya dauko min wanan aina kade don ba karamin yaki zanyi dashi ba a kanta.
To amma ai gidansu tallakawane kuma naji ance sokoto za,a daura mata aure fadan sarkin musulmi kafin takai aya wata daga cikinsu ke fadin tace kila zama ya kawota gidan mana.
May be relative ne da gidan yasa ta zauna a nan din ashe ban tsamanin hakan don yarinyar fa dama kalar manyace ita dibafa dan Allah kamar ita tayi kanta ni tun lokacin nasan tana da wani daya tsaya mata.
Lokaci daya aka juye case din nan ya koma babba ni yadda naga anyi tun lokacin nasan ba karama bace nima ila ya jani ai da zafin kishi don wallahi na raina kaina a karshe su daddy sunce babu ruwansu a kulleni suka kwashe da dariya lokaci daya.
Sannu a hamkali Dj ya saka wani busa mai taushi mai saka natsuwa a zukatan mutane wanda hakan yaja hankalin kowa a wurin ana kallon me zai faru.
Can muryan hjy Battula data karbi mic din ta soma magana don Allah uwayen amarya naso a basu fili da yarsu suma su fito su nunawa mutanen arzikin da suka taru wajen nan kauna da godiya tare da nunawa yarsu kauna irinta mahaifa.
Yar duniyace tasan ciki da wajen kaduna tasan kan Nageria kuma don idonta a bude yake amma bata bar gida tana shiga Somalia ta dade a can tana zuwa kuma harkan kasuwancinta ko ina.
Busane sai mawakiyar dake jera kirari koba kajin yaren zaka fahinci hakan wani sauti ya fara fitowa mai kama da kidan kwarya irin ta kasansu din.
A hankali Ammi ta sauko dani daga inda nake zaune zuwa tsakiyan fili ido kowa ya sauka a kan mu yaga tasu bajintar wasune masu turaren wuta suka shigo su biyu suna dan hurawa hayakinshi yana tashi yana sauka a jikina.
Kafin kidan ya canza sai gasu suna tasowa a kujeransu da suke zaune ba a farga dasu wajen bama sai lokacin don sun shigone lokacin da waje ya kicime da rawa da kidan iyayyen ango lokacin suka hallara sukuma.
Innalillahi wata ta fada ke da gaskiya akwai hadimai ashe har yanzu wa yancan fa jakkunan su suka dauko masu ko wace ta tsaya a bayan nata uwargijiyar sai ta bude bakin jaka kawai tayi tsaye.
Kudine ba pieces ba a,a bandur dinsu aka fara watsawa lokaci guda nan lafaya ya koma kasa sarkukin wuyansu dogaye suka baiyana hannu daya kuma ana kadashi kai na rawa suna mika hannu daya suna daukan kudi a jakarsu.
Abin ya zamo abin kallo don hakan bakon al,amarine a wajen mu nan yadda kasa take a cikin wani hali wanan yasa tsegumi ya tashi a wajen kowa na fadin albarkacin bakinsu.
Anyi barin kudi kamar ba gobe uwayena sun haskani sun kwato min daraja da kima da abinda yafi mafi soyuwa a zukatan mutane a yanzu watau kudi.
Don su akafi darajawa da komai a yanzu don kana basarake ba kwabo ko kana malami ba kwabo ko kana da wani nasaba a tarihi mafi daraja idan ba kudi a yanzu wanan ya zamo kamar ba kowa kake ba a cikin al,umma.
Kowa ya tafi yana murna da jin dadin wanan taron sai yan kalilanne ke kwashe da bakin ciki irinsu hjy Laila da tawaganta da wasu bangare masu jinin mahassada asalin ta hanyar bakin kishi.
A cikinsu ko akwai maman biyu akwai matan mahaifin Bashir sai hjy saudiya da rabin zuciyanta kyashi rabi kuma ta kasa gane kanta gaba daya.
Ita kuma hjy laila da tawagarsu fada takeyi tana fadin wanan ai ya zama riya a kasan nan zasuzo suna muna haukansu na larabawa da su basu mayar da dukiya bakin komai.
Amma dai wa yan na mantan manyan kasansune sukazo ko wata daga cikin tawagar ta tambaya hjy Laila din tace kema aida gani ba sai kin tambaya ba sun manta lokacin da suka cika kasan nam suna bara a taimaka masu.
Nasan a lokacin ne mahaifin yarinyar ya auri uwarta kinsan mazan mu in sunajin motsin aljihunsu suka kyala ido akan farar mace zance ya kare a nan.
Wani tsararen gidane a unguwar new GRA gidan yana tsakiyan unguwa a tsakiyan mutane suke duk da hakan bai hana a aje security a kofan gidan ba kasancewar gidan gidan babban soja a kasa aka zuba mai security masu tsaron su.
A can cikin gidan dakin kwana Basmace a kwance ta kurawa mijin nata dake ta faman shiri don haraman zuwa daurin aure abokinshi na karatu da yakeyi kuma aminai na kurciya kafin kowa ya kama gabansa bayan girma.
Dan muskutawa tayi tana gyara kwanciya tace wai kasan yarinyar da gifted zai aura don sunan da suke masa lakani dashi ke nan mijin ya dan juyo yana fadin.
Ni ina zan sani tunda ba tsayi zanyi in bincika ba ni dai ya gaiyaceni daurin aure kuma zan tafi insha Allahu don yadda muke dashi don haka aiba sai nasan matar ba wanan tseguminku ne kawai na mata bin didigi.
Ya juya yaci gaba da cusa kaya a jakka don tafiya sokoto din da zaiyi saboda hartan daurin auren kome ya tuno sai kuma ya juyo yana fuskantar matar tasa yace na katseki wacece matar da zai aura din ya tambayeta.
Dan murmushi tayi kafin tace kodai kasanine kakeson ji kuma daga bakina again amma au baki sanni da wanan halin ba tsayawa tsegumi kan abinda bai shafeni ba.
Tace yes hakame kuma fa ba wata bace sai kamiya miyan daka tashi kwaso min wanan Fatima yar malali din da mukai case a kanta koka tunanata yanzu ?
Wani kallon mamaki yai mata yana fadin wai kina nufin Fatima dama ita gifted zai aura tace kwarai gama photonta dana dauko jiya wurin buki ka gani .
No ki barshi ya fada cikin juyawa da sauri yana cigaba da harharda kayanshi yana mai jin wani iri a zuciyarshi don gani yake kamar zolayace kawai matar nasa take masa a lokacin.
An kasaka don baka da karfin Bashir jin hakan yasa ya juyo inda take yana fuskantar ta yace kema kinsan wanan karyane idan ban jaye ba shi gifted bai isa ba wallahi don na rigasa zuwa.
Halinki dai yasa na jaye kada ki halaka yar mutane da bakin kishin nan naki na banza amma waye gifted shima yasani ai ya fada yana hararanta ya bar dakin zuwa kasa koda ya dawo tana bayi tana wanka.
Wayan ya dauka ya duba tabbas Fatima dince kuwa Basma bata fadi karya ba ya mayar da waya ya aje ya fice motarsa ya nufa kai tsaye sai malali layin mu ya tsaya da isa mai shago ya fara haduwa.
Nan take isah din ya shedashi ya fito daga shago yana fadin rankai dade barka da zuwa suka gaisa yace gashi ko mutumiyar na cikin jamma,a ganinta zaiyi wuya yanzu.
Saidai in a waya zaka kirata dai wata kila in tana kusa da wayan ta dauka OK yace ya dauko wayan nasa har ya fara neman layin nawa sai kuma ya dago kai yace nace ba taron me akeyi gidan nasu ?
Yallabai bata fada maka zancen aurenta bane ai itace zatayi aure don har naji ana fadin mahaifiyarta tazo daga kasansu na larabawa.
Mahaifiyar Fatima din don yasan da zancen batar uwata yasan kwaram din mu da mutanen gidan mu saboda shakuwa da dadewan da mukayi tare dashi.
Yace a ina zatayi auren waye kuma mijinta din ne yace to yallabai ni dai bani ganinsa kamar yadda na saba dakai haka amma ance wai yana zuwa gidan saidai in zai zone a cikin tawaga yake zuwa don haka ba zance na ganeshi ba.
Amma naji wai wai ance wani fitacen mai kudine kuma dan sarki a kasan nan saidai,,,,,, don Allah ya isa zan kirata a waya idan na koma yaja mota da karfi ya tafi isah din ya tsaya yana kallonshi cikin mamaki.
Tunda ya sallame sallah yake zaune a wajen kusan awa daya yana addua akan Allah ya kawo kowa lafiya ya mayar dasu kuma gida lafiya yadda sukazo tako wani bangare.
Zancen zuciya da saurin tuno da abu sai lokacin da bawa yake bautan ubangiji mutum yakebe yake kokarin saduwa da ubangijinsa a daidai lokacin shedam kuma ke kokarin nisanta bawa da ubangijinsa ta hanyar shedancinsa.
Ya Allah ka tsare mu daga sherin shedan komai kankantanshi amin ya Allahu shima a yanzu adduan ya katse ya fara wani tunane a kansa da wasu abubuwa na rayuwa.
Cikin hakane lokaci daya wani bakon yanayi ya ziyarceshi don tunda yake bai taba jin wanan yanayin ba sai wanan ranan a daidai wanan lokacin daya yake zaune saman sallaya
Don ko mazakutarshice yaji ya motsa masa saida yakai ya dafe maranshi lokaci guda yana furta ya subbahanallah a fili don bai taba jin irin wanan yanayin ba a rayuwanshi sai wanan lokacib.
Shiru yayi yana tunanen meke shirin faruwa dashi ne wai a yanzu kuma har yagama ya shafa adduan a dadafe ya mike ya dan kwanta kafin gari ya karasa waye.
Nan ma barcin ya gagaransa yayi don ya kasa komawa barcin duk da gajiyan dake jikinsa a lokacin can yana kwance idanunsa a rufe lokaci guda guda yaji yana zama namiji a hankali .
Abinda bai taba faruwa dashi ba dai a rayuwanshi yanzun yake tsuntar kansa a ciki ido ya lumshe tare da kifa cikinsa saman gadon ko zaiji saukin abinda yake ji din a lokacin.
Zubur ya mike lokaci guda ya dan zauna kafin ya zuro kafafuwansa kasa ya zauna da kyau a bakin gadon kansa ya dafe da hannu biyu na dan lokaci.
Addua,ne dauke a bakinsa yana neman tsari daga Allah kada hakan yazo ya zama mashi matsala babba a rayuwanshi ya danyi yana tofawa a hannu yana shafan inda yake jin yana damunsa din.
Zuwa wani lokaci sannu a hankali yaji ya koma normal ya barjin abinda yake ji din da farko lokacin ya dan koma ya kwanta rigingine ya dora hannayensa saman kansa.
Can ya dan murmusa yana fadin Allahu akbar Allah yajikan maza, mazan sun kwanta dama, mazan kwarai sun tafi da baiwansu da basira tare iliminsu da saninsu.
Tabbas mutanen da suna da lakani da waibuwan sanin rayuwa mai amfani ga dan Adan mafi yawansu sun abubuwan amfani ga dan adam wanda a yanzun duk an yarda wanan al,adan ana ganin an waye.
Tabbas alkwarin tsohon kakansane yake cika a kansa yanzu inda ya fara dan tuno da abinda ya fa alokacin da yake daura mai wani dan zare a kunkurun shi .
Yana zaune a gefensa yana wasa wani dan zare mai launin ja ya dauko hankaden wurin zamansa bayan yabi zaren yana masa wani tofi yana tofawa kamar yana jan tasbaha a hannunsa.
Kafin ya jawo Bashir din yana daura mai zaren yana motsi da bakinsa saida ya tabbatar zaren ya dauru mai ya dakyau ya shafo kansa yana fadin takwara kayi karko irin na dabino kaji shiko duk da baisan abinda kakan nasa yake nufi ba sai ya amsa mai da toh.
Allah yayi maka albarka kaji ya kara amsa mai da toh din bai san yace masa ami ba a lokacin akwai dan duhum kai ba kamar yaran yanzu bane da suke bude baki da irin maganan manyansu don babu kwabo a yanzu kome yaro ya fada sai iyayyesu dara.
Juyawa yadanyi yana runtse ido yaci gaba da tunane akan kakan nasa tsohon da bai taba mantashi a rayuwansa tsohon daya dorashi a hanyoyi da dama ya koya masa tsoron Allah tun yana karaminsa ke nan.
Yau mutuwa tayi masu katanga a tsakaninsu a???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? daidai lokacin da yakan yawan tuno da ace kakan nasa na raye shima daya nuna masa gata fiye da wanda shi ya nuna masa a baya.
Yaci gaba da tuno irin wanan rayuwan na zamani kakan nasa cikin dan abinda zai iya tunowa dasu lokacin da ya shiga makarantar primary ta L,E,A wata rana ya dawo da gajiya ya sameshi a fadarshi yace masa takwarana .
Da badon karatun nan nada amfani gareka nan gaba ba danace ka zauna ka huta a gida kamar kowa sai dai kayya wanan karatun nan gaba kadan zamani mai zuwa zaizo ya koma kamar bauta ga mutane.
Gara kayi tun ana gudunsa a yanzun din ya mika masa kwanon da ake dama masa fura a ciki mai hoton tsohon shugaban kasan lokacin ya karba zai fara sha yace a,a takwarana ina horonka da bakinka ya saba da bissimila a ko yaushe zaka kai abu ga bakin ka.
Hakan ko akayi yace Bissimillah a fili sai tsohon yayi dan murmushi shi kadai yasan abinda yake murmusawa a lokacin can ya kusa shanye fura sai yaga tsohon yakai zaune yace miko min hannun ka nan in gani da sauri ya ture kwanon ya mika masa hannun nasa ya rike yana bin tafin hannun nasa da kallo na dan lokaci.
Sai ya dan girgiza kai yana fadin takwara Allah ya tsare ya kare min kai a duk inda ka shiga a duniyan yace toh kaka yace Amin zakace yacw Amin din.
Can kuma yace miko min hannunka na hannunka na hagu nagani shima ya mika mar yadan kura mai idanun kafin ya girgiza kai yana fadin ikon Allah kusan kaddaran ku daya da abokiyar rayuwan taka ai takwarana.
Sai a wanan ranan wanan zancen yake fado masa arai har take ganin kamar yanzu yake zaune gaban kakan nasa suna wanan magana watau mutanen da can baya suna da sani kan abubuwa da dama wanda yanzu addini ya kawar da wanan ga mutane.
Tambayan kansa yayi kome kakan nasa ya gano a lokacin har yayi masa wanan maganan haka sam ba zai iya fahintar komai ba a lokacin don da yanzune zai tambayesa meyasa yace hakan gareshi.


ZAINAB IDRIS MAKAWAL

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
9?? 2??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Bukin gidan sarauta ba kasafai ake daura auren mutum daya ba hakan ya kasance ko a namu don mu kusan ashirin da bakwai aka daurawa aure rana daya yan mata da zawarori duk wace Allah ya datar da min sai akai sunanta fada idan idan iyayye sun shirya aurarwa a lokacin.
Idan kuma basu shirya ba sai a dakaci gaba har wani daurin auren a daura da yarka ni a wanan lokacin anyi dace da za,ayi a daidai lokacin shine yayan mahaifinmu ya saka sunana a cikin list din.
Taron daurin auren yaga baki da yawa daga bangarorin Nageria dama makwabtan kasa hardana ketare sun samu halarta suzo wa wayanda suka gaiyacesu a lokacin.
Don hakane filin yake makil da bakin da suka harci daurin auren ma wanda mutum yazowa kara bawai nawa ni kadai ba a a saidai ba yabon kai ba nawa din yafi haskawane .
Don kusan bakin nisa duk zakaji sunce daga kaduna sukazo auren Bashir inda wani abokinsu na sokoto Mustapha Bello ne mai masaukin su don shi ya kama masu masauki a giginya.
Anyi lafiya an watse kuma lafiya inda tunka maza su dawo gida labari ya samu mata na yadda abubuwa ya kasance a wajen ckki mutunci da sanin addini ba karya ko riya a fadan sarkin musulmi din na sokoto.
Dan akasin da aka samu shine sunyi fadan rashin zuwa da Amarya nan sokoto din sai aka basu hakkurin hakan kuma sukayi ba tare da bacin rai ba.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login