Showing 315001 words to 318000 words out of 347556 words

Chapter 106 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8722

naji banson su tafi kuma.
Maman Yunmah ki bar min ita a nan koku bar min Liliya mu zauna cewa da yayansu dariya suka kwashe dashi suka kwashi yayansu da zasu tafi har kofa na rakasu Abbas yace inya fito in fada mashi sun tafi yana ganin sallah yakeyi a ciki.
Bayan wucewansu na juyo ina kallon katon falon dashi wanan milk color din set na kujeru masu masifan kyau aka zuba mashi har set biyu amma akwai fili duk da hakan a cikinsa.
Hakama set din dining table din dake wani dan kwana shima mai kyau dashi ya hadu komai na falon dai abin tsayawa ka kallane don gidan ya hadu iya haduwa.
Muryanshine yasani kaduna yana tsaye a matakala yana kallona yake fadin sun tafi ne ko nashiga na watsa ruwa nayi sallah ne yana karasa saukowa yake fadin hakan gareni.
Nima wanka nake sonyi na kwanta na fada ciki ciki don ban dauka zaiji abinda na fada din ba ashe yaji lokacin dana fadi hakan har ya sauko ban ankara ba naji yace ki bari ki danci wani abu sai ki kwanta din.
A kasalance naja gwiwa zuwa kujera kusa dashi na zauna cikin tsigar gajiya yake fadin zakiko iya zaman jirgi zuwa Chaina nan da kaduna kike wanan gajiyan haka na dan bata rai ina fadin ba haka bane kawai dai rabuwan mu dasu baba tun lokacin nake jina wani iri don ban taba nisa dashi haka ba tunda nadawo hannunshi da zama.
Lokacin ya juyo yake fadin da a ina kike zama na dan nisa ina fadin wajen anty safiya ta rasu tun ina da shekara g oma sha uku lokacin na dawo kaduna da zama wajen baba shine dalilin da baba ya kashe dakinsa daya ya gyara min daya nake zaune a ciki don matansa lokacin sunce basu zama dani waini manyace nacinye anty safiya.
Inna lillahi naji ya fada da karfi na dan murmusa na takaici da bakin cikin tuno hakan gareni kafin na dan dara koshi na tsigar bakin ciki ina fadin unguwarmu har sun yarda da hakan da farko sai daga baya dana fara girma suka fahinci sherin mamace akaina.
Wacece mama a cikinsu ya tambaya yana mika hannu yana bude ledan da Abbas din ya aje muna na dago na karba daga hannunshi ina fadin maman su hassana wace sukai jinyan baba a nan Abuja yace wanan marokiyar dama nasani nayi tunanen hakan yadda na dan fahince ta a zamansu duk da ba zama nakeyi ba dasu.
Da matar da miji ke nan duk mun zama mayu a wurin yan gidan mu nima haka su hjy Laila dasu hjynki na saudiya suke fada a kaina wai tsafi nakeyi kudi yana shigo min sun bata min suna kala kala a wajen mutane.
Sunce bana aure ina luwadine don hakane bana son mata sai maza donsu ba aje Samuel a gidanan don kawai su dauka haka din ne da suke tunane wani kazafin ma ban taba jinsa ya kawo gareni ba har yau.
Har da Ummu na tambaya a cikin mamaki yace wacece Ummuh nace hjy saudiya yace eh ba tare take dasu hjy Laila din ba saidai nata da sauki don tunda na girma nake hango nadama a idanunta nine kawai ban yarda da ita a yanzu.
Shiru nayi ina tunane har ya miko min drinks daya tsiyaya yana fadin nasan zasu nemi taimakonki a kaina ta hanyan nuna maki so a garesu daga nan su dauka zasu iya cuta min ta hanyar ki don daman su nagaba ke nan nake hasashe.
Ni kuma yace kwarai zasuso suyi amfani dake wajen cuta min don haka kiyi taka tsatsan dasu duk da banda zargi a kanki yanzu yadda naga kin iya rufe ido kin fita zancen hjy a rayuwanki.
Karba nayi ina fadin wullakanci da rainin wayaune bana so a rayuwana don ina yar tallaka ba zan dauki rainin kowa a kaina ba tunda ba laifi mukaiwa Allah yayimu tallakawa ba.
Nan dai na bashi labarin yadda mukayi a saudiya da ita da yadda muka dawo nida Fadila a karshe ba dadi tun zuwan hjy Laila din wajen bukinsu ya kurbi ruwan lemo yana yagan nama kafin yace sun fi da nan indai sune basa son kowa ya rabesu a rayuwa ai.
Naji dadin hakan wata kila rabonane ya rabaki dasu don da ace kina tare dasu ba zasu taba bari ki aureni ba don ko macen da basu sani ba sukaji ina nema sai sunje sun bata zancen.
Wanan karon da mahaifinki yaki yarda da jita jitansu shine suka aika a kwashe kayan auren daga gidan ku hakan bai masu ba kuma suka tura ayiwasu Ammi fashin dukiyan da gari ya dauka sunzo dashi wanan ma aka gane hakan yanzu bansan shirin da sukeyi a kan mu ba kuma.
Kofin hannuna na aje ina kallonshi kafin nace duk a kan me laifin me mukai masu haka suke son illanta mu yace saboda ni mana don kun yarda zaki aureni keda iyayyen ki.
Mami mutunce daga ita har diyanta sun min kokari a rayuwana yadda bama zan iya saka masu da komai ba a rayuwa saidai addua kadai da zan aika masu .
Fatima ina son ki rike Mami da kowa na Abbas tankar yan uwan da muka fito ciki daya dasu don Allah bana son naji wani matsala ya fito daga gareki
Idan kin min hakan kin gama min komai a rayuwana don Allah ina rokon ki kisan yadda zaki zauna da kowa sirina ya zamo a cikin gidana bani da ra,ayin boyewa mata komai kamar yadda nake fatan kema zaki kasance a gareni.
Insha Allahu na fada bamu tashi wajen ba saida ya tabbatar da cewa na danci wani abu kafin mu shiga dakin na rasa meyasa komai nasa yake a tsare babu shiririta a cikinsa.
Dakin baiyi wani girma na azo a gani ba kodan kayan alatun dake cikinsane ya cika dakin don baikai na kaduna da muka baro ba girma a idona kodana shiga wanka na fara neman yi a lokacin.
Inda nayi sa,a ya dan fita zuwa falo don naji yana waya gashi saukowa ya fice hakan ya ban daman samun sakewa har nayi wanka na fito na danyi shafe shafena bai shigo ba da har na fara tunanen yadda zan tube kaya yana dakin don na fahinci zaman nan tare dashi zamu zauna a daki daya tunda bai kaini wani daki ba na daban.
Na gama daure kaina ina saka hula ya shigo dakin yana fadin har anyi wankan na danyi murmushi don na gane ya fahinceni ina dari dari dashi har yanzu kunyansa nakeyi.
Kince kina jin barci ni kuma hira nake son muyi dake don dare baiyi ba har yanzu goma da rabi yanzu yayi nace me kake son ji kuma labarin maitan da mama ta dafa min yayi murmushi yana kamoni yace ta dafawa kanta dai don itama tana da yaya.
Kwanciya mukayi yana dan jana da hira hannunsa na yawo a jikina sai jin na sake nayi barci ya dan kira sunana yaga da gaske barcin dai nakeji a ranan yayi min kiss a goshi shi kawai zan karas a lokacin na danji na kara narkewa a jikinshi sosai ina shigewa kamar ina jin sanyi.
Sai dare dana falko don in kewaya fitsari naga yadda muke kwance dashi a hankali na zame jikina daga nasa na dan mike cikin sanda don kar yaji motsina ya farka naje na kewaya na fito.
Ina kai kwance naji ya rungumoni cikin jikinshi ashe ya falka a lokacin nan zance ya juya sai da ya biya bukatansa a kaina kafin wani barcin kuma ya dauke mu har ya kaimu ga makara sallah safe a r???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?anan.
Washe gari din bai bari na sauko ba bayan munyi sallah yana makale dani muka koma barci sai sha daya da wani abu shiya fara tashi yayi wanka kafin na tashi jin motsin shi ya fito yana waya yasa na tashi na shiga ban dakin nima.
Ban fito ba saida nayi wanka na goge jikina na fito har lokacin yana shiri zama nayi a gaban mirro ina kokarin shafa mai shi kuma yana zaune bakin gado yana daure takalman daya saka yake fadin .
Ina son in fita saidai ba zan dade ba zan dawo kallonsa nayi ta cikin mirror din ina fadin breakfast fa yace ina aon in koyi karyawa da rana tsakane irin naki da sauri na juyo ina fadin .
Ka rufa min asiri kada ka rame nasan brother na shine mutum na farko da zai fara cina taran hakan a kanka yace na bar masa kai kana rama a tsaye daga shigowana gidan ka.
Shine dan sa idon kuwa in kiba nayi zai fada in kuma yaga akasin hakan saiya fada indai wanan dan bakin ne don shi surutu baya isan sa ko yaushe cikin zuba yake kamar mace.
Koda ya fita na sauko kasa na samu dan anace ya girka abinci ya aje muna ruwan shayi nasha sai Irish da aka soya da kwai na dan zauna falon ina kallo a cikin kadaici.
Don banda kallon sai barci da zanyi tunda ba waya a hannuna lokacin ni kuma ban tambayesa ba don bansan dalilinsa na karban wayana ya rike a wajensa ba ni dai ido nasa masa don ba zan taba tambayansa dalilinsa nayin hakan ba gareni don dole yana da wani manufa akan hakan.
Ina nan zaune ni kaida a falon na kurawa tv ido ina kallo yayin da zuciyana yake tab da tunane kala kala naji bell din kofan na kara alaman wani a wajen gidan yana so shigowa.
Hakan yasa na mike na nufi wajen kofan na bude a hankali wata farar mace ta girme min sosai tare da wasu yan mata biyu a bayanta ne tsaye kofan.
Har suna shawaran komawa a lokacin sai sukaji an bude kofan suka tsaya take fadin har zamu juya mun dauka ba kowa a gidan ne ai nace kuyi hakkuri banji bane da wuri idon yan matan a kaina kur suna kallona.
Ku shigo mana na fada cikin fara,a ina kaucewa a hanya na basu waje suka shigo suna bin ko ina da kallo kafin muka zauna na fara gaida matar saboda ta girmenu sosai a shekaru gaskiya don zatayi sa,an Anty Safiyan mu marigayiya a shekaru.
Bayan mun gaisa take gadin dazun mai gidan nan yake fadawa Alh yayi aure kuna nan kunzo shine Alh yace muzo mu tareki da zuwa na danyi murmushin dake kara min fasali ina fadin nagode Anty.
Ba komai Allah ya bada zaman lafiya na amsa da amin ina murmushi a sanyaye sai mukai shiru ta sake fadin ku mutanen yolane halan ?
Nace a,a mu yan kadunane tace au na zata ai daga yola kike ko bauchi ai na girgiza kai son hakan dabia tace wani lokaci she so beautiful kamar ba yar kasan nan yar babban ta fada.
Uwar tace wanan bakin naki akwai surutun tsiya hasina nace suna mai dadi Hasina tace eh su din yan ukune ai dayan na mijine baya bin mu idan zamu fita irin hakan yana jin shi ya girma yanzu.
Ai gaskiyane kada a ja mai raini a wajen mata kai aida yana kusa da yaji dadi irin hakan yake so a dinga bashi girma ko yaushe shine dadinsa shi.
Ta mike tana fadin tau amarya mun gaisheki zamu koma dama munzo mu gaida kune don bamu da wasu hausawa a layin nan sosai sai gidan barrister Hannatu ita kuma ba zama takeyi ba a kasan ko yaushe.
Sai lokaci lokaci ake ganin gidan bude wani lokaci ma ba ita bace yarantane idan sunzo hutu kasan zasu zauna su kwana biyu a nan din kan su tafin.
Ganin sun mike yasa na daga ina fadin ina zuwa na shiga daki sabulai na dauko masu sai turare wa uwar nafito dashi ina basu hakkuri take fadin ba zasu karba ba su sun shigone kawai don ai zumunci dama.
Nace don Allah a bari su yan biyu su karba yace to angode amma ki daina hakan har ta juya zasu tafi sai kuma ta tsaya tana fadin ni sunana Halima yarana kuma hassan hassana da hassina.
Zaki iya kirana da maman hassina ko hussaina ka bymar yadda ake kirana a nan layin nake fadin nagode kasa kasa yarinyar tayi magana tace wanan Allah ya shiryaki wai baki fada muna sunan kiba ke ?
Na dan kalleta cikin murmushi ina fadin sunana Fatima uwar tace to kunji sunanta Anty Fatima yaran suka dan kalleni kafin suce dani sai an jima nace ina gaida da big brother Hassan .
Zaiji ta fada tana dariya muka fito har haraban gidan dasu take fadin kinga wanan barin daman naku gida na biyu shine namu yaran nan ai najin an kawo amarya suka dameni da zumudin zuwa su gani ko bahaushiyace ke.
Ba wasu hausawa a layin nan sosai sai gidan Barrister Hannatu ita kuma ba mai zama bane tana dadewa tana kasan waje wani lokaci yaranta kanzo hutu nan din sai dai ba wani sabawa mukayi dasu ba.
Allah sarki na kara fadin nagode Anty suka tafi ni kuma na juyo zuwa cikin gida ban zauna ba na dan fara zagaya gidan ina kallo gidane me dakuna hudu da katon falo daya.
Kowani daki yana gyare da gadonsa da komai da zaka sama a sauran dakuna sai sai ta waje dake da dan fili kadan har na kawo kitchen din gidan na shiga shima komai nasa tsab ga katon freezer kwance yana aiki kayan girki na wuta kala kala akwai a kitchen din.
Kofan dana gani cikin kitchen din na tura ashe store ne ga kayan abinci nan kusan duk ciman dan arewa an tanada a store din idona ya sauka a kwalin indomei na karasa na dauko daya na tsaya nan na dafa na fito na zauna ina ci ban dade ba sai gashi ya dawo lokacin.
Yanayin fuskansa kawai zai nuna ma gajiya ko bacin rai a tare dashi lokacin na dago ina mashi sannu da zuwa ya amsa cikin yanayin kasala idonsa akan abincin da nake ci din yana zauna a kusa dani.
Yana kokarin cire necktie din dake wuyanshi yace sai yanzu kike cin abinci fatima ina kokarin mikewa tsaye nake fadin na karya dazun da safe ai na duka ina cire mashi takalman da yake kokarin cirewa lokacin.
Naga ya lumshe ido yana sauke nunfashi tare da mayar da kansa saman makarin kujeran da yake zaune yana fadin nagaji sosai tun fitana ina can ana kokarin visa dinki don suna son su kawo muna delay a cikin zancen.
Nagama cirewa na mike tsaye yake fadin akwai abinda zanci kuwa don ban karya ba tun safe nace ga abinci can mai aikinka ya shirya maka a dinning.
Ya dago ya dan kalli wajen kafin yace shine kuma kikecin wanan flawer ke nace ban son cin mai nauyi ne yasa naga yakai hannunshi saman goshin shi yana dan murzawa a hankali kafin yace.
Kiyi hakkuri idan mun dawo daga tafiya zan sallami Samuel sai dai kuma mami zata turo muna yar aiki tace a tambayeki yarinya ko tsohuwa kike son zama da ita.
Jin hakan yasa na tsaya ina fadin duk wace ta turo mun gode nasan mami ba zata turo wace zamu samu matsala da ita ba OK kawai yace ya kara balance a zaune yana lumshe idanu.
Sama na hau nakai masa takalma da dan jakkarsa na aje na sauko zuwa kasan ina fadin da kaci abinci sai ka watsa ruwa ko zakaji jikin ya dan sakema .
Zan daici abincin amma wanka saida dare zan dan watsa ruwa kafin na kwanta to ka tashi muje in zuba ma na fada bai kiba ya mike daga inda yake zaune din ya biyoni baya lokacin har na bude abincin wanda white rice ne da miyan kaji na danyi murmushi ina mamakin yadda mutum zaici shikafa haka zallah a kullum kuma bai damu ba.
Agaskiya in nice ba zan iya haka ba idan baida abokin hadinci ko sha,awa ba zai bani ba zai fita min ne daga rai don mu sai a gidan mu mun saba ana sarrafashi ta hanyoyi daban daban walau tuwon shinkafa ko jeloup ko shimkafa da wake ko da taliya ko doya ko dankali ko da mai da yaji amma ba fari kal haka ba gaskiya.
Shike cin abinsa nike tunane a zuciyana saida naji muryanshi yana fadin hey na dan dago yake fadin me kike tunane hak zuba min ruwa nace nayi saurin daukan goran ruwan ina tsiyayawa na mika mashi.
Bayan ya gama ne yake fada min cewa sunyi waya da mahaifinsa yana tambayana nake fadin suna lafiya yace kalau suke ya mike ya koma saman kujera ya zauna.
Ledan daya aje a gefenshi ya dauko ina tsaye ina kawar da kayan daya ci abinci ya kirani nazo ya miko min sabuwar waya a cikin kwali yana fadin akwai sim card a ciki sabon layi da zaki dinga amfani dashi wancan naki nada kuma yana cikin aljihun jakar dana dawo dashi in akwai layin da kike son dauka.
Duk a kasalance yake min bayani idonshi a rufe lokacin wani irin runguma da nakai mashi yasashi bude idanun sa dan murmushi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login