Showing 135001 words to 138000 words out of 347556 words

Chapter 46 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8775

shigowa dakin tace Bantu naji kina nemana mama ta dauko shirme tana fadi don Allah kiyi hakkuri da halin mama tunda kin saba dashi yanzu ai.
Dama kayan nan nace ko zaki duba idan akwai wanda kike so a ciki saiki dauka wanda bakiso kuma sai in bawasu haule can kasa.
Wace haule don Allah nuna min ni in kwashi abu mun gode Allah ya kara budi mukan ai mun gode wallahi kingani ko arziki na kiran mu tana son muna bukulu ta hanamu samu.
Gasu nan na nuna mata tace me don Allah ki bari wa yan nan sabbin kayan haka batu aiko mun gode wallahi shi nake fadawa Ussaina jiya da dare wallahi in tana fita haukan su mama mu zauna lafiya ta fita.
Ta dade tana son sayen da tawul takasa sai gashi jiya mun samu dakin mu har uku a sana dinki kuma meyafi hakan dadi don Allah yanzun kuma ga wanan.
Haka dai ta fita dauke da kayan a hannunta zuwa dakinsu ina jin baba ya fito yana gyaran murya nayi but na fito daga dakin tun daga kofana nace baba ina kwana ya amsa yana juyowa gareni.
Fadimatu an tashi lafiya na amsa da lafiya kalau baba ya kasuwa yace Alhamdullahi baba yau zan tafi dama kai nake jiran ka fito in sallameka.
Wani kallon mamaki yayi min lokaci guda kafin yace fadimatu kin karyane da zakibi hanya yanzu baba ba yanzu zan karya ba sai na isa can na fada.
Kallon mama uwa yayi dake tsaye kofanta yace anyi wani abin ke nan kuma ko tace za a rasane da ita dasu Lantone da samira kan kayan bukin da suka rakata jiyan da suka dawo shine Bintu ta raba muna abinda suka samo a can samira ta fito tana fada da ita wai don me zatayi hakan.
Ai kaji matsalan idan kana abu ka hada harda yaro ka koya mashi halin banza banda haukan yarinta irin naku ina uwayen ku taba abin nan bana wani ba.
Yaja tsuki yana fadin kada ki tafi haka sai kin karya nace to baba na mike na shiga dakina saida aka gama koko kamar yadda baba din yace na dan kurba sanan nabi hanya.
Na isa zaria da wuri sai ganina gwaggo tayi kwatsan na fado bayan mun gaisa Aliyu almajiri ya shiga min da kaya dakinmu tare dashi muka gyara dakin yadda nake son shi ya koma neat na zuba kamshi na koma saman katifa na kwanta in huta sai barci.
Ban farka ba sai wajajen karfe uku na fito na debe ruwa na watsa a jikina na dauro alwala nazo na tayar da sallah muryan Aliyu naji yana tambayan abinci gwaggo ke fadin .
Na fadama ban samu girka komai ba da ranan nan saida dare murya nasa na kira yaron yazo na bude pos dina na ciro two thousands na mika mashi nace ka dauki babban kulan nan kaje can wurin shagon abinci kace a hadama na duka yace to ya karba ya fita lokacin na fito waje.
Nace gwaggo doyane a cikin buhun nan ga kuma manja da dankali a karamin buhun nan a hanya da zan dawo na sayo ranan a hanya tace kai maddala .
Da wanan alherin kamar kinsan dan shimkafan daya rage nake dan tatalinsa kada ya kare yasa na daina dahuwan rana yanzu gidan.
Haba gwaggo ai abin daga Allah ne yadda muka samu wanan haka Allah zai kawo muna mafita nan gaba kuma insha Allahu ta karasa min zancena dashi.
Sallaman Aliyuce ra katse muna zancen nace har ka dawo yace eh sunce wai tuwo nace a,a su ban dai shinkafa da miya mai hadi sai ya dan ban dariya nace kawo roban ka in zubama naka kayi ka tafi kada a zauna karatu baka.
Kusan rabi na juyewa yaron na dan kyafaci kadan nace ka mikawa gwaggo wanan bai iya boye murnan shi ba ya kai mata ya zauna nan yana cin nasa gwaggoma budewa tayi ta fara ci muna hira.
Aliyu idan ka karasa ka juye wanan buhun kada zafi yayiwa doyan nan yawa sai ka juye wacan dayanma a kasa yana gamawa ya dauki ruwan pure water daya ya zuge ya nufi wurin buhun.
Ba laifi doyan yana da kyau sosai don manyane hakama dankalin tana faman saka albarka nace Aliyu da ace yau baka karatu ai da munje kasuwa dakai munyi sayayya.
Yace gobe zan fadawa malam sai mu tafi yagama kwashe doyan ya tafi makaranta ni kuma na shiga don nayi sallah la,asar don an kira na bayan na idar na fito na fara aikin gyaran gida tare da dora girki.
Gwaggo na fitowa take fadin yaron nan dai kwana biyu baizo nan ba nace wani yaro ke nan gwaggo ?
Tace wanan mai abin arzikin nan tun kan kiyi tafiyan nan rabonshi da gidan nan ai a lisaafina wai soja kike nufi gwaggo na tambaya ?
Shifa sai na canza fuska tare da fadin yana nan mun hadu dashi dana dawo din nan baya zamaneshi sosai ko yaushe suna tafiye tafiyene ai.
Yaron akwai kirki sosai da mutunci na tare da fadin gwaggo ashe yana da aure fa ban sani ba aure to yar nan in baki sani ba aishi ya sani kuma yake sonki hakan .
Kada ki soma irin wanan ra,ayin sai wanda baida mata a rayuwanki irin hakan kana barwa Allah zabine ya zabama abinda yafi zama alheri a gareka ai.
Niko wanan da uwarku take hauka a kansa ai don naga bakyasone yasa na kyale da kina ra,ayin hakan suwaiban me can ita ta isa ta hana abinda Allah ya halastane ?
Gwaggo bar zancen wanan don abin ya koma hauka yanzu wai ashe samira ya koma nema a yanzu ga kuma ita mama tace hassana zata bashi ya aura.
Ba,a sanda zancen samira ba nan dai na kwashe yadda akayi na bata labari ranan yan gidanmu sunsha zari da zagi a wajen gwaggo sosai ranan.
Ta juya kaina tana fara fada tana fadin aiko don yan banzan nan ba zakiki wanan sojan ba don da alama yana da dan rufin asirin shi don haka indai yazo kada ki gujeshi don yana da mata.
Shiru nayi ban iya magana ba doni tunanena daban a lokacin ba komai nake tunane ba sai yadda naga matanshi da alaman koshi yana tsoronta yadda naji tana bayani da kuma dan fahintar danayi a kansu.
Gwaggo tayi faman mita akan Samira da mamanta inda ta nuna laifin na mahaifiyartane duk bamu bar wajen ba sai magariba.
Washe gari Monday na shiga school duk da dalibaine amma ni kaina saidana tsargu don yawan nunanin da sukeyi kan wana dan tallan systems din da nayi akan amfaninshi ga mutum mussanman dalibai .
Department din mu ko ina shiga suka fara bayani yadda nayi din yasa na dan murmusa kafin wani yace dani ke baki dan jona mu muma mu samu shiga na fada maku duk boyon take muna tun farko amma ita din babbace fa.
Shigowan lectural ajin yasa kowa natsuwa bayani yake muna inda masu system suka bude nasu suka fara dubawa suma hakan yasa na jawo nawa da ba kowa yasan ina dashi ba nayo searching din abinda lectural yake koyarwa a lokacin.
Sai karfe hudu na samu nabar makaranta na isa gida kuma na samu kuma Aliyu almajiri yana zaunen yana dakon dawona gida a lokaci muje kasuwa ban samu hutawa ba haka muka kama hanya zuwa kasuwa dashi.
Na dan sayo abin amfanina dana amfanin gida da shi kanshi Aliyun na saya mashi dan sutura don tun wanda yazo dasu yake faman ja har wanan lokacin kuma sun kode sosai.
Mun dawo ana batun sallah magariba don haka ban tsaya ba na nemi buta na kewaya ina fitowa na fara alwala mijin gwaggna yashigo gidan dawowanshi ke nan daga kasuwa.
Nayi mai sannu da zuwa ya amsa ya nufi dakinsu nikan nayi alwalana nashige daki ina ciki naji dawowan Aliyu nasa mashi kira ya shigo dakin .
Duk wani abu dana sayo donshi na cire na mika mashi nace wanan nakane wanan kuma ka aje minshi a can na nuna mai inda zai ajemin kayan nawa na gida kuma nace yakai kofa gwaggo ya aje mata.
Yana fita ina jin wani yaro na kwada sallama wai ance ana sallama da fatima Aliyune ke tambayan waye jekace ance waye ?
Lokacin gwaggo ta leko tana fadin kai dan duniya kai akace ana nema daka sharbe zancen harda cewa aje a tambayo maka.
Halinshine fadin yi hakkuri hjy yana aje kayan dana aikeshi dasu din gefen kofan dakin nata yaron ya dawo yana fadin ance wai Mohammed ibn Sa,id ne .
Kai Aliyu na fada jin sun kyale yaron ba amsa tunda gwaggo ta hanashi Aliyun magana nace jekace na kwanta kaina ke ciwo.
Ya fita da sauri don zafin jikin tsiya gareshi yaje yace anty tace ta kwanta kanta na mata ciwo murmushi yayi yana fadin itace tace ka fada min hakan ko wani ?
Yace itace ta aikoni yaron ya fada, jekace nace ta fito ta amshi magani yanzun nan zata daina jin komai sai gashi ya shigo har kofana yana fadin anty na amsa daga cikin dakin .
Yace wai yace kizo ki karbi magani ciwon kanki ya warke jekace nasha naji sauki barci nakeyi yanzu din bai jima da fita ba sai gashi ya dawo yana fadin anty wai yace gashi nan shigowa ya dubaki.
Na zabura nace ina don nasan zai iya sarai ban ko tsaya shirin komai ba na saka takalma na fita zuwa wajen yana tsaye ya fito daga cikin motan yana kallon wayanshi.
Yana jin motsin bude gida ya dago kai nice tafe yace ai da ki tsaya nazo dabaki wahal da kanki ba nashigo na dubakini .
Don ba zanyi tafiyan banza daga kaduna zuwa zaria ba kuma in koma hakana lafiya dai malam kake bibiyata haka ka kuma na fadama banda lafiya ina kwance.
Shiyasa nima ai nace aimin izzini wurin tsohuwa na shigo na duba babyn tawa sai kuma gaki kin taso ko yaron ne bai fadi sakon nawa daidai ba.
Dakata malam ni yanzu an shani na warke yace da kyau nace eh don yanzu na daina yarda kowa balle a yaudarani, don shine na daina yarda dakiwa akaina. Don haka don Allah fadi abinda kake nema a wajena ka tafi malam ina son shiga in kwanta kaina ciwo yake min wallahi.
Sorry baby waya shaki haka kika warke fada min kowaye yau din nan basai gobe ba in tafi in harbe maki shi yana tura hannu a aljihun wandonshi na baya ya ciro wata yar bindiga karama yana wani huci.
Au kanka zaka harba ke nan ai sai ,saika gwada mu gani kaban mamaki kwarai wallahi daka zo min da tsigar yaudara alhali kana da mata ashe baka fada min ba tun farko ?
Babyna kanki daya kuwa don ina da mata and so what ko hakan ya sabawa addinin kine baki tsayi da mai mata ?
And saboda ina da mata sai akace kada inyi magana da kowa kome ya kura min idonshi da sukai ja lokaci guda.
Ganin hakan na bishi da wani irin kallo yace yes kece ma kika ban mamaki bani ba a yanzu don wanan maganan da kikayi ya sabawa addini da kuma al,adan malam bahaushe.
Dama basona kike ba ke nan tunda tunda kin dauka banda mata ko somethings like that har kika iya fada min hakan kai tsaye.
Don hakan kin bam maki kwarai da kaske wallahi ni banzo nan da wata mumunan manufa ba a gareki.
Don banyi karyan cewa ni din banda mataba alhalin inada ita, asalima ga bakina kika fara ji zancen matana ba a wani ba don haka meye na mamakina a yanzu ?
Bana karya ko yaudaran mutum tunda nake zuwa nan wani zance daya shafi rayuwata ko iyalina haka mai zurfi bamu taba yinshi dake ba .
OK is enough hakan ya isa yanzun na fahinta amma don Allah ka barni in huta hakana please ohh har kin fara korata ke nan ?
Banyi mamakin hakan ba da sauri a gareki duba da yadda yanzun kika fara wasa da dolar a hannun ki don haka zaki iya yin abinda yafi hakan ma a yanzu ai.
Dakata malam a dakace nake malama don ke nake saurare saboda wanan hujan da kika kawo yanzu gareni ba mai kwari bace don nasan kedin dai yar musulmaice kamana .
Don haka munsan me addini mu ya sharada akan mu mun kuma san abinda ya hanemu dashi kada mu aikata saboda haka ki natsu ki fahinceni.
Idan ka gama ni zan koma na fadama banda lokaci yanzu don kaina ke min ciwo na fada ina kawarda kaina gefe daya .
Sai naji yace yaron bai fada maki abinda na fada mai bane dana aikeshi aina dauka maganin kikazo karba yanzu ?
Juyawa nayi a fusace don ban iya wanan wasa kwakwalwan tasa daya saba min don yanzu gaba daya haushinsa ma nake ji sabanin da dayakan zo musha dariya .
Har in baizo ba ni zan nemeshi a waya inji lafiyan shi mu dan taba hira muyi sallama da juna sai yau na tsunci kaina sam ban son ganin shima ga baki daya.
Wanan menake nufi ina kishin shine ke nan ko kuwa dai don banson shi yanzu nayi hakan nida kaina na tambayi zuciyana wanan maganan.
Nakuma ba kaina amsa da don yana da mata zancen gwaggo ya fado min a raina muryan Aliyune ashe bai tafi ba yana waje ya zauna idona ya rufe ban ganshi lokacin.
Fadi yake anty in shigo gashi yace in kawo maki ya karasa shigowa da ledan kayan cikin dakin.
Nabishi da kallo har ya aje ya koma da sauri sai gashi da wani jin hakan yasa na mike na kara fita lokacin yana ribas da motarshi zai bar kofan gidan ke nan ya ganni amma hakan baisa ya tsaya ba sai horn daya min da mota yatafi ya barni a wajen tsaye.
Koda na koma daki sai na samu wayana tana haske alaman an kirani ko wani sako ya shigo min daukan wayan nayi na duba sakone daga gareshi na bude na fara karantawa.
Baby kin ban mamaki ban taba zaton hakan daga gareki ba na dauka zaki fahinceni amma naga kin min fahinta da wani manufa nagode.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
4?? 2??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Soja ga wuta ga harbi ran maza ya baci don ni dai har lokacin ban gane nufin shi a kaina ba ga kuma uban sayayya da yai min na gani na fada.
Mazan yanzu suna bada gudun mawar bata tarbiyan mata ta hanyan nuna bajintansu garesu zaka san mace ba yar kowa bace amma ka dinga kashe mata kudi kan abinda kasan gidansu bata amfani dashi wai duk hakan burgewane a wajansu.
Suko iyayye ana kawowa suna farin ciki suna karba akan gani sa,ane ko baiwa hakan a garesu sam ban san hakan bane sai lokacin da na shigo gida na samu gwaggo da Aliyu suna zancen kayan daya kawo min tana washe baki sai hakan ya ban mamaki.
Badon komai sai bayanin da mukayi da ita a kan sojan ke nan dai koda ba zaje a zauna lafiya ba indai soshi hakana ko zaman banzane muyi dashi ba abin damuwa bane hakan .
Ban tsaya ba na shige dakin ban kara lekowa ba don nasan zaman da tayi na jiran ince gashine ko zargina kantane hakan don naji haushin kowa a ranan oho ?
To me yake nufi a kaina shi dai ban taba jin zancen aure a bakinshi ba haka kuma yanzun ma din da muka rabu babu wani zance daya furta wanda ya shafi ai zan aurekine ke ma balle in dan ji dadi a zuciyana game dashi.
Ban fito ba sai washe gari da zan tafi school najawo kofa na rufe na fara gaida ita kafin na sallameta nafice kafinma ta fito daga dakin duk da nasan ba tana haka bane don bata kaunata ko wani abu agareni amma dai a dan fahintana shine.
Tunda yanzu na dauketa uwa ya kamata tana sakani a hanya madaidaiciya a rayuwata ba komai nayi ta saka min ido ba irin yadda take min din sai idan maza sun bani ta karbe.
Wanan rayuwan shike damun Samira a yanzu ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login