Showing 213001 words to 216000 words out of 347556 words

Chapter 72 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8774

aiba tafiya zanyi ba gaba daya zan dinga zuwa ya hakkura.
Saidai yace daya gama kaduna zai biyoni ba zai zauna zaria ba tunda ya sauka a lokacin a haka muka rabu dashi da kuka da komai har ita gwaggo din ta rakani da fatan alheri tare da kara jadda min cewa duk abinda na gani na dinga kira ina sanar da ita halin da ake ciki a nan kaduna.
Service zan tafi yanzu abinda nake jira ke nan jiran zaman saka mako a lokacin yasa na yanke wa kaina shawaran fara dan wani abinda zan rage zaman kawai duk da kudina har yanzu suna shigo min na contract dina na talla a company digital da nayi signing dasu na shekara biyar.
Matsala dai shine sun dakatar da talla din wanda ni bansan dalilin hakan ba amma kudina cas suke shigo min ko wani karshen wata a account dina.
Zaman gida ba dadi amma ya mutum zaiyi ina tsare kaina da kama mutuncina a haka wani yammaci na samu baba a waje shi kadai na zauna muna hira dashi na jefo masa tambayan daya dukar da kai yana tunane.
Don cewa nayi dashi baba nikan mahaifiyata wai yar wace garine don ina son inje inda take banson har Allah ya kawo min miji ba tare da nasan taka maiman inda take ba koda bata raye insan yan uwanta.
Shine sai naga baba ya dukar da kansa kasa yayi shiru na dan lokaci kafin ya dago ya dan kalleni yace zamu maganan dakw nan gaba kadan din hango baba mai mota da yayi tafe lokacin.
Nayi mamakin ganin yadda yanayin baba din ya sauya lokaci guda don tambayan danayi masa din na mahaifiya wanan re,action din dana gani a fuskan baba ya dan jefani cikin damu kwana biyu.
Wanan yasa na dan tuntubi mama uwa ranan nace waini mama mahaifiyana asalin yar inace ita dasu waye ta zauna a garin nan har baba ya ganta ya auretane.
Kallon mamaki naga mama tayi kafin tace ke ba wanda ya taba fada maki komai ne game da mahaifiyarki dama don ni gaskiya lokacin bawai wani shiri mukeyi da kowa a gidan nab ba.
Ban damu da sai nasan komai dake wakana agidaba ma amma dai a yadda naji suna fada cewa su yan gudun hijiane suka shigo nan nageria a lokacin don har yanzu sunan wurin na yan gudun hijara Somalia.
Tana sana,an abinci a nan suka hadu da malam har sukai aure daga baya kuma sai yan uwanta suka koma suka barta a nan lokacin tana da shigar cikin ki .
Lokacin nan malam yana tashe sosai na kudi don aiki ya kawoshi garin nan daga sokoto zuwa wanni lokacin kuma da zaman kaduna yayi dadi har ya zauna zama na dindindin a nan bai koma gida ba .
Yasai gida nan don a lokacin shi mai haline sosai a garin nan saboda sana,a daya fara dukshi ke dauko kaya a wajensu yana rabawa yan uwa idan an sayar a bashi kudi ya hada ya dauko wani.
Don gaskiya aurenshi da mahaifiyarki akwai falala sosai a tsakaninsu don arzikinsu ya hadu akasin da aka fara samu shine wani haihuwa da ita yaya tayi bayan sunyi arba,in ne mahaifiyarki ta goya yaron a hannunta zazzabi mai karfi ya kama yaron ashe ciwon ajaline ya kamashi don yaron ya fito da ciwon nimoniya ba a sani ba.
Tun wanan karon yaya ta dorawa mahaifiyarki kafa a gidan nan tana cewa itace ta kamawa danta kurwa tunda lafiya ta mika matashi da akai masa wanka.
Wanan zancen idan ba yanzu ta daidainashi ba zakiji tana kiranku da zurian mayu tana jifanki dashi harke dako lokacin bakizo duniya ba amma ke kika koma a madadin mahaifiyarki da bata nan.
Daga waje aka kira mama tazo an kawo kayan cefane ta fita zuwa dubawa wanan ya katse muna hiran mu nayi mamakin jin cewa wai ada can baya baba yayi kudi sosai da har zai iya daukowa layinsu kaf kaya su sara a wajensa.
A haka ina dan buga bugana har zuwa cam din mu yazo inda aka turani Fatakwal hakan ya bata min rai sosai nayi kokarin samun canji akace sai dai daga baya kan.
Ban taba saka rai zan koma wanan kasan ba sai gashi da rana tsaka tafiya can ya kamani ba yadda na iya don baba yace sai in sauka a wajen Samira dole idan naje.
Ban dauki kaya da yawa ba ga tafiyan don nasan banda lokacin sakasu a can tunda cam zan shiga don haka no need in dauki wasu kaya masu yawa.
Don kada naki zuwa a gabana baba yai waya da ya habibi yana sanar mashi da zuwana ranan da zan tafi mama Lanto da dan sakonta zuwa ga yarta dake can ta bani.
Ban isa ba sai da dare muka sauka waima a cikin motar tayi sauri ke nan lokacin dole dana isa na kirashi da layina cewa na iso don yazo ya daukeni.
Yace bai gari amma ga yaronsa nan zuwa ya daukeni zuwa gidan nasa bayan kamar rabin awa sai gashi ya iso yayi saurin ganeni don shigar musulmai dake jikina a lokacin.
Aahe bai fadawa Samira zancen zuwana ba sai ganina tayi kwatsam a cikin dare nayi sallama lokacin dana shiga wasilace da yarta a falon zaune suna cin abinci ga tv a kunne suna kallo.
Ta dago kai tana kallona da alama dai bata shedani ba a lokacin wanda ya kawonine ya karasa shigo min da yar troler dina cikin gidan yana fadin wajen amarya naza daga arewa
Tana jin hakan ta kawar da kanta da sauri sai naji yace dani ga kofan part dinta can wasila din ta dago tana fadin dama yasan inda zai kaita ya tsaya mata magana don rainin wayau.
Har na fara tafiya na juyo na tsaya nace a ciki waye dan rainin wayau dashi dake ke wata irin mace ce da baki san musulunci ba ko har abin naki yakai haka yanzu ?
Muryana ta dago sai naji ta kwashe da dariya tace wai dama kece ashe ban ganeki ba kin kara zama wata big gurl ayanzu ?
Ke kema anzo a kara dakene mu cika ukku don naga kun mayar da gidan nasa nagadon ku kuba kunyane daku ba.
Murmushin takaici na sake nace dadin abindai ramin mu macijiyar ta shigo bamu mukayi kwadayin ramin taba dai don kowa yasan ramin mune wanan.
Gida namune sai kuma yadda mukeso zamuyi a cikinsa ba na juya na tafi a daidai lokacin samira har takawo kofa tayi tsaye tana min kallo a cikin mamaki.
Sai kuma ta dan murmusa tana tafa hannayenta waje daya tace wai Bantuce nake gani nan ko mafalki nake yine wai don abin ya ban mamaki wallahi.
Kallon yanayin data canza nake mata nace nice dai ba mafalki kikeyi ba wai dama ya habibi bai fada maki ina tafe ba don baba ya kirashi tun ranan tuesday da cewa zanzo.
Muryan Wasila ya katsemu da take fadi har kofan Samira a shirye nake da zuwanki dama kece aka gaiyato kizo kici min mutunci kallona samira tayi da hannu tayi min alaman tambaya dawa take ?
Ni don da shigowana taso ta karanta min hauka na tayata dorawa kanta sabon hauka dan dariya Samira din tayi tana fadin dama kar tasan kar keda ita ai ?
Tambayana take me nazoyi na dan kalleta ina fadin ke baki san zamu shiga camp bane ranan wanan monday mai zuwa da sauri ta kalleni tace wai kina nufin har kin hada karatun ki ke nan kome ?
Wanda yaje cam aiya gama insha Allah sai kuma adduan samun aiki a take naga yanayinta ya canza lokaci guda ta dan fuske ta dan shiga dogon tunane kafin tace dani .
Gashi babu wani abinci don ban girka komai ba da yamman nan nace kada ki damu ko kin mantane da halina ko akwai ba zan iya cin abinci yanzu ba nikan saidai nasha abu mai dan ruwa na bata amsa.
Nace wanka kawai zanyi yanzu inyi sallolin dake kaina in kwanta take fadin ga bayi nan ki shiga nasan halin Samira dayiwa mutum bincike don haka na sakawa jakkata security na shiga bayin don inyi wanka .
Haba dai Samira kan badai kazanta ba don ban iya yin wanka ba saida na wanke bayin nan tas don ga komai nan kan na wanke bayi a gidan.
Ina fitowa daga wankane wanan daya daukoni ya shigo da ledejuji a hannun sa yana fadin gashi aba baku ina daga ciki ina jinsu tana fadin bakuwa ta gode.
Tashigo dashi lokacin har na tayar da sallah don shike a zuciyana saida na rama sallolin dake kaina a lokacin tana zaune sai dakalan wayanta takeyi a lokacin ganin na idar yasa tace gashi nan akace a kawo maki.
Mefa na tambaya ina dan waigowa inda take sai na hango ledoji a gefenta ta aje ban kula ba na juya naci gaba da addua saboda yanayin ta gaba daya ya canza wanda ban san dalilin hakan ba.
Ko akan zuwanane ko kuma zancen karatun da mukayine ya bata mata lokacin dole dai akwai wani abinda ya tabi zuciyanta a yanzu fita tayi zuwa kitchen kafin ta dawo nashafa namike na kalli gadon baida wani gyara nake fara kakabeshi sai gata.
Au wai fa so nake inzo in gyara yanzu banyi magana ba saida nagama gyara taga kwanciya zanyi a lokacin take fadin ga abinfa bakici ba naga zaki kwanta kuma ?.
Ban iya cin komai a lokacin nan nagaji sosai wallahi na dade rabona da irin wanan tafiyan bina tayi da kallo na gyara tsab na kwanta sai naji wayanta yana kara ta dauka da sauri da yake a kusa dani take zaune sai naji tana fadin yakawo.
Amma ta kwanta wai tagaji bata iya cin komai muryan shi naji kamar me fada ashe cewa yayi ke wata irin doluwace wai ya zaki barta ta kwanta hakana da yunwa ?
To bata zanyi dole taci yace idan kika kuskura kika bata min sunan gida wajen sakarci zamu hadu wallahi ki bata waya muyi magana da ita sai naga ta miko min wayan rai bace na kalleta .
Yace na baki wayan na dan kalleta na karba yace ke fatima ya zaki kwanta da yunwa haka ki tashi kici abinci kafin ki kwanta nasan ba zasu girka a gida har ki samu ba yasa nace yaje ya hado maki take away.
Nagode yaya na fada a ladabce ya lumshe ido yana fadin ba matsala don Allah kada ki kwanta da yunwa wani abu yazo ya sameki zuwa safe zan dawo ina Makodi wajen meeting yanzu.
Allah ya dawo dakai lafiya ya amsa da amin na mika mata wayan ina juyawa bansan meya fada ba naji taja tsuki bayan ta kashe wayan .
Samira na ambaci sunan ta ta juyo nake fadin zaman nan naku gidan nan kamar akwai matsala don zuwan nan nawa na hango abubuwa da dama a cikin gidan nan.
Kada ki cuci kanki ki hana rayuwan ki da zuciyarki sauki a lamarin duniya duk da bansan ya kuke zama ba kece dai zan dorwa laifin a yanzu tunda kece nawa a nan dole jn fada maki inda matsalan naki yake.
Nasan yaya mijinkine a yanzu amma duk yadda kika sanshi nafiki sanin halinsu tun farko donshi mutum ne na farko da baison kazanta ga alaman hakan nagani tun yanzu wajen ki.
Wani kallo tayi min nace yes kina da matsala tun farko ya kamata ki fahinci waye mijin ki meyake so meye baya so meye matsala da yasa ya kara aure da abinda yake hadaku a yanzu dashi ?
Bantu ba zan boye maki ba ni wallahi nayi dana sanin yin wanan auren a yanzu don sam yaya ashe baida hali ba mutumin kirki ba a boye baisan darajan mace ba balle tausayi.
Da sauri na katseta da fadin a,a samira kada kice hakan nina san yaya ba me ra,ayin tara mata biyu bane dole yana da dalili nasanshi fa sosai kema kin sani.
Look samira ki kodewa Allah da nice nazo na sameki a haka daba wanine a gidan mu yazo ba don dai nikan ba wanda zai taba jin komai a bakina kema kin sani don haka muyi magana dake irin ta yan uwa ciki daya ba boyo tsakani a yanzu.
Nafazo na sameki a haka kuma kina amarya hakan maigida zai dawo ya sameki cikin wanan kayan saboda Allah ko uwayen mu da girma ya kama ai kina gani duk wace keda girki tana iya kokarin ta ranan wajem gyaran jiki gida kula da hakkin kowa a gida.
Dolefa sai kin kula da hakan ni nasan Wasila na kuma sanki kada ki mayar da kanki daya da ita har hakan ya dinga jawo maku matsala tun yanzu da mijinki.
Gari ya waye da dakinki zaki fara kina gamawa ki koma nasa kin dora girki kafin ki idar kin gyaro masa daki tunda sammakon fita yakeyi shi saidai idan ya bari a yanzu.
Kin gama kin hada mai ruwan wanka kin koma falo inda zai zauna kin gyara kafin ya tashi ya gama abinda yakeyi kinyi wanka kin fito don ki bashi abinci ki tuna kina da kishiyafa samira duk wanan sanyin jikin ya kamata ki barshi.
Idan ki biyewa waya sai ki kashe auren ki ga banza ki koma gida ku dora inda kuka tsaya da mama don ba fasawa za,ayi ba ya fita ki kwashe kayan ki gyara wuri ki dan taba wasu aiyukan kafin ki kwanta don Allah fada min ina za a samu matsala a nan dake da mijin ki ?
Yamma yayi tashi ki dora masa girki ki kara gyara gidan ko baida gyara ki gyara don saukin kanki don gobe kin gama kin caba adom ki gudun kada ya dawo maki girshi a gidan ya sameki kaca kaca samira ya dawo ki tari mijinki cikin haba haba ki kula ki tausaya kina jero masa sannu .
Nasan komai hutsancin shi dai dole ya amsa gaisuwan ki amma kin zauna kina biyewa wanan mara addini kun zama daya ta ina zakiji dadin ahi ki fada min ji bandakin ki fa samira baki gyara ba balle nasa daki baki gyara ba balle nasa kinsawa sonki son jiki kina manne da waya ko wani lokaci haba don Allah.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
6?? 8??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Fili Jirgin Nnadi ezekuwai dake Lagos wanda yafi ko wani filin jirgi girma a kasan Nageria jirgi daya sauka tab da bakin turai wasu daga nan gaba sukayi wasu kuma iya nan zasu tsaya su karasa wasu jahohin cikin Nageria din.
A hankali ya sauko yana gajiye sosai ba abinda yake so a lokacin sai hutu dan dakatawa yayi saman matakalan jirgin yana bin ko ina da dan kallo kafin ya huro iska daga bakinshi ya furzar yaci gaba da tafiya a cikin tako irin na kasaita.
Bai riko komai a hannunsa ba sai yar karamar jakkarsa da Laptop dinsa da wasu yan takardu duk abinda ya sayo suna cikin kayansu na company ya saka dama hakan yake tafiyashi.
Tun daga nisa ya hango Abbas da Yusuf da sukazo taronsa sukaiwa juna hannu ya samu ya karasa iya inda yan taro zasu iya tsayawa suka gaisa tare da kama masa yar karamar jakkat tasa suka dunguma zuwa wajen da motarsu take.
Kafin jirgin Abuja ya tashi zaiga company su na nan Lagos akwai abinda zai danyi a nan din don haka suka shiga gari kamar yadda suka tsarayi.
Sungama komai a ranan suka bar lagos zuwa Abuja suka sauka shadayan dare don haka ba kowa yasan da dawowanshi ba lokacin.
Kwanan shi biyu yana hutu a gida kafin ya nufi kaduna don akwai wani abinda zai kaishi can din daga nan kuma ya wuce zuwa gida ya duba mahaifinshi daya danji jiki bayan tafiyanshi.
Babu zancen ya kwana gidan mahaifin nasa ko gidan wani dan uwa suma kaf dinsu sunsan da wanan zancen tunda ko ruwan garin ya kaura da dandanashi shekaru da dama robonshi da hakan.
Tun bayan faruwan ala,amarin daya daga masa hankali har ya bar gidan mahaifin nasa a lokacin tun wanan lokacin saida dalili mai karfi yake zuwa garima ga baki dayansa.
Hakama yan uwa a yanzu sungaji sun yafeshi a cikin dangi don ba ruwansa da kowa saidai can ba,a rasa ba suga aike da za,ace daga garesane ya aiko a rabawa dangi din daga hannun mahaifinshi.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login