Showing 153001 words to 156000 words out of 347556 words

Chapter 52 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8800

Don dan shiga Abujan da nayi na kwana biyun da nakeyi hakan ya haska min rayuwana sosai don yanzu dan kauyancin da nake dashi ya dan rage min .
Sallah nafito na tayar tare da addu,oina na neman tsari ga ko wani abunki da zai iya cutawa rayuwata wanda na sani da wanda ban sani ba a rayuwana.
Aka kira sallah na mike na gabatar ban yarda na kara kwantawa ba wuri na haskawa na dan mike na fara gyara dakin nawa kafin in fito don zuwa kitchen .
Babu wanda zance ya fito a lokacin don ko kitchen din a rufe na sameshi ina dan turawa sai ya bude na shiga kayan abinci kan akwaishi irin nasu na larabawa dama irin namu na gida najeriya yawancin abincin hausawa duk akwaishi a cikin store din katon kitchen din gidan.
Nan na dan tsaya ina tunane abinyi kafin dabara ya fado min cikin dan lokaci nayi tunanen in hada wani abinci hausawa local food da mukeci a gida wanda ba zasu damu dashi ba a nan.
Sauri sauri nake aikin nan da nan gidan ya dauki kamshin soyan kosai da kokon dana hada irin na gargajiya nagama zuzuba cikin manyan warmers din dake a wani waje na daban aje.
Nagama komai na gyara kitchen din na kusa gamawa lokacin masu aikin nan dayan su ta shigo tana kallona da mamaki tana magana cikin larabci kafin ta fara bubude kulolin tana washe baki ganin yadda na hada abincin tsab.
Kaita fara kadawa cikin mamaki da yabawa naci gaba da gyaran da nakeyi din har nagama na fito na koma dakin na shiga wanka nayi na dauko dayan rigan danazo dashi na saka a jikina.
Banyi wani kwalliya a fuskana ba tunda nasan ba fita zanyi ba lokacin kofan dakin aka turo mamace maigidan ta shigo tana fadin


ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
4?? 7??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Mamana da zuwanki kikai wanan uban aikin haka bakiko huta ba a raina nace wani hutu zanyi tunda abinda ya hadani daku ke nan har kauna da alheri haka ya shigo tsakanin mu.
Sannu da kokari idan kin hada sai mu hadu a falo a ci abinci nace ba yanzu zan karya ba mama sai zuwa anjima.
Kallona tayi da mamaki kafin tace ai kya danzo ko bakici sosai ba a zauna tare dake a san juna duk da dai mafi yawansu ai kunsan juna dasu a baya.
Na gyara tsayi ina dago kai na gyada alaman hakane ta juya zata fita tana fadin ki karasa shiryawa ki fito muna falo ban fito ba saida na kara gyara jikina tsab.
Su biyar na samu a falon zaune da alama kamar jiran fitowana sukeyi kawai a lokacin da sallama na karaso inda suke zaune din lokaci daya suka dago kai suna kallona tare da amsa min sallaman nawa kuma.
Ina kwana nayi masu a lokacin da mama ke fadin inzo in zauna a wajen kusa da ita haka yasa a kunyace na zagayo na zauna inda ta nuna mindin.
Ba abinda ke ban mamaki sai yadda suke hausansu a can da naji su Al,amin nayi a lokacin na dauka dai wayewane kawai yasa suka mayar da harshensu hakana.
Sai gashi har tsofin matan nan masu aikinsu suma haka harshensu yake idan suna hausa yanzu ma hakan dana zauna shi na tare da mama din suke min na azon lafiya ya hanya ina amsawa.
Kofi suka miko min kafin a fara zuba min kunun dana dama din a ciki haka kuma ta aje plate a gefena zata fara loda min kosai da sauri nace daya ya isa mama.
Haka muka sha muna gamawa aka kawo wani ruwa shayi yana tururi aka fara zuba muna ana mikawa kowa don su manya din har sun fara sha duk da zafin shi a lokacin.
Mamana wanan kanwar maugidan mune tana aurene a nan itama sai wanan yayatace itama tana zama damune a gidan nan wanan kuma yayan dan uwan babansu Al, amine.
Sai ta juyo kaina ta dafa kafadana tana fadin da fatan zakiji dadin zama da kowa cikin mutunci yadda ya dace na dago ina kara gaidasu naji dayan cikin wanda tace ai yayan yan uwan maigidansune tace.
Amma wanan kan ko a cikin yan uwanku kamar tafi kowa kyau akai dariya nan dai suka shiga hira a tsakaninsu kafin dayan mai dan sauran kurciya daga ciki tace dani.
Ayyah ki taso muje ki danga gari kafin mu fita zuwa sallah hakan yasa muka mike a tare muka bar falon wanda a zatona ko fita zamuyi sai naga ta nufi saman bene dani.
Mun bula wani dan fili daga saman kamar wurin shakatawa duk a jikin gidan nasu daga sama da kujeru a wajen na zama a huta a sha iska daga gefe muka tsaya a tsaye muna hango cikin gari daga inda muke.
A lokacin abinda ta fara fada min shine kinga ga Haram can massajid masalcin Annabi SAW kingashi can a tsakiya gari yake yanzu tako wani angul din garin nan kika fito shi zaki sama a tsakiya.
Da sauri na dago kai ina duba tare da addua a kasan zuciyana ina mai farin ciki da ganin wanan babban nasaran da nayi a rayuwata.
Anan inda muke take nuna min direction din komai na garin tare da bayani a kai ina dan mata tambayan wanda ban gane ba nima a dan lokaci lokaci.
Muryan Al,amin ne a bayanmu yake fadin ashe kuna nan na dauka ai har yanzu wana tana ciki tana barcin gajiyane ita ai ?
Zama yayi a saman kujerun dake wajen yana shan kokon da ya daure da madara ban dauka zasuso kokon nan haka ba don gaskiya danayi masu garinsa mai yawa da zan zo din amma nazo da kadan kuma gashi yayi rana don kowan su ya yaba da hakan.
Goma muka shiga suna fadin nayi wanka mu shirya za a fita kamar na sani na saka dayan rigan da yafi wacan din kyau lokacin make jin wanan matashiyar ta turo kofa tana fadin idan na shirya mu fito mu tafi.
Koda muka fito motace galleliya a waje kusan kowa ya shiga sai mu ukun ne bamu shiga ba nida ita sai hjy dake bayan mu data fito
Duk muna baya hjyce a gaba sai Al,amin dake jan motan bamu tsaya ko ina ba sai masalacin wurinda ake aje motoci idan kai ba mazauni garin bane ba zaka gane wurin ba amma su da yake sun zama yan kasa sunsan ko ina a kasan.
Mamana marhabin da zuwa masalaci mafi daraja a duniya wanan shine daya daga masalatayan duniya dasukafi girma da daraja a wurin Allah.
Wani irin dadi naji na lumshe idanuna lokacin guda ina addua a kasan zuciyana don tun a gidan da wanan yar uwan tayi min kwatance nake addua a zuciyana ina hamdallah ga ubangijina Allah ma daukakakin sarki daya nufeni da zuwa wanan wurin a yanzu.
Mun fito munyi tafiyan da dan nisa muna tafe ina bin ko ina da kallo ina baza ido ina kallon gari a cikin mamaki don gaba daya saina koma bakauya hjy ko sai bayani take min ina daga gefen ta tafe.
Ranan dai a can mukai sallah azahar har la,sar da magariba da isha,i mukai ziyara a rauda bayan sallah la,asar din da mukayi a waje naji dadi sosai nayi addua ana rokon Allah abinda yafi tsaya min a raina sosai a cikin rayuwata.
Bamu dawo gidan ba sai dare kamar wanan lokacin da suka dawo jiyan suka samemu mun iso ban taba jin dadin wani rana ba kamar wanan haka na kwata da farinciki ranan ko abinci ban tsaya naci ba.
Sati daya jere ga juna bamu zama a gidan muna wuni a masallaci muna ibada sai sati muka dakata kowa ya natsu a gida ranan ba wanda yayi saurin fitowa ana daki ana ramuwar barci da yada gajiya su a ganin su fa.
Nikan ko gezau don natashi da wuri wanda ya saba wahala a banza yana zuwa karatun boko a wahalce yanzu zaiga wanan ibadan a matsayin wahala kuma gareshi ?
Don hakane nikan banji komai ba na gama gyaran dakina na fito waje har lokacin har yan aikin babu motsin kowa a gidan don hakane na shige kitchen din nasu.
Dambu nake son hadawa matsala babu shinkafan da zaiyi dambu don haka nayi dabaran yin bleending dinshi wani kuma na dan cacakashi sai gashi ya wadata min duk da bai gama samuwa ba yadda nake so amma haka din ya danyi da ganyen carvej nayi amfani tare da ganyen na,ana,a ya dan bashi koren kala a ciki haka na daure nayi dabaran hadawa .
Kafin na fara masu dan abu mai sauki da zasuyi breakfast dashi na hada komai yadda nakeso har dasu ferfesun rago nan dai na hada gaban dinning din komai tsab.
Karshe wa yan nan yan dattawan biyune suka taimaka min nayi komai yadda nakeso kafin na barmasu zuzubawa saidai a kan dambun nayi warning dinsu da zan tafi kada su saka min hannu don Allah da sunan dandanawa don zai iya lalacewa yayi bashi.
Don hakane ban chakudashi da mai ba saidai na soya kawai na aje a gefe daya nafice na shiga wanka na fito na shirya falon na nufo a cikin rigana maikyau na dan yafa mayafi a kaina ya dan rufo min jikina.
Turus naja na tsaya gani a ranan kamar ma kusan kowa a family din hjy yana gidan illa uncle da ban gani a cikinsu ba dai don har Abbu yana zaune suna karyawa a tsakar falo.
Yar siririyar sallama nayi da zan shigo falon wanda ya makale min lokaci guda ganin maigidan a gidanshi danayi hakan yasa lokaci guda ba koma bawai bawai kamar zan juya in koma sai kuma na tsaya ina gaidashi bissa ga al, adan hausawa yadda muke gaida manya a cikin hausa.
Yallah yallah tahrik tahrik ya fada yana nuna min da hannuwa in tashi kada in duka saida duk da na gane hakan baisa na mike ba ina a wurin na sada kaina kasa lokaci guda.
Yata tashi ki zauna da kyau ban ganki ba saida na sheda maganan mutanen ki wurin iya girkinki da suka dawo gida suna santinshi ashe nima da rabon zan dandana naji a bakina.
Kinyi kokari matuka dole a yabawa kokarinki don a yanzu na sheda gaskiyan hakan da kaina tunda har kika iya hikimar yi muna wanan abincin haka.
Zanso a ranan taron mu a samu irinsa haka a girka muna idan zai yuyu ai muna hakan sai ayi hjy dake gefenshi babu abinda takeyi lokacin sai murmushin jin dadin satin da mijin nata keyi.
Da sauri na dago kai na dubi Abbu din dattijo mai kama da iyalinsa maza sak zakace shi din yayan su Aliyune ba mahaifinsu ba don da sauran kurciyanshi ace shine mahaifinsu gaskiya a ganina.
Na dubeshi ina sada kaina kasa don maganan da yayi din yazo min a bazata saboda hjy bata riga da tayi min bayanin komai ba tunda nazo sai ibada muke zuwa yi a masallaci ko zama bamu samuyi ba da ita.
Bamu kai ga wanan maganan da itaba tukun na barta ta hutane kafin mu zauna muyi magana tunda da sauran lokaci har yanzu ai.
Sai naji yace ko akwai lokaci ya kamata by now tasani ai don asan abubuwan da za a sa azo muna dashi daga Nageria wanda zata bukata din a wurin aikin kafin masu zuwa suzo.
Mikewa nayi a hankali na juya zuwa dakin don gani Abbu din da nayi zaune da matarshi a falon don haka na koma na kwanta ina tunane sai barci ya daukeni hakana ban sani ba a wajen.
Barci dana ki kwanci da safe inyi shina rama a wanan lokacin don haka ban san ma a inda nake ba lokacin sai a zahar dinsu na tashi nayi sallah na fito in samu abinda naci na samu hjy da maigidanta sun fita.
Abincin dare na tabayesu suke fadin sukan girka duk abinda ya samune aci don haka wai wani abincin larabawa zasuyi na filawa.
Nake fadin me zai hana muyi tuwon shinkafa suke fadin basu da abin miyarsa don hakane basu sonyin tuwon shikafan.
Dan tunane nayi kafin nace ai babu damuwa zansan ya zamuyi zuwa lokacin tsofin nan sun fara min kallon banza ina kawo masu iye iye ga harkan su.
Tuwon na dora duk suka jaye suna kallona bawai don basu iya ba sai tunanen ya zanyi in tuka tuwon taron gidan nan a yanzu yadda suke da yawa din nan gidan ya cika.
Don hakane suke son suga iyakata a gidan niko ko a jikina don yar babban tukuyansu na dora din duk da hakan ina tambayan wace tafi tsufan don tafi ban fuska a cikinsu.
Ban fita kitchen din ba ina kula da girkina don haka nayi amdani da daman na dora miya sai a lokacin ne shawaran gwaggo na zuwa da tsaraban kayan girkin yai min amfani don tunanen babba yafi na yaro dama.
A nan din dai na dora miyan kuka daga can inda suke zaune suke jin kamshin dadawa kalwan asali yar gargajiya yana tashi sai gasu a kitchen din sun shigo.
Miyar kuka nayi wanda yaji kashi sai kamshi asali ke tashi a cikin sa da kayan yaji wanda yaji hadin masala da gwaggo ta daka min da hannunta ke tashi.
Wani jan miya na daban na hada na romo nama zalla kuma dan kadan na gama na tuke tuwon na samo ludayin a kitchen din nayi malmala mai kyau kaf har na kwashe tuwon ina jerawa a cikin wani dan babban kula mai kyau dake rikon zafi daidai lokacin miyan roman ya gama haduwa shima nakwashe tsab na juye komai kafin na fara gyara kitchen din na wanke komai danayi amfani na kife don haka shine kammaluwan diya mace a wurin girki.
Falon na koma na gyarashi tsab nafito zuwa ko ina na gidan ga kamshi nan kala kala na hayake gidan kafin na koma daki nayi wanka daga nan kuma ban sake fitowa wajen ba.
Na nemi wuri na kwanta wayata kawai naji ta dauki ringing sai abin ya bani mamaki don ban taba tunanen za a iya samuna ba a nan din sai gashi naji waya yana ringin a lokacin.
Na lalubo na fito dashi sunan sojana na gani sai abin ya ban mamaki kamar kada in dauka sai kuma na danna dauka na kara a kunnena naji yana fadin.
Lah laima baby ban kiraki ba kema kuma baki kirani kinji meya sameni ba kin dauka kin barni ke nan ko fushi kika dauka dani haka.
Humm nace kawai don mamakin shi da nakeyi don abinda nake jin yana fadi a lokacin yace baki yarda ba ke nan ko nace dame fa ?
Sai naji yace yanzu dai ki fito gani a kofan gidan ku tsaye muyi magana zaifi nace wani gidan yace zaria mana ko kina kadunane ?
A, a ban kaduna ban zaria kuma da sauri naji yace kina ina ke nan ya tambaya tare da sauraraw yaji nace Abuja don hakan yake zato a zuciyarshi lokacin.
Nace ina saudiya tun last week sai naji yace what saudiya fa kikace baby ya tambaya da sauri nace ka aika ciki a tambayo maka gwaggona mana idan ka dauka fada kawai nayi.
Saudiya saudiya fa naji yana fada cikin mamaki nace eh nazo umurah ne a ko hakan laifine kuma yace a, a ha kinyi lafiya har ba, a fada baby .
Nace ko yace dole ince hakan mana zakiyi tafiya irin wanan ace ko nemana ba zakiyi ki sanar dani ba baby dole abin ya ban mamaki in fadi haka ai.
Meye na mamaki a cikin zancen saudiya dama in Allah ya horewa mutum ai yana saka ran zuwansa ko yaushe don haka Allah ya nufa nazone .
Dawa kikaje saudiya din naji ya fada sai tambayan ya ban mamaki sosai don haka nima na bashi amsa da fadin da wa yanda ya dace inzo nazo ina fadin hakan na kashe wayana.
Cike da takai na mirgina ina tunane ashe dama haka daukakan diya mace yake idan bata da aure ni dai nasan ubangiji Allahne ya daukaka min rayuwata a yanzu duk da aure gareni ba.
Amma kuma babban matsalan shine mutane suna sukana da zargin banza tare da mumunan zato a


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login