Showing 255001 words to 258000 words out of 347556 words

Chapter 86 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8817

yake hukunci tunda mahaifinki ya riga yaba bawan Allah nan ke kuma a dan nazarinsa da nayi bamga wani abin asha ba a tare dasu.
Amma ban sanarwa boye ba don yau mutum sai Allah don haka sai mu barwa Allah zabinsa idan hakan shine alheri a gareki ubangiji Allah ya tabbatar da hakan gareki.
Idan kuma ba alheri a cikin sha,anin ya Allah kaga irin rayuwan da boyar nan naka tayi a duniya ya Allah ka mayarda yin hakan yazama alheri a gareta Allah kaika san daidai bamu ba ubangiji mun bar maka zabi akan hakan duk abinda yafi zama daidai Allah ka tabbatar dashi akan boyar nan naka.
Muka amsa da Amin saidai ni a ziciya na amsa ban amsa a fili ba don gudun rashin kunya a lokacin saidai wunin ranan kan a kwance nayisa sai aka dauka ai gajiyace ya jawo min hakan.
Baba sun zauna da Ammi sunyi zance daya dace a kaina wanda baba ya nuna yana fushi dani a lokacin kan tafiya wurinta da nayi bam fada mashi gaskiyan inda zan tafi ba.
Hakkuri Ammi ta bashi da farko kafin ta kuma nuna rashin kyautawashi da bai nemeta ya sanarda ita ina raye ba alhalin yasan tana kasan ita.
Sundai fahinci juna bayab kowa yabawa dan uwa hakkurin kuskuren da aka samu a tsakani ko a nan saida Ammi ta tuntubi baba akan zancen aurena.
Abin mamaki a nan baba ya nuna baisan zancen bashi nan ta koro masa bayani har cewan da sukayi zasu kawo kayan auren nawa duk ta sanar dashi yace ikon Allah to ba zance na sani ba ko ban sani ba.
Don kwanan nan Nura dan wajena ya fito min da zancen amma dana tuntubi ita uwar biyu sai cewa tayi aikowa yasan wanan zancen zafin ciwone yasa nayi alkawari alokacin.
Mutumin banza take son mayar dakai ko kuwa ita kanta Fadima da mutanen nan suka bita a wurina bayan yafiyansu ta mayar min da komai na kuma bata hakkurri na tausheta don kai yanzu kuma za asa kayi magana biyu a yanzu din.
Kada kai baba yayi yana fadin kada ki damu hjy amincewan Fadima shine burina dama son mutuncin da yaron nan yayi muna iya abinda zan iya saka masa dashi ke nan in bashi Fadimatu idan ta yarda da hakan.
Don alkawari nayi ba zan taba aurar da ita ga mijin da bata sonsa sai wanda take son don Fadimatu diyace diyace dako wani uba yakeso yake alfahari da haihuwan irin ta a gida.
Sanadiyar Fadimatu yau komai da kika gani a gidan nan ya samu garemu nan dai ya dauko labari tiryan tiryan ya fara bata labari.
Shi yana sharan hawaye itama Ammi din lokaci lokaci tana goge nata hawayen da haban lafayan jikinta data nade daga sama har kasan jikinta dashi.
Zance dai ya tsaya ga cancantan tashi da aka gani don haka Ammi zata kara zama dani kafin ta tafi sun dan taba hira baba nason ya tambayi kanwarta Nuratu yana jin nauyi da kunyan hakan gareta.
Haba da nauyi mana matan daya wullakantawa yar uwa yau itace kuma tazo gidansa bata kuma nuna masa komai kan abinda ya faru ba wancan lokacin duk da yasan akwai tabon hakan a zuciyarta har yanzu.
Don Allah hjy a turo min Fadimatun ina son magana da ita ya fada koda tazo a lokacin mun fita nida su Maryama suna son suga gari da muka dawo kuma gidan su hjy muka yada zango sai bayan magariba muka shigo gidan.
Sai a lokacim Ammi din ta fada min sakon baba wanka na farayi kada dare yayi na sauya kayan jikina saiga mama Lanto tana fada min baba nason ganina.
Yana zaune yana cin abinci nayi sallama nashigo ina gaidashi ya amsa min cikin dadim rai tare da nuna min waje in zauna hannu ya tsame a cilin abincin ya wanke a roban dake gefenshi.
Kafin ya kalloni yana fadin tau Fadimatu aikin gama ya riga daya gama kin nemo inda mahaifiyarki take duk da kokarin hanaki hakan danayi a baya don wani zato nawa wanda bashi bane ashe.
Ki sani ban boye maki hjyn gashuwa don kada ki santa ba a,a naki fada makine kuma na hana kowa ya fada maki don a zatona koda kinje wajensu ba zasu karbeki ba sai wullakanci.
Nayi mantuwa da cewa su mutanen arzikine fiye da tsamanin ki hakama wanda take aure shi din dan malamaine ba irin wanan a tare dasu.
Sai gashi kinje sun karbeki hannu bibiyu sun maki shatara na arziki a cikin mutunci da karamawa a garesu ina fatan ba zaki rikeni da wanan ba a zuciyanki kuskuren fahinta aka samu.
Kuma duk wanda ya sanar dake ita ya taimakeni ya tsamoni daga halaka don tunane bai taba bani cewa zasu karbeki yadda suka karbeki a yanzu ba duba da yadda muka rabu da ita Nuratu din a baya.
Nasan baki samu ganinta ba dai ko don banyi tsamanin tana kasan nan ba har yanzu don da tana nan watarana za a samu labari game da ita.
Lokacin nayi kokarin motsawa bakina da yai nauyi wani abu ya tokaremin makoshina ina jin wani iri dani nadan jawo natsuwa na dorawa kaina lokaci guda kafin nace dashi.
A,a ita ba a kasan nan take zama ba tana London da zamane amma yanzu tana nan Somalia don mijinta yana takaran siyasan kasan da zasuyi akace.
Tace dani sai komai ya lafa zata shigo nan tazo ta ganni ta dai ban hakkuri itama kan kuskuren da aka samu na rayuwana tsakanin mu.
Allahu akbar ita Nuratu din ke zaune a London koda yake ba abin mamaki bane da ikon Allah Nuratu taci wanan sakaiyan ga ubangiji harma fiye da hakan duba ga irin rayuwan data shiga a baya amma na kasa duba hakan gareta a lokacin shine abinda yanzu idan na tuna yakeci min rai a yanzu duk lokacin dana tuna hakan.
Wasu miyau masu dumi naji na hade daga cikin bakina kafin bace baba ai wanan ya wuce abar tuna komai a yafewa juna tunda ana raye.
Nasani Fadimatu nasani komai yanzu ya zama tarihi a wajen mu wani abin kuma sai munje gaban ubangiji don wani sharian bai yuyuwa a duniyan nan .
Zancen wanan bawan Allah mai dawainiya nake ji yanzu a bakin maman naki zasu kawo kayan aurensu gareki to shine na kiraki naji ra,ayinki kan hakan game dashi don banayi maki dole.
Yadda ban tabawa wani da nawa dole ba a cikin gidan nan kema ba zan maki dole akansa ba in kin amince ina maraba dasu idan kuma baki amince ba sai yayi hakkuri.
Kome kikace nace hakanane baba don darajan ka da kimarka ba zance banayi ba don kada ka zama mai magana biyu a idon mutane kai kace mashi ka bashini su kuma suka rike hakan don su cika maka alkawarinka ba wai don nakai darajan da zai aureni ba ya yarda da hakan .
Yau nice kuma zance ni ban yarda ba sai a sami matsala daga wajena bayan mune suka taimakawa a cikin wanan zance har kaga dacewan hakan atsakanina dashi baba.
Yadda kaga dacewan hakan har ka furta a gareni nima ina son zanyi biyayya a gareka in zauna dashi don kai har tsawon rayuwata insha Allah banda wanda yafi mun kai da uwata aduniyan nan donku ina iya komai matukar bai sabawa fadan Allah ba.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
8?? 1??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Bani da zabi a rayuwana dayafi na iyayyena da duk da dama fargaba da zargine ya tsaya min a rai wanda gaskiyane kuma ga duk mace mai hankali mutum kamar Boss dinmu bashir yafito da rana tsaka da sunan aure.
Aure kuma a gahauce haka ba wani dogon sanin juna don ko za a tsureni nidai bandasu oga Abbas da oga yusuf bansan kowa nasa ba.
Abinda nasani shine shi din dai dan jahar kadunane amma bansan a wani yanki ya fito ba a cikin jahar illa dai nasan Oga Abbas ya fada min cewa suma yan gadunane dai.
Shi din dai Abbas shine kamar saurayin dashi ake hira da komai har zuwa wanan lokacin ba zance ga abinda ya taba hadani da boss din mu ba.
Saima ince yanzu din ni dai tunkan mu hadu a Gashuwa ya fara kara daure fuskanshi gareni don koda suka sameni gidan Ammi bazance ya dago ya kalleni koda sau daya ba.
Su yan gidanmu sun dauka saurayinane abokin aikata masha,ana a karshe muka buge da aure don na taba jin mama na fadi suna hira da mama Lanto tace.
Ai kinsan mazan zamamin nan sai sun fara dandana mace a waje sunji tayi masu zakiji sun yarda su aureka in kuma bakai masu ba shike nan an shaka banza.
Wasu kuma da suka iya shege da fice sai kiga sun kama kafan namiji sun rikeshi tamau bakada hanyan gudu kaida ganin irin auren nan kasan aikin asirine.
In bashi ba wani hadin ai kasan bana kai sake bane andai yishine kawai ba saboda Allah ba karshe sai anyi aure kaji tonon asiri yana tashi.
Bayan angama dagawa mutane kai anfi kowa sa,an miji ban ko anga abinda ba,aso tun waje sunsan dadin juna ina za,aje ayi mutumci koga abokai da suka san komai.
Watama shi saurayin yaja abokai suja kowa na diban rabosa tunda ta zama nakowa cleanic zuma ba gari duka dadi kowa ya tara ya kayar ya haye.
Da farko na dauka dani da samira takewa gugab zana haka amma jin mama lanto tayi shiru bata amsa mata ba yasa na gane tayi mata kyafcin idanu kan cewa dani take ke nan.
Don halin mamane yin zunde dan ta iya gulma harda kafa da ido ai hakan ya zama mata jiki ko a mede baki ko da hannu in wani ya dan bada baya.
Ina mutum zai iya kishi da irin su mama da idonsu ya goge wajen mugun abu sani halinta danayi kamar yunwar cikina yasa nagane dani take wanan zancen a lokacin.
Wanan hiran nayiwa Ammi sai gashi ranan da baba ya fito da safe yake fadin to Allah dai ya nufa za aikomai na yarinyar nan fadimatu kamar na kowa don ko ga yar uwarta a gari anyi daidai don yanzu aka bugo min waya za a kawo kayan auren Fadimatu gobe gidan nan.
Kayan aure gaba daya ba baiko ba komai balle duniya ta sheda hakan baiko sunnace mai karfi ya juya yana tambayan mama din.
Ba sunna bace amma hakan ai al,adace mai karfi ga bahaushe don shine matakin farko shirmen banza ke nan tunda ba littafi ya fadi hakan ba ko larabawa suka kawo hakan ba ai.
Yau idan aure sukace min zasuzo a daura ya tabbata hakan don koni na haifi abina bawani keda yata ba da zai dora min ga yadda ya dace inyi.
Amma gani nayi kowa sai an masa baikon nan a gidan nan kafin aure sai kantane za ace ba ayi yanzu haka na tsara abina hakan kuma zanyiwa yata ko akwai wani magana bayan wanan.
Ammice ta leko tana fadin babushi malam don ko kaike da abinka ke uwar biyu kubar zancen nan haka kada yayi nisa tunda ga yadda yace zaiyi a binsa.
Ai dole hjy dolene tunda ya nuna bamu isa ba naga dai ba yau aka fara hakan ba gidan nan Ayyururirrr mama uwa ta fada daga kofanta ashe gobe da kallo gidan nan ke nan akwashi kam baba ya fada ya juya zai koma dakinshi da yar sandanshi dayake dogarawa a hannunshi.
Haka Allah ke ikonshi aure da haihuwa koba shiri idan yanzo lokacin da Allah ya tsara abinsa hakan za,ayisa ba wai sai an tsaya jiran wani ba.
Baiwane kowa da yadda Allah ya tsara masa a rayuwa mu daine mutane da namu zargi yaron nan nan kowa ya sheda dan arzikine a kasan nan amma a zancen banza sai kaji ana fadin wai sungama shashancinsu yaga ya dace ya aureta .
Idan ma wani shashanci yau fadimatu keyi na tare da ita kaf suna da kamishon hakan don abinda ta samo a wurin shanshanci tare akeci da kowa kuma a koma ana zaginta a baya.
Alhamdullahi da kowa ya haifa idan ka shedi naka duniya ta shedi wani Fadimatu bata da gadon iskancin saidai na aure don haka aure zatayi da yaron nan a yanzu inji Allah ba mutum ba don inda mutum ne saidai ta tabbata a gida zaune ana kollonta.
Shiru kowa yayi a lokacin itako Ammi taana kawowa ta juta zuwa cikin dakin tana maici gaba da magana yar nan taga duniya yau Allah ya yanke mata wahala me kuma za a tsaya jira yanzu ?.
Haka zancen yake ba,ako tsaya jiran komai tunda mai wuya ya samu miji Allah kuma ya kawo mijin a yanzu dama shine karshen magana ai aure.
Ya tabbata kin zamo Karan Dafi a cikin ygidan nan don gabadaya babu yar da tayi farin jini da sa,a irin naki a gidan nan daga zuwan miji sai aure haka ba jiran komai.
Ba,abin jira a yanzu ga uwa ga uba duk a raye saidai muji rana don rana baya karya akace saidai uwar diya tayi kunya wanan uwar diyan ko ba kunya don da shirinta ta baiyano muna a gari kai tsaye da yarta.
Sai kuma ta dora da guda daga inda mama take zaune taja tsuki tana fadin aiya kamata a baki loudspeaker ki yada a gari tunda mun samu marokiya a cikin gida.
In gaskiya tazo a fadeta komai dacinta yaya abinne na Binta akwai ikon Allah a cikin lamarinta komai nata haka yake zuwa kamar an tsara matashi a rayuwa dama.
Allah yaba na baya suma irin nata don kowa na fatan hakan ga yar shi yanzu naji zance aina zata abin naki zolayane ashe suduk duka kikewa kirarin gaba daya.
Wanan matar da saura har yanzu waiko kanta daya kuwa na dan murmusa cikin karfin hali kafin nace ita kadai ke maganinta a gidan nan itake fada mata abu kai tsaye a zauna lafiya duk dama dukansu yanzun haka suke mata ai kuma bata daina halinta.
Abin ne da gajiya suma ba sasu zauna irin bayaba su saka mata ido tana mulkansu dolene yanzu suma su tashi tsaye tunda sunsan halinta.
Balle Allah tun a duniya yanzu yake fara hisabinsa ga mutum mai hankali sai ya gyara yanzu zan kira umma hauwa na fada mata don tazo ayi komai a gabanta.
Fadila ki kira min matan can a waje naji yadda al,adamsu yake a nan idan za a kawowa mutum lefe don mu acan akwai wani al,ada da akeyi.
Ammi don Allah idan sunzo kiyi masu zancen gyaran gida kada azo a samemu haka gajal a gidan kallona Ammi tayi tana min dakuwa kafin tace uwayenkine ai gara azo a samesu a hakan cikin kazantarsu.
Sun iya budan baki suna fadin an gyara masu gida sun koma amare yanzu zancen ki nan ya tuno min da wani abu na hikimar g??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????yaran gidan nan da yaron nan yasa akayi don akwai kunya mutanen su suzo su samu gida a haka rubabe.
Dan turo baki nayi ina fadin ai ban kirasa ba abinda ke garemu zamuyi ai yasan mu bamasu arziki bane wayata yayi kara a lokacin na dauka Oga Abbas ne a layin.
Ina dauka yana fadin Amaryan boss na matsu goben nan yayi muga ankawo kayan nan an tsayar da ranan buki naga idanun ku don karya ya kare ke nan yanzu dai.
Yayana kaike fadin haka idan kana wanan zance saina dauka cewa akwai wani abu a kasane kan abokin naka da kake boye min nidai nasan da zuciya daya zan auresa kamar yadda kuka umurceni da yin hakan.
Wallahi kada kiji komai don nasan sai kin saka min albarka yafi dubu wai kinsan abinda mutane ke fadi a kansa kuwa ?
Na amsa da a,a zan fada maki don inada yakini a kanki duk wanan abin baki taba fushi ko nuna wani abu ba akai kan aminina don sunansa yafi a kirga ance.
Shine bin maza yan uwansa da sauri nace subbahanallahi yace kwarai sunce dan shan jinine shi sun kuma ce ko hannu kasha dashi sai yayi tsafi dakai.
Wanan yasa kike ganin bai kula kowa kamar yana tsoron mutane na fada maki wananne don da zaran sun gane kece zai aura zasu kawo suka a kanshi hankalinki kuma zai tashi gara kiji hakan daga bakina zaifi.
Yyana kasan hakan kumacka hadani da Allah nice na dace na aureshi ko


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login