Showing 249001 words to 252000 words out of 347556 words

Chapter 84 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8776

ranan da muka hadu don zan gane rabamu akayi ta hanyar dole.
Ba zanso ince lamarim ku harda asiriba don bamu yarda da hakan ba amma a wanan kasan suna haka a raba da mahaifinsa ko miji da mata ko wasu aminai ta hanyar asiri wanda su sunyarda da hakan.
Yau wace tayi aikinan da tasan ta kashe maciji bata sare kansa koke da bata barki gidan ubanki ba sai tasan yadda tayi takawar dake tun wancan lokacin yanzu ko ta makara lokaci yayi da Allah zai mayar mata da aniyarta tun nan duniya.
Tun zuwan ki bamu taba zama na fada maki irin rayuwan da mahaifiyarki tayi a gidan mahaifinki don tun auren bawan Allah nan ba karamin hakkuri da kokari boyar Allah nan tayi har aka sameki ba.
Ga lokacin ba wayan nan na hannu ga nisa dake tsakanin mu da ita haka tayi ta shanye bakin cikinta a can ita kadai bari kuwa kafin asameki saida tayi bari sau hudu jere da juna sai wani zuwa datayi nan malam ya taimaka mata har aka samu cikinki ya tsaya aka haifeki.
Banji haihuwanta ba saidaga baya lokacin ba abin magana haka kamar yanzu din ina ji ban tsaya ba na shirya naje a lokacin na sameta cikin wani hali na kunci don kariyan arzikon daya kama mahaifinku ance wai itace sanadi ke har maita da sata sun dafawa mahaifiyarki a lokacin.
Wanan dai zance na cewa itace da farar kafa tun baya yarda da asiri yai yawa har yazo ya yarda sukai mata koran kare wanda ko tsinke bata fito dashi ba daga gidan ku harke kuwa data sama a gidan sun karbe sunce badake tazo ba ai a nan ta sameki don tsaban iya sheri kina wata takwas da haihuwa suka rabaki da mahaifiyar ki.
Sai da ta hada da bara da neman taimako ta samu ta iso nan inda nake don yan uwa sun koma gida a lokacin wasu kuma sun mutu a nan din kafin a koma gida.
Ki auna wanan rayuwan kuncin da mahaifiyarki tayi a gidan mahaifinki idan kece ya zakiji a yanzu dolene mun kuma lurar da ita aikece kika kawo kanki a yanzu ta tuna aure da haihuwa ba rabuwa gashi an kara hadewa a wani wajen duk da makiya sun manta hakan yana tafe.
Shiru nayi ina nazarin zancen Ammi din yau nagane dalilin da mama ta dafa min sunan yar gadon maita duk ta dalilin kishine ashe na samu wanan sunan na maita har yaso ya bini a baya Allah ya rufamin asiri na samu sunan ya bace.
Kwanta nan ki huta don nasan jiya bakiyi wani barcin kirkiba ki kwanta a nan yanzu ki huta insha Allahu yau zamuyi magana da alhaji ya saka muna ranan tafiya kada mu shanya bawan Allah nan a nan yana zaman jiranki.
Nasan yayi hakan ne don kada kizo mu rikeki gari nan kamar yadda saida suka biyoki suka tabatar da inda kike din ko gaskiyane kina nan sin a wajena kinga wanan sai wanda ya damu dakaine zaima irin hakan.
Fita tayi daga dakin ta barni nan wai inyi barci maimakon barcin tunane na farayi na abubuwan da muka zanta da ita gashi na kasa zama in bata labarin rayuwana a gidan mu na yadda na taso din.
Don gani nake wanan wani sirinane kada mutuncin gidan mu ya kara zubewa a idanunsu idan sunji irin rayuwan dana fito a baya din cikin matan ubana da yan uwana.
Bani na falka daga barcin ba tun wajajen goma da rabi da barci ya daukeni sai karfe biyu da rabi na rana sallah na fara yi kafin nazo na tube kayan dake jikina na fito falo.
Ammi kawai na sama a falon take fada min ta aiki su maryamu can bakin ruwa basa nan sunso zuwa dani kodon naga ruwan garin da suka tsalako a wacan lokacin zuwa nan Nageri don tafiya a mota bayayi don haka suka dinga bin igiyan ruwa zuwa kasashe mafi kusa dasu.
Nan muka zauna tana ta ban labarin yadda kasan nasu ya shiga wani hali a lokacin yakin kabilaci daya hade dana siyasa har ya raba kan kasan nasu biyu a lokacin.
Wanda nake jin abin har cikin raina don na fahinci shi dai nasara baya kawowa al,umma cigaban rayuwa saidai abinda daga baya zai zamo illa a garesu don haka nakara tir da Allah waddai da lamarin bature dake kokarin rusa rayuwan al,umman Annabi a yanzu din.
Su maryama ne suka shigo da katon kwali na kifi suka aje muna a gaban mu kafin su koma su dauko wasu kanana guda uku da basu kai wanan din girma ba suka shigo dashi falon.
Tambayansu Ammi tayi kun tabbatar basu saka kanana a cikin duka kwalinba ko sukace a gabansu aka hada ko wani kwali kamar yadda tace.
Kallona Ammi di tayi tana fadin tsarabankice wanan nayi tunanen abinda zaki kai masu na tsaraba sai naga nan kifin dai shine kadai abinda zamu iya rikawa daga nan din muje dashi.
Don ranan Jumma,a idan Allah ya kaimu zamu tafi mu kwana biyu saimu mu dawo akwai wata boyar Allah aminiyar mahaifiyar ki wace ake kira balaraba a lokacin ban sani bako tana raye ko suna unguwar naku har yanzu itace keda wanan kwalin karami dayan kuma wani abokin malam zamu kaiwashi daya kuma wanan abokin yaron nan da sukazo tare shi zamu kaiwa tunda bamu samu bashi komai ba dasukazo.
Kinga mun manta da driver nan naku yanzu fadila dole sai kin koma don gobe bamu da lokacin hakan ki karbo wani a wajen sale, shikuma wanan babban na gidankune ko hakan dana tsara baiyi ba takare zancen tana tambayana hakan ?
Na dan nuna mamakina a fili na wanan kokarin da tayi min nan na bude baki da zuman yimata godiya amma ta hanani aikata hakan a gareta dole naja bakina nayi shiru a lokacin.
Ummi amma damu zaki tafi ko Fadila ta fada daga inda take duke tana daukan kwalin kifin zata kai kitchen din Ammin.
Ta jiyo ta galla mata harara wanda yasa ta dauki kwalin kifin bashiri tabar dakin da sauri don tasan kwanan wasan karshe zagi zata sha idan ta tsaya a dakin.
Kallon Ammi din nayi na dan marairaice ina fadin kiyi hakkuri Ammin kije dasu don Allah don wata rana su sheda suma suje garin mu tunda da motan daya aje zamuyi tafiyan.
Haba Fadima mu kwashi jiki muje mukai masu dawainiya a,a Amin ba dawainiya anan nayiwa yan uwana can dawaini su dasuke dankina na uwane ba zanwa ba a lokacin ne na dan bata labarin rayuwana yadda ya kasance saidai na boye mata wani daga ciki wanda bai dace taji ba a bakina.


ZAINAB IDRIS MAKAWA


KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
7?? 9??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Ya Sagir babban dan Ammi shike zaune gaban motan tare da driver nida Fadila da maryama muna tsakiya sai sit din baya da Ammi da Abokiyar zamanta daya da mijinta malam ya hadamu tare donta rako Ammi din suke baya a zaune.
Wasu akwai karamci da sanin ya kamata don ni dai tun zuwana gidan malam nakan naje part din sauran nagaidasu da safe tare dasu Fadila wanan kamar tsarin gidan ne haka.
Suma duk wanda ke gidan yana sammakon fitowa yazo part din Ammi ya gaida ita bayan hakan ba abindake kaini kuma suma na kula da hakan ba hayaniya ko sa ido a junansu irin na haukan nan wai kishi.
Bawai ba,ayin kishin bane amma karyanka kagane akwai wani zama na karkashin kasa a tsakaninsu na boye har ka karar da abinda ya hada ko yaushe suna haba haba da junansu a cikin mutuntawa da girmamawa a tsakini.
Nayi ta nazarin wanan zaman nasu tare da sha,awan hakan a gidan mu inda a karshe na gano daga jajircewa maigidane ga iyalinsa da kuma yadda macen farko a gida take nuna biyaya ga miji dole na baya idansunzo suma su bi hakan idan ba kishin hauka a tsakani.
Ban kara gaskanta hakan ba sai hiran da sukeyi a cikin motan inda na fahinci yan uwan kishiyoyin Ammi din sune masu juya mata dukiyanta don garin kusan noma da kamun kifi shine sana,ansu .
Ido na lumshe na jingina kaina a glass din gefen da nake zaune don fadilace a tsakiyan mu nida maryama mun sakata tsakiya komai za,ayi a cikin girmamawa akeyinsa da mutunci a juna.
Tun ana tafiya Fadila na dan tambayana wanan wani garine anty nakan dubi signboard din garin na fada mata don nima ba sanin wanan hanyar nayi ba idona yafi budewa a jaharmu da gefen kudu.
Ta jos muka fito don yafi muna sauki hakan yasa nasa driver ya tsaya a wani gari na sayi buhun dankali tumatur da sauran abubuwa mai yawa wanda hakan yasa ya Sagir ya kasa shiru saida yayi magana kan hakan murmushi nayi kafin don banyi magana ba sai Ammice ta bashi amsa da fadin kabar wanab kanwar taka a inda ka ganta da hakan ta ginu a rayuwanta.
Kagako hakan ba abin mamaki bane don duk abinda ta samo akan dawainiya da mahaifinta da yan gidansu yake karewa kuma duk hakan baisa sun mata kallon yarsu ba.
Rashin makwabin kwaraine a kusa da ita da zai lurar da ita hakan da take tayiwa kanta tanadi ba tare da watsi da abin hannunta a kan kowa ba idan ka kula sanadiyab mahaifinta data bude ido dashi ya jawo hakan.
Kut wanan rayuwan na wasu mazan baiyi ba wallahi illan sakin mace ke nan kabar yaranta a cikin maraici da tangaririya a tsakanin dangi da yawa irin wanan halin wasu yaran kan fada cikin halaka a karshe yanzu inba ubangiji daya duba yarinyar nan ba tunda suki rike mashi ita da me kake zaton zata zama a yau.
Ka haihu da mace kan dan karamin tunane ka saki mahaifiya kazo ka raba tsakanin da da uwa kun bar yarinya da maraici karshe da Allah ya tashi ikonsa kuma kuka dawo kuna cin arzikinta.
Ni dai ina kurum ban nuna alaman dani suke zancen ba don driver dake cikin mota zaune a lokacin banyi aune ba kuwa naji muryanshi yana fadin ai malam in fada maka rashin tunane za a kira abin ko kaddara kaga irin wanan rayuwan ya shafi Ogana dakake ganinsa.
Shi nasa da bambamci donshi marayene amma matan uba da yan uwa suka kasa rikonsa a tsakanin su sai wani bare sabba wanda ba hadin jini a tsakaninsu shiyazo ya rikesa a karshe har yazama haka a yau.
In fadama bawan Allah nan yasha wahalan rayuwa a wurin yan uwansa don zuriansu kaf Allah yai masu arziki ga sarauta kuma a jininsu.
Ai in gajarce maka hiran nan yanzu sai antona a samu mai arzkki irin nashi cikinsu yanzune kuma suka san dan uwansu yake shi kuma bai saba dasu ba a yanzu sai wanan abokin nasa da kuke gani kamar yaronsa shine amininsa wanda a sanadinsa yayi wanan arziki haka don iyayyensane suka rikesu a tare.
Allah ke nan ya sagir ya fada daga inda yake zaune yanzu wa zai ganshi yace haka ya faru dashi yace ka ganni nan makwabcinmune su a lokacin tunda na girmesa nine nake dan jansa a jiki kafin a daukeshi zuwa karatu cikin kaduna .
Sai gashi da Allah ya buda masa ya nemoni ya daukeni aikin tuki a ma,aikatansu kasan yaro baya da mantuwa daka taimakawa babba wani lokaci gara yaro sau dubu yaro baya mantuwa a kwakwalwansa.
Shiru nayi ina saurare watau dai shima yasha gwagwalmayan duniya ke nan kafin ya kai haka to ina irin wa yanda sunsha hakan kuma haka zasu koma ga mahalicinsu ba tare da sun more rayuwansu ba kuma ?
Astangafurllah Allah na???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? godema da wanan ni,iman dakayi min a cikin rayuwata na fada ina lumshe idanuna sai naji dan labarin nan na malam Audi ya tsaya min a raina yaki fita.
Tafiya kan munsha tafiya sai wajajen karfe shidda muka shigo kaduna lokacin yamma tayi sosai haka muke wuce unguwani da shaguna da majalilsu har ya kawo kofan gidan mu ya faka ba tare da nayi magana ko masa kwatance ba tunda yasan guri dama.
Majalissan isah na gefe yayin dana dattawan unguwa su baba ke gefen bangaren gidan mu a na renon tsufa su hudune a zaune muka sama lokacin
Haka kallo ya dawo ga motar daya tsaya din kamar yadda akeyi idan anga bakon abu a waje kuran da bakar motar ta kwasone zai nuna maka motar ta fito wuri mainisan zango a lokacin.
Ya sagir ya fara fitowa daga motan kafin malam Audi ya bude yana fitowa shima sai bangaren maryama data bude amma bata fito ba tada fitar da santala santalan kafata waje tana mike su don gajiya da zaman mota da akayi
Ta bangaren dasu babake zaune na bude nawa kofan motan na fito nima a gajiye fuska ya nuna alaman gajiya a tare dani baba mai mota na ya dan dago yana fadin wai Bintuce ?
Na amsa da eh baba nice mun sameku lafiya ikon Allah ashe dama kinyi tafiyane jiyan nan fa naso na tambayi malam garba ke sai kuma na manta har muka watse ban tuna hakan ba ashema bakya nan kinyi balaguro .
Nida yar mahaifiyatace muke tafe amsan dana iya bashi ke nan a lokacin jin hakan yasa babana ya dan juyo a zabure lokaci guda yana fuskantar mu yace a,a tare kuke tafene ?
Yana kokarin mikewa tsaye su Ammi suka fito daga motan nan suka dan tsaya suka fara gaisawa dasu sama sama yana fadin hjy kin tasone Ammi ta amsa da ehh malam yata na rako gida.
Suma su baba mai mota suka taso ana gaisawa dasu nan baba yace kaisu ciki mana fadimatu ganin Ammi yasa baba ya sauke fushinshi dani a lokacin.
Cikin gidan muka nufa saiga Nura ya dan kura ido kafin yace Bantu sai kuma ya juya yana fadin wallahi Bantu ta dawo hakan yasa su Usaina suka kwaso zuwa kofan gidan sai muka hade dasu ana sannunku da zuwa.
Can na hango mama zaune tana da wani mugun dabia na zama ba riga a cikin gida haka kai ba dankwali duk da ta fara furfura akanta lokacin.
Hakan ko yanzu muka sameta ganina da bakin da bata taba zato ba yasa ta dan fara kame kame tana dan wasan baki da fadin bakin marance ne muna haka tafe ?
Ko ya mama ke magana dakai saita dan jefama arshi a zance da wani manufa ta kirani nida iyayyena da bakin marance din data fada su Ammi kan sai haba haba akw masu ana gaidasu .
Dakina na nufa kai tsaye dama key yana a hannuna tun a mota na ciroshi daga cikin jakkata din dake hannuna na bude dakin kafin nashiga nayi sallama na kunna wuta haske ya gauraye dakin lokaci guda sai ga Nura ya shigo da kayan mu har cikin dakin tare da wasu da suka kama mashi shigo muna da kayan mu har cikin daki nan akaiwasu Ammi din iso bisa jagorancin maman Uwa data shigo dasu dakin.
Muna zama hassana tana shigowa da kayan sanyi har ruwa a hannunta wanda naji dadin hakan har cikin raina a lokacin sai faman ina aka saka dasu akeyi Allah ya taimake mu malam Audi duk inda sallah ya riskemu zai tsaya mu sauke nauyi kafin mucigaba wanan ya rage muna nauyi a lokacin.
Ammi na zaune a kasa inda sukayiwa kansu matsuguni ita da umma hauwa kishiyarta don dama suba ma,abotan zama sama kujera bace sunfi ganewa zama a kasa ko wani lokaci.
Sai kallon kallo akeyi tsakaninta dasu mama suna ganin har yanzu tana yadda suka santa ita kuma tana kallonsu duk sun gajale mata a idonta.
Umma hauwace ta fito daga bayi ta dauro alwala kafin Ammi ta mike tana kallon mu dasu hassana munata zuba a tsakanin mu lokacin ta tambaya sune yan biyun da aka haifa wani lokaci ?
Sune nan kuwa mama suka zama dirka dirka din nan mikewa nayi na fito da sallayana sabo dana fito camp dashi na shimfida masu a daidai inda ba wani mai gittaya don su wala a wajen.
Na daga gado na fito da center carpet din da nake faman boyo wani tanadin gaba na kai a kusa da dan filin don zama kasa da sukeyi wanda duk gidan ba wanda yasan ina dashi sai ranan dana fitar don iyayyena.
Mama Uwace ta leko dakin ta kirani nazo take fadin wai abinci zamu dora na rasa me za a girka a yanzu ai saurin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login