Showing 237001 words to 240000 words out of 347556 words

Chapter 80 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8789

kawo kayan abinda babu su sai sukarasa a wajensu kafin a kai kayan.
Wanan ne dalilin dayasa Abbas ya sakashi a gaba saida yaga ya tura kudin wa daddy Isma,il ya kyaleshi don mami ta jaddada masu cewa kafin azumi ya kama take son ayi aurem bana ba zaiyi azumi gwauro ba.
Ranan kan sun sha waya suna bincke dama sune masu fada aji gidan su ukune zuwa biyu hjy saudiya sai hjy tantano sai kuma ita hjy kaltume din da bata faye biye masu ba don tana da matsalan rashin haihuwa.
Wanan yasa take bin duniya a sannu tana tare dasune amma ba wajen sheri ko hali yazo daya ba matsayin su dai na sarakan gida daya a lokacin.
Iya bincike duk kansu sunyi kansu gano wacece zai aura sun kasa hakan don sun saba da wanan halin don akwai lokacin da irin haka yaso ya faru amma aka rasa wanda yabi rana yabi dare ya bata zancen da fadan munanan kalamai a kansa.
Yanzun ma da hakan ya taso suyi iya binckensu kalma dayace shine dai ba,aga wani alaman aure a wajensa ba kuma ba,aji kowa nasa yana zancen auresa ba.
Don har yakai an tuntubi mai marta mahaifinsa yace sam baisan da wanan zance ba don hakane karshe suke fadin kila aurensu na Jinsi zaiyi yasa yace hakan.
Har yakai an bugawa hjy Kaltume waya ana bincikanta wai wani kalan kayan aure sukaje saya a Dubai tambayan ya bata mamaki amma hankalinta bai kawo ko don me ake tambayanta ba din sai cewa tayi.
Wallahi kedai kaya na alfarma na gani na fada ga duk diyar da akakaiwa shi kuwa sai sun girgiza don ba karamin kudi ya narka ba ke bakiga wasu sarka da awarwaron da muka samu ba masu bala,in kyau saidai tsada.
Bata dau yake sonyiwa mutane kawai hjy Tantano ta fada don gaskiya baida wata mace a kasa da zai aura yanzu son shi sha,anin aure ai baya bace don da yana nema da anji kishin kishin a gun mutane ai.
Ita dai jin hakan baisa ta fasa abinda ya kaisu ba ta tsaya ta hado mashi lefe na alfarma da daukan ido yadda yace hakan akayi aka sako masa shi a jirgi zuwa Nageria .
Gidansa aka kai kayan duk kuma suna da labarin hakan sun kashe kunne suna jiran jin gidan da za a kai kayan subi dare daya su bata komai kamar yadda suka saba don hjy tantano tafi ummu din zafi da danyen kai don wani abu ita kadai ke aiwatar dashi.
Sam hjy bata taba kawo cewa nice mai wanan sa,an ba asalima a tunanen ta ina can cikin wahalan talaucin rayuwan data sanni dashi a baya tunda tasan asalimu mu fakiraine a wajenta son haka zance na sam bai kawo a kanta ba don a nasu sanin .
Sunsan cewa yan family din sai yan gidan masu fada a kasa kowansu ke aure don haka sunsan shima sai ya garje din idan har zaiyi din ma ya nemo yar gidan wani babban kusa a Nageria ya aura.
Don yadda yake jin motsin naira gaba da bayanshi a yanzu ko wanan daman daya samu don sunsan bature baya daukan tsegumi koshi da hjy Tantano tasan yadda ta shiga ta fita ta sokw wanan harkallan tasa a can wurin abokan hurdanshi din.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
7?? 5??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Uwa maba da mama uwa gishinkin rayuwa rabin zuciyar bawa uwa farin cikin dan adam uwa mai dadi uwa ita kadai ta taka tsanin dako bata duniya kaji mai sunan ta sai kaji sanyi kota fado maka a rai uwa ke nan share hawayen bawa.
Duk wanda keda uwa a raye ko kusa dashi ya godewa Allah ya kara kaimin wajen nuna mata so kauna kulawa don da zaran ta kwanta dama kafin kiyi alheri da Allah zaiyi saurin baki falala sai kinyi sau barkatai bakiga haske a rayuwan ki ba amma idan tana raye zaki taganin komai yana zo maki a cikin sauki da zaran ta fadi kuwa kamar kin rasa wani bangare na rayuwane.
Ya Allah ka bamu ikon kyautatawa iyayyen mu da suke raye wa yanda suka rigamu gidan gaskiya ubangiji Allah ka rahama masu kasawa abinda suka bari a duniya albarka amin ya Allahu.
Dalilin bayanin nan a ranan na tashi cikin wani farin ciki rayuwana kamar an min busharan gafara daga ubangiji don kawai na samu wani bangare na uwana duk da ba itace naganiba.
Amma ina jin wani dadi da sauki a kasan zuciyana na sakawa hjy balaraba albarka yafi kwado tsakanin jiya da yau a lokacin don itace silar hadani da wanan farin cikin da nake ciki a yanzu.
Duk da banji komai kan Nuratu ba amma hakan yai min dadi don a yanzu dai nasamu yan uwanta ina tare dasu abinda ban taba mafalkinshi ba a rayuwata .
Don ina karama mama tasha ikirarin cewa yar banza dangin mayu haka zaki tabbata mujiya wullakance a cikin mu har abada ba zaki taba sanin kowa na uwarki ba har abada kedasu sai lahira idan ana haduwa.
Duk da nake karama amma wanan kalamin ya tsaya min a kasan zuciyana sosai a lokacin don ace tsafi gaskiyar maishi bansan abinda abinda mama ta takaba take min wanan ikirarin a gaban kowa.
Sai yanzu nake gane ma,anan hakan da take yawan fadi ke nan ta raba tsakanin baba da ita har abada ta raba tsakanin mahaifiyata dani har abada ba zata taba shigowa kaduna bake nan.
Fitowa na daga dakin kwanan mu ke nan zuwa falo nakai zaune a gefen Ammi yayin da take rike da chasbaha a hannun ta tana dan ja a hankali nazo na zauna a kusa da ita .
Kaita dago ta dan kalleni ta katse abinda takeyi tace dani ga abinci can ki diba kici akwai tuwo akwai shikafa duk daga gidan yan uwanki aka kawo muna shi.
Na amsa da toh Ammi ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?zan jira ayi isha,i sai naci na bata amsa da hakan tace komai naki na mahaifiyar kine sak fatima har da wanan dabian na rashin cin abincin nan duk kin kwashi kalan rayuwanta duk da baku zauna a waje daya ba da ita.
Nuratu a yanzu tana kasanmu a can take zaune tana aure tun barin ta nan bata sake dawowa kasan nan ba saidai kafin ta tafi tayi dan shekaru damu a nan har zatayi aure garin nan kuma sai Allah bai nufa ba a lokacin saboda yan wasu dalilai.
Saiga dan uwan mu yazo daga saudiya shiya dauke ta suka tafi gida tunda yaki ya lafa a lokacin komai ya koma daidai yan kasa sunata dawowa gida.
Ba karamin aiki bane ga mutum yanzu yace zai kama kasan mu don sai kana da kudi da zai wadaceka zuwa Somalia yanzu.
Da adane ko jirgin ruwa kabi ba zaka kashe wani kudi mai yawa ba amma yanzu koshi din zakabi said ka tanadi kudi mask yawa a aljihun ka.
Ammi mahaifiyata tana raye dama na tambaya cikin mamaki ina kurera da ido ta dan murmusa tana fadin Nuratu ko na raye shi nake fada maki yanzu haka tana Somalia sunzo don mijin ta yana takaran siya a kasan mu.
Wani iri naji a zuciyana wai ashe tana raye a doron kasa amma ta kasa tunani nan take naji zuciyana na ban shawara kawai dana koma gida ko yanzu na wadata tunda nazo inda yar uwarta take.
Wani zuciyace ko kusa kada ki fara nasa hakan a zuciyarki uwarkice ko a bola tayar dake itace dai uwarki balle gidan ubanki ta barki kinsan dalilinta nayin hakan ?
A hankali na lumshe idona ina maijin zafi can kasan zuciyana dafani naji Ammi tayi yasa na bude idon da sauri tace kada kiji zafin hakan don bayin kanta bane ta barki bata waiwayoki ba haka.
Yau nasan da Nuratu tasan kina raye koni data saka naje na dubaki tunda muna kasa daya dake sabanin ita da take wani nahiyar daban.
Nuratu taji zafin rabakun da akayi lokacin tayi kukan hakan har ciwo yaso ya shigeta saida kyat na samu na shawo kanta da taimakon Allah muka samu har ta fara mantawa da hakan ta dawo daidai.
Basu kyauta maku ba gaskiya amma ku yafewa junan ku dake da ita don aikin gama ya gama tunda har Allah ya tsareki kika taso haka kika girma a tsakiyansu komai bai sameki ba kuma aisai a godewa Allah.
Wasu miyau masu daci na hade kafin nace kome ya faru ba zan dauki zafi da kowa ba don haka Allah ya kaddarawa rayuwana tun farko.
Sallaman ya mustpha dab wajen Ammi din na biyu daya shigo ya katse muna hiran da mukeyi muka tsaya gaisawa dashi sama sama ya amsa min kafin ya juya wurin mahaifiyar nasu yana gaida ita naji tana tambayansa yaushe ya dawo yace da yamman nan.
Kana ta tambayesa iyalinsa ya amsa da suna lafiya takwaran tace dai ya sama tana zazzabi ya fito ya sawo mata magani.
Ikon Allah amma uwarta ta kasa sanar min narasa meyasa wanan yarinyar take haka ni dai a sanina komai bai taba hadini da ita ba tun kan ta aureka amma yarinyar nan ta shigo gidanka dani a zuciyar ta yau har yakai tana kokarin nisantani da jikokina yayan da dana na cikina ya haifa.
Ina jin haka na mike tsab zan shige tace ina zaki dawo ki zauna kici abinci fuska na bata lokaci guda na nuna ba zanci abincin ba.
Meya faru kuma ko zancen mahaifiyarki da mukayine yanzu dake na kula tunda kika zo garin nan bakya cin abinci fa.
Da sauri nace ba haka banw Ammi kawai dai bana son kifin nan da ake sakawa a cikin miyar nan ne yasa banaci salati ta saka kafin tayi magana danta ya farayi yace bakya magana sai ki zauna da yunwa.
Dukar da kai nayi kasa ba tare da nayi magana ba ya kalli uwar yace kinsan wasu basa son kifi a rayuwansu ko kadan saboda yana taba lafiyansu daidai lokacin fadila ta fito tace ko jiya bataci ba yadda na saka matashi haka nazo na sameshi aje.
Ina zuwa yace ya mike ya fita daga dakin nan Ammi din ta hauni da fada tace ba saiki magana ba a sama maki abinda zaki amma kya zauna da yunwa haka.
Bawai bana cin kifi bane saman saidai idan naci ya dan min yawa sai na fara ciwo sai ya kaini kwance yasa na daina cinsa tun ina karama .
Gidan mu kuma ba,ama cinsa sosai sukan dade ba,aci kifi a gidanmu ba sai wani lokaci can mai tsawo kuma da yawan mu bama cin kifi a gidan mu.
Lalai kune fulanin asali kuwa da yawa cikin fulani basa cin kifi amma na dauka yanzu ai ba wanan saboda wayewan kai dayazowa mutune.
Sallaman dan natane ya shigo da manyan leda bakake guda biyu ya miko min daya ya aje dayan gaban mahaifiyarshi yana fadin.
Akwai kayan tea a ciki da dan abinda zakici yanzu gudun hakan yas mukaso ki zauna a gidn Sagir tun zuwan ki don can zakifi sake jiki da matanshi sosai.
Banda problem din komai a nan ko wanan don Ammi ta matsa sai naci abincine har aka gane amma ko ina na zauna haka nake har nabar waje babu mai fahintana.
Murmushi Ammi din tayi tana fadin yata tun zuwaki garin nan na fahinci wasu daga cikin halayanki na zahiri amma ke baki san hakan ba.
Na danyi murmushi saiga Fadila da waya ta biyoni dashi yana ringing na karba ina dubawa Ezekiel ne wanan course mate din nawa nan muka juya harshe da turanci muna hira sukai shiru suna sauraren mu.
Bandashi daya mayar da hankalinshi akan wayarshi na kula duka yaran nata miskilaine basu da yawan magana idan sun shigo zasuyi zaune sai idan uwar tajasu da hira su dan bata amsa.
Fahintar hakan da nayine yasa ban kulasu muna gama wayan na mike na dauki ledan da tunda ya aje min ban bude naga abindake ciki ba zuwa dakin mu har nakai kofa na juyo nace nagode yaya saida safe na shige dakin ba tare da najira amsanshi ba.
Yar nan da alama karatu mai zurfi tayi Ammi din ta fada yace sosai ma nima abindana fahinta ke nan yanzu don gaakiya da alama tana da ilimi sosai.
Ysushe zata koma ya tambaya tace bamuyi wani zance da ita ba har yau din nan don bata da sakin jiki sosai ko yaushe tana daki kwance bata son yawan magana sam.
Nayi mamakin zuwan ta garin nan ba tare da kowa nataba koda yake ba abin mamaki bane don munganta nan din ita daidai ba wani a tare da ita.
Dole dama idan ta sani tazo nan din don kece kawai yanzu na kusa da ita a kasan nan da zata fara nema taji labarin mahaifiyarta din kin fada mata dai inda take yanzu ko ?
Na soma fada mata ka shigo so nake na auna fahintar ta na kuma auna yarinyar nada mutunci sosai tunda tazo garin nan bata nuna wani abin rashin mutunci ko asha ba a gareta.
Na fahinci hakan nima saboda ta waye da yawa hakan bai hanata kamun kanta ba ina ganin kawai a bata lamban wayar uwar suyi magana koda a wayene kafin su hadu.
ina da niyar hakan amma ba yanzu ba sai nayi magana da ita Nuratu din mun fahinci juna yadda ta hau akan zancen yar nan na boyewa yarinyar bacin ran mahaifiyanta kan dangin ubanta da matansa harshi kansa ban bari ta fahinci komai ina dai lalabata a hankaline yanzu.
Zaune muke a dakin namu fadila tana gefena tana kallona maryamu kuma tana nade kayan wankin da tayi datayi da rana ledan daya kawo din na bude kayan shayine dasu cornflakes da suga sai exotics na kwali mai sanyi guda biyu da nama mai yawa mai zafi a ciki.
yau Gaban Fadila din na tura kayan ina fadin gashi muci sai suka kalli juna ita maryamuce tace a,a ke aka sayowa ai idan yaya ya samu munaci fada zai muna sosai ke bakuwace da alaman kina da daraja sosai tunda ya Mustapha ya sayo maki wanan.
Ko kuma don mararsa bata kusane yau yayi kokarin kyautatawa wani haka kici kawai ki koshi ta fada ta juya tana abinda takeyi a lokacin.
Kallon mamaki nake masu tare da tunanen ko ina akwai matsala ke nan dole inbi a hankali har in samu in koma gida lafiya yaren da sukeyi tsakaninsu yasa na dago kai na kallesu.
Ina fadin wanan wani yare kukeyi hakane dam dariya Fadila tayi tana fadin yaren mu na Somalia mana shine yaren mu a can ummi ta dauko mu zuwa nan tun muna kanana maryamu aka fara daukowa saini daga baya nazo lokacin da zan fara secondary.
Matar yaya mustapha din nan batada dadi ko kadan dan dama dama matar ya Mahmud wani lokacin tana da dama sosai bisa ga matansu yaya mustapha din kishin tsiya garesu balle sun ganki da kyau haka ai ke kan kilama bakwa gaisa dasu ba.
Dariya ta ban yasa na dan dara tace zaki gani ai sufa har Ummi basu bari ba yanzune ma ai abin ya danyi sauki don gashi suna bari suzo gidan nan su kadai ai saidai suzo tare.
Kallonta nake ita mai kyau take kira min kyawo haka nina rasa meyasa mutane ke fadin ina dakyau amma nakan dauki hakan a matsayin gani ido a gareni yauma sai gashi kyawawan yan matan nan suna fada min hakan abinda na yarda dashi shine gyarane kawai yasa mutane ke ganin hakan gareni.
Tare muka zauna mukaci koma daya sawo min suna kuma ban labari a kansu cikin kashe murya kada Ammi tajisu sosai yaran sukaci sai zuba sukeyi ina nazarin zancensu.
A takaice dai kamar ko wani gida wanan din ma suna da tasu irin matsalan na daban don sun nuna min Ammin tana fama da matsalan sarakanta matan da diyanta suke aure.
Wanan shine matsalanta kuma bayanshi banji wani matsala a game dasu ba a cikin hiransu muka gama suka dunkule takardan suka yar aka dauki nata wanda muka cire mata suka kai mata falo son bata nan falon andan dauki lokaci mukaji muryanta tana kiran maryamu.
Bansan meta tambayeta ba sai gata da naman ta dawo dakin dashi tana fadin ummi tace muci ita ansayo mata gashi nan ije bataci ba.
Ban kara fita wajenta ba sai washegari danaje gaisheta a nan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login