Showing 81001 words to 84000 words out of 347556 words

Chapter 28 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8766

wanan karon tunda gwaggo tana can zan zauna a wurinta.
Kai bintu na dai fahinci zaki bar gidan nan ke nan don halinmu ko zaki gujemu a yanzu don wanan abinda ya faru tsakanin ki da yaya ko ?
Idonane ya kawo ruwa nace mama gara in gusa in bata wuri abinda na tsare mata taganeshi a fili ko dazun kindai ji da safen nan abinda anty Altine ta shigo tana fadi.
Don su zaki bar gidan ubanki Bintu mama ai zan dinga dan zuwa donki keda baba kuma muna waya daku ai lokaci lokaci ina fadin hakan na fito kada ta kara min zuciya a lokacin.
Wasu tufafina na kwaso na kawo ina fadin mama ga wanan idan zasu shigeki ki dinga amfani dasu daki kuma ga key idan zakuyi kallo don Allah mama a kula min da dakin nura ya zauna a ciki har in dawo saidai ya dinga share min shi don Allah.
Wayana yayi kara na dauka Al,amin nagani ina dauka yace fatima kin tafine ko nace a,a yanzu zan wuce dai fitowana daga gida ke nan yanzu dai.
Ki bari nazo na kaiki kiban two minis don Allah gani nan zuwa hakan yasa na kara bude dakina saiga hussaina na fadin Bantu wanan kayan fa haka kamar mai barin gari.
Zan dan kwana biyune ban shigo ba yasa na dauki kaya da yawa amma ai zan dinga dan zagayowa lokaci lokaci yaro ya shigo yana fadin wai Al,amin yace Fatima ta fito gashi a kofan gida.
Au shine zai kaki ashe nace yanzu ya kirani nasan mamace tasa ya kaini shine ya kirani yanzu wai gashi ya iso kongode ai gaskiya suna da kara wallahi .
Ni zan koma mama na fada jin hakan yasa Samira fitowa daga dakinsu tana fadin wai har zaki koma ke nan nace Samira sai ki karaso ke nan.
Saidai zuwa gobe ko jibi zan shigo nace Allah ya kaimu a nan na kara sallama da kowa ina fadin nina tafi ke nan hussaina ce da yara suka dan rakoni har zuwa cikin mota magana hussai din yayi min a cikin kunneba nace shine bakiyi magana tun muna cikin gida ba yanzu kan saura nawa na da danake amfani dasu kawai suka rage zanyi waya da mama uwa ta diba maki.
Al,amin yaja mota ya tafi tana min godiya muka kama hanya dagani saishi saida mukai nisa yake fadin ai naso sai kin koma zaria in maki bazata saidai ki ganni kwatsam a gidan ku.
Keda banzo ba yaya zakiyi da wanan uban kayan haka nace da dabakanan ya nakeyi mashin zan hau zuwa tasha in shiga motar zuwa zaria din .
Ikon Allah kuma da wanan uban kayan haka to Al,amin yadda Allah ya halice bawansa ba haka zaiyi rayuwansa cikin taka tsatsan ba ashe.
Hakane fa Allah ya kyauta nace masa amin yaci gaba da tuki can kuma naji yace waike dama tafiya zakiyi ba tare da munyi sallama kuma jiya muna tare har dare baki fada min yau din zaki koma ba ai.
Murmushi nayi kafin na sauke ajiyan zuciya nace nakoma yau din shine alheri a gareni don idan na zauna za a iya samun matsala dani da matar babana da diyanta kaga ai gara kawai in tafi din shiyafi.
Shiru yayi yana tunane na dan lokaci kafin yace amma in kikai hakan sai suga ai sunci galabane a kanki yanzu nace nasan zata furta hakan amma haka dai yafi min alheri don gaba nake duba tunda har mama ta fara min haka duk da tun ina karama take bina da sheri irin haka ai.
Iska naji ya furzu daga bakin shi yace da ace nagama hada karatuna wallahi daukeki zanyi daga nan muje can inda basa ganin ki har abada.
Kallon shi nayi cikin mamaki ina fadin ina zaka dani inka daukeni yace gidana mana ko baki zama dani Ok kai dan wayau ko don naje inama girki kana cika ciki dashi tona ganeka Allah yasa kasa da a cikin zancen ka.
Murmushi naga yayi yana shafan fuskanshi kafin yace ke kin rainani ko don kingan mu abokai a yanzu kin dauka iya iya yinkine yasa nake ra,ayinki ?
Ji mun yaro da wani zancen rigima in ba hakan ba din meye kedai kawai aina fada maki matsalata a yanzu don nasan ina kawo wanan zancen yi zasuyi kamar zasu cinyeni da raina nasan halin yan gidan mu sarai tunda uncle da kike gani bai muna da wasa ko kadan.
Gaskiya yana da kama da muggan mutane in ba yanzu ba da farko na tsani in shigo wurin mama in samesu a ciki sai yanzu na fahinci ashe ba mugu bane yanayinsane kawai hakan.
Yace waya fada maki hakan kedai kawai baki shiga tarkonsa bane ko yanzu da zan fito gida saida yai min fadan wai kada naje nayi rawan kai najaki a sannu shi baison gudu.
Ni din har wani zabi nake dashi idan da motan kasuwa na shigafa yaya zaicewa driver su da suke gudu da diyan mutane kamar Allah ya aikosune.
Kinsan me ji nake kamar nayi sharia da wanan matar inda wajene wallahi sai kunyi sharia da ita ko baki kai karaba makwabtane zasukai akan abin nan da takeyi maki.
Na barta da Allah tunda itama ta haifa ai da sauki gida daine nabar mata shi ke nan saidai inzo in dan dubasu in koma koshi don babana da yan uwana.
Hira muke daya shafi rayuwana har muka isa garin zaria din da kwatance na kaisa gidan gwaggo din yake fadin kina ganin nan din yafi maki can ni naga gara dai ki zauna a gida zaifi wanan gudun.
Babu komai Allah yasa hakan yafi min alheri nasan ko a nan rayuwa sai a hankali amma baida matsala nan din dai zan zauna don yafi can din sauki a gareni.
Shiya tayani shiga da kayan cikin gida suka gaisa da gwaggo na fada mata shi ko waye ta nuna jin dadin ganinsa take fadin ya gaida hjy da uncle yayi mata godiya sosai a wurinshi.
Waje muja fito don yace zai tafi nan kuma muka dan tsaya dashi muna hira kafin ya shiga motar shi ya barni lokacin na makara don haka na share zancen zuwa school ranan bayan na shigo mun kara gaisawa da gwaggone take fada min ai yarta nan tazo daga Anchau don can take aure .
Nayi murnan jin hakan don nasanta dama tace ta tafi gidan yarta wuni sai dare zata dawo tunda na shiga daki ban fito ba don kwanciya nayi ina tunane sai barci ya daukeni a wurin har gwaggo ta gama girkin shimkafa da wake da mai da yaji da salad.
Karfe hudu na falka ina salati da sauri na fito don inyi alwala nayi sallah lokacin dana idarne na hango abincina aje wanda gwaggo ta aje min.
Kulan na jawo ina budewa ganyen har ya dan lagabe saboda zafi motsawa nayi na dauko ruwan leda guda don muna sayen bagen ruwan leda mu aje a daki don sha.
Shina dauko na zauna na fara cin abincin sosai yai min dadi don yajin ya hadu tunda dakan gidane gwaggo da kanta ta hada yajon don amfanin mutanen gida.
Naci saida na koshi na kwashi kayan zuwa kitchen din mama nan naga kayan a tare wanda yayi fani dashi na kwasa na wanke jin motsinane yasa gwaggo fitowa tana fadin kin tashi dai ke nan aina leka kina barci.
Na juyo ina fadin ehh gwaggo sanu da gida naga abinci na gode ke akul na kara jin kin min godiya gidan nan kan abinci sai na saba maki ni yanzu ba dadina bane zaman nan daku ?
Zuwanku gidan wurina alherine sosai a gare mu zuwan ku ya zamo muna alheri mussan ke din nan a sanadin ki yanzu muke dora tunkuya kashi uku a gidan nan muci.
Manya na fadin wanan zancen cewa idan ka sauki bako ko ka rike wani mabukaci kana ciyar dashi insha Allahu Allah zai horema abinda zaka dafa a gidan ka.
Wanan zuwan naku gidan nan na gaskanta hakan don tun ranan da kika zo kike kokari da dawainiya damu sanadin ki cikin mu bai bari mun zauna da yunwa ba kona dan lokaci kulun yanzu a koshe muke gidan nan sai masha Allah.
Nayi murmushi na nufi wirin randar ruwa na diba na shiga dakin mu don in canza kaya na bude jakata dana dawo dashi na dauko wani zani nawa da nake son in mayar dashi yanzu na zaman gida.
Zip din rigata na zuge na rage dagani sai dan bujen under wear dake jikina sai breezy da dan part ta ciki tunda ba kowa a dakin lokacin ni kadaice a ciki.
Zanin na walwale ina neman ta samanshi in daura kamar ance in kalla naga inda aka saka ko almakashine ko reza ko yuka aka yanki zanin nawa a cikin hikima ta yadda sai ka kula zaka gane hakan.
Indana kurawa wurin ido ina nazari kafin na juya na fita har nakai kofa na tuna da yadda nake na dawo na dauki rigan na kara zurawa a wuyana.
Sai wajen gwaggona ina kwala mata kira ta dago a gigice tana fadin lafiya nace gwaggo ki duba min nan don Allah wai wanan ba yanka bane haka ?
Yanka kuma yar nan ina kikaga makiyi irin haka yankan tufafi ai ba karamin al,amari bane gaskiya ga mai shi ta miko hannu tana amsan zanin daga hannuna tana dubawa.
Kafin tace kwarai kuwa yar nan yankane ga inda aka diba wanan abu akasa aka yanka kegen zanin nan, wayayi maki wanan karan aikin haka yar nan ?
Tsorone ya kamani da farko nace ban sani ba gwaggo nima dai yanzu na gani na dauko zan daura saina gansa haka.
Kada ki daurashi kuma miko nan anjima da magariba muje Kusfa muji ko waye yayi wanan aikin haka don asan abinyi.
Gwaggo kusfan wani wajene tace malamai mai masu aiki kamar yankar yuka bila,adadin a cikin unguwar yanzu da muje zamuji ko mai insha Allahu.
A,a gwaggo gara dai nabar maishi da Allah ubangiji Allah ya mayarwa maishi da nufinsa akansa ni dai nasan ban nufi kowa da sheri ba don haka duk wanda yai min sherinsa ya koma masa insha Allahu.
Balle gwaggo wazai min idan ba mutanen gidan mu ba nasan dai sune tunda ban zuwa gidan kowa irin haka don ko wanan zuwan da nayi saida muka kwasa da mama.
Daga kawai wanan uwar dakin nawa da nake baki labari gwaggo ta saudiya din nan tayi min abin arziki shine mama taje gidan tace wai baba ya turota ta bincika idan ba sata nake masu ba ?
Lah ha,illa ha,illah lahu Muhammada rasulullilahi yanzu ita suwaiba da girmanta tayi wanan karan aikin kai jama,a wanan abin kunyan ina zan kaishi yau nan dai na bata labarin komai daya faru.
Tana fadin assha aiko suwaiba idan tasan kunya tajishi wallahi kai wanan zancen baiyi dadi ba wallahi ni gwaggo zan dade ba je gidan ba yanzu don hakanema nazo da kaya masu yawa don nan zan zauna abina.
Yi zaman ki kan tunda nanma gidane gareki ai ba mai magana inci mutuncin mutum haka kawai sun hana uwarki zama ku rayu tare yanzu kuma ta tafi suce kanki zasu koma wallahi sunyi kadan .
Tunda na kula baki zuwa ni gobe in rai yakai lafiya insha Allahu ina zuwa kusfan naji ko wacece tayi wanan karan aikin don ba zan zuba ido haka su cutar dake ba gaskiya.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
2?? 5??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A KANKI ,A WURIN UBANGIJI ALLAH DOMIN AMANACE BABBA AKANI, , , , , , ,
KINSHIGO KARANTA ANAN KI BARMIN KAYANA BASAI KIN TUWA WANI BA DON ALLAH,,,,,,,

Mahmoud dake takowa a cikin mamakin abinda Nuran gidan mu ya fada masa nacewa anty Bantu ta koma zaria yau da safen nan ai ya bashi mamaki amma ya wayence wa yaron da cewa.
Kamar dai wace ake kora jiya jiya da gama buki ta nade kaya ta koma school duk wanan uban aikin da sukasha gashi ina son ganinta muyi magana akan yaran nan naga ita ke min kokari sosai game da harkan yaran nan.
Shiyasa nake son inganta mu tsara yadda zan dinga turo mata kudi tana cigaba da masu hidima don kona turo nan sai ace anyi wani laluran da kudin.
Ba ai masu yadda nakeso shine naga ya dace na dinga turowa ta wurinta yanzu Nura duk da yarone ce masa yayi idan kayi haka kuma yaya ina ganin zaka kara shafawa anty Bantu bakin jini.
Don hjyn ka da maman biyu zasu iya cewa aita shige masu gaba a cikin harkan jikokinsu kuma ita bata damu ba unguwan nan kaf kowa yasan yadda take kula da lamarin yaran nan har kiransu ake da yayan bantu.
Haka yasa na fara tunanen maye gurbin uwarsu da wata uwar don wanan matar nawa ba zan iya bata yayana ta rike minsu ba gaskiya.
Zakice Nura sa,anshine yadda yake hira da yaron kamar ya samu wani babba yana zancen dashi a lokacin Nura din ya bashi amsa da fadin ko haka zai faru indai a gidan mune sai ita anty Bantu din dai.
Kuma hakan yana da wuya nasan kodon yadda suke da maman biyu ba zata yarda da hakan ba gaskiya don ko shekaran jiyan nan saida sukayi wani babban case da ita akaita koke koke a gidan namu rayuka suka baci a banza duk kuma laifin na maman biyuce.
Inba sheri ba anty Bantu zata dafawa kazafin sata a gidan mutane su kuma da taje sai suka gwaleta don su suka bata abinda take cewa ta sata din.
Yanzuma kafin in fito din nan naji tana sababi duk da anty Bantu bata nan tana fadin wai don an rena mata wayau halan ba arzikin yarta anty bantu take ci a gidan kuba har take nuna tafi kowa yanzu a gidan ?
Wai har yanzu wanan kiyayyan da mama take nunawa yarinyar nan yana nan ke nan aina dauka yanzu data girma naga ta zama babban yarinya ta daina mata hakane ?
Saidai idan bata kyala ido ta ganta a gidan ba yaya amma kuklun abin kara karuwa yake akan anty bantu da mama bata sonta bata kaunarta ko kadan.
Labari sosai ya bashi na yan gidan mu don yana daukanshi dan gida yanzu shima ga shirmen nura ya zage yana koro masa sirin gidan mu kaf.
Aikensa yayi ya sayo mashi drinks shine nura din ya tafi shi kuma ya zauna ya nazarin maganganun nasu da yaron sai mahaifinsa ya dawo ya daga zai bisa cikin gida ya gaidashi a wanan lokacin wayanshi tayi kara ya ciro yana dubawa din.
Ya fiddota a cikin aljihun gaban rigansa da sauri yana dubawa a zatonshi abokin kasuwancinsa ne da yake dakon kiransa ya kirashi a lokacin.
Ganin wanda ke kiran nasa sunan Wasila matarshi yagani yaja dogon tsaki kamar ba zai daga kiran ba sai kuma kome ya tuna oho sai kuma ya daga wayan ya kara a kunnensa.
Honey kana inane wai gani fa na shirya tun dazun ina jiran ka kazo mu tafi kada yamma yayi muna a hanya don Allah ka duba time mana kagani.
Dafe kanshi yayi yama rasa me zaice mata a lokacin shiru ya dan biyo baya sai wasilan tace waiko baka jinane ?
Yayi saurin tattaro numfashinsa cikin natsuwa yace ki jirani gani zuwa yanzu ya kashe wayan da sauri ya tura aljihunsa ya shiga cikin gidan nasu donsu gaisa da mahaifin nasu a lokacin.
Ya dade suna zantawa da mahaifin nasa akan al,amuran duniya da kuma abinda ya shafi shi kanshi habibi din da kuma gidan nasu kafin aka sallamawa Alh ya fito ya barsu a zaune tare da yan uwansa.
Wanan karon layin Ibrahim dinsa ta kira tana tambayansa ina honey yace gamu tare wurin Alh ka fada masa rana nayi fa ya amsa mata da to zan fada mai ya kashe wayan ido ya tsurawa dan uwan kafin shima ya kallosa yace madam dinka cefa wai in fadama lokaci yana kurewa.
Don Allah shut up kada ka bata min raina a banza kyaleta can mara hankali inta gaji ta daina nemana bata ma da notin kai ko kadan dariya ibrahim din ya kumshe a cikinsa kafin yace haba honey kasan abinda take neman ka dashine yanzu ?
Wani kallo ya watsawa dan uwan nasa wanda ke tatare da zamu hadu dan iska kafin yaji ya usman na fadin wai ya hamza yace ka bashi key ya marya da hjyn Rigachikum gida.
Au zata koma yaune usman din ya amsa da haka nake gani gashi can dai tare da ita


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login