Showing 138001 words to 141000 words out of 347556 words

Chapter 47 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8791

dauki karyan duniya da isan baka isa ba ta sakawa zuciyanta lokaci guda tana wahala kan hakan.
Don yanzu ba boyo hassada da bakin cikin samira baya boyuwa a gareni don hussaina ta kirani take fada min watau samira munafukace na dawo na samu tana ba su mama labarin karya kan bukin nan.
Sai me Ussaina nasan dai niba yar iska bace yadda ake zato Allah kuma zai baiyana hakan komai dadewa a garemu mukai sallama na kashe wayan.
Zaune nake ina karatu a ajin gaba nake wasu matan auren ajin namu mutum biyu suna ta bayana suna dan hiransu kus kus caraf kunena yaji dayan na fadin ai na sayo wanan karan dafi da akace kin ganshi nan gashi nazo dashi ki gani.
Jin hakan yasa na dan juyo daga inda nake ina satan kallonsu wani abune na gani daure a wuri daya shiba ganye busashe ba shi kuma ba bawan itace ba.
Dauri biyu dayan da alaman ja haka jikinshi dayan kuma yayi kalan tsiro ya bushe din nan haka daure kasa hakkuri nayi na juya da kyau ina fadin .
Antyna meye amfanin wanan abin ne ina dai jin sunan shi amma ban taba ganinsa ba haka a fili don matar babana tana yawan min lakani da sunan karan dafi din nan idan mun samu matsala a gida.
Kai wanan din ai shine kata,un wurin duk wani matsalan mata kin ganshi nan kakar wanan tace mu nemoshi kin gashi nan ban tsaya sanya ba nasa aka sayo min shi jiya tana nuna min a fuskana.
Na dan kai hannu na juya shi dakyau ban gane komai a cikinsa ba na mayar mata ta karba take fadin amfaninshi ya wanci gun matane musanman masu matsala a ciki zuwa gabansu.
Tace damu mahadine sosai a wajen mata wanan din duk macen da take amfani dashi bata taba zama bora gun miji muko kinsan yanzu ma wata daga cikin matasa yanzu aiko saninsa bamuyi bama.
Matsalan shi dai tace ba,a son mace mai ciki tana yawan amfani dashi sosai hakana hardai hadin dake da balma a cikinsa sai idan cikin ya tasarwa haihuwa mace zata iya dan amfani dashi koshi ba mai yawa ba.
Ke kin gashi nan gashi baida kudi sosai wanan fa dauri akan dari dari aka banshi kinga mun bar abu mai amfani mun koma ga kaya nasara dake muna illa a yanzu.
Aida ace ke macen aurece a yanzu zan baki sirin wanan din amma yanzu saidai in fada maki wanda zai amfaneki akan matsalan affections donshi ke damun mata har yara kananu sosai.
Shigowan malamin namu daya dan makara yasa mu natsuwa lokaci guda har aka tashi kuma ban samu ganinsu ba saidai abin yana raina don ina son insan amfanin wanan karan dafin da mama ke yawan fada min ko wani lokaci.
Gida na nufa direct nashigo da sallama gwaggo na daki don haka na nufi kofan ta ina fadin sannu da gida gwaggo daga ciki ta amsa min tana fitowa don ni har na bada baya lokacin naji muryanta tana fadin.
Dazun ko bayan fitanki yar uwanki tazo gidan nan wai zata kwashi kayanta amma dakin na rufe tayi niyar fasawa amma ban yarda da hakan ba don bansan kudirinta ba.
Daukan kaya kuma wanda zata canzane ko kuwa tace cewa tayi dai kayanta tazo dauka koma meye nace taje ta dawo ai sai aji don ban tsaya ta kanta ba don na hango ruwan fitsara a idanunta.
Allah kyauta nace na nufi dakin nasa key na bude ina godewa Allah da gwaggo tayi hikimar hanata bude dakin a lokacin.
Don ba karamin barna zatayi min idan har kayanta tazo kwasa da gaske yadda gwaggo ke nufi din don nasan sai naga abinda raina zai baci idan nadawo.
Nashiga ban dade ba naji muryan Aliyu ya shigo nasa mashi kira yazo nan ya tayani gyara komai ko tsinke ban hada da nataba duk kayana na jibgesu a wuri daya hakama nata din.
Naba yaron dari biyu yace anty ki barshi nace karba na bakane kawai ai ya karba yana min godiya zai fita nake cewa ya diba min ruwa a bucket in watsa a jikina don haka nake da wanka kamar agwaggo duk da hausawa sunce yawan wanka na zubarwa mutum da arzikinshi.
Nafito wanka ina saka kaya a jikina naji gwaggo na kiran Aliyu tana fadin kai zoka kaiwa antyn ka abincin nan don nasan ba tambayawa zatayi ba ina jin hakan na karasa shiri na fito a nan na zauna don inci.
Doyace da miyan tantakwashi miyan tsofi yayi dadi sosai na zauna inaci Aliyu nage suna hira ?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 da gwaggo din mukaji sallama ciki ciki kowan mu ya dago itace dai din ta dawo tana fadin gwaggo ina wuni ta amsa daga inda take tana gyaran shinkafan hausa.
Ta amsa batace komai ba ta nufi hanyar dakin ina ganin hakan na tashi na bita zuwa dakin tsaye na sameta tana bin kayan da kallo kafin tajini shigowa ta juyo tana jan tsuki tare da fadin.
Ta Allah bata mutum ba wallahi zaki san shayi ruwane ai daga mutum ya huta da yan sa idoma ga hakan ke kika rage yawon labe laben gidan mutane yanzu kuma.
Ta fara daukan kayan zuwa waje tana fadin kai Aliyu zoka kama min fitar da kayan nan sai bataga yaron ba ashe gwaggo tayi mai ido ya fita dole ita keta daukan kayan zuwa waje wurin me Napep data tara.
Ya rage buta data sayo sai wani tsohon bukitin roba da muke aje ruwa ta dauki dutse ta tarwatsashi a tsakar gidan jin hakan gwaggo ta fito tana fadin ke ke lafiya ya hakan kuma ?
Lafiya kalau bandai amfani dashine a can inda zan koma kaico daki barwa yar uwarki gara kin fasa tayi shiru batace komai ba nima ban tanka mata ba iyaka na zauna a wurin kayana kawai ina kallon wayata.
Ganin hakan har ta kai waje tace Allah ya rabani yau da wahala zan kuma duba idan kayana basu cika ba wallahi zan dawo don bazan yarda ba.
Allah dai ya raka taki gona nayi arziki tunda mun rabu lafiya dake ai ki fadawa uwarki hakan indan kinje bata tankawa gwaggon din ba ta dai fice can bayan andan jima mukaji tayar da mashin din.
Sai ga Aliyu ya shigo yana fadin yau naga masifafan mace can ta tareni waje tana zagina waini dan iska tabar muna shegen gidan mu mai kazanta yau.
Sai kuma ta fara fada da dan mashi wai ya aje mata kaya a wullakance zai zubar mata a hanya haka dai suka tafi suna rikoci dashi.
Na tabbarar akwai abinda ya faru tsakanin su da baba da har ya yarda ta bar gidan nan don nasan yana da wuya baba ya amince haka cikin sauki.
Koma meye dai tayi gaba badai gidan nan ba kuma tunda ta kwashe kayanta ta barmu mu kazamai muyi ta rayuwa a cikin kazantan mu.
Kada zancenta ma yadameki don ban dauketa mai hankali ba idan gidan nan yana da kazanta ai haka tayi shekarun nan a cikinsa ko ita gidan nasu yafi wanan ne kyau ?
Jin abindana fada yasa gwaggo din danjin sauki tace bar sakarai har kadunan zanje in sameta gaban uwar nata in yanke mata kauna kiyi hakkuri gwaggo na sake fada cikin damuwa.
Babu wanda ya kira gida akan zancen tunda muna ganin cewa sun san da zancen barin gidan gwaggo din da zatayi don haka nima na share kowa akan hakan.
Ba muma yawan haduwa don tun barinta gidan sau biyu muka hadu koshi akwai dan tazara a tsakanin mu don haka bamu gaisa ba a lokacin.
Karatuna nake facing sosai don gujewa samun matsala don haka na mayar da hankalina akansa don shine babban burina a wanan lokacin.
Haka kuma ba wani namijin da yake damuna a lokacin yasa hankali kwance nake karatuna gashi na samu dan alawans din wanan contract din yana shigo min don haka ne yasa banda matsalan komai shi nake dan tabawa ina abubuwana na rayuwa dashi .
Sutura kuma Alhamdullahi gaskiya muna shirin canza aji alokacin don haka karatu yanzu yai min tsanani sosai sai yama lis nake shigowa gida ko a gidan banda time din tsayawa shiririta a yanzu kuma.
A cikin irin hakan muna gab da fara exam na dawo gida a gajiye ga yunwa don tun safe banci komai a cikinaba har lokacin biyar da rabi ya wuce ana batun karfe shidda na yamma.
Cornflakes na dauko insha ina zuba ruwan ke nan wayana dake gefe yayi kara haushin hakan naji a zuciyana duk da hakan hannu na mika ina daukan wayan.
Al,amin saudiya yadda nayi serving na gani hakan yasa na dan sake murmushi a fuskana na dauki wayan ina fadin yau bakin balarabe ya tuna da yar boyar Allah nan ne ?
Muryan maman saudiya naji tana fadin Ayya diyata nasan kinyi fushi damu kiyi hakkuri wayatace ta lalace sai komai da nake dashi a wayan na rashi ayanzu.
Yau din nan Al,amin ya shigo nake tambayanshi lambanki don ya kwana biyu baya saudi yana Dubai yana wani aiki tare da mahaifinsu.
Kunya naji sosai na fara gaida ita ta amsa har ina jin dariyanta take fadin ya karatu ya mutanen wajen ku kuma kowa lafiya ?
Lafiya kalau muke mama yasu Anty Aisha dasu ya Aliyu da Abbuh tace Alhamdullah Alhamdullah masha Allah mafi,miskilah kalas kwana biyun nan muna ta tunanki .
Ya karatu dai da saura ko kun hada sai naji gaba daya hausanta ya juye min ya canza kalar ta larabawa sak nake jin harshenta a lokacin.
Bayan mun gama gaisawane take fadin hayyah nace ko hutu kuke yanzune ko kun komane nace nan da sati biyu insha Allahu zamu samu hutu shiga zangon ajin karshe insha Allahu.
Masha Allah kai abu yayi kyau sosai wallahi ai hutun yana da dan tsayi ko don muna son ki kawo muna ziyara nan insha Allahu.
Saudiya na fada ido waje tace kwarai kuwa idan babu takurawa ga hakan muna son ki shigo daga nan ki tsaya kiyi aikin hajji tunda lokaci ya karato .
Nagode mama nagod,,,,dakata mamata hakan dai ba zai taba karatun ki ba ko nace insha Allah zanyi reporting a school kafin mu rufe din tace shike nan zaki turo muna da account dinki za a turo maki kudin da zaki fara zirga zirga kije kiyi visa da sauran abinda ya kamata.
Zaki kuma hadani da mahaifinki idan kin koma gida in masa bayanin komai in roki alfarman zuwan naki wurinsa idan zai yarda duk da nasan bazan samu matsala ba .
Amma ya dace mu sanar masa kafin mu fara komai ki bari ni zan kirasa da kaina kada yaga mun shige masa gaba na kara mata godiya ta kashe wayan.
Wani ajiyan zuciya na sauke tare da daga hannu sama ina fadin Alhamdullahi Allah nagode ma Allah nagode sai hawaye sha na farin ciki.
Ban fadawa kowa ba a ranan kuma na tura mata account dina da lamban babana nace idan ta kirashi a sanar dashi kada ya fadawa kowa sai tafiyan nawa ya tabbata.
Haka na karasa exam a dadefe nakuma rubuta application na tura department din mu yana kaiwa wurin HOD aka kirani yai min wasu yan tambayoyi na bashi amsa takardan ya tafi incase koda zan samu matsala na dan bata lokaci a can din.
Shigana kaduna biyu saidai in samu baba a kasuwa muyi maganan da zamuyi in wuce na ukun ne na samu Nura wurin shi har na bashi sako yakaiwa mahaifiyarsu da Ussaina.
Sai satin da zanyi tafiyan na fadawa gwaggo tana ta mamakin hakan zanje Abuja don sakon dana tura masu suka kirani suna aon ganina.
Motan direct nashiga irin zuwan farko danayi na samesu a bakin aikinsu office din Abbas na nufa sai na samu sun shiga meeting na zauna waje ina jiranshi a waje.
Allah ya taimakeni ya fito daukan wani takarda baiko farga dani ba a wajen saidana gaisheshi ya amsa sama sama har yasa kai zai shige office din sai kuma ya juyo ya sake kallona yace.
You yaushe kikazo ne nace dazun nan na iso na samu kana wajen meeting na zauna har ku fito baiyi magana ba saida ya shiga office din ya fito yace dani taso muje ciki .
Jin hakan yasa na tashi na bishi a baya dakin meeting din ma,aikatan muka shiga kusan duk wani babba a wurin wanda yawancinsu yan kabilune daban daban na fadin kasan nan kowa na ciki a lokacin sunkai su goma sha.
Suna zaune a saman taburin meeting ganina dashi yasa sauran suka bini da kallo sabanin shi Boss din daya zauna ya kurawa computer ido a lokacin.
Baya na dan dakata na tsaya ya isa har inda yake zaune ya danyi mai magana a kunne sai ya dan dago ya kallo inda nake tsaye din ina tsaye na takure kamar anyi bakuwar buzuwa.
Sai naga Abbas din ya jawo kujera ya zauna ya dan juyo inda nake yana fadin kizo ki zauna miss Fatima muna son magana dake a yanzu.
Kujeran daya nuna min na zauna din kafin shi Abbas din ya fara fadin don Allah kuyi hakkuri kunga na shigo da ita yanzu dama issue dinta ya kamata ace mun fara dashi.
Kowa yasan ta dai a nan to yanzu don ko baka taba ganinta a fili ba kun sheda fuskanta a tallan mu da take muna sunan miss Fatima daga kaduna tana karatu a A,B,U zaria.
Ta hada contract damu na shekara uku amma yanzu ta nuna ba zataci gaba da hakan ba shine muke son muji ko akwai wani abinda ya faru da ita game damu ?
Ya dan kallo yana fadin hjy muna son muji ko meya faru kikace ba zaki samu cigaba da muna wanan aikin ba a yanzu ?
Ko fitowan ne bai gamsheki ba na yadda aka tsara maki da sauri na dago kai daga inda nake zaune cikin dan rawan murya nace ba hakana bane.
Kawai zan danyi tafiyane zuwa saudiya zan kwana biyu a can yasa na turo da hakan amma a gaskiya ba hakan bane a zuciyata.
Don maganan da mahaifin mu yayi min ne ya tsaya min a raina tun lokacin banson abinda zai zubarwa mahaifin mu da kimarsa a idon jama,a a sanadina.
Zance yau naji muryan shi a fili don tareni yayi da fadin wanan ba excuse bane da zaisa ki rubuto muna kin jaye daga wanan aikin?
Dole akwai wani dalili na naki na fadin haka don haka ki fada muna koma meye ba zamu tauyeki ba a nan dan shiru nayi ina kallon table kafin in dago ince dasu shine kawai.
Ok jeki ki jiramu idan mun fito zamu ganki ya fada nikan na mike na fito na barsu a ciki raina bace don aiba dole bane aiki dasu din tunda nice maiyi na kumace na fasa yanzu.
Ina nan zaune sai guntun tsuki nake ja ni kadai a zaune gashi banzo da niyar kwana garin ba don a zatona zuwa zanyi kawai inyi signing din jaye aikin.
Don dole saina saka hannu aikin company ne zasu iya kaini kara kan hakan idan nayi sakaci sai karfe biyu suka fito kuma suka wuce sallah an dade bayan sun dawone aka kirani wani offie can da ban taba shigansa ba.
Da dan tsoro a zuciyana na shiga shi kadaine zaune office din ya hadu ya tsaru sosai wajen haduwa jin nashigo ya dago kai yadan kallo kofa yana fadin bissimillah shigo mana.
Na karasa ina gaidashi ya amsa tare da fadin kince zaki bar aiki damu duk da nasan dole akwai wani kwakwaran dalili badon zaki tafiya yasa hakan ba .
Nasan da zaki samu kalubali daga wajen mutane idan ba kinkai zuciya nisa ba kin daure daga munanan kalaman da zasu rika jifanki dasu ba zaki taba zama wani abu a duniyan nan ba idan kinbi ta mutane yanzu.
Don haka idan har kina ra,ayi zamu baki dama ba tare da mun dakatar dake daga tafiyanki ba zaki samu daman yin tunane har na tsawon wata uku zuwa hudu masu zuwa shike nan.
Abbas zai sakawa takardan ki hannu kan tafiya duk da nasan har zakije ki dawo ba tare da mun nemeki ba a nan komai ke nan zakiji daga Abbas din ya fada yana mikewa nima na mike da sauri.
Ya fara fita na fito suka hade da wani bako dayazo ganin shi naji bakon na fadin mayen karfe kardai ince wance gaskiya ka iya zabe abinda naji ke nan a lokacin na wuce zuwa kasa.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
4?? 3??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login