Showing 273001 words to 276000 words out of 419207 words

Chapter 92 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1522

kyaleni tun dazun ban son irin haka koda kuwa mun samu sabani ne a tsakani mu dake.
Gane cewa danayi hankalin kowa yana a kanmu ashe kamar auren mu yafi na kowa rikicewa ne kuma ga yadda shi yake kokarin kwantar wa kowa da hankali yasa nayi danmaran bin mijina sau da kafa a zauna lafiya kamar yadda kowa ke bukatan hakan a tare damu.
Wanan ke nan haka yasa shakuwa da kaunar dani dashi duk muke a sabon shiga don ba rayuwan aure irin na malam baushe yasan dashi ba irin wanda mukeyi a yanzu kuma muke fatan kafawa a gidan mu nan gaba in Allah ya nufa muna raye.
A wanan lokacin da hjyn su ke zuba ido taga dawowanane gida kuma salma suka samu matsala da Ahmed inda yai mata dukan tsiya ya korota gida a wani safiyan.
Wanda hakan ya dagawa hjy jummai hankali sosai don a daidai lokacin da take gani fa,idan auren Ahmed din da salma tayi a lokacin ne kuma aka samu matsala mai karfi a tsakanin su.
Don hjy tasha tambayan shi kudi ya turo mata ta account din ta dayaga abin ba zai fishe shi ba ya daina koda sun roke shi din sai ta tura salma na zaran mata idan ya shigo da kudin shago kafin su kai banki.
Ganin zata kashi a kunya ranan ya shigo da kudi sunyi dare bai samu kaiwa banki ba sai ta zare dubu hamsin a ciki.
Washe gari da ya tursasa ta ta fito da kudin tace ba ita ta dauka ba inda ya matsa mata taki fitarwa ya bata wa,adin kafin ya dawo ta tabbatar da ta aje mai kudin shi a inda ta dauka din.
Saida ya fita ta kira uwar tana sheda mata abinda ya faru nan ta hau diyar da fada yaya akayi har ta bari ya gane tana zara .
Tace hjy bafa darin da kikace in dauka ba na diba hamsin kawai na diba kuma saida ya gane na taba kudin.
Hjy tace kaji dan kawai yo kudin na waye da zai hanaki taba kudin uban ki ina nashi shi wahalan banzane nasa a ciki don dole ya baku dukiyan ku a karshe a raba maku bayan ya gama wahala daku.
Hjy amma dai da kibari in mayar mai da kudin shi don yayi fushin haka sosai wallahi tace na fada maki ba za,a mayar ba duk abinda zaiyi yaje yayi.
Da Ahmed din ya dawo ya samu bata mayar mai da kudin ba shine yai mata duka ya kuma amshe yarsu dake shan nono a lokacin yace kada tasha nonon sata.
Ya turo salma gida da sasafe yace taje gida ta fadi halin da take mashi da bakin ta .
Salma ta dawo da kukan ta da yawa na gidan sunga shigan ta a cikin wani yanayi tunda safe haka .
Ran hjy jummai ya baci sosai da dukan da yaiwa salma hakan yasa ta samu kawu a falon shi tana fada wai kamar Ahmed don a wullakanta mata ya anbashi zai mata duka irin haka.
Har ta gama kawu baice mata komai ba ta gaji da bambami ta fita a lokacin ya kira mamu yace ta kira mai mama da gwaggon ta Amma ke nan.
Bayanta dawo ne ya tura dan wajen hjy din autan su yaya Umar ya kira mashi salma a part din su don ko da yaushe yaron yana lake da mahaifin su.
Bayan sun zo sun zauna ne ya kalli salma yace uwata sai naji wani labari kuma da banji dadin shi ba duk da nasan halin Ahmed tun farko amma baka shedan mutum yanzu.
May ya kawo wanan dukan haka har kuma ya koro ki gida da safen na ya karbe yarshi cikin kwanciyan hankali yake mata tambayan.
Salma jin yayi shiru ta dago kai a hankali ta kalli mahaifin nata tace a cikin kuka daddy ka gafarce ni ya Ahmed yana da gaskiya.
A daidai lokacinb lokacin hjy ta fado dakin tana fadin ni bansan abinda yasa ba a bani yancina yanzu a gidan nan matsalan kowa zai taso ayi shi asiran ce amma idan yazo kaina sai kowa ya gama sanin komai.
Ki fada min nan waye bare a gurin nan yanzu mahaifiyata da ta kawo ni duniya ko yar uwar haihuwata abokiyar shawarata ko bana raye zata kula da abinda na haifa.
Kallon inda suke zaune ta danyi ta yatsune fuska kafin tace nidai bana jin dadin hakan don ba haka akewa kowa ba bai kulata ba ya juya wurin salma yana fadin ina jinki uwata .
Ganin ma haifiyar ta a zaune yasa ta kasa fadin abinda tayi niyar fada din a lokaci sai kukan da takeyi.
Waya ya dauka ya kira Ahmed yace gashi tafe an dan jima sai gashi ya shigo da sallaman shi yana rungumay da yarsu a kafadan shi da alaman yarinyar tasha kuka na rashin uwar tane.
Ya gaida su a jam,i ya dago kai ya kalli Alh yace gani Alh yace eh na kiraka ne don naga uwata ta dawo gida ga duka ga ka kuma ka karbe mata ya da wani zataji wanan hukunci yayi tsauri sosai mana mlm Ahmed ?
Dan dukar da kai yayi kasa yayin da hjy daga gefe take sake mai magana a fakaice ya dai girgiza kai yace Alh ka gafarce ni dole nayi wa salma wanan danyen hukunci don tana gap da sakani a kunya idan banyi hankali ba Alh.
Kunya kan ai kariga da kaji shi tunda har kake iya dukan ta kan abinta don baka da ta ido hjy tace daga gefe.
Hannu kawu ya daga mata tare da fadin jummai banson i kara jin maganan ki a nan gurin don ban gaiyato ki ba kin sani.
Ya juya wurin Ahmed din yace ins jinka malam Ahmed sai Ahmed din ya dan gyara zama yana gyarawa yarinyar kwanciya ajikin shi mama hadiye???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? tace miko tana aida farko naki karban ta ne don da baifi da ba ni ka linkidawa nawa yar duka zan lalashi naka yace dolene gwaggo in duki salma.
Yana mika ma ta yar yake magana a lokacin, muna jinka Amma dake gefe a kule ta fada eh kaka wallahi salma gata nan ba a binda ta nema a gurina ta rasa.
Koda banda halin shi a lokacin zanyi kokari inga na saya mata daga baya sai dai tun lokacin da naga suna son jefani a cikin wani rikici ita da hjyn su na fara canza mata a karshe da sukaga na sauya hali sai kuma ta koma zaran kudi shago idan na shigo gidan dashi.
Sadiq ya ban shawara in dinga kirgawa tunda ina zargin ana tabawa nakoyi hakan sai gashi na samu ta zare dubu hamsin a ciki daga safiya zuwa washe garin jiya.
Innalillahi kawu yace salma yashe kika fara haka a ina kika koyi wanan halin mara kyau dole ko nine ylin karbe ya yata ka kyata min da baka koro muna ita gida ba kawai saida sheda halin da kai mata don nima da ina da karfi da yau na karamata akan wanda kai mata.
Ya juya wuri hjy yace jimmai kinga abinda kikaja wa yarki ko har kikazo nan kina fadan karya da gangan dama daji nasan kece da matsalan komai donma mlm Ahmed ya saya wani abin bai fada duka na ke nan.
Yes nasan ka saya duk wanda yaji bayanin ka kuma yai nazarin sa zai sanda hakan ka saya maganan don kawaici.
Yanzu ga yarki nan ba zan bashi hakkuri don ya mayar da ita dakin ta tunda bansan lokacin da kika koya mata yin hakan ba.
Dama ba inda zata koma tunda banda duka har kazafin sata yai mata kuma salma naji haka tasa kuka tana fadin daddy ka bashi hakkuri na daina dama mamace ta dorani a hakan don Allah daddy kada kai fushi dani ina son mijina wallahi na daina daga yau din nan.
Ke tafi can albasa batayo halin ruwa ba wallahi akan namiji namijin ma wanda keci a karkashin mahaifin ki har zaki zauna kina wanan kukan haka ?
Ke ya isa haka mara kunyar banza kawai dama haka Allah yake sakamakon shi idan kace ruwan wani baya tafasa kai naka ko dumi baiyi.
Kinso a sako yar mutane ai mata wullakacin da ba ita keda laifi a kanshi ba sai Allah yaki ta taki aka koro maki yarki gida da mugun sheda.
Mai yafi haka zafi da akaiwa yarki jimmai har don baki da kunya kike budan baki kike fadan magana hakan nan ke kan bansan lokacin da hankali zaixo maki ba wallahi.
Mutum da riko kamar jikan fir,auna haka a,a hajiya may ye laifina a cikin zancen nan da har kike laka min wani zance da ban sani ba can inma nace a sako wata ai danane ko ba dan wani ba kowa yayi iko da nasa dai.
Tana fadi haka ta tashi tafita daga falon kallo Amma kawu yayi yana fadin da alama dai tayi wani abin kuma aka boye min Amma ta mike tana fadin tana fasawa ne ita kasan mai hali baya barin halinsa ai.
Ta kalli Ahmed dake zaune tace kaga jikana kayi hakkuri idan tana da hankali wanan ya isheta ishara ai.
Babu komai kaka kamar yadda yake kiranta komai ya wuce tunda ta gane laifin ta kawu ya kalleta yace ina kudin da kika daukar mai salma ?
A hankali ta dago kai tana fadin naba mama da nazo dama ita tace tana son kudin .
Ya girgiza kai tare da fadin kin gani uwarki zata kashe maki auren ki salma naku bai hadaki fada da mijin ki ba gashi ta turaki yin abinda ba daidai ba.
Kada ki kara haka na rokeki kiji uwata wanan ba tarbiyan zuri,an mu bace ko kadan sai ya dukar da kanshi kasa don bakin cikin da yake ji a lokacin.
Abin gulma ya samu a babban gida irin wanan nan danan maganan ya fara yaduwa a gidan kowa na fadan albarkaci bakin sa.
Alh bai kara bin ta kowa ba saida aka kwana biyu har salma ta koma dakin ta a lokacin shi da kanshi ya mayar da ita yaba Ahmed hakkuri kan abinda tayi mai.
Ya samu hjy jummai har dakin ta bayan ya dawo daga kaita din suna zaune da Nafisa a falo suna kallo da dan autanta dake kwance saman kujera yana karatu yana kallo.
Shigowan mahaifin nasu yasa yara tashi bayan sun gaida shi ya samu wuri ya zauna da kyat hjy dake zaune ta zubamai ido don tsan magana ya shigo dashi wurin ta.
Ya danyi shiru yana kada sandar hannun shi kafin yace jimmai guri ki nazo yau sai dai magana nake son yi dake na karshe a kan diyana.
Ina sauraren ka tace yace haka na da kyau yanzu kinga abinda nake gudu har yakai ga diyana ko halin da kike min a gidan ina daga maki kafa don ba girman ki bane yin hakan.
Yau gashi kin koyawa yarki zatayi magana ya daga mata hannu yace dakata in gama magana ta.
Yanzu ke dadin kine mijin salma ya kawo karanta gidan nan karan ma akan sata jimmai satan kuma ma da hannun ki a ciki don salma ta fada muna rana kudi data dauka nasa yana hunnun ki ta baki do ke kika turata ta daukar maki.
Ita salma ta fada maku haka ita salman tace ni tabawa kudin kaga Alh idan wani sheri kake nema ka lakamin ka fito fili ka fada zaifi.
Ba sheri a ciki maganan nan idan nayi maki sheri in karu damay kina uwar yayana damay zai karani dashi.
Kin san dai muyi haka dake a shekarun baya har kika koma gida irin haka tun kan a haifi ita kanta salma di ko kin mantane ya fada yana tsure ta da idanuwan shi da sukai ja tsantsan bacin rai a fuskan shi.
Ina kin tuna hakan yanzu yau kuma ga yata zaki koyawa wanan halin jimmai ya fada yana kada kanshi.
Yau ko yar rikon gidana akace tana wanan halin ba zan yafe mata balle ace yar cikina ne tayi hakan.
Shin kin san abinda yasa na kyale salma ban dauki mataki ba akan maganan nan ?
Don zafin ciwon da kike dauka ya yi min illa baikai yadda kike zato ba jimmmai duk kika karbi girki tun kwancina ciwo kada ki dauka don ban taba magana bane dan kudaden da nake ajewa gidan nan da wanda nake samu bana gane kansu sai ranan Allah ya nuna min kina dauka a zaton ki ko nayi barci ne saidai baki san idona biyu ina kallin a safiyan ne kuma da zaki kula nace na dakatar daku girki a gidan nan bado komai ba kada in maki ke daya ayi zaton abu.
Duk da ita maryam tana da nata halin a wani bangare bakuji tausayina ba a halin da nake ciki jummai sai yaushe zaku tausaya mi kuma.
Yau matar da take da zuria haka irin naki a gidan nan zatai maka haka inaga wata dabaka tara zuria da ita ba.
Yau idan diyan ki sukaji wanan jimmai yaya kike son suyi da ranau mai suka kasa maki dashi na rayuwa jimmai ?
Ni dai a bangare na ba wanda zaiji wanan zancen sai idan ke da kanki kika dabawa cikin ki wuka kika fito fili kika fada amma ina rokon ki jummai kiyi min addalci kada ki bata min yara da halin banza mu sam man matan nan don wuyan aure zasuyi ga al,umma insha Allah ga mazan ma banda abin da zance dasu sai addu,a a garesu.
Sai magana na karshe zancen yaran nan dake kasan waje jimmai ina rokon ki daki bar min yara su zauna lafiya do Allah kin daiji abinda hajiya ta fada a kanki.
Yana fadin haka ya mike ya digara sandan dake kara mai karfin tafiya ya bar dakin a jiyan zuciya ta sauke da karfi tabi baya shi da kallo har ya fice.
Dama tayi tunanen ranan ya ganta do a yadda yake kwance ba haka ta juyo ta samay shi kwance din ba sai dai ta dauka ya gyara kwanciyane kawai ashe duk yana ganin ta hakkuri irin nasa yasa bai mata magana ba.
Jikin ta yayi sanyi sosai tare da na daman sai kuma danta babawo daya ya fado mata a rai tace cikin takaici yanzu dan nan babu halin yin siri dashi tsakani da shi ke nan daga lokacin ta dauki fushi dashi sosai.
Bata kirashi ba sai dai shi kan turo mata sakon gaisuwa kullun garin Allah ya waye ko sakon barka da jumma,a sai kaji gidan shiru kwana biyu fitina da tsegumi ya rage sai an samu wani haka babban gidan ya gada dama.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:26 - ??5惙5惙5?: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM YA HAIYYU YA KAIYUMM, , , ,


GA MASU BUKATAN LAYIN KIRA ZAKU IYA KIRAN 08036959257 KO 09026931792 .
DON TURA KUDI SAYA ZAKI IYA TURAWA TA WANAN ACCOUNT DIN KAMAR HAKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN KIRA NA DARI UKKU KACAL NAGODE

Bayan watanni sun shude sun bada baya abubuwa sun faru dama a wanan lokacin ciki harda rikici sosai da merry da yaya umar sukayi akan yar shi har wurin hukuma.
Inda hukuma taba uwar daman rike yarta akan addinin ta har zuwa lokacin da yar zata kai shekara sha bakwai ko takwas a lokacin tana da daman zaban addinin da take so a rayuwan ta.
Wanan matsalan shi ya kara ja baya da alakan su sosai suna haduwa don yarsu saidai ba kamar baya ba da ko yaushe suna like da junan su cikin so da kulawan juna irin na family din dake cikin farin ciki a rayuwan su.
Ga Allah yasawa yar son mahaifin ta a ranta ita zata matsa sai uwar ta kira mata uban sunyi waya ko ta tursasa mai yazo tana son ganin shi.
Zuwan bai haifar da wani jin dadin rayuwa a gare su don a karshe zasu kare da fadane don uwar bata taba yarda ya ya koyar da yar wani abinda ya shafi addinin shi can.
Wanan kan hada su fada sosai har yai fushi ya bar masu gidan ganin ya matsa akan sai yar ta koyi addinin shine yasa yanzu ma ta daina zuwa birnin London din sosai.
A rayuwa irin nasu na turawa nacan hakan da farko bai wani damay ta ba don tasan zai gama fushin shi na dan lokaci ne ya dawo gare su don baida wata ya da yake gani a duniya bayan faith din ta.
Da wanan tunane ta watsar da zancen shi tana jiran dawowan shi gare su a duk lokacin daya kare fushin shi dasu din .
Don iyayyen merry din suna tsaye sosai a kan yarsu don sun tabbatar da basu taba yarda ya ja ra,ayin ta zuwa wani addini haka yasa ko yaushe suna manne da yarsu don kada kewan hakan yaja ra,ayin ta ga mijin ta.

Yau Friday bamu dadewa a school kamar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login