Showing 15001 words to 18000 words out of 419207 words

Chapter 6 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1389

cuta masu dai a gidan nan ta wani famni ko ?
Ya kamata ki dinga nazari idan kinga na aiwatar da abu ba wai ki dauka nayi hakan don ra,ayin wata bace a gidan .
Tunda ya fara magana har ya ambaci sunan hajiya maryam jikin ta yayi sanyi akan maganan nasa da yaga yanayin nadama a gurin ta yaci gaba da fadin.
Ni da zaki bi ta nawa ki kwantar da hankalin ki don bada ke ya kamata kullun a rika ji bakin a gidan nan da maimuna ba tunda dai kece babba.
Shi kuma auren maimuna da nayi ba haramun bane yinsa sai karin zumunci idan kin matsa na saki maimuna ma wata zan kawo gidan nan tunda yanzu na gane auren mace fiye da biyu kuma.
Wani kallo ta watsa mai daya fadi hakan tare da fadin watau ma ba zancen zama da mace daya kakeyi ba ke nan ?
Kwarai kuwa ban maki wanan alkawarin ai tun farko kinga idan kun fitar da maimuna wace zan kwaso kila tafi maimuna fitsara da kuke fadin tana maku ko yaushe tazo ta gyara min zaman ku a gidan nan tunda ita maimunan tana bin ku a hankali bai maku dadi ba.
Mu maza ba ai muna haka ku bar mu da abinda muka gani muna so on haka gara maimun kin santa tun farko kin san halinta .
Gaba daya jikin ta yai sanyi da jin maganan ta hankalinta yafi tashi dajin yace ko maimuna ta fita wata zai kwaso masu take natsuwa ya kamata har take fadin.
Ai sai mu zauna muci kan mu nidai dama raini ne ban son a gidan nan don haka sai a kiyayye don gaba.
Yace ba wanda zai rainaki a kidan nan muddin ina raye don haka ki barni nasan abinda nakeyi ranan hjy jummai da tunanen maganan shi ta kwana a ranta.

BAUCHIN YAKUBU, , , , , ,

A cikin garin misau gidan malam sale ba wani babban gida bane na azo a gani gidane irin ginan kwatas din nan da ake sayarwa na gwauni aima ma,aikata gwajon shi su saye.
Gidane na mata biyu sai falo a tsakiya da ban daki sai kitchen wanda kowa yake sharing a gidan
Yaran malam sale tsohon malamin asibiti ne a primary health care aiki ya kawo shi misau daga azare har ya zauna misau din saboda dadewan shi garin da kuma auren yar garin misau din da yayi.
Yaransa goma wanda mata biyun suka haifa mai sai dai yanzu wasun su sun girma do haka ba zaman gida sukeyi sosai ba.
Gidan malam sale gidane da mata ke iko a cikin shi hakan ya jawo lalacewan tarbiyar yaran gidan kamar yadda wasu dake gane masu suke hango hakan a gare su.
Don uwar yaro zata iya saka shi yin abu yaro ya kafe akan ba zaiyi wanan abin ba ko a hana shi yace sai yayi .
Hakan ya samo asali kan rashin zaman gidan da malam sale din bai faye yi ba din da zaran ya dawo daga gurin aiki zai wuce chemest di shi da yake dan sayar da magani a kasan uguwar su.
Malam sale wane ga marigayi Abubakar mijin hjy maimuna na farko da Allah yayiwa rasuwa shekaru biyar da ya wuce inda ta dawo kano da zama a lokacin ta bar yarta can a hannun kakanta mahaifiyar marigayi din.
Sai lalura ya kama tsohuwar zaman su yanzun ya dawo misau din gidan danta wa ga marigayin danta.
Kamar yadda kowa yasan mutan misau da karatun addini dana boko suna noma da kiyo kamar yadda yake al,adane hakan ga kasan hausa sai wani dan sana,an daba,a rasa ba.
Sai dai gidan malam sale abin yasha bambam don yaran gidan gasu da son hutu sun ki tsaya su dage ga karatun boko ko na addini wanda hakan yana cikin matsalan da hjy maimuna take hangowa yarta akan zaman gidan.
Wanan yasa da zaman su fatima yar gurin hjyn ta dawo nan karatun nata ya fara rawa aje yau gobe ba a zuwa har ma a debi lokaci ba a je ba.
Gashi ba wani kula a gidan zakaga yaro ya shigo da ledan idomie yana dafawa ya bad abincin gida bai ci ba duk da malam salen yana iya kokati shi gurin ganin ya kawo abinda za a sarafa aci a gidan wanda shine ya jawo mashi wanan bakin wahalan bayan yayi ritaya.
Ko dan makarantar da take zuwa sai da taimakon gwagon ta kanwar mahaifin ta Adda ta samu take zuwa makarantar jefi jefi don ba,a sata da zaman su ya dawo garin ba.
Da kyar yaran gidan suke kare secondary school di wanda dags nan sun kare karatu ke nan sai zaman bin gari da yawon buki.
Wanda duk wanan abubuwan yana cikin abinda ya tayar da hankalin hjy maimuna da zama ta gidan ba wanda ke kula lamatin wani kowa kansa ya sani a gidan daga manyar har kananan.
Dan abinda kakan ke samu take tallafawa rayuwan yar jikan nata dashi idan kuma bata dashi sai dai su hakkura ke nan.
Hakan baisa yarinyar ta dan canza ga tarbiyan da take dashi ba sai dai akwai inda take da dan rauni wanda zaman gidan yasa ta koyi rashin kunya sosai don hakan taga anayi a gidan itama ta koya ta iya.
Ga yawo bin makwata saboda gudun aiki da aike tula mata a gida don sun ganta da zafin nama aiki baya sha mata kai ko kadan
Kamar yadda kowa ya sani mutanen azare gauraye ne sai dai akwai fulani da yawa a cikkn su hakan zuri,an su fatima ma fulani usuline don har yanzun kakar tata bafa jin hausa a baki ta sosai sai ta hada da fulanci.
Itace komai na kakan tata da farkon zuwan su babu mai taimaka ma lalurar kaka sai da Adda tazo gidan tayiwa mata gidan yankar kauna kafin su fara dan taimakawa dattijuwar.
Yau ma zaune take a gaba kakar nata tana ci dan abincin da ka saka masu wanda wani lokaci dole kaka ke hakkura ta barwa jika nata tacinye sai dai tausayi kakar nata wani lokaci bai barin yarinyar taci abinci sai tace ai taci a gidan su kawar ta Rahama gidan da ke makwabtaka dasu inda duk yawon ta idan ka nemay ta ana zaka samay ta.
Dan kadan ta taba shinkafa da waken da take ci tace da kakar tata ta koshi don kakar ta samu itama ta taba bawai don ta koshi tace hakan ba.
Sai da yarinyar mai tausayi ta tabbatar da kakan ta koshi ta debo ruwa ta kawo mata ta wanke hannu ta kawar da kayan ta dawo ta dan zauna a dakin nasu wanda ke ta wajen gidan da aka gina aka kewaye da kwano ya shigo ta cikin gidan.
Ganin kaka nata ta dan kishingida yasa ta mikewa don tasa yanzun za a kwala mata kiran aike ko wani aiki na gidan wanda ya kamata ace yan matan gidan sunyi gasu zagada zagada dasu amma basu kawar da kara a gidan nasu.
Na fito ke nan daga dan dakin mu da aka ware muna a gidan ina sanda don kada wani a gidan ya ganni ya aike ni ko yace in mashi wani aikin.
Ta kai daidai kofan fita tajiyo muryan mama saude tana kiran ke ke ke Fatima ina ji hakan tuni ba baza da gudu na bar gidan ina jin tana fadin ai zaki dawo ko yaushe kika gama gantalin ki kika dawo wanke wanke yana nan yana jiran ki a gida nan.
Jin hakan ya falkar da kakan nata da bata san fitar yarinyar daga dakin su ba sai murya taji ana kwala mata kira daga waje kuma tasan bata dawo ba tunda taji kalamin saude din kan yarinyar.
Da kyar ta samu ta mke ta dan dogara kafan ta zuwa waje ta samun sauden a zaune tana wanki tana sauraron wankan yan wasan hausa tana bi.
Sai murya dattijuwar saude taji a kanta tana fadin haba saude yar nan ita kadaice a gidan nan ina ga yaranan birjit a gidan nan su ba yayan moriya bane sai wanan yar marainiyar Allah kwaya daya tilo a gidan nan da ba uba uwa kuma tayi mata nisa ita kadai ce ko yaushe tsaye a gidan nan.
Yarinya babu daman ta motsa kowa dai fatima fatima don Allah ku bar yar nan ta huta hakana mana, ko kwatanta a kan ku idan haka ya samay ku ko yayan ku.
Tsohuwar bata kai ga ci gaba da maganan ta ba tajiyo muryan Tj bayan ta daya daga cikin jikokin ta na gidan yana fadin dallah ji wanan tsohuwar.
Yomar idan ba a saka ta aiki ba wani moriya take dashi a gidan nan bayan dan aikin da takeyi mafarin ki lalata yarinya kawai.
Shiyasa ai yanzun bata tsoron kowa a gidan nan wata jikan nata da taji ana maganan ta fito daga daki tana daura dankwali a kanta zata fita yamma yayi zata ta zubar din da suka saba .
Take fadin kema wai manjo ina ruwanki kiyi fama da kanki mana kina wani fada kan wata fatima can kamar ita kadaine jikan ki a gidan nan.
Da anyi magana kice yeyeyeye, , , , wai yar marainiyar Allah ce ita kada a taba ta ubanta ya mutu waye waye da sauran su.
Ikon Allah yanzun ni kike kwakwayo yar nan komai abinku dai nice na haifi uban ku sai yaro farko yace yo ai shi kika haifa bamu ba sai kije ki ta haihuwar su can.
Badai zaji taba haihuwan mu ba mu tace wa ni Allah ya tsari gatari da saran dutse da in haifi irin ku ai gara in zauna ba haihu yafi mun jika ji shigan ka kamar ba dan musulmai ba ji kanwar ka a haka zata fita uwayen ku na ganin su.
Shine bakin cikin ki inji yarinyar da ke murza janbaki a bakinta ta gyaran fuskanta ko inzo in shaga mak ne dallah ban wuri gantalaliyar da bata san ciwon kanta ba .
Diba uwarki ne nan zaune take wankin kayanta da kanta baki san ki kama mata ba aini yarinyar nan Fatima tafi mun ke sau dubu wallahi a gidan nan.
Ke tafiwa ba muba inji namijin kai rufe mun baki mai sufar arnakun farko jika ji wanan shigan a haka kake bin gari kamar wullakantace.
Haba babba zagin yayi yawa hakana ai shigan zamanin nan ne haka ba wai ra,ayi bane Saude dakan ki kike fadan haka a gaban yaran nan.
May ye a ciki babba yanzun akan yar jikan ki da kike so kike wanan tada jijiyan wuyan haka yaron ya matsa kamar zai mangare yar tsohuwar.
Salati ta saka tana fadin yau naga yaron kawai Allah ya ban lafiya in bar gidan nan da kafana.
Aike ne dai da aiki fatima ba zatayi ba yau a gidan na soke wanan a gare ta caraf uwargidan malam sale ta fito daga dakin ta tana fadin.
Babba kibar wanan zancen don Allah kada yarinyar nan taji dadin kara finjiraiwa a gidan nan hinjira kan ai ga hinjirarun nan a gaban ku su da ba a iya aike ko nan da can.
Aikine daga yau idan fatima bata yi shi ba bazata kara cin ko loma a gidan nan kunji na fada maku.
Manjo dake kallon ta a ciki mamaki ta kasa magana sai cewa tayi Allah ka kawowa yar nan dauki a gidan nan ta huta ganin wanan warin a gidan wan ubanta.
Ta juya da kyar zuwa dakin ta na faman mita akan abinda akewa yarinyar a cikin gidan.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
16/11/2021, 22:37 - ??5惙5惙5?: YA ALLAH KA GAFARTA MUNA KURA KUREN MUN WANDA MUKA SANI DA WANDA BAMU SANI BA UBANGIJI KAJI KAN MU KA GAFARTA MU.
KASA MUNA YSORON KA DA IMANI A CIKIN ZUKATAN MU YA ALLAH KA BA MU IKON BAUTA MAKA BAUTA TSARKAKKE A SAURAN RAYUWAN MU AMEEN YA ALLAHU, , , , , , ,

Lokacin da nafito dan gidan baffan nawa bayan na gama jin umma saude tana kwala min kira wanda nasan kiran na dayan biyu ne ko aiki ko aike da bai kare min a gidan muddin ina cikin gidan sai idan Manjo ta hanani zuwa ko fita na ke samun sauki.
Shiyasa na kwammace zuwa gidan Atika ita kadaice kawata a garin tunda nazo tsiwa da fada bai bari muyi nisa da sauran kawayen da suke sona da kanwance a garin.
Amma ita Atika banda matsala da ita yanzun zamuyi fada mu koma mu shirya hakama mahaifiyar Atikan takan nuna min kulawan ta sosai kasancewa ta marainiya a gidan da ban samun kulawan da ya dace.
Da sallama na shiga gidan wanda doka ne hakan ko kana dan gida zaka shigo dole sai kayi sallama kafi shiga idan ba haka ba sai ka koma baya ka kara sallama zasu barka ka shiga.
Ba iri gida Baffa na ba da kirikiri kana sallama suna ji ka za, a kyale ka wasu ma suce ka damay su da sanaben yin sallama idan zaka shigo ka shigo kai tsaye.
Atika ce zaune tana tsifan kai a yar kujerar mata ina ganin hakan na bata rai don nasan za ai dayan biyu ko in taya ta ko mahaifiyar ta malle tace nima in sance nawa kan ai muna kitso a tare.
Wanda ban son hakan ko kadan naki jinin abinda zai taba min lafiyan kaina a rayuwana sai kitso yai min wata daya akai har tsagan kitso ya fara bacewa akaina ban sance shi sai wani yaji tausayina yasani sance kan dole zan kwance kan.
Atika tana ganina bayan karba min sallama da tayi tace yauwa kamar kin san yanzu malle ta gama maganan ki kizo mu kwamce kai mu tafi kitso yau.
Harara na watsa mata tare da fadin ki dai tafi kitso ni har yaushe kaina ya tsufa da zan sance kai tace lah yanzun wana kan da nayi kitso uku bayan wanan zaki fadi haka.
Fuska na bata ina zama tare da fadin kin san Allah Atika bana son abinda zai taba min lafiyan kan nan nawa ko kadan .
Tace rashin sabo da yi a koda yaushe ne yasa baki saba da taba kan ba har yanzu amma mutucin mace ai shine gyara kitso kuma na cikin gyaran mace don da zaran wani yaga kanki a haka sai yai maki kallon kazama.
Na harare ta tare da fadin kina nifin ke nan ni kazamace ko haka ma ranan ya sadi ya kirani da kazama wai na daga karyayi ball dani gurin da yake cin abinci.
Sai kuma naja tsuki tare da fadin koda yake wa yan nan ma ko may nayi haka zasu ce min don babu mai kaunar zamana a gidan don ciwon Malle kawai muke zaune a gidan nan.
Yanzun mu guduwa nayi ina jin umma saude na kwala min kira nasan wani aikin zata sani ga jaka sun samu a gidan ke nan ko ?
Atika tace ko basu son ki tunda Baffa shi yana son ki da Malle ai shike nan dama don Baffa di kuke zaune a gidan ai.
Nace matsalan ai shi Baffa baya zama agida kullun yana wurin tsaron shagon shi Malle kuma kinga ba maganan ta suke ji ba tunda sunga yanzun bata da kafa da zata mike ta daki mutum.
Mikewa nayi ina fadin kowa kibiyar in kama maki tace ke ba zaki kwance naki kan ke nan ba raina kara batawa ina fadin idan baki so na zauna.
Ta miko min kibiyan na shiga kwance mata kan muna hira wanda hiran duk zagin yan gidan mu nake muna fadin halin kowa a gidan.
Muryan Malle mukaji a kan mu tana fadin yau naga ikon Allah Fatima bana ce idan kin shigo ta fada maki ki sance wanan kan daya komar dake kamar mahaukaciya ba.
Ba dama in magana saboda nauyi da kunyan marar da nake ji a raina yasa na sakewa Atika kanta na samu guri na zauna.
Daki ta koma sai gata ta fito da wani kibiyan ta miko min nan na fara kwance kan nawa na dole ba don na so ba.
Saboda wanan kitson da muka tsayayi yasa na kai dare ban dawo gida ba abinda ya kara tunzura ran yan gidan mu ke nan fiye da yadda nayi tsamanin zasuyi min dama idan na koma gidan.
Ga laifin da nayiwa umma saude ga kuma wani na kara a samsn shi nasan kuma Manjo na can cikin damuwan rashin dawowana gida da wuri don duk dadewa na a gidan su Atika ban kai magariba ban shigo gida ba.
Ban yarda na shiga gidan ba kai tsaye sai da na dan leka ko babu kowa a waje ganin basu kusa yasa nayi wuf zan shige dan dakin mu wurin Manjo.
Naji an kai

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login