Showing 240001 words to 243000 words out of 419207 words

Chapter 81 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1460

kuma.
Tace idan zaki garin ku zakije dani ta fada a marairaice nace why not idan kina son zuwa.
Ina kallon yadda merry fuska ba annuru ko kadan yarinyar zata kara magana ta dakatar da ita ta hanyar fadin will you kep quaint dear ?
Da sauri ta mike ta fada jikin uban tana fadin daddy mumm tana min shauting ba dalili.
Dan rugumay yarinyar yayi yana shafa bayanta a hankali ta lafe saman jikin shi abincin da baici gaba da ciba ke nan ya barshi.
Ni dai na gama na mike na koma saman kujaran falon na zauna ina karatu a cikin wayana sam na manta da wani zancen new year sai lokacin da naga merry ta fito cikin shiga ta alfarma tana fadin zasu church wurin addua,a ita da yarta yarinyar tana bata fuska rai bace.
Daga sama uban ke jefo masu baki akan idan yarinyar bata zuwa ta barta a gida ta gallamai wani harara ta fisgi hannun yar nata.
Kamar zata wuce bata sallamay ni ba komai ta gani tace sister inlaw zamu tafi sai sun dawo nayi mata tare da fadin queen tayi min addu,a idan sunje kila kalami na yaiwa merry dadine tace zasuyi suka fice.
Da farko ganin da nakewa yaya haka sai nake daukan shi miskili mai ji dakai kamar yafi kowa marason magana ko wani lokaci a cikin daure fuskan shi yake.
Sai dan zama na dasu London din nan nake fahintar koshi waye sannu a hankali don na fahinci baison ganin mutum a cikin damuwa ko kadan bai kula da mutane amma idon shi na akan duk wani na tare dashi.
Gashi dai yan kwanakin nan yana nuna min kulawan shi amma ni sai kama jikina nake dashi ban sake mai don kada in wuce iyakata a ranshi.
Ina kwance a dakin nayi karatun Allah nayi na boko na gaji nayi barci sai da azahar na mike don inyi sallah bayan na idar na zauna bakin gado ina game a wayana don haka hankalina ya dauke banji shigowan shi dakin ba.
Muryan shi naji a kaina yana fadin waike baki gajiya da game a wayane haka ko rashin nayine wanan duk.
Ki tashi mu fita zuwa cikin gari tunda ke?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? zama wuri daya yana damun ki nasan nan din ma a takure kike yanzu.
Dago kainayi jin yakai aya nace barni na koma da sunana na fatimana gida kada matar ka ta kara zargina kan wani abin tunda bata san koni din wacecen kaba har yanzu.
Maimako maganata ya bata mai rai sai naga ya dan kara matsowa har inda nake yana fadin kina tunanen ina tsoron fada matane ko may ?
Sai da yayi min wani lalatacen kallo kafin yace ni ba irin mazan nan bane masu tsoron matan su har in tunanen ki yana baki don kada ran merry ya baci ne nake maki hakan.
Ciki ciki nace ga abu a baiyane kuwa zaka wani noke yanzu don kaga bata gidan ai kayi dadin, , ,
Tsawa ya daka min tare da fadin ke kada ki bata min rai don kinga ina kokarin tsare hakkin ki dake kaina.
Na dan fadi a fili ina gusawa daga inda nake zaune nace aini bance sai an sauke min wani hakki ba can a barni inyi rayuwata ni kadai mana agani.
Zarah ashe rashin kunyan da ake fada naki har ya kawo kaina har kin kai ki kali idona kina fada min magana kai tsaye.
Kina nufin dan ance kina matata zaki fada min magana irin haka ki kama kanki yarinyar hakan ba yana nufin wai harki rainani bane don kina kurin ina mijin ki.
Duk da jan idon da yake min da nuna min bacin ranshi a fili hakan baisa na rufe bakina ba lokacin sai cewa nayi aini ba matarka bace zaman kanwar kace nakeyi ko dako gida muka koma .
Juyawa yayi zai fita daga dakin bayan hararan daya watsamin din sai kuma ya sake juyowa ya kalleni cikin na tsuwa yana fadin.
Da na dauka kina da wayau da zaki gane abinda nake nufi da yin haka gareki na dauka ko ban fada bake hakan ba zai damay ki ba.
Sai gashi ashe har yanzu wayau naki baikai ki gano hakan ba ba laifi nasan kina mutuntani a wani bangare sai dai kada zancen ki da merry yasa kice zaki rainani yanzu.
Na dukar da kaina kasa cikin karamar murya nace ni zancen merry bai shafe ba gareni ta fada min na fada mata don ba zata zagan min iyayyena ko yan uwa in kyaleta ba ko addinina.
Yace koma dai may ye ki sani aurena dake ba,ayishi akan so ko wani kauna ba anyi shi ne kawai bisa kaddaran rabon sai anyi don haka yadda kike jin ko maynene a ranki hakan kowama ke jinsa.
Don haka ki ban lokaci har in gama tsare tsarena kafin in waiwayo ki mu san mafita yana fadan haka ya juya ya fita baiko sake kallona ba.
Yana fita na fashe da wani irin kuka mai cin rai tare da kunan zuciya lokaci guda ke nan nazama matar kushe wace aka auro ta a bisa wani kaddaran.
Zuciya mai nashe nashe har ta fara naso min irin rashin mutuncin da zan kula mai idan mun koma gida yayin da wani bangare na zuciyana ke fada min in fito fili in fada matarshi gaskiyan koni wacece a wurin shi.
Tunda ya fita ba wanda ya kara leko dakin gama tun zuwana banga Greco a gidan ba ba hurmina bane don haka ban tambaya ba.
Ina idar da sallah magariba cikin ikon Allah sai ga wayana yayi kara na dago daga inda nake ina duba mai kiran wayan nawa.
Mamu nagani rubuce na dauka da sauri da sallama a cikin dakusashen muryata dana ci kuka dashi yau.
Shiru tayi ba tare da ta amsa min sallaman ba sai na fara sheshekan kuka muryan ta naji tana fadin sayadi kina son in daina kiran layin ki ke nan ko ?
Na daina mamu nace da sauri don jin abinda ta fada nasan kuma zata iya din ba iya fadi a baki tayi ba.
Ko mainene hakkuri da mika kai ga Allah shine maganin sa ai sayadi ba wai kukane mafita ba gare ki harki jawa kanki wani ciwo can.
Sayadi ina son ki sani daka cuci abokin zama gara ka barshi shi ya cuce ka kina dai gani na a nan bana yarda in wullakanta aurena sayadi.
Idan namiji ya cuceka ke mace ki daure ki zuba mai idanu saboda watarana ko ance yai hakan gareka ba zaiyi ba ai, kuka na somayi sosai don zanyi magana ta hanani.
Amma duk da hankan sai dana samu na furta abindake cin raina nace mamu yau yaya fa cewa yayi auren mu nidashi ba aurene naso da kauna ba.
Aurene da akayi shi bisa wani kaddara wanda sai dai mu barwa Allah lamarin sa abin mamaki amsar da mamu tabani a likacin shi yaba mamaki matuka don cewa mamu tayi ai ya fadi gaskiya sayadi.
Ehma ko ba auren kaddara din kukayi ba keda shi fada min dole sai kowan ku ya yaki zuciyar shi dama ai a zauna lafiya muddin kina son kici riban auren ki.
Ko ni da kawun ki an fada maki munyi wani soyayyane kafin auren mu da fada min da saka rana duk baifi kwana biyu ba tsakani.
Yanzu fa sayadi wa zai gane hakan akayi sai wanda yasan tushen labarin zai sani.
Shi hakkuri ai baibar komai ba da wansn wautan taki da kikeyi garama da Allah yasa ba a gida daya ya barki da kishiyar taki ba don da zuwa yanzu ta gane halikin na rashin hakkuri ta dan kara min nasiha akan in daure in kara hakkuri dai ta kashe wayata ta barni da tarin bakin cikina.
Ke nan kowa laifina yake gani akan auren nan shi basu ganin nasa ko kadan har zai fada min hakan mamu tace wai banda hakkuri ko din
mahaifina baya rayene yasa kowa baisona a duniyan nan.
Barci na samu ya daukeni a hakan bayan naci kukana na gaji can cikin dare ina barci na dinga jin kamar hayaniya a gidan tun ban falko ba hardai na bude idona tar jin hayaniyar yayi yawa yasa na sauko daga saman gadon ina saurare.
Muryan yaya nake ji sama sama hakan yasani komawa na kwanta don bai wuce wani abin ne tsakanin shi shida matarshi kuma.
Hayaniyan sai dada karuwa yake inda nake jin muryan wasu mutane na daban yana tashi.
Kamar in fita gashi barci yaki daukana kuma naga idan na fita na kula dasu kenan don ance tankawama yabawane.
Nan kuma wata zuciya ta tuna min da gargadin mamu na kada in sake in bari a gane ina kishi ko wani abu tambayan kaina nayi ni yanzu yayi to fita kawai zakiyi zuciyata ta bani amsa.
Gabanane ya fadin ganin harda yan sanda a gidan a hankali na taka zuwa inda dandazon taron yake ina sauraren bayanin dan sandan.
Daga inda nake na fahinci merry ce sukayi accident da suka fita ashe bayan zuwan su church da aka taso suka wuce yawon su na bukin new year.
A can ne suka hadu da wanan kadaran don tana a cikin maye wai ashe tun fitan shi daga dakina ake wanan rikicin ban sani ba yanzu ma yansanda sunzo tafiya da itane bayan ta gudu daga asibiti inda aka kwantar dasu din.
Ga bayanin dansanda dayayi karshe na gane har yarsu queen tana asibiti kwance wanan lokacin.
Ga uwar ta gudu ta dawo gida tabar yar can asibiti shine mijin ya kira yan sanda suzo hargida don ba zai yarda yarshi ta salwanta ba yace.
Kai wai wanan wani irin aure mutanen nan keyi na tambayi zuciyana hakan ina karewa yadda merry din ke fama.
Daga inda yake ya watso min wani irin kallo mai kama da harara har na dauke kaina daga kallon shi sai can na tuna a yanayin dana fito falon sake dan kallo shi nayi har lokacin yana watsa min harara hakan yasa na juya da sauri zuwa dakina na sako hijjab dina.
Sai dan ban sake fitowa ba ban kuma san yadda suka karkare ba a can don ban kara jin duriyan su ba kuma a gidan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:21 - ??5惙5惙5?: BISSIMILLAHI RAMANIN RAHIM ALHAMDU,LILLAHI RABIL ALAMIN, , , , , ,


Nikan dai ranan naga abin mamaki a gidan cike da tunane da fargaban merry na kwana a rayuwata da safe dai fashin sallah nakeyi don haka na tsabtace jikina tare da shirya har tsoron fitowa waje nake daga dakina a yadda nake tsoron dan giya a rayuwata yadda muke kyamatan su nan gida Nigeria.
Kwance nake na lafe saman gado ina rub da ciki naji shigowan yaya dakin ban juyo na fuskance shi ba ya kuma san ba barci nake ba a lokacin.
Ki tashi muje asibiti mu duba queen sai lokacin na dan juyo na fuskance shi kindai ji abindaya faru dasu don itama merry din tana asibitin sun mayar da ita saboda ta bugu a hannun ta sosai.
Har lokacin banyi magana ba shi kuma yana tsaye tsakiyan dakin saida yaga na yunkura zan tashi yabar dakin da sauri nikan kayana gaba daya na hada don a ranan nake son komawa gidana ba zan yarda yar giya ta illantani ga banza ba don harga Allah tsoron merry ya kamani har cikin raina.
Ina gama hada komai nawa na fito na samu baya falon dan zaman jiran shi nayi na dan lokaci sai gashi ya fito da alama wanka yayi ya sauya kayan jikin shi sai kamshin da yakeyi lokacin.
Ban tsaya jiran yace wani abuba na mike da sauri ya dan kalleni don ganin jakkar kayana dana dauko lokacin.
Bai min magana ba illa kitchen danaga ya nufa wurin masu aiki duk na kagu ya fito mu tafi lokacin.
Sai gashi ya fito masu aiki na biye dashi da abinci a zato asibitin za aikai abincin sai naga sun nufi dining da abincin.
Sai da suka gama jerawa ya nufi wurin ya zauna ya juyo yana kallona tare da fadin ba zaki zauna kici abinci ba.
Nace na koshi wani tsareni yayi da idanun shi saida tsorata dashi a hankali na tako zuwa dining din dake da dan tazara daga inda nake tsaye kamar ina jiran umurni.
Ina karaso naja kujera zan zauna naji yace may kikaci jiya da dare bayan kina daki kina fushin banza da mutane.
Dan kunkuni nayi ban fitar da maganan a fili ba yana kallona na dibi abincin maimakon in zauna sai na daga zan bar wurin.
Maza ki zauna nan kici yace kamar ya samu yarshi dama kuma ai yar tashi nake don da uwata suka taso dashima mace ce da yanzu kila yana da sa,ata.
Sannu a hankali nake kai abincin bakina duk a kyamace don sai ban yarda da yan aikin ba ga baki dayan su.
Zakici abincin ko sai raki ya baci yanzu naji muryan shi yana fada min nayi firgigit na tsakuro abincin zuwa bakina yaci gaba da fadin.
Ba zai yuyu kina zama da yunwa ba wani abu yaje can ya samay ki ace gidana akwai yunwa ki bata min suna ga banza.
Nace bashi nazo yi bani ga dai may shirin bata ma suna nan tana abinda taga dama har dasu shan giya da auren ka.
A natse naga yayi murmushi maimakon yai fushi kan maganan dana fada mai mai zafi sai naji yace ai ba gidan ki bane gidanane kuma matatace a haka nake son zama da abina.
Nace da wani yace maka shi matarkace kaje kaita zama da ita ko da zindir zatayi yawo mana.
Ban iya fadi kalaman sosai a fili ba sai na dadi ciki ciki ina murguda baki banyi aune ba sai ganin shi nayi gabana ya cafki bakina dana murguda mai yana fadin mara kunyar banza wace bata san rarashi ba .
Wai may yasa ku mata baku san ya kamata ba sai anyi tsiya daku ko wani lokaci wai harda ke wanan karamar yarinyar kin iya takon tsiya wa maza ko ?
Dan ja nayi baya ina fadin nika sake min bakina mutum da baki shi a hana shi magana na fada ina kwace kaina daga rike baki dayayi min.
Yana sake min yayi gaba tare da fadin in kingama ki samay ni waje ban tsayaba na mike tare da mara mai baya kusan a tare muka fita daga gidan dashi.
Motar ya bude min na shiga da kayana sai lokacin yake fadin wanan kayan fa ina zaki dasu haka banji komai a rainaba nace gida zan koma yau ni.
Wanan ba gida bane shi ko wani ya takurawa rayuwan kine a nan sallon kiji dadin fita yawo kice zaman kadaici ya isheki a can ko ?
Ni dai gida zan koma daga asibitin na kara bashi amsa baiyi magana ba ya zagaya ya shiga motar muka dauki hanyar asibiti kai tsaye.
Asibitin babba ne sosao mai benaye da abin hawa saida muka shiga lifter ya kaimu sama dakin yar shi muka fara zuwa tana kwance an daure mata kafa har cinya da plaster hakama hannun wata na barin hagu da kafan shima a daure yake an rataye kafan a jikin wani karfe kafan yana lilo.
Sannu mukai mata mun samay ta tare da wata dadtijuwar mace matar tana saye da wando da rigan t,shirt kanta babu gashi ko kadan an aske ga makeup tasha a fuskan ta bakar fatace matar wuluk da ita.
Bayan mun kare gaida yarinyar na dan rike mata hannun dayan dake da lafiya ta sake tiedy din dake rike a hannun ta ta rike hannun nawa.
Matar ce ta tambaya wanan ce kanwar taka dake karatu a nan a cikin daure fuska naji ya bata amsa da eh itace.
Wani kallo tayi man kamar wace taga abokin gaban ta saita kawar da kai daga kallona da tayi bani kadai naga wanan kallon ba har shi yaga irin kallon da taimun da idon shi.
Oya les pray yace wa yarinyar tare da juyowa gareni yana fadin ki muna addu,a ban samu bashi amsa ba naji yana cewa yar komai taji ya fada itama ta amsa da Amin tace Ameen yace No say Amin
Ya juyo ya dan kalleni sai na daburce na rasa abinda zan karanta a lokacin fatiha na fara jerowa kafin in dora da adduan .
Sai cewa suke Amin yana hadawa da ya Allah jin yadda yake kiran Allah yasa hankalin dattijuwar matan ya tashi gaba daya har ta kasa boye yananin ta a dakin.
Mun gama ya dan zauna yana hira da yar shi ina gefe daya a takure ina kallon su sai matar ta fita ya juyo yana fadin bayan fitanta wanan itace uwar merry.
Da mamaki nace wanan din subbahanallahi ke may ye haka yace mun nayi saurin dukar da kai ina

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login