Showing 105001 words to 108000 words out of 419207 words

Chapter 36 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1453

nan naki na zaman gida ta saka kada taje masa haka nasan shike kara hadasu da yaya.
Ba tare dana kallo inda suke ba nace yayifa dauda mamu tace daya ne halan dan Allah shiga ki dauko mata kinji ta fada a cikin zafin rai.
Haka yasa na mike na shiga na dauko mata bakin dan just to cover na fito dashi na mika mata tabi da kallo tana dan dariya tare da tambayan yaya zata saka ?
Ya juyo inda nake zaune yana fadin taimaka mata ta saka mu tafi dole na taso na gyara mata ta dinga wani rawa ba kunya a gaba shi tana wani juyawa shiko gogan yana lushe ido yana binta da kallo cikin sha,awa.
Ya rike mata hannu suka jera a tare suka fita daga falon suna dan magana yana kallonta yana murmushi.
Suna shiga falon ta kara gaida daddy a cikin gurbatacen hausan data koya a lokacin kawu dai ya karba mata.
Bayan sun natsu kawu yace may sunan ta yana kallin dan nasa yake tambaya yace merry da sauri.
Kawu ce merry take to mu nan zamu kirata da maryam ya fada mata cikin harshen turanci ta danyi dariya tace that's my name.
Kawu yace maryam ina fatan kin san wanda kika aura ma,ana addinin sa da yaren sa da al,adun mu ?
Da sauri ta amsa da yes uncle yace good sai dan zan kara fada maki idan ma shi bai fada maki da kyau ba ki sani mu ga addinin mu mata basu shiga irin wanda kika shigo gidan nan dashi.
Kai ta sunkuyar kasa don nauyin maganan kawu din gare ta don ko shi umar din yayi mata korafin hakan.
Sai na biyu kin dai san umar musulmine tun kan ki aure shi kika yarda kika aure shi a hakan ta gyada kanta alaman ta sani.
Kawu yace good masha Allah yace adfinin mu bai hana mu aure ku ba matukar ba zaku sauya mijin da kuka aura i zuwa naku addinin ba.
Sai dai mu Allah ya haramta ma yayan mu ta auren yan naku addinin ga baki daya addinin bai yarda da hakan ba.
Da sauri ta dago kai tana kallon Umar din da kanshi yake sade yana sauraren maganan mahaifin nasa.
Kawu yace don haka ne nake horon ki da ki bar min yarona yayi nasa addinin tunda mu bamu kyamaci addinin ki ba.
Sai dai idan kikai kokarin yin hakan ki sani ni mahaifin shi ne zan iya raba auren ku a duk lokacin da na fahinci haka a gare ki.
Tace cikin sauri i will never try that uncle and beside Omar is riligious somebody he will never accept that.
Kawu yace again kin ga family din mu babba ne ga al,adan mu shi babba a gida kamar uba yake a gun kowa na wanan family din kada naji wani yaje gurin shi an samu matsala dake.
Ita kan may yai zafi haka wanan tsohon yake ta kidanya mata sharuda haka dama haka auren musulmi yake ko nasu al,adan ne haka merry ki rayawa a ranta.
Ita dai burin ta shine suyi accepting din ta as a daughter inlaw din su idan ma sun barta a hakan ya wadatar da ita may ya shafe ta da wani al,adun su kuma su da suke can uwan duniya mai nisa in ba ma shi da ya matsa zaizo gida ba yaushe zasu gansu ma.
Kawu yace kin san addinin mu ya bamu daman auren mace da daya don duk lokacin da umar yaso kara aure a cikin kabilan shi yana da daman yin hakan.
Da sauri ta daga ta kalli tsohon inda yake zaune ta sake juyowa ta kalli umar din kafin ta sada kai ganin umar ya girgiza mata kai alaman ta yarda kawai.
Kawu yace sai na karshe dole ne dana ya ding zuwa nan dubamu duk bayan wasu watanni akala sau uku a cikin shekara ko biyu idan kuma zamuyi sallah ya kasance yana gida tare damu a matsayin na babban da a gidan nan .
Idan wanan yayi maki a tsarina baki da matsala komai damu muna maku fatan alheri da samun zuri,a masu albarka.
A sanyayr merry ta dago kai tana fadin taji tagode kwarai yace ba matsala cikin daga masu hannu yana kokarin mikewa tsaye don zuwa maslaci don sallatan magariba.
A daidai lokacin kuma hjy jummai tana shiyan ta tana bala,i jin cewa su umar na gidan tun dazun shiyan hjy maimuna ta dinga surfa ji dali da sauran yaranta.
Tana fadin ita bata yarda da wanan tsarin ba watau maimuna mamircin data kulla ke nan na janye mata suruka a wurinta don ta jata a jiki saboda taga wurin ci ko ?
Tana cikin wanan masifan ne Umar din ya shigo da merry don su gaisa fuskanta babu annuri take karba masu gaisuwan su.
Tare da tambayan shi ance tun dazun kake gidan nan kana wurin maimun da wanan yarinyar makitcin da maimuna zatayi min ke nan tanan take ganin zata bullo min taci galaba na.
Ido merry ta tsura mata duk da bata jin abinda ake fadi tana iya gano fada matar keyi da Umar din sai dai bata sa ko a kan may bane ?
Umar daya tsaya sauraren maganan mahaifiyat tashi jin tayi shiru yace haba mama tace haba din may babawo yanzu har kai kokarin hada wani alaka kakeyi da matar nan.
Nifa daga ita har kakar taku da kake wani soye mata ban yarda dasu ba dukkan su makasa nane idan sun samu wuri don haka ban yarda da hakan idan kunzo gidan nan ku shigo nan kai tsaye daga yau.
Yace mama ba haka na bane tun dazun a gurin Alh muke muna magana dashi fa har yaushe muka zauna a gurin maimuna din.
Tace Alh may kuma ya kiraku yake fada maku shi bai son a zauna lafiya ina ganin sai na fito masa ta hanyar bayan gida a zauna lafiya don kawai an cusa mai ra,ayi a kanku na kiyayya shine har yanzu abu yakici yaki karewa a tsakanin ku.
Innalillahi mama nine fa nakai merry din su gaisa saboda ta damay ni tana son su gaisa da shi na kaita yau dana yana gida sai muka tsaya ya danyi muna nasiha.
Daga nan nake fada mai irin plan din dana shiryo a can kafin in dawo and kuma daddy yayi muna magana ta fahinta sosai wallahi.
Sai lokaci ta dan sauko tana fadin oho ai dai na dauka wani abi ne kuma yake sharada maku don shi bai gajiya da tsincen mata.
Haba mama tun dazun kina ta fada haka a gaban surukan ki mun fada maki ba komai bane kinki ki gane ai shi brother yana da wayau shi .
Salma wallahi ki fita a idona tun ban saba maki rai ba yanzun nan a gutin nan abinda nasani zaki tsaya kina mussamin akan shi.
Hannu ya dagawa salma din tare da fadin is ok mama don Allah ba haka zancen yake ba zan tafi sallah idan na dawo zamu wuce a nan zan barta.
Ya juya yana fadawa merry shi zai tafi masallaci ta zauna a part din mum din shi har ya dawo mikewa merry tayi tana fadin No ba zan tsaya a nan ba nafi jin dadin wacan part din don muna hira dasu a can sosai.
Dan tsayawa yayi yana rarashin ta fafir merry tace ba zata tsaya a nan ba don ta karanci hjy dan zuwan ta matar bata da marmari sam tana da dan fada da jin kai.
Daidai lokacin har ta fara tafiya ta nufi hanyar fita daga falon sai hjy tace ba masalaci kace zaka ba ita kuma ina zata ?
Yace a cin cool voice tace gun maimuna zata tafi tafi sabawa da ita can ai kaga matsalan tun ba,aje ko ina ba abinda nake fadi ke nan ya fara fitowa.
Mata da kinibibin tsiya harda wanan da zuwan ta ta sace mata zuciyar ta wai a haka ake son i hada zuria da ita ina wallahi ba zai yuyu ba sam.
Merry ka har ta kai kofan mamu can taga fitowan shi hannu kawai suka dagawa junan su ya fice daga gidan zuwa wurin sallah.
Haka yaje sallah ya dawo ya samay su a falo da mamu suna dan hira hefi jefi ba wani hira bane sai labarin irin al,adan hausawa da sukeyi.
Haka ya shigo ya samay tayi da daya a falon ta sake jiki ga plete din ferfusun kayan ciki a gaban ta tana sha a hankali.
Yaji dadin hakan da mamu ke nunawa matar tasa wanda har kasan zuciyar shi ya yaba da hakan sosai don baiga wani kissa da mahaifiyar shi ke fadin mamu tanayi ba shi kam.
Don mamu sai kokarin farantawa merry take don kawai ta ingata darajan shi a gare ta wanda ko na munafunci tayi mai dai ya gode da hakan.
Yace maimuna zamu tafi dare ya soma da sauri mamu tace dashi km kaci abinci ne Umar da fa abunci nan na zuba maka kai da matarka.
Yace banda lokacin cin abincin nan yanzu maimuna ta taso mu tafi kawai in kaita ta huta akwai maganin da zata sha karfe tara.
And ina son mu shiga mu duba Amma kuma lokaci ya kure sai dai idan mun sake dawowa kuma.
Mamu tace sai ku tafi da abincin don daku na girka dama ta mike tana kokarin zuwa kitchen don dauko basket ta saka masu a ciki.
Ina daki ina jin duk yadda sukayi a tsakanin su don tunda na shiga sallah da gangan naki fitowa falon do takaicin mijin da mata saboda tabaran su a gaban kowa babu kunya a tare dasu ko kadan.
Mamu ta fito tana kwala min kira na fito na kai masu abincin bakin motar su yace No ki barta zan dauka dare yayi yanzu ba kowa a wajen gidan nan.
Sun fito bayan sun mata sallama ne suka hade da hjy maryam data dawo daga unguwa tace a, a umar ashe ku shigo gidan namu ?
Yace eh yanzu muke shirin komawa bata damu da kallon ta da yakeyi ba gulma ya cita tana karewa merry kallon kurlla tsab tana kada kai ya wuce merry da bata san tana yi ba tabi bayan shi zuwa inda ya aje motar shi a waje.
Da gulma a bakin ta fam ta nufi part din ta cike da tsegumin merry wa yayan ta lokacin nan suka zauna suna dariyan shakiyanci wa halitan merry din suna dariya.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:03 - ??5惙5惙5?: ASSALAMU ALAIKUM JUMMA,AT MUBARAK YAN UWA MUSULMAI ALLAH SADAMU DA ALHERUN SA AMIN ???a


Hjy jummai dake zaune har lokacin tana fada dakin ta yaran ta kowa na harkan gaban shi don dun gaji da bata hakkuri taki yin shiru suka fita batun ta.
Kawu da shigowan shi daga masalaci ke nan ya na dan zagawa dakunan matan nasa ya fara da sashenta don itace babba a gidan idan ya gama sai yaje gun Amma itace karshe su dan taba hira ya dawo part din shi mai girki ta samay shi a can wanan zagayawan da yake a lokacin yakan ji korafin diyan shi da damuwan su.
Tun da ya tunkaro sashen yake jin muryan hjy tana masifa ya karasa shiga da sauri don ganewa idon shi da wanda take fadan.
Sai dai ga mamakin shi babu kowa a cikin yaran ta da alama ya nuna dashi take fada a lokacin wurin da take zaune ya diba yana fadin ke dawa ke fada haka muryan ki har waje ?
Yi tayi kamar bata ganshi ba a wurin taci gaba da fadan ta saida ya tambaye ta a tsawace tace.
Alh ina son ka tsawatawa maimuna ta fita harkata don ban shiga nata ba da zatai min kakagida don neman waje da sarakuwa na ta jira zuwan nata sarakan nan gaba.
Ya gyara tsayuwa yana fadin haba jummai wai ke may yasa baki hankaline klun yanzu may ya kawo wanan irin maganan don Allah ?
Yanzu ace wanan yarinyar sam bata son ma shigowa wurina sai dai taje gurin maimuna inba tasan abinda tayi ta rabani da ita bane.
A kan wanan kike wanan fadan haka don kawai an maki kara an karama sarakuwar ki sarakuwa ma kafira har kike wanan jidalin haka ba kunya a idon ki ?
Eh banyi mamaki don ka fadi hakan dama kai ba zaka taba hango illar hakan ai do ko mai maimuna tayi daidaine a gidan nan.
Ya girgiza kai yana fadin kaji matsalan ki ai indon wanan ne zanwa maimuna magana tafita harkan kafiran sararkuwar ki ina shike nan.
Duk da tasan ya gasa mata magana hakan bai hanata cewa daya fi ba haka kawai don munafunci ki shishigewa yarinya ke kinga wurin ci.
Fitowa Nafisa tana fadin daddy sannu da dawowa ya hana shi yin wani magana a cikin sakin fuska yace Nafisa an wuni lafiya ya karatu ?
Salma ma da lastborn suka fito suka gaida shi ya amsa tare da danyi raha da yaran ya fita zuwa part din hjy maryam dake zaune suna cin abinci da yaranta ga waya a hannunta tanayi.
Sun gaisa nan ma yadanyi hira dasu ikilima yai masu saida safe har yakai kofa yaji muryan hjy jummai tana fadin nikan Alh wai maina kashewa Umar ne har yau fa bai shigo nan ba balle ya kawo min matar shi mu gaisa.
Amma zai iya kaita wurin maimuna ko ni da wata manufa yake daukana a gidan nan ne.
Yace don wanan maganan kika tsayar dani maryam ki tambaye sa mana idan ya shigo tunda kina son shigowan su nan din ne.
Yasa kai ya fita yana jin zafin maganganun su duk akan abu daya wanda ba komai bane sai zalla kishi akan yar uwan zaman su din.
Zaune muke a kasa saman carpet muna cin abinci sai fauziya dake gefe daya tana fitina kan dan uwanta wai ya sha mata ruwa.
Yin sallaman shi yasa duk muka shiga cikin natsuwan mu tunkan ya karasa shigowa muma shiga gaida shi yana amsa muna hankalin shi yana kan fauziya dake kuka.
Yace mai akai mata take wanan kuka haka fitina kawai take ji mamu ta bashi amsa yace mutum na fitina babu dalili ina dan dariya nace kawu da ita da samir ne ke fada wai ya sha mata ruwa sai ya debo mata wani ruwan.
Yace fauziya baki son kuyi zumunci da dan uwan ki ko baki son ki bashi abinki idan kin girma shima ya baki nasa.
Kada kiyi rowa fauziya ke ba antyn shi bane ki kara ruwan yadda kowa zaisha ki kwashe ladan aikin ki ko baki son ladane ?
Ya tambaye ta yana kallon fuskanta mamu tace fitina da gangan takeyin shi don kawai ta azawa mutane tashin hankali niko yanzu dan banzan duka zan mata idan bata rabamu ba da kukan banzan nan.
Kawu ya duka ya rike hannun ta yana fadin a, a akan may zaki doketa gadon uwar ta jummai tayi mai rikicin gangan don jummai sarkace ko ba dalili sai tayi fada.
Aiko tayo mugun gado inji mamu tana dan ya mutse fuska yanzu na samay ta tana jidali tun ina waje nake jin harshen ta na shiga ina tambaya wai dake take fada.
Mamu tace subbahanallahi dani kuma may nayi mata ni dake nan yau zan iya cewa tun safe ma bamu hadu ba a gida nan da ita.
Yanzu dai tace in maki magana ki fita harkan sarakuwanta ki jira taki sarakuwan in su hussaini sunyi aure.
Wani irin gulolon bakin ciki ne ya ziyarci zuciyata lokaci guda tare da yiwa mamu gwai a raina da taba kafira fuska ga goron data samu a baya.
Itako mamu cewa tayi ikon Allah ni na dauka hakan karane a gare ta amma ba matsala zan kiyaye in Allah ya yarda .
Dayafi maki alheri don jummai bata san ya kamata ba ita sai abinda zuciyar ta ya anyana mata.
Allah yasa mufi karfin zuciyar mu mamu ta fada yace Amin ya juya gurina yana fadin yau fatima may aka karanto a islamiyan ne kafin in bashi amsa mamu tace yau basu shiga ba wai malam suna wani taro.
Nace kawu kayan islamiyan mu sun dake muna ranan har an dukemu kan hakan wai hijjab dina baikai kasa ba sosai.
Yace shine baki fada min ba yana kallon mamu tace da rigima take banace zan yanko masu yadi a dinka wani ba mantawa nakeyi wallahi.
Yace gobe insha Allahu za a kawo maku idan na fita yai muna saida safe ya bar part din wurin Amma ya nufa.
Sun dan dade da Amma suna hira ya koma part din shi inda mamu ta samay shi bayan ta tabbatar da na rufe part din.

Ammace zaune a falon ta tana taunan goro daya zama mata jaraban rayuwa idan tana

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login