Showing 135001 words to 138000 words out of 419207 words

Chapter 46 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1451

na sake dagowa ina fadin don Allah mamu ki taimake ni ke kadai nake da a garin nan ki hana aimin wanan auren don Allah mamu na karasa cikin kuka mai ban tausayi da marairaice muryana.
Au sayadi har kawun ki zai saki abu ki iya watsa mai kasa a ido ke nan ban sani ba ashe shi yana ganin yayi bugun gaba dake ya nuna ma duniya shiya isa dake kike son bashi kunya to ki matsa har ya sani baki da biyayya kamar yadda ya zata zaki mai.
Tana fadin haka ta shige uwar dakin ta itama kukan take a daki data shiga abin duniya ya taru yai mata yawa dama tasan za a rina duk ranan dana tsunci zancen.
Jin shiru mamu bata fito ba naci kukana ya isheni a gurin sai yan kanne na da suka zagaye ni kowa yai tagumi saman kujera sun zuba min ido suna kallo na kawai.
Na mike da kyat na nufi part din Amma a cikin kuka da yai min yawa har ya fara sakar min da ciwon kai lokacin.
Ina shiga na samay ta saman sallaya tana sallah isha,i lokacin ban ma san lokaci yayi haka ba sai dana fito zan shiga wurin ta naga ko ina yayi duhun dare.
Ban damu da wai tana sallah ba haka na zube a gabanta ina kuka Allah yasa ashe tahiyan karshe takeyi zaune.
Cikin kuka ina fadin wayo Amma ki ceci rayuwana ki taimakeni su kawu da mamu zasu ci amanan yar marainiyar Allah da suka dauko.
Sun rabani da yan uwana da sunan karatu Amma sunzo nan zasu min auren dole kuma yanzu Amma an tsaneni gidan ga dama ba a sona ban dauka har da kawu da manu basu sona ba sai yanzu Amma.
Amma son Allah kisa a mayar dani gidan mu inda aka dauko ni kar ai min auren nan wayo ni amma na shiga uku na lalace agarin mutane.
Ban dauka takai adduan da takeyi ba ta shafa ta dago cikin damuwa da kulawa a gareni tana fadin haba A ruwa ba tsana bane wanan so ne kin taba ganin iyayyen da zasu haifi da su tsane shi.
Yanzun ke ba abin alfahari bane wanan hadin a gurin ki yaron da yafi kowa kwazo da sanin yakamata Allah ya zabar maki.
Kwazo Amma wanan mugun da bai sallah cikakke ne zanyi alfahari dashi Amma kin fa sani matarshi kafirane kuma wayo ni Amma su kawu sun tsane ni dana sani inbi su manjo mu koma tare jiya.
Tunda nan ba,a sona an kini har ana sadaka dani Amma sai na fashe da kuka sosai na kasa ci gaba da maganan sai kuka nake sosai.
Su Aisha da sukaji kukana wurin Amma daga dakin su suka fito suma kukan sukeyi daga inda suke tsaye sun kasa furta komai a wurin.
Naci gaba da fadin Amma kin san fa bai sallah ko shigar shi kika kala bana musulmai yakeyi ba bai mu,amula da kowa a cikin yan uwan shi sai kannen sa ranan fa har giya mukaga matar sa nasha a gidan sy kuma ya gani baiyi magana ba.
Amma wanan mugun ai ko kasheni zai iya yadda uwarsu bata son mamu damu din nan a fili suke nuna muna tsana fa.
Ran Amma ya dan tabu da aibanta mata jika da nakeyi da wasu maganganu da nake fadi ba a cikin hayacina ba.
Sai data daure tace yakashe ki hauka yakeyi komai lalacewan shi ai ba zai fara ya baki wani mugun abu ba a gidan sa.
Ke zama aure fa zaki dole sai kin sauke wanan tsiwa naki da kaifin bakin nan na tsiya idan ba haka ba ki sha bakar wahala inkinje masa da rashin kunya haka don kin san su umar bakar zuciya ne dasu shima wanan yana da zuciyan yasa kikaga bai faye mu,amula da mutane ba sosai.
Na kalli Amma da idanuwa da sukai ja don kuka nace Amma kema kin yarda da maganan kawu ke nan yanzu a aurani ga wanan mugun?
A ruwa zan hana abinda Allah yace ayi ne aurene fa sunnan ma,aiki don may ba zan zamo cikin masu so ba nikuwa.
Kaina jijiga nace yanzu na gane Amma yanzun na gane komai wallahina gane dalilin rabani da kakata mai sona da kaunana tsakani da Allah.
Wayo babana wayo daddy na ka dawo ina bukatan ka a yau kusa dani banda kowa sai Allah sai manjo na Addah kuma an rabani dasu anzo nan za a cuce ni.
Amma bata iya cewa komai ba gaba tasani tana kallona kamar yadda kowa yake kallona cikin mutuwan jiki suna sauraron kalamina.
Mamu ce ta shigo falon tana fadin ashe nan tayo wurin ki gwoggo da shirmay ta tazo zata daga maki hankali da daren nan ko ?
Kamar kada inga mamu na fara kuka da karfi ina fadin wayo daddy na ka dawo ka dauke ni mu tafi tare na kwanmace ma in mutu in bika da a zarga min wahala a kaina daddy basu sona basu kaunana sun rabani da manjo na sunzo nan zasu cuceni.
Kayau kayau mari har biyu mamu ta sauke min a fuska sai da nayi mutuwar wacin gadi lokaci guda kafin in tashi in ruga da gudu sai mukaci karo da kawu ya riko ni yana fadin yaya hakane may akai mata kuma ?
Ya sake tambaya a hasale yana fadin nace may akai matane haka fuskanta ya hau cikin takaici Amma tace dukan ta tayi wallahi a gabana .
Ya juya wurin mamu yana fadin wanan ai cin zalin ne maimakon abi yarinya da lalama sai kuma ki hada mata da duka haka.
Ko kene da girman naki za ai maki haka ai ba zaki ji dadi ba lokaci daya wanan wani irin haline haka maimuna ?
Mamu tace yaya don may yarinyar nan zata daga muna hankali haka tazo ta saka gwaggo a gaba tana fadin wai mahaifin ta ya dawo ya dauketa hannun makiyanta.
Kawu yaja tsuki yana fadin banji dadin haka ba wallahi ba abakin yara yan uwanta ya kamata yarinyar na taji magana nan ba taji kuma sai a hanata shiga wani hali.
Zaki samu yarinya da duka kamar jaka dawani kike son taji dukan ko wanan magana kawu yayi fada sosai kafin ja hannu zuwa wurin kujera ya zaunar dani a kusa dashi yana kiran sunana da Fatima.
Share hawayen ki kinji ki saurare ni mu nan da kike gani kaf ba makiyan ki bane mu illar masayon ki kina ganin ni zan cuce ki ko mahaifiyar ki koko hajiya zata hada baki damu ta cuce ki na girgiza kaina alaman a, a gare shi.
Fatima kin taba ganin inda uba yaki yarsa yayi abinda zai halakata ko baki dauke ni mahaifi bane a gare ki cikin kuka nace kawu na dauka Amma don Allah kada ka hadani aure da mijin arniyar nan koma waye ka bani ba wanan da bai sallah ba yana auren kafira.
Kawu yadan runtse ido yace naji to ki kwantar da hankalin ki yanzu zamu san abunyi amma fa sai kin kwantar da hankalin ki haka zai faru ko kina son gani bacin raina ne dana mahaifiyar ki.
Na girgiza mai kai ya kama min magana a cikin nasiha da lalashi har ya samu na rage kukan da nakeyi din sai kuma ya lura da rawan darin dana soma a lokaci guda haka yasa yakai hannu shi a goshina yaji jikina ya gashe gaba daya.
Da sauri ya mike yana fadin ina zuwa ya fita daga dakin sai can gashi ya dawo da goran ruwa da serchers din panadol a hannun shi ya bare ya bani biyu yace in sha.
Nasha yace in samu wuri in kwanta na mike ya tambaya ina zani nace part din mu yace dawo ki zauna nan guri hajiya ban yarda ki koma wurinta tunda bata san ta rarashe ki ba.
Ban zauna ba nace a wahalce sallah zanyi ya gyada min kai na shige dakin Amma na barsu a falon suna ma mamu fada a kaina.
Na dade a ban dakin ina kuka kafin mama hadiye ta kwala min kira na fitoda kumburarun idanuna ina neman hijab.
Aisha mama ta kwalawa kira tazo tace kawo ma Fatima hijab ta saka sallah zatayi ta koma da sauri ta shigo dakin Amma ta kawo min .
Rana dai a dakin Amma na kwana har dare barci yaki zuwa min sai tunanen banza nake barkatai a raina ina jin Amma ta tashi zata je alwala tana magana ita kadai.
Wanan rayuwan damay yai kama ace ta ko ina babu dadi duk jummai ta rikita min rayuwan gida wanda ma bakayi zaton zai iya abu ba halinta ya koya mashi.
Mata kamar ibilishiya kun hana min farin ciki a rayuwana dana iyalina baki daya wanan yaron dake kokarin ganin ya gyara tarbiyan gidan shine kuma yazamo makiyin su a yanzu.
Taja wani uba tsuki ta dan dade a ban dakin koda ta fito ta samay ni a zaune bakin gado ta kalleni tana fadin tashi kikayi nace banyi barci ba dama Amma.
Ido ta zaro waje tana kallona yar nan ai gara ki ba kanki lafiya ki runtsa shima wanda ake rikicin kanshi nacen bai san abinda akeyi ba yanzu.
Wuce ta nayi ba tare danayi magana ba na shige ban dakin nima alwala na dora na fito na tayar da sallah koda na sallamay na dade a gurin zaune na hade kaina da gwiwana ina hawaye.
Ban san lokacin da kukan nawa ya tsananta ba har ya fito fili daga inda Amma take tace Allah buwayi gagara musali yar nan har yanzu kukan nan bai kare ba.
Ina kunyi magana da kawun ki yace zai duba a kai kodai makiyin ki za a daura maki ai kyaba kanki hakkuri ko ?
Nace cikin kuka Amma ki taimakeni ki ceci rayuwa ta kada ki bari a aurani ga wanan mutumin don Allah wallahi Amma tsoron sa na nake ji wallahi.
Ki kwantar da hankalin ki yar nan ai tunda na fahinci bakya so ba maiyi maki dole idan kuma sun matsa sai anyi ni da kaina zan warware auren idan naga yana maki ba daidai ba.
Nace Amma baki faga iskancin da sukeyi da matar sa ba ko a gaban kowa ne baida kunyar rungumar ta Amma haka Allah yace ayi don Allah?
Tace ina fa yar nan nima yanzu ai na gano ki sosai ba so hadin nake son ayi ba amma fa kinga sai idan kin kwatar da hankalin ki.
Don kada su dauka kece baki da tarbiya tunda shi namiji yayi shiru ke mace mai zai hana kema kiyi kamar yadda yayi .
Kin san mutane a ruwa sai a dauka baki da kunya da har kika tsaya kina fito na fito da iyayyen ki a kan auren ki gashi kinji har kawun ki ya fara fadin ko baki daukeshi a matsayin mahaifi ba.
Wanda hakan nasan ranshi ya baci sosai ne ga irin abinda yaga kina nunawa akan dan cikin sa kamar kin nuna shi bai haifiki ba ke nan tunda shi yayi biyayya ga mahaifin shi bai musa masa ba tunda ya tunkare shi da zancen.
Jin haka da sauri nace Amma nima in sha Allahu zan dauki shawaran naki kamar yadda kikace.
Tace to kiyi shiru duk abinda sukace kice masu to kamar yadda suke so kinji ko nace to Amma na gode.
Tace nasan manufar mahaifin ku kan wanan hadin shine yaga rayuwan ki dama ya inganta ne kamar yadda yake tausayin ki ke kadaice gun mahaifin ki kuma gashi ba wani mai karfi a gidan ku .
Haka yasa yai wanan hikimar ki samu suma yan uwanki su samu ta karkashin ki suci arzikin da Allah yai maki.
Shiru nayi ina sauraron ta tace ai da farko itama uwar taki tayi wanan haukan sai dana zauna muka fahintar da ita manufan yin hakan ta kafin ta sauko ta yarda da auren .
Don ba wanda ya zaci haka daga gurin ki tunda ai kina da ilimin ki yanzu kin san abinda ya dace mai kyau da marakyau ashe abin ba haka yake ba ke a gurin ki.
Jikina ya fara sanyi don tulamin kasan da Amma keyi don dai kawai taga hankalina ya kwanta a lokacin.
Na nisa kafin ince Amma nifa duk wanda kawu zai ban ya bani amma dai ba wanan dan hjy ba tunda ta nuna bata so na shima nasan ba zaisoni ba Amma.
Tace kwantar dai da hankalin ki yanzu abinda nake so dake shine ki samu iyayyen ki da safe ki basu hakkuri akan abunda kikai masu su yafe maki.
Sanan da kike fadan wau ba zai soki ba ai halin su ba daya ba da mahaifiyar sa kuma ke mace ce A ruwa zaki iya jan hankalin duk wani da namiji komai shekarun shi ko mukamin sa balle umar da yake mai saukin kai wani lokaci.
A hannun mu fa yake har yanzu ko da kike wanan maganan da uwarsa zata iya raba sa da abinda yake so da nine mutum na farko da jummai zata rabashi dani a duniya.
Sai dai ba yadda zatayi jinina ne shi din ko taki ko taso dole ne diyan ta su bini don nice dai kakar tasu balle ke da zaki zama matar shi nan gaba tasan lokacin da zaki kama abinki ga hannu ne.
Kai na dago na kalli Amma don jin furicin ta na karshe a gare ni sai dai ban iya furta komai ba don yadda nake jin bakina yayi nauyi ga magana yanzu.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:07 - ??5惙5惙5?: BISSIMILLAHI RAMANIN RAHIM DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAIJIN KAI, , , , ,

Saida akai sallah mun dade zaune kafin nakai kwace a gurin in faras barci barci mai nauyi ya dan dauke ni har Amma ta fita daga uwar dakin nata zuwa office din ta inda a nan zata wuni har dare watau falon ta.
Bai fi minti talatin ba na tashi zubur ina dube dube a dakin sai kuma na mike na nufo falo inda na samu Amma ita kadai tana dube dube cikin kayan ta tana ganina tace da sauri badai har kin falka ba yar nan nace Amma zanje wurin mamu ne.
Tace ki bari gari ya iddasa wayewa mana na dan tsaya kamar mai tunane nace Amma barin je kawai na nufi part din mamu din yayin da Amma ta bini da kallon tausayi tana gyada kai kawai.
Na samu part din a rufe haka yasa saida na tsaya na kwankwasa kafin ta bude tare da tambayan waye ?
Da muryana da bai fita nace sayadice ta bude tare da jayewa hanya na kutsa kai ciki ina shiga falon naja na tsaya guri daya yayin da ta mayar da kofan falon ta rufe kamar yadda na samay shi.
Ta tako a hankali zata shige dakinta nayi saurin kaiwa kasa cikin sheshekan kuka ina fadin mamu ki yafe min don Allah sai kuma kuka yaci karfina a lokacin.
Kamar zata wuce sai kuma taja ta tsaya guri daya ba tare da tayi magana ba ita kuma bata wuce ba.
Samun wuri naga tayi ta kai zaune kafin ta fara magana sayadi kiyi hakkuri da hukuncin da yaya ya yake akanki dani dake duk a karkashin ikon sa muke.
Haka Allah ya kaddara a kanmu sayadi kin san idan ta nawa ce bazan taba yarda da wanan auren ba don kamar yadda hjyn umar bata son auren nan kusan nina fita rashin son shi a raina sai dai ba yadda zanyi ne tunda ina karkashi ikon iyayyena da mijina.
Don haka kamar yadda nayi iyawa yina wurin ganin na hana yiyuwan wanan aure bai samu hannuwa ba na barwa Allah zabin sa haka kema nake son kiyi hakkuri kada ki yarda ki rsgin kunyan da za a tsane ki gidan nan har ai Allah waddai da halin ki.
Addua bai bar komai ga dan adam adduan mumumini bai taba faduwa kasa banza kin sani don haka don Allah sayadi ina rokon ki Allah kiyiwa Allah ki sakawa zuciyar ki salama kamar yadda na sakawa nawa na barwa Allah alamarin shi.
Ki koma ga Allah kamar yadda muka saba mika alamari a gare shi idan babu alheri cikin auren nan ubangiji ya wargaza shi tun kan a yishi.
Ki nunawa mara kunya cewa ke din diyace mai tarbiya da biyayya ga iyayyen ki kamar yadda shima yake kokarin nuna biiyayya gun mahaifin shi din.
Kema ina son ki taushi zuciyar ki duk abinda zakiji ko ki gani sayadi ki toshe kunnuwan ki da idanun ki a gidan nan.
Sai yanzu na fara gane manufan yaya akan wanan hadin da yayi wanan bin kuma bake kadai yaiwa shi ba dake da Aisha ce da Rukaiyyan gida yaya balarabe.
Babu wanda ya nuna tshin hankali daga bangaren su don haka sayadi mu may zaisa mu kasa hakkurin haka mu nunawa mutum mai adalci da mutunci a gare mu gazawan mu a cikin jinin shi.
Kukana ne ya yawaita alokacin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login