Showing 21001 words to 24000 words out of 419207 words

Chapter 8 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1525

mai son raya zumunci.
Ganin zasu rikice a falo yasa hjy maimuna bari falon ba tare da Alh sani ya farga da fitanta ba nan dai ta barsu suna kwama rikici a tsakanin su.
Part din ta koma ta gyara yaran ta zuwa wurin gwagon su hadiya dake zaune tare dasu a gidan don idan tana da girki tun zuwan hadiye gidan a gurin su take kai yaran su kwana ita kuma taji da dawainiya da maigidan.
Yanzun ma data shigo ta samu har yaran sunyi barci a falo inda ta barsu suna cin abinci kafin ta fita zuwa sashen maigidan don gabatar da hidimomin shi na yau da kullun da suke may kafin shiga barcin shi.
Gyara yaran tayi kamar yadda ta saba yi kullun sai ta shirya su tsab tare da kayan bukatan su takan goya daya a bayan ta ta rugumay dayan ita kuma mama ta rike mata hannu zuwa part din hadiye dake hade da gwagon ta sarakuwan su ke nan.
Suna zaune a falon su suna hira ta shigo da sallama suka amsa mata Amma dake taunan goro kafin shiga kwana tace yanzun nake maganan ku a raina banga an kawo min mazaje na tun dazun nace ko basuyi barci bane.
Kamar kullun sai da tayi halin nata watau murmushi a fuskanta tace ina gwago aikin san hali su basu kai tara basuyi barci ba.
Yabzu ma na san shiga hadama baban su shan shine na dawo na samu wai har sunyi barci a inda na barsu suna ci abinci.
Ba magana yara kamar kasa a gurin barci hadiye kama mata na hannun nata mana taji dadin sauke na bayan ta wa yan nan manyan diya haka tubarkallah dasu kamar su kadai ubansu yake ciyarwa a gidan nan.
Amma ta tabe baki tare da fadin ke kama bakin ki kar kisa a saka masu ido kuma a lalata min kimar yara ba,a fada ba sun tsone ido inaga an fada din kuma.
Hadiye dake shimfide yaron saman kujera tace yaya ko zasuyi dasu sai gani sai hangeb don Allah ya riga da yayi ikom shi.
Da jummai tasan yadda zata kawar dasu tun suna jarire aida ta kawar dasu a gidan nan don wanan matar kishin ta sai ita.
Maimuna tace yanzun ma ita tasa na fito suna can suna kwasa da yaya a falon shi daga magana ta hau fadar bakaken magana don kawai Alh yace yanzun ko maganan Umar muke yi dashi shike nan ta hau fada don may zaiyi maganan diyan ta da bare.
Da sauri Amma dake ta ya tsunan fuska tace waye bare a gidan nan banda ita da maryama kaji min mata da fada karya rikicin Jummai wani lokacin kamar mai motsi a kai.
Tayi ta gama don yanzu na kula shima yayan hali nata ya fara fita kanshi don ya fara gane halin ta ko kuma abinda akai may ne ya fita kan shi ba.
Amma ta karasa fadi cikin kunan rai da halin rikici iri na hjy jummai wanda ba gaira ba dalili takeyin shi a kan dan abinda bai kai ya kawo ba a gidan.
Sun dan zauna sun taba hira a part din sai lokacin da ta kwatanci hjy jummmai ta bar gurin Alh ta mike tana fadin barin leka wurin maigidan ko sun gama badakalar su.
Jummai mai rikicin gangan fada ba naki ba ya zama naki ni har mamaki halin mulkin ta ke bani ko ance mata samun wuri haukane ?
Ita dai hjy maimuna bata kara tsunkawa ba don bata faye son maganan kishiyoyin nata ba a gurin kowa, takan ce daukan nauyi ne hakan.
Har ta gama shirin ta ta rufo part din ta zuwa sashen maigidan hankalin ta yana ga maganan hjy jummai da tace mata wai ita din bare ne gun yayan mijin su da yake wa a gurin ta.
Ba abinda ta tsana kamar mutum ya ci mata fuska irin haka don muzantawa ne ba kadan ba.
Ta koma ta samay shi har ya gama abinda yake ya kwanta ta shigo dakin sai da ta tsaya ta kashe kayan wutan dake aiki a falon ta karasa uwar dakin shi.
Zaune yake saman sallaya da alama shafa,i da wutiri ya gabatar a lokacin yake addu,a ta shigo dan dago kai yayi ya kalle ta tare da fadin kin rufe kofa da wutan falon ta bashi amsa da eh tunda ban gan ka ba a falo na san ka shige ke nan .
Ai tun fitan wanan mara hankalin na shigo daki, mata kamar wata mai kwankwamai a kai ban gane ma Jummai ba a gidan nan tunda na auri maryam halin jummai ya sake baki daya a gidan nan.
Yaya laifi fa kayi mata kuna zaman ku na dadi rai daga kai sai ita da yan yaran ku, ka karo mata iyali a gidan don may ba zatai fitina ba da kai ?
Ku mata shine matsalan ku ai kada dai na miji yace daku zai kara aure yanzun komai dadin ku da mutum za a jiku da
shi.

Yau na wuni da murna da farin ciki a gidan mu ba don komai ba sai don jin Baffana yace Addah mu zata zo ganin mu daga malammadori.
Fita nayi zuwa gidan su Atika don in sheda mata zun gwagon mu garin misau yau in Allah ya yarda.
Na fito da murna na daga gida naji ance ke ina zagi haka kike shirin buge mutane baki ganine ko tsaban rashin kunyar takine ya tashi kuma.
Ganin babu mai cetona a gurin yasa nace a tsorace ba gidan su Atika zan shiga ba in fada mata zuwan Addan mu yau na bashi amsa ina dan ja da baya.
Uban wa yace ki yi yawon shelan sirin gidan mu a makwabta don kina munafuka ko ashe kece mai kwasan sirin gidan mu kina badawa a gari ?
Cikin inda inda nace wa ni wallahi a a ban taba kai maganan kowa na gidan nan wani guri ba ni may na sani da zan fada.
Mumushi ya dan sake na keta ganin yau ya sami gamina a waje yadda manjo ba zata jimu ba ya gasa ni yadda yake so.
Sai dai kuma yadda yaso inyi din ba hakan nayi ba don ban tsaya mashi tsiwa ba ashe dama iskancin naki a gaban manjo kike yin shi don kinga tana kama maki iya shegen ki a gidan nan ko ?
Ban tanka shi ba don Allah Allah dai nake ya matsa in samu in shige tun bai min wani muguntan daya saba min ba.
Kina ji ko duk naji kin fadawa wani zuwan Adda sai na balbalaki a gidan nan ko wa yai maki tsaye yau da sauri nace to kawai na dan gwauta shi na wuce.
Tun rikon da yai min nake ranan nake matukar tsoron yaya sadin don na dade manjo na shafa min robb a gurin don ciwon da hannun ya dinga yi min.
Ina shiga gidan na manta da gargadin da yaya sadi yai min saboda doki na fara ba Atika labarin zuwan Addah da dadin da nake ji wurin ta idan tazo don ita kadai ke nuna min kulawan ta sosai.
Mahaifiya ta yanzu ba zan iya tuna dadin ta ba tunda tun ina karama aka rabamu ko hutun danaje gurin ta banji dadin shi ba ga rashin sabo ga kuma matsin mutanen gidan su.
Kullun muna part dinta zaune sai kuma idan munje gidan Amma wanda ba kullun ake zuwa ba da kyar nayi satin biyu na dawo Azare.
Ashe tafiyan safe adda tayi ina can gidan su atika ashe har ta iso ban sani sai da aka aiko kirana daga gidan mu koda naje ba samu Adda mu ta iso ko.
Da murna na , na tare ta hanyar kankamy mata jiki ina fadin oyo yo addana ta rike ni tana fadin kai kai kai Fatima kece kikai wanan girma haka kamar na shekara ban ganki ba.
A,a tubarkallah masha Allah yarinya ba inda ta rago mahaifin ta wurin kama wanan ai kamar photo copy din marigayi ne sai dai da yake ke mace ce kindan dara shi kyau gaskiya.
Nace Adda yaushe zaki koma halan ?
Kaji min ya daga shigowan ki sai tambaya ina dai yanzu ta iso ba kya, barta ta huta ba dai.
Manjo na matsu mubar garin nan ne wallahi mu koma azare sai dai don Atika ce ban son barin garin .
Na juya gurin Manjo dake kallona ina magana nace Manjo kinga mugun nan ko dazun ya tashi kara masgana Allah kadai ya kwace ni a hannun shi.
Da yau sai dai kiga an kawo ni karara a gidan nan manjo tace kina nufin yaron nan Sadi bai fita hanyar ki ba har yanzu.
Adda ta kura muna ido tana sauraren zancen mu da manjo tace badai dukan yar nan yaran nan ke yi ba manjo ina fatima ina wanan yaron har da zancen duka a ciki.
Kema kya fada dai ni yanzun kullun addu,a nake Allah ya kawo muna mafita a gidan nan mu tattara mu bar masu gidan su.
Manjo yanzun ma zancen Fatima ne ya kawo ni gari nan don munyi waya da mahaifiyar Fatima akan tana son zaman Fatima ya koma guri ta.
Baki na turo gaba ina fadin ni ba inda zan tafi in bar manjo na ni gaskiya a bar wanan magana Addan mu.
Idan kin so ki kama bakin ki kawai ba wanda ya isa ya rabani dake A ruwa sai Allah daga manjo sai Amma ke kirana da Aruwa a duniya kancewa an haifeni lokacin malka sosai ranan da aka haife ni tun asuba ake ruwa har yamma.
Wanan dalilin yasa tsufin ke kirana da aruwan da suke ce min ita da Amma yar birni kamar yadda na laka mata saboda abubuwan more rayuwan da na gani a gidan ta lokacin danaje masu hutu.
Manjo taci gaba da fadi cikin hawaye yar ita kadai nake gani in tuna da Abubakar a duniya tana debe min kewar ubanta dana rasa sosai a rayuwana.
Barin jikin Addah nayi na koma wurin manjo na make a jikin ta kamar a lokacin za a rabani da ita nake ji.
Na masan fadi ne kawai manjo ba zata taba bari a rabamu duniya don haka na sake ajiyan zuciya.
Don jin manjo nake a raina kamar ita ta haife ni a duniya banda wani wanda na shaku dashi irin manjo na .
Don haka nake daukanta komai nawa itace uwa da ubana dana sani kamar yadda kowa yasan dadin mahaifan shi.
Jin abinda manjo tace yasa Addah taja bakinta tayi shiru sai dauko wani hiran tayi don dai kawai ta kwantar muna da hankalin mu a lokacin tayi hakan.
Don ta manta ina dakin ta kawo wanan magana don a gaskiya yanzun tafi bukatan mahaifiya ta ta dauke ni ko don bayanin da tai mata akan rayuwa na a nan gaba.
Ni dai tun wanan lokacin banji an kara ta da zancen ba ban kuma tayar masu ba tunda na nuna ban son zama da mahaifiyata din.
Zaman da Addah tayi damu na dan kwanaki zamane na jin dadi a gare mu don da kanta zata girka muna abinci muci sai mun koshi haka yasa na rage shiga gidan su Atikan da nakeyi yanzu.
Wanda dama ashe yunwa ne ke kaini gidan ban sani ga gyaran da nake samu ko ban wa Allah wanka biyun nan yanzu dole in yi shi.
Don sai dai tace min ga ruwa can a ban daki in tashi inje inyi wanka tu ina ki har nazo na saba da hakan.
Lokacin da naga ta fara shirin komawa garin da take aure sai kuma hankalina ya tashi sosai nake ji kamar in bita mu tafi tare saidai kuma ba zan iya barin Manjona ba a lokacin.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
16/11/2021, 22:38 - ??5惙5惙5?: YA ALLAH MUNA NEMAN KARIYAN KA GA DUK WANI ABIN KI DAGA GARE KA , ALLAH KA TSARE MU DAGA HALAKA KA SADA MU DA RAHAMOMIN KA AMIN YA ALLAH, , , , ,


Amma na zaune saman sallayan data kare sallahn la, asar bata daga a wurin ban tun bayan idar da sallah nata Alh sani da ya dawo kasuwa a lokacin ya nufo part din nata.
Jin muryan shi yasa ta dago kai cike da farin ciki tana mai amsa mashi sallaman shi a cikin fara, a da sakin fuskan irin na da da maaifiyar shi.
Yayin da har saida ya samu guri taga ya zauna hankalinta na a kansu tana duban su shi da yaran biyu da ya riko ma hannu cikin so da kauna kamar kullun .
Hannu ta mikawa yaran su zo inda take sai yaran suka noke alaman basu zuwa gurin ta a lokacin tace .
Lalai yau don kunga uban ku shine zakuyi min butulci irin haka har da kai hussaini da nake ganin kafi dama a gurin kyuya ?
Shi wanan dama zubin wan sa ne sak yz kwaso wurin miskilamci bai ragewa umar komai ga hali gashi suna da zube dashi sosai da umar yai aure sai ace yaran nan nasa ne wallahi.
Alh sani yayi dariya don jin abinda ta fada yana shafa kan yaran yace a she bani kadai ke ganin hakan gare su ba hajiya idan sunyi wani abin sai su tuna min da umar lokacin da yake karami.
To abin ne bai faduwa a gidan nan sai ya zama karamin magana tunda uwar su umar din na fadin yaran ta kaman su daban sun fi kowa zubin kyau a gidan nan.
Cikin dan tsuke fuska cike da damuwa yace Hajiya ko bata son a danganta ta da yaran nan yaya zatayi tunda Allah ya nufa zasu fito a tsatso daya.
Halin jummai yanzu ya canza ga baki daya sai addu,a amma ni ban taba ganin kishi irin nata ba a duniya mace sai kace bata tunanen makomar ta.
Babu garin Allah da zai waye yanzu Jummai bata tayar min da hankali ba a gidan nan don kawai na karo mata abokan zama kamar da can da zan aure ta nayi mata alkawarin ban kara aure ne.
Ki duba yanzu yaron nan dake can yayi zaman shi yaki ya dawo gida tunda ya kare abinda yaje nema a kasan ai ya kamata ace ya dawo gida yanzu dai.
Amma ita Jummai taki gane abinda nake nufi da dawowan nasa gida a kan lokaci yanzu shekara biyar ke nan fa da ya gama karatun sa wai sin bashi aiki a can england din.
Duk wani aiki da zaiyi can yanzu akwai makamancin shi a na kasan amma ita ta ki ta gane hakan sun hada kai dashi duk lokacin da zan mai maganar gida sai ya kai karana a gurin ta nasan kuma ba komai bane sai dan abinda take ganin yana dan turo mana nan ne yake tsone mata ido kawai.
Tun da ya fara magana ido kawai ta tsura mai tana sauraren shi har lokacin da taji yayi shiru ga maganan shi ta sauke ajiyan zuciya tana fadin.
Nima dai wanan zaman da yaron nan ke yi kasan masu jajayen kunnuwan nan bai kwanta min a rai ba sam duk da na gari ai gida aka sanshi ka gama abinda ya kai ka sai kuma ka dawo gida a san ka gama amma may ye amfanin zaman shi a can shi ba iyali ya ajeba.
Balle a ce don su yake can zaune wani kasan kuma da hakan ne ma ai hankalin kowa zai fi kwanci dashi koda yana can din.
Sai dai ina ganin ita uwar bata tunanen hakan gare su don dan abinda suke aiko mata din dashi nan tana famkama wa mutane ita ta iya haihuwa.
Kamar tasan abinda Allah zai mayar da sauran yaran nan gaba idan Allah ya raya muna su ai shi mutum ba a gama hallitan sa sai ranan da ya mutu.
Zaman su gida shine kimar mu da cikar kamalan a garin nan don ba abin alfahari bane ace danka ya tsabbari ya koma wata kasan na uwan duniya ba tare da iyali ba.
Alh sani ya sunkuyar da kanshi kasa yana nazarin maganan tsohuwar daya girgiza mashi zuciya ya kasa furta komai ga hakan .
Sai dai a zuciyar sa yana nasawa dole ne yaran nasa su dawo gida yanzun don gaskiya mahaifiyar tasu ta fada yanzun don haka zai dauki mataki a kan komai.
Da haka ya tashi yai mata sallama tare da yaran ya nufi hanyar fita daga part din cikin sanyin jiki bayan yai wa mahaifiyar tasu sallama.

Yana aiki a shago kira ya shigo mai bai dakatar da abinda yakeyi ba don kada lissafin ya kubce mashi sai da wayan ya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login