Showing 336001 words to 339000 words out of 419207 words

Chapter 113 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1446

kashe wayan idan ba kunnena ya rudeni ba zan iya cewa harda guda irin na larabawa naji kafin kashe wayan.
Zaku gama ku kawo kan ku na fada ina aje waya don ba zan yarda mamu ta bisu ba sai dai su su kawo kansu gare ta badan komai nake son haka ba don hjyn su yaya kawai nakeson haka ya kasance din.
Ranan haka suka wuni kirana suna min tambayoyi muryoyi daban daban ina basu amsa dake sasu nishadi da alama zancen yana masu dadin ji don kowa nason ya tabbatar da hakan a cikin su.
Nayi masu kwatancen komai da yadda zasu iya kawo kansu garemu idan sunzo garin kano din har address din gidan duk na basu.
Washe gari na shirya naje gida da dakin hjyn su yaya na fara saidai ban sameta gida ba ta fita a lokacin na fito na shiga na gaida hjy maryam dake son jana da hiran abinda ya faru ranan.
Ban yarda na bata wani amsa ba saidai na bata amsa mai kama da sako nace shi mutum ai ba a debe rai gare shi idan ba ya mutu ba don wata rana wanda kake gani banza shine wani abu gare ka.
Na barta na fito zuwa wurin Amma mun dade muna hira kafin in shiga wurin mamu don kawu bai gida a lokacin ranan ya fita kasuwa.
Mun dan dade muna hira kafin ince mamu gobe zaki kwashe kujerun nan a saka maki sabbi da duk wani abinda baida amfani a part din nan don zakiyi baki cikin kwanan nan ba zanso suzo su samu wurinki a haka ba.
Sayadi da gaskiya zasu zo na kwashe duk yadda mukayi dasu na fada mata addua naji tanayi a lokacin kafin in mike ina duban abinda ya dace ace an kawar a lokacin.
Na fita tare da murja zuwa wani shagon dake decoration din daki mukayi cinikin wasu set har da gado na gani mai kyau na hada dashi da labulaye masu kyau mukai jinga na biya su yaran shangon suka biyomu da kayan a take har gidan.
Lokacin marance yayi saidai hakan bai hanasu aikin su ba kafun dan wani lokaci har sun hada komai don nan na barsu suna aikin don kiran me nake a gida har wanan lokaci da yaya ke min a waya.
Washe gari muna barcin safe sai ga kiran hjyn su ya tayar damu daga barci inda na fahinci zancen take mai lokacin da naji yace kaya kuma mama wallahi ban san zancen da kike min ba yana kallona.
Tashi nayi na shiga ban daki a lokacin ban fito ba sai da nayi wanka na tsane jikina na fito ina goge ruwan a kaina yana zaune a bakin gado naji yace min.
Wani gyara kikaje gida jiya kika sa akawai maman twins a part din ta ne ?
Nace ina kallin shi cikin rashin tsoro ko darr din shi gyaran part din kawai nasa ayi mata don zatayi baki kwana nan .
Ba zan so azo a samu maxaunin ta a haka ba yasa nayi wanan shawaran na gyara mata part din don yanzu kawu baida karfin hakan garesu ita kuma kasa ba aiki takeyi ba ai.
Ya danyi dan shi kafin yace mai yasa baki fada min ba kafin ki aiwatar da hakan don gashi yanzu kin ja min magana wurin mama aida kin fada min sai in saka ai masu gyaran yadda ya dace ga baki dayan su.
Kayi hakkuri banyi tunanen yin hakan ba don naga hakan kamar ba komai bane shiyasa.
Baiyi magana ba illa idon daya tsura min na dan lokaci kafin ya mike ya shiga bandaki hakan ya bani daman fita daga dakin nashi na kuma nawa part din.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:16 - ??5惙5惙5?: Na koma dakina cike da mamakin hjy a raina ina fadin watau ita dai nata rayuwan ke nan bata son taga dayan su ya karu ta ko ina a gidan sai ita kadai.
Har nawa na kashewa mamu wanda ya tsone mata ido haka ta kira danta da wanan safiya haka .
Duk daz baiyi magana ba na fahinci baiji dadin hakan danayi ba sai dai kawai ya kyale nine don yawan magana da bai son yi amma ranshi ya baci da hakan.
Saida na gama abinda nakeyi na fito falo yana zaune ya saka faran suit a jikin shi farare kal dasu kayan sun makur karban jikin shi sosai.
Yana zaune ya harde kafa a cikin dan uwa yana amfani da wayan shi ta hannu wanda hakan ya dauke mai hankalin shi a lokacin.
Har na karaso kusa sao lokacin ya dago kai ya kalleni har na karaso inda yake zaune na zauna a hannun kujera da yake zaune akai jikina yana dan gugan jikin shi a lokacin.
Bayan na zauna nace mai barka da hutawa ya amsa min ciki ciki na dan yi shiru kafin ince nazo in baka hakkuri akan kuskuren danayi na yiwa mahaifiyata abu batare dana sanar dakai bane yaya.
Bai tanka min ba a lokacin nima banyi magana ba har tsawon wani lokaci muna zaune a hakana kafin yace.
Ba ina nufin idan zakiwa mahaifiyar ki alheri sai kin fada min ba ko yaushe amma ina son ki sani irin wanan bake mace ya kamata kiyi wanan ba.
Don kin san ina nan kuma in kince ga bukatan ki dole zanyi masu gaba dayan su a lokaci guda.
Amma ke kinyi bugun gaban kanki kin aiwatar da kudirin ki wanda yin hakan yaja min magana gun tawa mahaifiyar don tasan ba aiki kikeyi wanda kudi suke shigo maki ba abinda ta fada ke nan wanda hakan gaskiyane kuma.
Jin shi nakeyi a fili banyi magana ba har lokacin amma kuma ina fadi a raina shike nan dai hjy ta mayar damu fakirai da basuda komai a duniya sai an bamu ko sai anyi muna.
A daidai lokacin da yace kinsan dan abu kiris take nema a gareki wanda zata samu mafakan da zata sokeki dashi ga kowa.
Nisawa nayi nace kayi hakkuri yaya na fahinta da maganan ka hakan kuma wani damane a gareni yanzu tunda dai mu bamu gaji arzikin da zan tsinanawa kaina ko uwata wani abuba a duniya.
Don haka ina rokon ka ka bani dama in fara aiki da kowa zai san inada madogara a yanzu wanda zan iya rike kaina da yan uwana dashi.
Dago kai yayi ya kalleni tare da fadin mafalkin ki ke nan kuma a yanzu Zarah aikifa kikace in baki dama kiyi ?
Nace ba bako abu bane nagani a wurin ka yaya don matarka tana aiki ai Ok nufin ki kenan don merry na aiki sai in barki kema kiyi aiki dom kina ganin kina da takardu yanzu.
Ba nufina ke nan saidai hakan kuma ya shafi magana mu a yanzu don tabbas nasan sai inada madogara zanyi abinda raina ke so don a zauna lafiya da kowa.
Don ka barni na fara aikina hakan ba zaisa a zargeka ko aga kasawan ka ba tunda kowa yasan merry ma ma,aikaciyace ai ita.
Har na gama magana ta na gaji da zama na mike zuwa dakin su maria bai kara kulani ba nima ban tankashi ba.
Don na fahince shi yanzu zamu kwashi rigima nan gaba idan nace aiki zan dinga fita zuwa yi.
Wanda maganan shi ta yau yasa naji a dole zan samu abinyi nima ta inda kudi zasu dinga shigo min a hannu na lokaci lokaci.
Gaskiya ya fada tabbas mace sai tana da madogara take cika mace duk da nasan bai rageni ta ko ina ba da hakan yana bani idan ina da bukata sai dai kuma meye amfanin bani kudin da yakeyi tunda banda yancin yin abinda naga saboda mahaifiyar shi kuma.
Kwana biyu haka mukayi shi sama sama dashi ranan da dare ina zaune bayan ya dawo ya shiga dakin shi ya fito ya dawo ya samemu falon har lokacin.
Yara suna zaune suna game yace daga inda yake tsaye zaki shiya kije bauchi cikin satin nan don karshen sati mai zuwa nake sa ran tafiyan mu.
Allah ya kaimu nace ba tare da nayi wani nuna doki hakan a gaban shi ba sai dai a kasan zuciyana nayi murna da jin hakan.
Shima halan na bashi mamaki ne ya tsaya yana kallo na don rashin nuna farin cikina a fili da banyi ba a lokaci.
Ya mayar da hankalin shi wurin abinda yaran keyi a lokacin sai lokacin nace ranan me kenan zamu tafi ?
Don in sani in fara shiryawa na dauka ai kin fasa zuwa ne a yanzu ya bani amsa da hakan.
Nace ba zan bar kasan nan ba ai ban tafi naga iyayyena da yan uwana ba dama don shekara biyar da wani abu ba wasa bane duk da banda mahaifi ko uwa a can amma ai ina da kakan da take kamar uwa a gareni can din.
Kafan shi yaja ya bar falon zuwa wajen gidan a lokacin na mike zuwa daki nayi waya da mamu ina sheda mata yadda mukayi dashi.
Tace ai sai ki fara shiri kada sai ranan tafiyan yazo ya sanar dake nace nasan halin sa ai mamu zai iya min hakan don yaga iyakata.
Kamar ko na sani washe gari da dare yake ce min da safene tafiyan mu don haka in kwana da shiri nace amma da yaran zan tafi duka ko?
Da sauri yace banda su Abdul su zasu zauna a nan tare da maria saidai zaki iya tafiya da sultana ita kadai.
Amma yaya idan kaimin haka sai nake ganin ka raina da iyayyena tunda suma zasi so suga abindana haifa ai.
Bayi magana ba yaja bargo ya rufa don baison dogon magana yasa ya kyaleni saidai har cikin ranshi hakan yake nufi ashe.
Washe gari kuwa na bashi mamaki bayan shirin da nayi ne naga magar gaskiya yake nufin yayi na kira kawu a karo na farko nakai karan shi wurin shi.
Kawu yayi fada sosai kan wanan magana yace da yaran zan tafi inda murja da fauziya zasuyi min rakiya can.
Ban san yaya sukayi da kawu ba ya shigo yana fada wai don me zan kai karan shi wurin daddy so nake in hada shi dashine ko mai ?
Sai dai ki sani a maimakon kwana biyar danayi niyar kiyi acan yanzu uku kawai a can naso yin magana kuma dai na shere shi ban tankashi ba muka dauki hanyar bauchi yana tsaye sai da yaga tashin mu ya tafi inda zashi.
Mun isa lafiya na gidan bai bace min ba yadda nayi tsamani don yanzu akwai ci gaba a ko ina saidai kuma muna shiga unguwar gidan su Atika kawai na sheda don namu gidan an canza mai fasalin ginan ya koma na zamani ta gaban gidan.
Sai da muka tambaya ashe yaya hashim ne ma a zaune ban gane ba a wurin da muke tambayan yana yar tireda a bakin kofan gidan anyi mai dan shago manne da gidan ya nuna muna hanyar shiga gidan inda zamu bi.
Can yace wai dai ko fatima ne haka ban sheda ki ba nace nice yaya nima da farko ban shedaka ba ai naga ka zama wani uztazu a yanzu.
Yo Fatima za a girma kuma aci kasa ai hakan baiyi ba rayuwa haka muka shigo gidan muna yar hira dashi har muka kai tsakiyan gidan da komai ya canza min yanzu na fasalin ginan gida.
Yace ku fito yau ga A ruwan manjo a gidan naku suna falo suna kallo sai gasu a lokaci daya suna fitowa daga dakunan su da yanzu aka rarabashi basu hade.
Wanan karon sosai na samu taron arziki ga kowa sai raba idanuwa nake inga kakata dana dade ban ganta ba a rayuwana.
Wani part dake daban naga yaya ya nufa da kayana yana kwalawa manjo kira hakan yasa hankalina ya dan kwanta don har gabana ya fara faduwa da farko.
Dakin muka nufa ga badayan mu ana ta shigo muna da kayan mu a ciki murna ba zan iya fada ba duk da akwai canji sosai a gidan dana gani sai dai bai hana inga manjo ta sauya min ba kamar yadda naga sauyawan Amma lokacin da muka zo.
Bamuyi wani dadewa da zama ba sai ga baffana ya shigo da murnan shi yana muna sannu da zuwa a cikin fara, a da haba haba duk da dama dai banda matsala dashini.
Bayan mun gama gaisawa ne manjo take tambayan ina mijin naki ba tare kuka zo ba dan albarka muna ta ganin sakon alheru sa lokaci lokaci.
Dama duniya haka ta gada sai Allah ya turo wani a rayuwan ka da baka sani ba ya taimaka ma ta wani dalilin ka.
A nan na fahinci dai duk yadda akayi yaya yana taimakawa iyayyena bai barsu a yadda ko yaushe nake a cikin damuwa da halin wahalan da muke ciki ba.
Bayan munci mun shane nake tambayan Atika da iyayyen ta manjo take fadin umman Atika dai tana nan lafiya sai dai mahaifintane ya rigamu gidan gaskiya a bara .
Salati nayi tare da mashi addua da fatan dacewa da rahaman ubangiji naji mutuwan bawan Allah nan har kasan raina don ban samu saka mai da alherun da yayi min a baya har Allah ya dauki ranshi.
Kamar tsohuwar tasan me nake tunane tace min mijin ki ya tallafa masu sosai lokacin da yake kan jiyar saidai Allah baiyi akwai shi da sauran shan ruwa gaba ba don har yaji sauki ashe na tafiyane sauki.
Wani dadi da sanyi naji har cikin raina nan take fada min ai har gaisuwa yazo yayi wanan zuwan naku da kukazo yace ba zaki zo ba sai an gama muna gyaran gidan nan daya saka ayiwa baffan ki.
Ga shago shi daya fadada masa yanzu yaran nan su hashimu suma yanzu suna da sana, a har aure sukayi .
A hankali na runtse idanuwana ina jin wani iri a raina da tunanen shi yaya wai wani irin bahagon mutum ne ?
Daidai da rana daya bai taba yi mun hiran wani daga cikin yan uwan nawa ba ko ya fada min irin alherun da yake masu din.
Atika fa nace bayan na sauke ajiyan zuciya tace tana gidan mijin ta zaune sai dai auren ne ita batayi dace ba ashe yaron baida kirki sai bayan aure aka gane hakan .
Hakan take zaune tana hakkuri dashi tunda ga zuria an tara kuma yanzu tana cikin min bayani ne mukaji sallaman Umma ta shigo tana fadin maraba da bakin turai.
Kullun muna ta saka ido mu gane ku don an fada muna kun shigo har da iyalin ki ta shigo dakin da sallaman ta.
Manjo tace yar halas yanzu haka maganan ki mukeyi nan ashe kina tafe ?
Nace umma kika taso yanzu nake shirin zuwa in gaida ke tashi nayi na rungumay umma sai kuma na fashe da kuka don ganin yadda umma yanzu ta ya mutse kamar ba umma da take yar gayu a daba da mijin ta yake raye.
Ba kuka ya kamata kuyi mashi ai yanzu addua ya kamata mu bishi dashi Fatima Allah ya rasu yana mararin ganin ki Allah bai nufi ganawan ku ba dashi.
Na kara jin zafi a raina saida na danyi kuka mai isata suna ban hakkuri kafin ince cikin muryan kuka Umma Atika fa.
Tace Atika na nan lafiya Fatima haihuwan ta biyu yanzu don bata dade da haihuwan na biyun ba ma.
Naji dadin jin hakan a gaban ta don ban yarda na nuna mata manjo ta fada min komai a game da ita.
Ummane da taga ina murna tace kayya Fatima mijin naku ai ba yaron kirki bane yar uwar ki tana hakkuri da auren zamanin nan.
Gashi ba wani ilimi mai zurfi tayi ba da za,a sama ta aiki dashi yanzu ma kasan nan ko masu ilimin suna zaune zube babu aikin yi.
Haka dai muke hakkuri abindana dan samu nake bata tana ci kardai auren ya mutu ta zauna dakin ta.
Nuna damuwa nayi a baiyane don na fahinci inda matsalan ya fara a wurin rashin abinci ne tunane nayi ina yayan ta bashir yake ne ?
Na dago kai a hankali nace yaya bashir fa umma tace yana Abuja kin san ya auri wata yar can ne ba yadda ban hanashi ba ya dawo gida yayi auren yarin nan ya kiya yanzu gashi bamu jin duriyan shi sakoma sai yaga dama ya tuna damu.
A raina nace wani matsala ke nan kuma sabo da iyayyen mu suke fuskanta mutanen da suna da gaskiya da suke matsawa diyan su auren a gida ashe.
Mun dan jima muna hira tana koro min matsalolin da suka fuskanta a bayana wanda na tausayawa hakan sosai.
Don ban manta irin alherin da wa yan nan mutanen sukai min ba lokacin da nake

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login