Showing 270001 words to 273000 words out of 419207 words

Chapter 91 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1477

ya koma ya kwanta a makarin kujera ya dora kanshi yana lumshe idanun shi a hankali .
Bai faye yarda da mafalki gaskiya bane amma wanan din yana da bambamci tunda shima yayi kusan irin wanda nayi din ai to mai hakan ke nufi ke nan ?
Ganin yadda ya kwanta yasa na kai kaina a jikinshi na dan mike kafafuwana ga makaran kujeran ta gefe na lushe idanuwa hannunshi naji ya dora a kaina yana wasa da gashina a hankali.
Wayan shi ne ya dauki kara ya dauka muna a hakka yadda muke da kusanci da juna din naji yace mama barka da asuba.
Jin hakan yasa na mike da sauri zanbar wurin naji ya rikeni gami da yimin alama in kwanta abina.
Barkan mu tace mai yace lafiya mama da safen nan haka kallon lokacin da yake kira safe nayi lokacin sha dayan rana yana batun yi a London.
Babawo akwai matsala a gidan nan nayi neman layinka in sanar dakai halin da muke ciki ban samu ba.
Naji yace may ke faruwane mama a gidan wai kamanni Alh zaice ya dakatar da girki a gidan nan kan wanan shedaniyar matar kaddaran da ya aura maimuna harda hjy maryam laifin ya shafeta don bai son gaskiya .
Abinda nake so dakai yanzu shine ka rubutawa yarta takarda ka turota jirgi ta dawo masu gida tasan munfi karfin ta ta ko ina don hakan kawai za kaimun ka wanke min bakin cikina.
Shiru kawai yaya yayi bai tanka ba a lokacin ita kuma mama taci gaba da aibantani da uwana ina jin ta kaf don ina saman jikin shi lokacin komai na shiga kunnena.
Can ko taji haushin shirun da yayi mata din ne bai bata amsa ba tace wai kanajina kuwa babawo ina magana kayi shiru ko kana nufin bukatana ba zai yuyu bane na sani.
Na fadama ban yarda da karatun da kace in bari ta karasa ba yanzun nake son ayita ta kare ba kare bin damo inhar ta kare karatun ai taci riba damu ke nan daga ita har uwarta din don yarta ta samu madogara ta dalilin mu don haka ina duban hanyar ta zuwa jibi ta kashe wayan don baida niyar bata amsa a lokacin.
Yana jin ta kashe wayan ta naji ya sauke ajiyan zuciya yana fadin mamake nan laifin wani ya taba shafuwan wani ne ashe ?.
Ya dago daga yadda yake kushingide ya zauna da kyau nima mikewa nayi zaune gaba daya yanayina ya canza ga baki daya lokacin.
Sai addua nakeyi a bakina don abin ya firgitani sosai Allah kadai yasan tsawon lokacin da hjy ke binshi akan ya sakoni don maganan ta ya nuna ba yau bane farko.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:25 - ??5惙5惙5?: BISSMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AMINN YA ALLAH,

GA MASU BUKATAN LAYINA ZASU IYA KIRA TA WANAN LAYIN KAMAR HAKA 08036959257 DON TURA KUDI KUMA ZAKU IYA SAKA KATIN KIRA KO TA ACC NOBA KAMAR HAKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK NAGODE DA KULAWAN KU.

Ki sani shi hakki kona haramun ne kamar yadda wasu ke fadi hakki daine, don Allah mu kula yan uwa .

Tunda na samu naja kafata zuwa daki da kyat ban kara fitowa falon ba ina kwance ina faman tunane ga ba wanda zan iya fadawa wanan halin da muke ciki.
Wani bangare na zuciyana yana bani in sulale kafin sakin ya biyo baya in koma gida da kaina inyaso ya kawo min takardan nawa a gida.
Ba irin shawaran da banyi ba a lokacin har rana tayi lokacin sallah yayi nayi sallah ina kwance ina abu daya a da(kina har lokacin bancin ma manufa ba saidai ina ga shawaran in gudu in koma gida har lokacin.
Tambayan kaina nayi ta yaya zan iya guduwa bayan banga visa dina ba tun lokacin da muka sauka a kasan ya karba daga hannuna.
Sai bayan sallah la,asar ya shigo dakin ina kwance rub da ciki saidai ba barci nakeyi ba a lokacin.
A hankali ya karasa shigowa dakin yana kallona don jin shigowan shi dakin baisa na dago daga yadda nake kwamce ba a lokacin.
Zarah kinyi sallah kuwa ko kina nan kwance kina tunanen banza tun dazun idona da ya cika da kwalla na dago kai ina kallon shi dasu nace ciki ciki nayi dazun.
Zama yayi bakin gadon yana kallona cikin yanayin tausayi daya san maganan da mama zatai mashi ke da yabarni natashi kamar yadda nayi niyaryi da farko da banji abinda zai daga mim hakalina ba yace a zuciyar shi.
Ki tashi muje falo kayana da na sayo danaje china sun iso akwai kayan dana sayo maki a ciki ko zasuyi maki kyau ban sani ba.
Bandago na kalleshi ba ina daga inda nake kwance a raina nace shike nan ta faru ta kare har ya soma min shirin zuwa gida ke nan ashe ?
Ganin ban motsaba yace zarah ke nan badai maganan mama ce ya tayar maki da hankalin ki haka ?
Zarah kin fara sona har hakane yanzu baki son kiji ance za a rabamu ko mai da har kika shiga tashin hankali hakan.
Da sauri don ya fahince ni nace dole ne yaya ya sake kallona a cikin yanayin tausayawa a gareni yace mama bata sani bane ai komawan ki gida yana daidai da komawan ta nasu gidan itama.
Bayan hakan ku zarah sai naga yadan girgiza kai kafin yace idan nace maki yanzu babu mai iya rabani dake zaki gamsu da magana ta kuwa ?
Da sauri don in kwantar mai da hankali kamar yadda naga yana kokarin yi shima nace mai zai hana yaya in yarda da kai tunda ban gaka da mugun hali ko kadan a rayuwan ka da zaka iya cutana sai naga yayi dan murmushi ya sake kalloni ya gyada kanshi da alama ya gamsu da maganata.
Ke nan zaki daure da duk wani halin da mahaifiyata zata nuna maki na kiyayya nan gaba ?
Nace nima ai mama mahaifiyatace koda ban aure ka ba yaya yanzun ma zafin kishin mamune ya shafeni ai har take jin bata sona a tare dakai.
Naga ya saki wani laulausan murmushi a fuskanshi yayin da hannayen shi ke dunkule a wuri daya yana dan buga kafan shi daya a kasa.
Zarah ke nan kin dai iya magana kamar wata babban mace to wai in tambayeki zarah shin kinsan taba noticing mai kalman aure yake nufi a wurin ma aurata ?
A daidai lokacin na mike zaune daga kwancen da nake ina bashi amsan duk wani magana da mukeyi sai da nadan yi murmushi nace .
Nace yaya ke na indai zaman auren kowa wace mace zatayi dace da namiji kamar ka to ina ganin kaman mata sun gama dace maza da jin dadin aure.
Don baka rageni da komai ba na rayuwa yaya kana ban cida sha ga sutura maikyau sai wanda na zaba zan saka uwa uba ga karatu inayi babu matsala ko kadan a cikin sa babu kyashi ko hattara a zaman mu.
Sai nake ganin indai auren namiji ne kamar ka babu wace tafini dace da aure wanan zamanin kaf a duniyan nan.
Dadin zancena ya kamashi ya jawoni zuwa jikin shi tare da dan bubuga min baya yana fadin nima ina alfahari dake zarah taso muje falo kiga kayan dana sayo maki idan zasuyi maki in basuyi ba sai in sayo maki wasu a nan don kinsan wani sati zaku fara shiga school.

KANO NIGERIA.
Murjanatu ce tsaye a bakin famfon waje na kofan part din su tana wanki don ko wani part akwai famfon a kofan wurin do laluran waje.
Ganin yadda hjy maryam ke dan waige waige zata shiga part din yasa tasan ba alheri zata kullawa ba a lokacin.
Samun kanta tayi da bin bayan ta ta window gefen dakin hjy jummai dake bude ta labe tana sauraren su.
A daidai lokacin da hjy jummai ke fadin ai na fada maki yadda suka kona muna mai a gidan nan sai na konawa ko wanin kaf rai agidan nan fiye da nasu.
Nayi waya da babawo da safen nace ya sako masu yar iskan diyan su yasata jirgi da takardan ta ya turo ta gida karatun da yake fadi tanayi ban yarda koshi ta karasa ba.
Da sauri murja ta dafe kirji tana fadin na shiga uku A ruwa kena za,a sako kowa da sauri tabar wurin jin yadda suke faman aiban tani da mamu.
Kayan ta tataro ta nufi part din su Amma da mama hadiye dake zaune suka kalleta bayan ganin ta da himin kayan da ta fita dashi don wankewa ta dawo dashi kuma.
Ke dai malalaciyace kin kuma kasa wanke kayan ki dawo dashine hakana sai kinjera kina sawa sun kare, daga baya ki dawo ki damay mu da korafi kuma.
Murja batai magana ba sai da ta mayar kayan daki su ta dawo ta zauna jiki ba karfi tayi shiru tana tunane haka yasa uwar ta farga da halin da take ciki a lokacin.
Kasa daurewa mama tayi abin da da mahaifi tace wai yana ganki kin dawo haka jiki ba kwari kuma kamar wace tayi gamo kuma data fita.
Kallon Amma tayi tana fadin Amma Allah yayi gaskiya daya hana lebe a rayuwan bawan shi don mutum zai iya jiwo kanshi ranan mutuwa shi a bakin wani.
Labe kika fara yar nan wallahi amma labe nayi na jiyowa kaina abi tashin hankalin da ban taba jiba yau.
Aiko baki kyautawa kanki ba ga maryam nan har girmanta ya zama mata cuta har yaran ta komai mutum yace sai yaji ko sai ya gani ya hana zuciyar shakat dagangan da gangan.
Wai ma may ki jiyo kinzo muna hankali a tashe haka kamar wani ya aikeki yin mugun abu ?
Wallahi mama ruwan famfon mu nai fita da sauri nace barin tafi shiyan hjy intara sai in kawo inda nake wanki din.
Sai ga hjy maryam da saurin ta zata shiga part din hjyn su salma har tana tuntube wurin sauri shine naji zuciyana bata yarda da ita ba lokacin sai na matsa bakin windon ina sauraren su mama kinsan abinda najikuwa ta fada tana kallin mama.
Sai kin fada uwar labe mu ina zamu sani tunda bamu aikeki ba kiyi labe.
Umhumm mama labena kila yai rana Allah dai ya yafe mun wallahi ji nayi suna fadin wai hjy su salma tasa ya Umar ya sako A ruwa ya turo jirgi da takardan tana saki kada ya hado ta da komai yadda sukaji zafin abinda kawo yai mata suma nan suji shi kamar su.
Taci gaba da fada masu sauran maganganun da taji suna fadi a kaina da mahaifiyata a lokacin.
Abu ga tsufa hankalin Amma in yai dubu ya tashi nan ta shiga sake salalami sai da mama hadiye ta taushe ta.
Kada su bari a san an gane wanan magana zata kira mamu yanzu ta tambaye ta layina nacan akan zasu kirani suji lafiyata daga nan sai suji mai ke gudana a tsakanin mu.
Amma kafin nan murja karbi kudi ki sayo mun kati don kiran kasar waje saida kudi mai yawa a layi.
Ta cire dubu daya ta mikawa murja ta fice da sauri a daidai lokacin hjy maryam ta fito daga part din hjyn su salma a cikin fara,an ta.
Murja tace munafuka mun daiji shirin ku bake kadai kika iya wanan laben ba muguwa kinsani yin abinda Allah ya hana yau.
Mamu mama ta kira a waya tana son layina don Allah mamu sai bata turo mata ba kamar yadda tace saida ta gama hadaw yara abincin bayan ta gama na kawu da yake ci ta nufo part din da kanta.
A daidai lokacin kuma murja ta dawo daga sayen katin dataje ta samu mai shagon ya rufe ya tafi sallah.
Maimakon mamu ta tafi sai ta zauna suna hira da Amma wace bata cikin hayacinta abuga wanda kasan halin sa take tambaya gwaggo wani abu ke damun kine ?
Da sauri mama tace mutumiyar dai nata take son jin muryan ta yau da ita ta tashi a rai shine zan kira mata ita ko hankalin ta zai kwanta.
Murja ta gama loda kudin a waya ta miko ma mahaifiyar nata wayan ta kira layin nawa akai dace ko kiran ya shiga.
A daidai lokacin da muna zaune muna cin abincin daren daya tursasa min cin shi don dole ya kafeni da idanu kuma.
Wayan na ringin ban kula in dauka ba yai min alama in dauki wayan da idanu nakai hannu na dauka a hankali.
Gani bakuwar nombane na bata fuskana tare da fadin ban san mai lauin nan ba saidai daga nageria ne kiran.
Yace dauki mana kiji ko waye kika sani ko daga gidane aka kiraki nayi received din kiran daidai lokacin danaji muryan murja na tambayan ya shiga ?
Fatima naji murya mama ta ambata da sauri na amsa da na,am ina wuni tace lafiya kalau sai na danyi shiru tace kin gane dawa kike magana nace a,a bangane ba.
Yana zaune ya kuramin ido yana saurarena tace mamanki hadiye ne da sauri nace lah mama kece ashe ?
Ina Amma dasu mamu ya murja da sauran mutanen gida tace kowa lafiya yake nan yaushe zamu ganki halan sai na dan kalli inda yaya yake zaune nace yaya yace sai na gama karatuna zanzo gida.
Ai hakan nada kyau kinga lokacin da jikokin mu zaki zo muna ke nan na danyi dariya cikin kunya nace kai mama wasu jikoki kuma.
Na katse zancen da fadin ina Amma a bata waya don Allah inj muryan ta ina nan na cika da kewan ta ina jin suna dariyata ta mikawa Amma wayan.
A ruwa kuna lafiya ko nace Amma zamu bata idan kina kirana da wanan sunan har yanzu fa tace to yar nema kin canza sunane daga wanda muka sani da farko nace kada ki bari mijina ya jiki kina batawa matar shi suna da wani aruwa can ?
Tace ja,ira har yanzu dai halin na nan har kike kiran mijin ki a gaba shi sadaukin bai fada maki bayana kuke ba kaf matan nasa .
Muryan mujane ke fadin miss you Aruwa nace a wuta dai yar iska ya labarine sai Amma tace ke A ruwa kina jina nace ina jinki Amma.
Tace badai lafiya kuke ba nace lafiya kalau amma babu wani matsala a zaman naku dai ko nace babu komai sai alheri Amma.
Bansan lokacin da yadago ba sai ji nayi ya karbe wayan a hannu na yana fadin to yar leken asiri muna nan lafiya may kike son ji kuma.
Ta danyi dariya naji muryan ta tar a kunnuwa na saida na lumshe idona don kewanta danaji a lokacin naji yayi shiru yana sauraren abinda take fadi.
Yanayin fuskanshi ya baci can naji yace Amma wani abu ya faru ne da kike fadin haka shiru nayi ina sauraren su tare da canza yanayin fuskana a lokacin.
Saida ya gama yace kashe wayan zan kiraki muyi magana a natse ina wayan ki na nan tace bata da waya yanzu ya lalace kasan kuma mahaufin ku ta kansa yake yanzu kada ki damu za a kawo maki waya yau din nan yace mata ya kashe wayan ban karasa magana dasu ba na dago na kalleshi fuska da mamaki.
Ya zauna a hankali ya kalleni kafin yace kin kira wanine kin fada masa wani magana ?
Da mamaki nace harga Allah ban kira kowa ba ko mamu da muke waya munkai sati bamuyi waya da ita ba.
Yace dole wani yasan umurnin da hjy ta bani a gamay dake maganan Amma yanzu ya danganta da wanan magana sak.
Anyway barin kira nasir ya kawo mata waya zan kirata an jima muyi magana sai dai ina son ki da rike sirin mu a tsakanin mu na sake fadin wallah Allah banyi waya da kowa a gida ba ka duba wayata ka gani mana.
Karshe ma haushi naji har ya fita ban sake magana ba naga ya dade bai shigo na mike na shige har nayi kamar in kwanta a dakina sai naga in nayi hakan banyi daidai ba duk kokarin shi na ganin ya inganta min rayuwan da yakeyi din ta fanni tunda ba haka mahaifiyar shi ke so ba a nata bangaren.
Can cikin barci nake tsinkayo muryan shi yana waya Amma na fada maki ku kwantar da hankalin ku don Allah babu abinda zai samu aurena matata.
Wanan kada ya tayat maki da hankalin ki don Allah idona na bude tar ina jin yadda suke maganan karshe dai Amma nata saka mai albarka sukai sallama ya kashe wayan .
Ke zarah na amsa ciki ciki yace wai fushin may kike hakane ni banyi hushi ba tunda ni ke zargin ki da rashin addana sirin mu sai ke yanzu amma ta fada min komai jinsu sukayi suna kitsawa da hjy maryam.
Ni ai dama ba fushi nakeyi ba na bashi amsa yace may kikeyi in ba fushi ba kina jin na shigo amma kika

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login