Showing 153001 words to 156000 words out of 419207 words

Chapter 52 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1437

daga tunanen da nakeyi da sauri ina bata hakkuri.
Don maganganu yan matan yasa hankalina dagawa har na shiga tunane ban san matar tana tafe ba lokacin.
Matar na fadin ba komai sai jin muryan hjy maryam mukayi daga bayan mu tana fadin ke A ruwa kanki daya kuwa zaki bangaji babban mace kamar wanan.
Ban san tana tafe bane maman ikilima kuma na bata hakkuri ai, ta watsa min harara tare da fadin dallah rufewa mutane baki marasa tarbiya kawai har da baki ma sai kin nuna masu halin ki sun sani.
Cike da mamakin kalamin ta na waro ido ina kallonta matar ta sake fadin haba hankalinta ne baiya a hanyan ai bata san ina tafe bane itama asali nima waya nake ban san da zuw ba goan ta ba.
Wanan ma aiko ta sani hakan zatayi don rashin kunya da take takama dashi da jiji da kai kin dai ga inda abin arziki yake don haka a daina kwadayin shiga manya mutane don ba kamun kai.
Sai duk wa yanda ke wajen suka sako muna idanuwan su suna sauraren ta kamar daga sama mukaji muryan hjy tana fadin maryam may kuma ke faruwa ne nan ?
Yanzu Asma,u ta samay ni ciki take fada min magana mara dadi wai matar DG wanan yarinyar ta bangaza don kawai tana takama da rashin kunya har na waje su sani.
A tausashe nace maman ikilima ba bangazan ta nayi ba karo mukayi da ita kuma na bata hakkuri .
Acikin tsawa suna hada baki in masu shiru da rashin kunya suna magana ina fadi don banda kunya ta tara taron arziki don bakin ciki zan wargaza mata taro.
Watace da ganin ta malama ce suna zaune a gefe ta daga nikaf din kanta sama tace haba ku dinga kyakyawan bincike kafin ku yada magana mu nan muna kallon abinda ya faru asalima ai matar dg itace ta buge yarinyar ba yarinyar ta zo ta bugeta ba.
Amma duk da haka hjy lami bata iya tausasa harshe ga manya ita ta bada hakkuri zata tsaya muna haka a kai kimkam.
Matar dai ta sake fadin yo ai wanan yarinyar nada kirki tunda tana bugeta ita tashiga bata hakkuri dazun akwai wata yar bakar yarinya data fito wancan part din kunsan mata kadani tayi a gidan nan cewa part din hjy maryam take nunawa.
Hjy jummai tace yaran banza ne kawai an tara muna su a gida babu tarbiya suna abun da sukaga dama wa mutane.
Kin fito kamar wata bakuwar buzuwa dake kina baza ido don gulma wa gaiyace ku gaiyan tsiya.
Na daga ido na kalli hjy dake ta muzantani a gaban bakin ta uffan ban furta mata ba har sai da matar mai kama da malama tace min ke wuce ki tafi inda zaki.
Jummai idan ta samu fada bata jin assh na juya nacewa matar nagode hjy tace kinji kilibibin ko ?
Wa yar da kike gani ta koyi kilibibi har ta gaji a gidan nan haka kawai zaki zo min cikin tarona kamar bakuwar shedan.
Dariya yan matan nan suka kwashe dashi har suna tabawa tare da fadin wuuuu.
Mama hadiye dake tsaye tace amma dai kunji kunya wallahi don kunyiwa a ruwa haka a cikin taro shi zai zama may ?
Tunda duniya ta wanke ta ga gaskiya ana fada kin fito da abinda ke cikin ki a fili a bainan jamma, a hakan ne zai hanata shiga gidan danki don kin muzantata ko may ?
Hjy ko tace bakikai labari ta hau mama hadiye da fada sai kallon ya dawo gare su nikan har na shige part din mamu ina jiyo hayaniyar su wajen.
A take zazzabi ya sauka min na karasa falon mamu da kyar na haye kujera na kwanta ina tunanen wanan wani irin kiyayya ne hakan tsakanin mu da matan nan.
Ina nan zube saman kujeran idanuwana a lumshe naji mamu tafito daga daki tana ganina sai tayi turus a wurin tana kallo na.
May ke faruwa ne waje sayadi naji kamar muryan maman ku hadiye da hjyn su salma ?
Nace sune mamu fadan dani ake mama ta shiga wai na bangaji wata mata alhali matar ta fada masu ban bangajeta ba itace ta bugeni bata gani ba.
Sayadi mai ya kaiki guri su don Allah mamu ta fada a cikin wani murya na bacin rai nace wallahi mamu banje gurin su ba na fito inzo inyiwa su fauziya wankane muka hade da matar a hanya na karasa idona yana kawo hawaye.
Sayadi banson abin fitina sam wallahi shiyasa kikaga na bar masu gidan tun safe ashe ban tsira ba daga sherin su.
Mamu ta ban tausayi yadda tayi maganan ya nuna ta gaji da wanan rayuwan na gidan su itama tana dai hakkuri ne kawai.
Kwana biyu bayan taro ranan asabar da dare ina falon mamu zaune da littafi ina karatu don jerabawan da zamu fara.
Kawu ya shigo part din namu yana sallama a ladace na zamo saman kujeran ina gaida shi ya amsa ya samu wuri ya zauna.
Mamu dake zaune kasa ta gaida shi da dawowa ya amsa ya dago kai ya dan kalle ni kamar mai nazarina yace.
Fatima kin ramay haka da yawa ko har yanzu zazzabin ne a jikin ki kuma ko damuwa dai kika sawa kanki haka ?
A ladabce nace a, a kawu naji sauki jerabawa dai zamu fara nake karatu.
Murmushi yayi yace shine kike matsawa kanki haka akan jerabawa ai nasa an saka sunayen ku cikin masu fita bana .
Na dago na dan kalle shi sai kuma na sada kaina kasa a hankali murna zanyi ko bakin cikin hakan ?
Mamu ne tace zata iya kuwa naga karatun nasu yanzu sai a hankali yace sai da nasa akai min bincike a kanta sosai zata iya insha Allahu.
Ya juya gurin mamu yace ina ganin idan akai haka zata tafi da kwalinta can kinga da taje sai kawai ta fada jami,a baki daya dama kin san tace likita zata zama ko kin fasa ne fatima yana kallon fuskana.
Ban san lokacin danace ban fasa ba kawu ina nan da kudirina har yanzu sai kuma naji kunya ya kamani daga baya na noke kai.
Ai fa ka tabo mata inda ke mata kaikayi yau da zancen zama likita sai dai itama gata da tsoron allura nagani sosai amma tana sha,awan tayiwa mutane ita.
Mikewa nayi zan fice kawu yace dawo ki zauna abinki nace zan je in kwanta ne kawu na fice tare dayiwa mamu saida safe.
Cike da farin ciki na shiga gurin Amma da dan guduna na rugumay ta na kama hannunta ina fadin Amma kawu yace bana zan fita school sai in shiga jami,a.
Tayi murmyshi tace aure yazo ke nan kusa tunda har zai katse maki karatun ki yanzu.
Da sauri na girgiza kai nace a, a Amma yace karatuna zan dora sai kuma nayi shiru tuna yadda yai maganan.
Dan jimm nayi sai na mike tsaye tace aure sha kan yaro sai gida umaru sanda babuga yarinya a can zaki digree ke nan ko ?
Fuskana bata na koma saman kujera na zauna na shiga tunane can kuma na mike na shiga ciki don in kwanta ita kuma amma tafi kwanciya a falo tana nafilfilin ta ba dare wanda yanzu zama da ita yasa ina koyo.
Can kusan barci ya fara daukana cikin tunane na naji muryan kawu gurin Amma suna hira tana fadin tana ciki nasan ta kwantane.
Yanzu tazo min da murna zaka katse mata karatu don nace aure yazo tayi fushi ta shige dakin.
Ai hakan yayi daidai don a wuce wurin kowa ya shiga hankalin shi zaifi fitina jummai yayi yawa haka kawai ki tozarta yarinya a bainan jamma,a don wata manufa taki kawai na banza.
Hajiya kin hana in mata magana ne danayi mata tsiya wanan karon haba a bainan jamma,a haka ki muzanta yarinya kankanuwa kamar fatima ?
Zubur nayi na mike daga inda nake kwance ina sauraren su naji Amma tace yanzu ai tsuntsun dayaja ruwa shi ruwa ka doka don dai ta kara kawo nesa kusa ne ai.
Toshe bakina nayi don kukan da yazo min a lokacin har kawu ya fita ina jin su suna magana ne duk a kaina da matsalan gidan shi.
Ranan dai barci rabi da rabi nayi shi da asuba koda na idar da sallah na jima ina rokon Allah yasa a fasa wanan auren ga baki daya.
Ya kuma kareni daga ko wani sheri duniya da lahira ga baki daya na dade a dakin kwance don naji ban bukatan fitowa saboda gani nake Amma tana cikin masu zuga kawu akan yin auren namu.
Har kusan goma ina kwance kuma ba barci nakeyi ba Amma ta shigo tana fadin yau ko barcin lafiya kike yar nan ?
A sanyaye na dago kaina na kalle ta da idanuwana da sukai luf luf dasu nace ba barci nakeyi ba ai.
Kallona tayi fuskanta ba yabo ba fallasa ta zauna bakin gadon da kyar tace banyi tsamanin kina da taurin kai irin hakaba yar nan ?
Ina maganan nan kunyi shi da kawu ki kin amince yanzu kuma zaki shiga wanan halin haka ki dami zuciyar ki.
Maimakon in bata amsa sai na barke da kuka ina fadin Amma kin dai ji abinda hjyn su take min wullakanci har a bainar jama, a.
Mikewa tayi ta fita daga dakin zuwa falon ta ba adadeba kamar daga sama naga mamu a kaina lokacin na kifa ciki ina kuka ban san shigowan ta ba dakin.
Jin kamshin turaren ta yasa na dago kai na na kallo bayana ta tsaye ta kura min ido tana min kallo tuhuma.
Tace sayadi nace na,am murya a dakushe .
Bata kara cewa komai ba sai tayi shiru kamar mai tunanen wani abu sau can tace ashe ba an gama maganan nan dake ba wai ?
Wani irin tsoro ne ya lullubeni na mike zaune tukun na dukar da kaina kasa ga barin kallon ta.
Karo na biyu ta koma kirana tace kina jina ai ina magana yau dai ayita ta kare kada ki boye mi komai na yarda in kashe nawa auren da in jefaki cikin damuwa ke.
Wani irin kaduwa naji dajin furcin ta da sauri nace mamu ni may nace yanzu kuma kan maganan ?
Tace gashi tun jiya kin tada hankalin ki dana tsohuwar nan dake kokari dake har ta fara yanke shawaran fadawa kawun ki a raba wanan auren da yake son hadawa tunda hankalin ki bai kwanta ba.
Nace a marairaice wallahi mamu ni bancewa Amma komai bai tunda dai nayi sallah ne na koma barci kawai.
Murmushi tayi tace ba gaskiya bane ko kina tunanen gwaggo zatai maki karya akan abinda bakiyi bane.
Da sauri na girgiza kaina nace na bari mamu ni ba kuka nake ba gani dai nayi kamar ba za a barni naci gaba da karatuna bane shine damuwa na ayanzu.
Wa yace ba zakici gaba da karatun ki ba indin abinda kikaji ya fadi ne jiya ai hakan yana nufin taimakon ki yayi da hakan.
Nan dai ta nuna min bacin ranta tare kuma da dan min nasiha na share hawayena karshe nayi wanka na fice zuwa part din mu don har lokacin ina fushi da Amma.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:11 - ??5惙5惙5?: .BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHEEM, , ,


Akwana a tashi ba wuya a wurin Allah abubuwa sun faru da dama a cikin gidan kawuna wasu na jin dadi wasu ko na tashin hankalin zamantakewa rayuwan mutanen gidan.
Izuwa wasu watanin da suka shude har hjy ta gaji ta debe tsammani akan auren don irin shige da ficen da taitayi na ganin hakan bai faru tsakanina da danta ba.
Sai dai bata sani ba a maimakon abin yayi tasiri kamar yadda take son ayi sai Allah ya juye lamarin ya sako ma dan nata rashin son gida gaba daya.
Don kamar yadda take tunanen ba wanda yasan takon ta a gidan bata san a idon makwarwa take shuka ba.
Ba hjy maryam kadai ba har shi kanshi maigidan da baya barci yana raya daren shi a tsaye gurin mika kukan shi ga Allah yasan da abinda ta bizzine a gidan kan yayan ta.
Wanda a da can bai dauki abin komai ba yafi danganta lamarin da sherin mafalkine kawai ke rudin shi.
Sai daga baya ya farga da zaran ya gama nafilolinshi ne yana zikiri wanan abin kanzo mai a mafalki.
Inda yake yawan ganin hjy din tasa danta gudu kullun da bai san may yakewa gudun haka ba.
Har dai ya gaji inda yakai koken yawan mafalkin nasa akan danshi da take yawan yi idan barci ya fisgeshi.
Kwanaki malam ya bashi akan zai dawo yaji abayanin daga baya sukai sallama sai bayan sati biyu ne kamar yadda aka diban mai ya koma gidan malamin don son jin ba,asin maganan mafalkin.
Nan malam yayi mai bayani yadda zai iya fahintar shi kamar haka, da farko dai kana da yara maza da mata a gidan ka sai dai dukkan su suna da ma bambanta iyayye a gidan a yadda nake gani.
Sai dai wanan mai dan tsayin da kauri itace matsalan gidan ka don matsalan daga gurinta yake don tafi sauran hasala a cikin su.
Nan dai malam ya koro mai duk abinda ke nan har yadda hjy tayi aiki kan danta sai dai an samu akasin aikin don aikin ya juyene ranshi ya bar gida gaba daya yanzu.
Shiyasa kake ganin sa a halin gudu da kake ganin shi yanayi ba kakautawa a mafarkin ka .
Kafin malam ya gama bayani har Alh sani yayi zufa sosai a goshin shi lokaci daya sai maimaita innalillahi yake a ranshi hankalin shi tashe.
Bai bar gurin ba sai da malam ya bashi addu,oin da zai dingayi don samun masallaha a al,amarin.
Alhamdullahi shi ya rike kuma yana ganin hasken adduan a lokacin don bai cika sati daya ba sai ga kiran Umar ranan a wayan shi.
Mamakine ya cika kawu dayaga dan nasa na kiranshi a waya ya dauka da addua a bakin shi tare da sallama.
Jin kamar ba zai amsa ba sai can ya amsa yana fadin daddy i am very sorry na rashin kiranka tsawon lokaci.
A cikin hikima da nuna ba komai ya katseshi ta hanyar fadi umaru sanda mazan fama ga aiki ga ban tsoro.
Dan murmushi ya sauke tare da ajiyan zuciya ya kara fadin sorry daddy aiyukane sukai min yawa a nan .
Kawu yace umar na sani ai in kaji shiru lafiya ne yaya wurin ita matar taka da amarya na dan gajeren murmushi yayi yana fadin suna lafiya koda yake na kwana biyu ban tare dasu ina nan mun zo aiki a kasan italy.
Kawu yace haka na da kyau amma a kula da hakkin iyali a dinga sauke masu hakkin su kada a raja,a ga aiki kullun .
Nagode daddy yace tare da danyin shiru na wani lokaci Alh ya kawar da shirun ta hanyan fadin kun gaisa da mahaifyar taka ko ?
Yace daddy idan mun gama yanzu zan kirata itama sun dan dauki lokaci yana janshi da hira mai kama da nasiha, kamar babu abinda ke damun shi a rai.
Kafin suyi sallama umar din yana mamaki da babu abinda mahaifin nasa ya nuna mai na rashin zuwa gidan da baiyi kuma baya kiransu.
Don shi haka kawai yaji gaba daya kasan ya fice mai a rai ko aikin daya fara ya dakatar da yin sa gashi saura kiris ya rage komai ya kammala gare shi.
Yayi mamakin jin daddy baimai fada ba kamar yadda yayi tsamani sai gashi karshe sun kwashe da wasa da dariya da mahaifin nasa.
Yana mamakin hali irin na kawu da ko abu ya bata mai rai bai faye fitowa fili yai ma mutum magana a kansa ba sai in abin yakai intaha zakaji yai dan fada dasu.
Ko case din merry yasan ya batawa daddy rai ne sosai yasa yai mashi hakan sai lokacin ya tuno da alkawarin auren dake kanshi wanda ya manta da zancen sam a cikin ranshi.
Gaban shi ne ya fadi har ya furta oh shit to amma kuma yaya akayi yanzu daddy bai jefo min zancen nan ba a hiran mu.
Wayan maman shi ya kira kamar zai tsuke ba,a dauka ba sai kuma can aka dauka tana fadin hello a kausashe.
Yayi sallama tare da fadin hjy mama an wuni lafiya tace yau kaga dama ka tuna damu ?
Ya danyi murmushi yana fadin mama tuba nake don Allah wallahi aiyukane sukai min yawa nan.
Rufa min baki aiyuka ko matarka ta dauke maka hankali gare mu har ka fara mantawa damu.
Babawo ka lissafa yau wata nawa rabonka daka kirani mu gaisa koda a waya ne ?
Yace mama ayi hakkuri abubuwa ne sukai min ya, , , ,
Kada ka mayar dani mutumiyar banza babawo ka tuna ban daga cikin irin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login